Shanun marasa ban sha'awa ramammu sun cinye shanun masu ban sha'awa da ƙiba.
Ƙananun kawunan sun haɗiye kawunan cikakku masu kyau kuma.
'Yan dabo da masu hikima basu iya fasara mafarkin Fir'auna ba.
Mai riƙon ƙoƙon ya faɗa wa Fir'auna cewa wani saurayin mutumin Ba'ibraniye ya fasara masa mafarkinsa da kyau da kuma mafarkin wani mutum a lokacin da suke tsare.
Yosef ya faɗa cewa Allah zai amsawa Fir'auna da tagomashi
Yosef ya ce Allah zai bayyana wa Fir'auna abin da yake gaf da aiwatarwa.
Shanun masu kyau guda bakwai suna wakilcin shekaru bakwai.
Shanun bakwai ramammu marasa ban sha'awa suna wakilcin shekaru bakwai na yunwa.
An ba wa Fir'auna mafarkai biyu domin Allah ya tabbatar da al'amarin, kuma Allah zai aiwatar ba da daɗewa ba.
Yosef ya ba wa Fir'auna shawarar cewa ya zaɓi shugaba ya ɗauki kashi biyar na amfanin Masar a cikin shekaru bakwai na yalwa.
Fir'auna ya faɗa cewa Ruhun Allah na cikin Yosef.
Fir'auna ya ba wa Yosef iko bisa gidansa da kuma dukka ƙasar Masar kuma shi ne na biyu ga Fir'auna.
Yosef ya ajiye hatsi kamar rairayin teku, da yawan gaske har ya daina ƙirgawa, saboda ya zarce ƙirgawa.
An sa wa 'ya'yan Yosef suna Manasse da Ifraimu.
Aka yi yunwa a cikin dukkan ƙasashen.
Yosef ya buɗe dukkan gidajen ajiya ya sayar da abinci wa Masarawa.
Dukkan duniya na zuwa Masar su sayi hatsi daga wurin Yosef.