Sura 6

1 Sai ya zamana da mutane suka fara ruɓamɓanya a duniya aka kuma haifa masu 'ya'ya mata, 2 sai 'ya'yan Allah suka ga 'ya'yan mutane na da ban sha'awa. Sai suka auri mata daga cikinsu, dukkan su da suka zaɓa. 3 Yahweh yace "Ruhuna ba zai dawwama a cikin mutum ba har abada, domin su jiki ne. Za su rayu shekaru 120 ne." 4 A waɗancan kwanakin akwai ƙarfafan mutane sosai, kuma haka ya faru ne bayan 'ya'yan Allah sun auri 'ya'ya mata na mutane, sun kuma sami 'ya'ya tare da su. Waɗannan sune manyan mutanen dã can, mutane masu jaruntaka.

5 Yahweh ya ga muguntar mutum ta haɓaka a duniya, kuma dukkan tunane-tunanen zuciyarsa kullum mugunta ce. 6 Yahweh ya yi takaicin halitar mutum a duniya, kuma abin ya dame shi a zuciyarsa. 7 Domin haka Yahweh yace, "Zan shafe mutum wanda na halitta daga fuskar duniya; mutum da manyan dabbobi, da abubuwa masu rarrafe da tsuntsayen sammai, domin na yi takaici dana halicce su." 8 Amma Nuhu ya sami tagomashi a idanun Yahweh.

9 Waɗannan sune abubuwa game da Nuhu. Nuhu adalin mutum ne, kuma ba shi da abin zargi a cikin mutanen kwanakinsa. 10 Nuhu yayi tafiya tare da Allah. Nuhu ya haifi 'ya'ya uku: Wato Shem da Ham da Yafet. 11 Duniya ta ƙazanta a gaban Allah, ta kuma cika da hargitsi. 12 Allah ya ga duniya; duba, ta gurɓanta, domin dukkan mutane sun ɓata tafarkinsu a duniya.

13 Allah yace da Nuhu, Na ga cewa lokacin ƙarshen dukkan hallita ya yi domin duniya ta cika da hargitsi ta wurin su, hakika, zan hallaka su tare da duniya. 14 Ka yi wa kanka jirgi da itacen sida ka yi ɗakuna a cikin jirgin, ka rufe shi ciki da waje. 15 Ga fasalin yadda zaka yi shi: tsawon jirgin kamu ɗari uku, faɗinsa kamu hamsin, bisansa kamu talatin. 16 Ka yi wa jirgin rufi, ka kuma kammala shi ka dalaye shi daga sama har ƙasa. Ka sa ƙofa ta gefen jirgin, ka yi masa matakala, ƙarama, da ta biyu, da kuma matakala ta uku. 17 Ka saurara, Na kusa kawo ambaliyar ruwa a duniya domin in hallakar da dukkan masu rai dake da numfashi rai dake a ƙarƙashin sama. Duk abin dake a duniya zai mutu. 18 Amma zan kafa alƙawarina da kai. Zaka shiga cikin jirgin, da kai da 'ya'yanka da matarka da matan 'ya'yanka tare da kai. 19 Da dukkan hallitu masu rai, kowanne iri biyu dole ne kuma ka shigar dasu cikin jirgin, ka ajiye su, su tsira tare da kai, dukkan su namiji da mace. 20 Da tsuntsaye bisa ga irinsu, da manyan dabbobi bisa ga irinsu, dukkan wani abu mai rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu, biyu daga cikin kowanne iri daga cikinsu za su zo tare da kai, domin ka tsirar da rayukansu 21 Ka kuma yi wa kanka tanadin kowanne irin abinci na ci ka adana shi, domin ya zamar maka abinci da kuma dominsu." 22 Sai Nuhu ya yi wannan. Bisa yadda Allah ya umarce shi, haka ya yi.