Ibrahim ya faɗa cewa Saratu 'yar'uwarta ce.
Allah ya zo wurin Abimelek a mafarki, ya faɗa masa cewa shi mataccen mutum ne saboda ya ɗauke matar mutumin ce.
Abimelek ya faɗa wa Allah cewa Ibrahim ya ce masa Saratu 'ya'uwarsa ce, kuma Saratu ta faɗa masa cewa Ibrahim ɗan'uwansa ne.
Allaha ya ce wa Abimelek ya mayar da Saratu wa Ibrahim; ko kuma, shi da dukka mutanensa su mutu.
Mazajen Abimelek sun tsorata sa'adda suka ji abin da Allah ya faɗa mashi.
Ibrahim ya faɗa cewa ya ji tsoro Abimelek zai kashe shi saboda saratu.
Saratu 'yar mahaifinsa ne amma ba na mahaifiyarsa ba.
Abimelek ya ba wa Ibrahim tumaki da takarkari, bayi maza da mata.
Abimelek ya faɗa wa Saratu cewa ya ba wa ɗan'uwanta azurfa dubu domin ya rufe duk wani laifin da yayi wa Saratu a fuskar duk wanda ke tare da Saratu da gaban kowa.
Allah ya warkar da Abimelek, matarsa, da bayinsa mata domin su iya haifa 'ya'ya.