Sura 5

1 Wannan shi ne lissafin zuriyar Adamu. A ranar da Allah ya hallici mutum, ya yi su a cikin kamanninsa. 2 Namiji da mace ya hallice su. Ya albarkace su ya basu suna mutane a lokacin da ya hallice su. 3 Da Adamu ya yi shekaru 130 sai ya zama mahaifin ɗa a cikin kamanninsa sai ya kira sunansa Set. 4 Bayan Adamu ya haifi Set, ya yi rayuwa tsawon shekaru ɗari takwas. Sai ya zama mahaifin waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa. 5 Adamu ya yi rayuwa har shekaru 930 daga nan ya mutu.

6 Da Set ya yi shekaru 105, sai ya haifi Enosh. 7 Bayan ya haifi Enosh, ya rayu har tsawon shekaru 807 ya zama mahaifin 'ya'ya maza da mata da yawa. 8 Set ya rayu har shekaru 912 daga nan ya mutu.

9 Bayan Enosh ya rayu na tsawon shekaru tasa'in, sai ya haifi Kenan. 10 Bayan ya haifi Kenan, Enosh ya rayu na tsawon shekaru 815. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata masu yawa. 11 Enosh ya rayu tsawon shekaru 905 daga nan ya mutu.

12 Da Kenan ya yi shekaru saba'in, sai ya haifi Mahalalel. 13 Bayan ya haifi Mahalalel, Kenan ya yi shekaru 840. Sai ya haifi sauran waɗansu 'ya'ya maza da mata. 14 Kenan ya rayu na tsawon shekaru 910, daga nan ya mutu.

15 Mahalalel ya rayu shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Yared, 16 Mahalalel yana da shekaru 830. Sai ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata masu yawa. 17 Mahalalel ya rayu na tsawon shekaru 895, daga nan ya mutu.

18 Da Yared ya yi shekaru 162, sai ya haifi Enok. 19 Bayan ya haifi Enok, Yared ya yi shekaru ɗari takwas. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 20 Yared ya rayu na tsawon shekaru 962, daga nan ya mutu.

21 Da Enok ya yi shekaru sittin da biyar, sai ya haifi Metusela. 22 Enok ya yi tafiya tare da Allah shekaru ɗari uku daga nan ya haifi Metusela, ya kuma haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 23 Enok ya yi shekaru ɗari uku da sittin da biyar. 24 Enok ya yi tafiya tare da Allah, daga bisani ya tafi, domin Allah ya fyauce shi.

25 Da Metusela ya yi shekaru 187, ya haifi Lamek. 26 Bayan ya haifi Lamek, Metusela ya yi shekaru 782. Sai ya haifi waɗansu 'ya'ya maza da mata. 27 Metusela ya rayu na tsawon shekaru 965 daga nan ya mutu.

28 Bayan ya yi shekaru 182, sai ya haifi ɗa. 29 Sai ya kira sunansa Nuhu, yana cewa, "Wannan zai bamu hutu daga aikinmu daga kuma aikin hannuwanmu mai wuya, da zamu yi saboda Allah ya la'anta ƙasa." 30 Lamek ya yi shekaru 595 daga nan ya haifi Nuhu. Daga nan ya haifi sauran 'ya'ya maza da mata. 31 Lamek ya rayu na tsawon shekaru 777, daga nan ya mutu.

32 Bayan Nuhu ya yi shekaru ɗari biyar, sai ya haifi Shem, da Ham, da Yafet.