Yahweh ya ziyarci Saratu sai ta haifi Ibrahim kamar a lokacin da aka alkawarta.
Sa'adda Ishaku na kwana takwas, Ibrahim yayi masa kaciya.
Saratu ta faɗa cewa Allah ya sa ta dariya.
Saratu ta gan ɗan Hajara na ba'a.
Saratu ta ce wa Ibrahim ya kori Hajara da ɗanta domin ɗan Hajara ba zai ci gãdo, tare da Ishaku ba.
Ibrahim yayi baƙin ciki da bukatar Saratu.
Allah ya ce wa Ibrahim ya saurare Saratu.
Hajara da ɗanta sun tafi cikin jeji.
Allah ya ce zai maishe ɗan Hajara babbar al'umma.
Allaha ya buɗe idanun Hajara sai ta ga rijiyar ruwa.
Ɗan hajara ya zama mafarauci sai mahaifiyarsa ta aura masa mata daga ƙasar Masar.
Abimelek ya so Ibrahim ya rantse cewa ba zai yi masa ƙarya ba, ko 'ya'yansa, ko da zuriyarsa. Abimelek ya ce wa Ibrahim ya nuna masa irin wannan alƙawari mai aminci da ya nuna wa Ibrahim.
Ibrahim ya koke game da Abimelek game da rijiyar ruwa da bayin Abimelek suka ƙwace daga wurinsa.
Ibrahim ya aika da matan tumakin guda bakwai domin su zama shaida cewa shi ne ya haƙa wannan rijiya.
Abimelek ya koma zuwa ƙasar Filistiyawa.
Abrahim yayi wa Yahweh sujada, Allah madawwami.
Ibrahim ya zauna a ƙasar filistiyawa na kwanaki masu yawa.