1
To maciji ya fi dukkan sauran dabbobin saura da Yahweh yayi wayau. Sai ya ce da macen, "Ko da gaske ne Allah yace ba zaku taɓa ci daga kowanne 'ya'yan itacen dake cikin lambun ba?"
2
Sai matar ta ce da macijin, "Ma iya ci daga cikin itatuwan lambun,
3
amma game da itacen dake tsakiyar lambun, Allah yace, 'Ba zaku ci shi ba, ba kuma zaku taɓa shi ba, in ba haka ba, zaku mutu."'
4
Sai maciji yace da macen, "Hakika ba zaku mutu ba.
5
Domin Allah ya san cewa a ranar da kuka ci idanunku zasu buɗe, zaku kuma zama kamar Allah, kuna sanin nagarta da mugunta."
6
Da matar ta duba ta ga itacen yana da kyau domin abinci, yana kuma ƙayatar da idanu, kuma itacen abin marmari ne yana sa mutum ya zama mai hikima, sai ta tsinki waɗansu daga cikin 'ya'yan ta ci shi. Sai ta bada waɗansu ga mijinta, shi kuma ya ci.
7
Idanun dukkan su biyun suka buɗe, sai suka gane tsirara su ke. Sai suka ɗinka ganyayyakin ɓaure suka yi wa kansu sutura.
8
Sai suka ji motsin Yahweh Allah ya na tafiya cikin lambun da sanyin yamma, domin haka mijin da matar suka ɓuya a cikin itatuwan lambun daga fuskar Yahweh Allah.
17 Ga Adamu yace, "Domin ka saurari muryar matarka, ka ci daga cikin itacen da na dokace ka cewa, 'Kada ka ci daga cikinsa,' saboda kai na la'anta ƙasa; ta wurin aiki mai zafi za ka ci daga cikinta dukkan kwanakin ranka.
22 Yahweh Allah yace, "Yanzu mutumin ya zama kamar ɗaya daga cikinmu, yana sane da mugunta da nagarta. To yanzu ba za mu taɓa barinsa ya sa hannunsa, ya tsinka daga itacen rai ba, ya ci, ya kuma rayu har abada." 23 Saboda haka Yahweh Allah ya fitar da shi daga cikin lambun Aidin, domin ya noma ƙasa wanda daga ita aka ciro shi. 24 To sai Allah ya kori mutumin daga lambun, ya sa kerubim a gabashin lambun Aidin da kuma takobi mai walƙiya dake jujjuyawa ta kowanne fanni, domin su yi tsaron hanya ta zuwa itacen rai.