Yosef ya ce ma ma'aikacin ya cika bahunan 'yan'uwansa da abinci, ya kuma maida wa kowannen su kuɗinsa cikin bakin bahunsa, ya kuma sanya kofin azurfa, cikin bakin bahun ƙaramin
Yosef ya faɗa wa ma'aikacinsa cewa ya tambaye dalilin da suka maida mugunta domin nagarta ya kuma yi zargin su da sata kofin Yosef.
'Yan'uwan sun faɗa cewa wanda aka same shi da kofin zai mutu kuma sauran zasu zama bayi.
Ma'aikacin ya faɗa cewa wanda aka same shi da kofin a wurinsa zai zama bawansa, kuma sauran zasu fita daga zargi.
Ma'aikacin ya sami kofin a bahun Benyamin kuma 'yan'uwan sun yaga tufafinsu.
'Yan'uwan suka rusuna a gaban Yosef har ƙasa.
Yahuda ya ce Allah ya gãno laifinsu.
Yahuda ya ce dukka 'yan'uwan zasu zama bayin Yosef.
Yosef ya faɗa cewa mutumin da aka iske kofin a hannunsa, zai zama bawansa, amma game da sauran, zasu tafi cikin salama.
Yahuda ya faɗa cewa ƙaramin ɗan'uwansu ne ɗan tsufansa kuma shi kaɗai ne ya rage ga mahaifiyarsa.
'Yan'uwan sun damu cewa har ya bar mahaifinsa to mahaifinsa zai mutu.
Yahuda ya faɗa cewa an tilasta su su kawo Benyamin domin Yosef ya faɗa cewa sai ƙaramin ɗan'uwan ya zo kafin su gan furskansa.
Isra'ila ya zata cewa an yage Yosef gutsu-gutsu.
Isra'ila ya faɗa cewa 'yan'uwan zasu gangara da furfurasa da baƙinciki zuwa Lahira.
Yahuda ya ce mahaifinsu zai mutu.
Yahuda ya faaɗ cewa idan bai maido da Benyamin ga mahaifinsu ba, zai ɗauki laifin ga mahaifina har abada.
Yahuda ya roƙe Yosef ya sa shi ya zama bawansa domin Benyamin ya iya koma wurin mahaifinsa.