Sura 4
1
Mutumin ya kwana da matarsa, sai ta yi ciki ta haifi Kayinu. Ta ce, "Na haifi mutum da taimakon Yahweh."
2
Sai ta sake haifar ɗan'uwansa Habila. Sai Habila ya zama makiyayi, amma Kayinu ya zama manomi.
3
Sai ya zamana wata rana Kayinu ya kawo wani sashe daga cikin amfanin gonar da ya noma daga ƙasa a matsayin baiko ga Yahweh.
4
Shi kuma Habila, sai ya kawo waɗansu 'ya'yan fari daga cikin garkensa da kuma sashe na kitse. Yahweh ya karɓi Habila da baikonsa,
5
amma Kayinu da baikonsa bai karɓa ba. Domin haka Kayinu ya fusata sosai, ya kuma ɓata fuska.
6
Yahweh yace da Kayinu, "Meyasa ka yi fushi meyasa fuskarka ta ɓaci haka?
7
In da ka yi abin dake nagari, da ba a karɓe ka ba? Amma in ba ka yi abin dake nagari ba, zunubi na ƙwanƙwasa ƙofa kuma marmarinsa shi ne ya mallake ka, amma dole ne ka yi mulkinsa."
8
Sai Kayinu ya yi magana da ɗan'uwansa Habila. Sai ya zamana a lokacin da suke cikin saura, sai Kayinu ya tasar wa Habila ya kashe shi.
9
Daga nan Yahweh yace da Kayinu, "Ina ɗan'uwanka Habila?" Ya ce, "Ban sani ba. Ni makiyayin ɗan'uwana ne?"
10
Yahweh yace, "Me ka yi kenan? Jinin ɗan'uwanka yana kira na daga ƙasa.
11
Yanzu kai la'ananne ne daga ƙasar da ta buɗe baki ta karɓi jinin ɗan'uwanka daga hannunka.
12
Daga yanzu duk lokacin daka noma ƙasa, ba za ta baka issashen amfaninta ba. Za ka zama mai yawo barkatai a cikin duniya."
13
Kayinu yace da Yahweh, "Horona ya yi girma fiye da yadda zan iya ɗauka.
14
Hakika ka kore ni waje yau daga wannan ƙasa, zan kuma riƙa ɓuya daga fuskarka. Zan zama mai yawo barkatai a cikin duniya, kuma duk wanda ya same ni zai kashe ni."
15
Yahweh yace da shi, In har wani ya kashe Kayinu za ayi masa ramako har niki bakwai." Daga nan Yahweh ya sa alama a jikin Kayinu, domin in wani ya gan shi kada wannan mutumin ya kai masa hari.
16
Sai Kayinu ya tafi daga fuskar Yahweh ya zauna a ƙasar Nod, a gabashin Aidin.
17
Kayinu ya kwana da matarsa sai ta yi ciki ta haifi Enok. Ya gina birni ya bashi sunan ɗansa Enok.
18
Ga Enok sai aka haifa masa Irad. Irad ya zama mahaifin Mehuyawel. Mehuyawel ya zama mahaifin Metushawel. Metushawel ya zama mahaifin
19
Lamek. Lamek ya aura wa kansa mata biyu: sunan ɗayar Ada, ɗayar kuma sunanta Zilla.
20
Ada ta haifi Yabal. Shi ne mahaifin masu zama a cikin rumfuna waɗanda ke da dabbobi.
21
Ɗan'uwansa shi ne Yubal. Shi ne mahaifin makaɗan molo da algaita.
22
Ita kuma Zilla, ta haifi Tubal Kayinu, shi ne mai samar da kayayyaki na jan ƙarfe. 'Yar'uwar Tubal Kayinu ita ce Na'ama.
23
Sai Lamek yace da matansa, Ada da Zilla, ku saurari muryata; ku matan Lamek, ku saurari abin da na ce. Domin na kashe mutum saboda ya yi mani rauni, saurayi domin ya ƙuje ni.
24
In an saka wa Kayinu sau bakwai, to za a saka wa Lamek sau saba'in."
25
Sai Adamu ya sake kwana da matarsa, sai ta sake haifar wani ɗan. Sai ta kira sunansa Set, ta kuma ce, "Allah ya bani wani ɗan a madadin Habila, domin Kayinu ya kashe shi."
26
Aka haifa wa Set ɗa, sai ya kira sunansa Enosh. A wancan lokacin ne mutane suka fara kiran bisa sunan Yahweh.