Allah ya faɗa wa Ibrahim ya tafi ƙasar Moriyah ya kuma miƙa Ishaku a matsayin baiko na ƙonawa.
Ibrahim ya tashi da asuba ya kama hanyarsa zuwa inda Allah ya faɗa masa.
Ibrahim ya faɗa wa samarinsa biyu cewa shi da Ishaku zasu je su yi sujada sai su kuma dawo
Ishaku ya tambaye Ibrahim cewa, "Ina ɗan ragon baikon ƙonawa?"
Ibrahim ya faɗa cewa Allah da kansa zai tanada ɗan rago domin baikon ƙonawa.
Ibrahim ya shirya Ishaku a matsayin hadaya ta ɗora shi akan bagadin bisa itacen.
Mala'ikar Yahweh ya ce wa Ibrahim kada ya cutar da Ishaku.
Mala'ikar ya faɗa cewa ya san Ibrahim na tsoron Allah
Akwai ɗan ragon da an kama a cikin jeji a bayan Ibrahim wanda ya yi amfani don hadayar ƙonawa.
Ibrahim ya kira wurin "Yahweh zai tanada."
Mala'ikar Yahweh ya faɗa cewa zai albarkace Ibrahim domin bai hana ɗan ɗansa.
Ta wurin hadayar Ibrahim, dukka al'umman duniya za su sami albarka domin Ibrahim yayi biyayya da muryar mala'ikar Yahweh.