'Yan'uwan Yosef guda goma, suka tafi sayan hatsi a Masar ba tare da Benyamin ba.
'Yan'uwanen Yosef sun rusuna masa da fuskokinsu ƙasa.
Yosef ya ɓadda kamarsa ya kuma yi wa 'yan'uwansa magana da zafi.
Yosef yayi zargin 'yan'uwansa cewa sun zama 'yan leƙen asirin ƙasa.
'Yan'uwan Yosef sun ce ƙaraminsu ya na tare da mahaifinsa a ƙasar Kan'ana.
'Yan'uwan Yosef sun ce ɗayan ɗan'uwan baya da rai.
Yosef ya faaɗ cewa 'yan'uwansa ba zasu bar Masar ba sai ƙaramin ḍan'uwansu ya zo Masar.
Yosef ya sa aka dukkan kulle su har kwana uku.
Yosef ya ce masu su bar ɗaya daga cikin 'yan'uwansu a tsare shi a kurkuku, sa'adda sauran su kai hatsi Ƙana'na su kuma kawo ƙaramin ɗan'uwansa.
Sun gaskanta cewa ana neman jinin Yosef domin abinda sun yi.
Sa'adda Yosef ya ji 'yan'uwansa suna magana game da abinda suka yi masa, ya juya daga gare su ya yi kuka.
Yosef ya sa wa 'yan'uwansa kuɗinsa a cikin bahunsa.
Zukatansu suka nitse sun kuma juya suna rawar jiki ga junansu.
Sun ba Allah laifi, suna tambayan dalilin da Allah yayi masu wannan.
Sun gane cewa kowanne mutum, jakkar azurfarsa na cikin bahunsa.
Yakubu ya ji tsoron cewa za a ɗauke mashi Simiyon da Benyamin.
Ruben ya rantse cewa zai dawo wa Yakubu da Benyamin daga Masar; ko kuma a kashe 'ya'yansa.
A'a, Yakubu bai yarda Ruben ya ɗauke Benyamin zuwa Masar ba.
Yakubu ya faɗa cewa zai yi bakinciki har zuwa lahira idan Benyamin ya mutu.