Yunwa ta yi tsanani kuma sun cinye hatsin da suka kawo daga Masar a tafiya na farko.
Yahuda ya faɗa cewa ɗole ne su samu ɗan'uwansu Benyamin domin su tafi zuwa Masar.
Yahuda ya faɗa cewa idan bai dawo da Benyamin ba, za a riƙe shi da hakkinsa.
Isra'ila ya faɗa wa 'yan'uwan cewa su ɗauki mafi kyau daga cikin amfanin ƙasar su kuma ɗauki kuɗi ka shi biyu.
Isra'ila ya roƙe Allah ya ba 'yan'uwan jinƙai a Masar domin a saki dukka 'yan'uwan.
'Yan'uwannen sun ji tsoro kila a kama su a kuma ɗaure su ya ɗauke su a matsayin bayi, saboda kuɗaɗen da a ka maido masu cikin bahunansu.
'Yan'uwan sun faɗa wa ma'aikacin cewa sun dawo da kuɗin da aka bari a cikin buhunnasu da kuma kuɗin sayan abinci.
Ma'aikacin ya ce kuɗin da aka bari a cikin bahunan ya fito daga Allah.
'Yan'uwan suka kawo kyaututtukan da ke hannuwansu cikin gidan, su ka kuma rusuna a gabansa har ƙasa.
Yosef ya tambaye 'yan'uwanshi game da lafiyar mahaifinsu.
Yosef yayi hanzari ya fita daga ɗakin saboda ya motsu sosai game da Benyamin sai ya tafi ɗakinsa yayi kuka.
Domin abin ƙyama ne ga Masarawa.
An shirya 'yan'uwan a teburin bisa ga matsayin haihuwarsa.
Kason Benyamin ya yi sau biyar fiye da na 'yan'uwansa.