Lutu ya roƙe su da su kwana a gidansa sai su tafi washegari.
Mala'ikun sun faɗa cewa za su kwana a kwararo.
A karshe, mala'ikun sun je sun kwana a gidan Lutu.
Mutanen sun so Lutu ya fitar masu da bãƙi biyun domin su kwana da su.
Lutu ya ba mutanen garin 'ya'yansa mata biyu a maimakon bãƙin.
Mutanen sun ce wa Lutu ya tsaya a can har sun kusa su ɓarke ƙofar.
Mala'ikun suka miƙa hannuwansu suka shigo da Lutu cikin gidan sai suka bugi mutanen da makanta.
Mala'ikun sun ce an aike su su hallaka garin.
Surukansa su ka ɗauka wasa ya ke yi.
Mala'ikun sun faɗa wa Lutu cewa ya ɗauke matarsa da ''ya'yansa mata su fita daga garin.
Mala'ikun sun fitar da su wajen garin domin Yahweh ya yi masa jinƙai.
Mala'ikun sun ce wa Lutu da iyalinsa su tserar da rayukansu, Kada su waiga baya.
An bar Lutu da iyalinsa su ruga zuwa wata ƙaramar birnin da ake kira Zowar.
Yahweh ya saukar da ruwan wuta da matsanancin zafi bisa Soduma da Gamora.
Matar Lutu ta waiwaya baya, sai ta zama umudin gishiri.
Ibrahim ya ga hayaƙi na tashi daga filin kamar na hayaƙin matoya.
Lutu ya tafi zuwa duwatsu domin yana jin tsoron zama a Zowar.
'Ya'ya mata na Lutu sun shirya sa mahaifinsu ya bugu, sai su kwana da su domin su samu 'ya'ya.
Mutanen Mowobawa da Ammoniyawa sun fita daga 'ya'ya matan Lutu.