Sura 1
1
A cikin farko, Allah ya hallici sammai da duniya.
2
Duniya bata da siffa, sarari ce kawai. Duhu kuma ya rufe dukkan zurfafa. Ruhun Allah kuma yana kewayawa a bisa fuskar ruwaye.
3
Allah yace, "Bari haske ya kasance, haske kuwa ya kasance."
4
Allah kuma ya ga hasken, ya kuma ƙayatar. Sai ya raba haske da duhu.
5
Allah ya kira haske "yini," duhu kuma ya ce da shi "dare." Wannan shi ne safiya da dare, a rana ta ɗaya.
6
Allah yace, "Bari a sami fili tsakanin ruwaye, Sai ya rarraba tsakanin ruwaye."
7
Allah yayi tsakani ga ruwayen dake ƙarƙas da kuma ruwayen dake sammai. Haka kuma ya kasance.
8
Allah ya kira tsakanin "sararin sama." Wannan shi ne maraice da safiya, rana ta biyu kenan.
9
Allah yace, ruwayen dake ƙarƙashin sammai su tattaru wuri ɗaya, kuma sandararriyar ƙasa ta bayyana," haka kuma ya faru.
10
Allah ya kira sandararriyar ƙasa "duniya," ruwayen da suka tattaru kuma ya kira su "tekuna" ya kuma ga suna da kyau.
11
Allah yace, "Duniya ta fitar da ciyayi da itatuwa masu fitar da iri da kuma 'ya'ya waɗanda ke cikin 'ya'yan, kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance.
12
Ƙasa ta fitar da ganyayyaki, da itatuwa masu bada iri kowanne bisa ga irinsa, da kuma itatuwa masu bada 'ya'ya dake cikinsu, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau.
13
Wannan ce safiya da maraice, rana ta uku.
14
Allah yace, "Haske ya kasance a sararin sama domin ya raba tsakanin haske da duhu, su kuma zama alamu na yanayi, domin ranaku da shekaru.
15
Sai su zama haske a sararin sama domin su haskaka duniya." Haka kuwa ya kasance.
16
Allah yayi manyan haskoki guda biyu, babban hasken yayi mulkin yini, ƙaramin hasken kuma yayi mulkin dare. Ya kuma yi taurari.
17
Allah ya shirya su a sama domin su bada haske ga duniya,
18
su kuma yi mulki kan yini da kuma dare, su kuma raba tsakanin haske da duhu. Allah kuma ya ga yana da kyau.
19
Wannan ce safiya da yammaci, rana ta huɗu.
20
Allah yace, "Ruwaye su kasance da manyan halittu masu rai, ya kuma bar tsuntsaye suyi ta firiya a saman duniya a sararin sama."
21
Allah ya hallici manyan hallittu na tekuna, da kuma sauran halittu kowanne bisa ga irinsa, da masu tafiya da kuma waɗanda suka cika ruwaye a ko'ina, da kuma dukkan tsuntsaye masu fukafukai, kowanne bisa ga irinsa. Allah kuma ya ga yana da kyau.
22
Allah ya albarkace su, cewa, "Ku ruɓanɓanya, ku hayayyafa, ku cika ruwaye a cikin tekuna. Ya ce tsuntsaye su ruɓanɓanya a duniya."
23
Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta biyar.
24
Allah yace, "Ƙasa ta bada hallittu masu rai, kowanne bisa ga irinsa, dabbobin gida, masu rarrafe dana daji kowanne bisa ga irinsa." Haka kuma ya kasance.
25
Allah kuma ya yi dabbobin duniya kowanne bisa ga irinsu, dabbobin gida kowanne bisa ga irinsa da duk masu jan jiki a ƙasa kowanne bisa ga irinsa. Ya kuma ga suna da kyau.
26
Allah yace "Bari muyi mutum cikin kamanninmu, bisa surarmu. Su yi mulkin kifaye na tekuna, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da kuma dukkan duniya, da dukkan abu mai rarrafe a bisa duniya."
27
Allah ya hallici mutum cikin kamanninsa. Cikin kamanninsa ya hallice shi. Mace da namiji ya hallice su.
28
Allah ya albarkace su ya ce da su, "Ku hayayyafa ku kuma ruɓaɓɓanya. Ku cika duniya ku nome ta. Kuyi mulkin kifaye na tekuna da tsuntsayen sama, da kuma duk abu mai rai dake tafiya bisa duniya."
29
Allah yace, "Duba na baka kowanne tsiro dake bada iri wanda yake a fuskar duniya, da dukkan bishiyoyi dake da iri a cikinsu. za su zama abinci a gare ku.
30
Ga kowacce dabba ta duniya, da kuma dukkan tsuntsaye na sammai, da kowanne abu mai rarrafe a doron duniya, da kuma dukkan halittu masu numfashin rai na baku kowanne irin koren ganye domin abinci." Haka kuma ya kasance.
31
Allah kuma ya ga dukkan abin da ya halitta na da kyau. Wannan ne asubahi da yammaci, rana ta shida.