Yosef ya yi kuka da ƙarfi sa'adda ya bayyana kansa ga 'yan'uwansa.
Yan'uwansa ba su iya amsa masa ba, domin sun gigice a gabansa.
Allah ya aiko shi domin ya adana rai, ya kuma ajiye su da rai ta wurin babbar kuɓutarwa.
Allah ya maida Yosef uba ga Fir'auna, shugaban dukkan gidansa, kuma mai mulki a cikin dukkan ƙasar Masar.
Yosef ya ce wa iyalinsa su zo su zauna a ƙasar Goshen inda zai tanada masu.
Yosef ya ce ma 'yan'uwansa su yi hanzari su kawo mahaifinsa Masar.
Abin ya gamshi Fir'auna da bayinsa sosai, ya kuma ce wa Yosef, ya ce wa 'yan'uwansa, su ɗauko mahaifinsu da gidansu dukka su kuma zo su zauna a ƙasar Masar.
Benyamin ya ƙarba azurfa ɗari uku da canjin tufafi biyar, jakuna ashirin ɗauke da hatsi.
Zuciyarsa ta yi mamaki, domin bai gaskata da abin da suka faɗa masa ba.
Isra'ila ya ce, yana so ya gan ɗan shi kafin ya mutu.