Sura 2
1
To an kammala sammai da duniya, da duk abubuwa masu rai da suka cika su.
2
A rana ta bakwai Allah ya kammala aikinsa da ya yi, domin haka sai ya huta a rana ta bakwai daga dukkan aikinsa.
3
Allah ya albarkaci rana ta bakwai ya kuma tsarkaketa, domin a cikinta ya huta daga dukkan aikinsa na halitta da ya yi.
4
Waɗannan sune al'amuran da suka shafi sammai da duniya, a lokacin da aka hallice su, a ranar da Yahweh ya yi sammai da duniya.
5
Ba wani filin daji kuma a duniya, ba tsire-tsire kuma a cikin filaye, domin Yahweh bai sa a yi ruwa ba tukuna a duniya, kuma ba mutumin da zai nome ƙasa.
6
Amma raɓa ta sauka a ƙasa ta jiƙe dukkan ƙasar.
7
Yahweh Allah ya halitta mutum daga cikin ƙasa, ya kuma hura masa numfashin rai a cikin kafafen hancinsa, sai mutum ya zama rayayyen taliki.
8
Yahweh ya yi lambun itatuwa a bangon gabas a cikin Aidan, a can ya sa mutumin daya halitta.
9
Daga cikin ƙasa Yahweh Allah ya sa ko waɗanne irin itatuwa masu ƙayatarwa da abinci su tsiro. Wannan ya haɗa da itacen rai wanda ke a tsakiyar gonar, da kuma itacen sanin nagarta da mugunta.
10
Rafi ya bi ta tsakiyar lambun Aidan domin ya jiƙa lambun. Daga can ne ya rabu ya zama rafuka huɗu.
11
Sunan na farko shi ne Fishon. Shi ne wanda ya malala a dukkan ƙasar Habila, inda akwai zinariya. Zinariyar wannan ƙasar tana da kyau.
12
Akwai kuma itatuwa masu ƙamshi da kyawawan duwatsu.
13
Sunan rafi na biyun shi ne Gishon. Wannan shi ne wanda ya malala zuwa Kush.
14
Sunan rafi na ukun shi ne Tigris, wanda ya malala gabashin Asshur. Rafi na huɗu shi ne Yufaretis.
15
Yahweh Allah ya ɗauki mutumin ya sa shi a lambun Aidin domin ya nome shi ya kula da shi.
16
Yahweh Allah ya umarci mutumin, da cewa, "Daga kowanne irin 'ya'yan itace na cikin lambun kana da 'yancin ci.
17
Amma ba za ka ci daga cikin itace na sanin nagarta da mugunta ba, domin ranar daka ci daga cikinsa, tabbas za ka mutu."
18
Yahweh Allah yace, "ba shi da kyau mutumin ya zauna shi kaɗai. Zan yi masa mataimakiyar da ta dace da shi."
19
Daga cikin ƙasa ne Yahweh Allah ya siffatta kowacce irin dabba ta saura da kuma tsuntsun sararin sama. Sai ya kawo su wurin mutumin domin ya ga yadda zai kira su. Duk abin da mutumin ya kira kowacce halitta sunanta kenan.
20
Mutumin ya ba dukkan dabbobi suna da kuma dukkan tsuntsayen sararin sama. Amma ga mutumin ba a sami mataimakin da ya dace da shi ba.
21
Yahweh Allah ya sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin domin haka mutumin ya yi barci. Yahweh Allah ya cire ɗaya daga cikin haƙarƙarinsa ya yi mace ya kuma kawo ta ga mutumin
22
Da haƙarƙarin da Yahweh ya ciro daga jikin mutumin, ya yi mace da shi ya kuma kawo ta ga mutumin.
23
Sai mutumin yace, "A wannan lokacin, wannan ƙashi ne na ƙasusuwana, tsoka ce daga tsokata. Za a kira ta 'mace,' saboda daga jikin mutum aka ciro ta."
24
Domin haka mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, zai zama haɗe da matarsa, kuma za su zama jiki ɗaya.
25
Dukkan su biyu tsirara suke, mijin da matar, amma ba su jin kunya.