Names

Abimelek

Gaskiya

Abimelek wani sarkin Filistiyawa ne bisa lardin Gera lokacin da Ibrahim da Ishaku suke zaune cikin ƙasar Kan'ana.

  • Ibrahim ya ruɗi Sarki Abimelek ta wurin cewa Saratu 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba.
  • Ibrahim da Abimelek sun yi alƙawari game da mallakar rijiyoyi a Biyasheba.
  • Bayan shekaru da dama, Ishaku ya ruɗi Abimelek da waɗansu mazajen Gera ta wurin cewa Rebeka 'yar'uwarsa ce ba matarsa ba.
  • Sarki Abimelek ya kwaɓi Ibrahim sa'an nan kuma Ishaku domin sun yi masa ƙarya.
  • Wani mutum kuma mai suna Abimelek ɗan Gidiyon ne ɗan u'wan Yotam. Wasu juyin sun canza rubutun sunansa domin su nuna a sarari shi wani mutum ne daban da Sarki Abimelek.

(Hakanan duba: Biyasheba, Gera, Gidiyon, Yotam, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 11:21
  • Farawa 20:03
  • Farawa 20:05
  • Farawa 21:22
  • Farawa 26:11
  • Littafin Alƙalai 09:54

Abiya

Gaskiya

Abiya sunan wani sarki ne na Yahuda wanda ya yi mulki daga 915-913 BC. ‌Ɗan Sarki Rehobowam ne. Akwai wasu mutane kuma da dama da ake kiran su Abiya a cikin Tsohon Alƙawari.

  • 'Ya'yan Sama'ila maza Abiya da Yowel shugabanni ne bisa mutanen Isra'ila a Biyasheba. Saboda Abiya da ɗan'uwansa sun yi rashin gaskiya da haɗama, mutane suka roƙi Sama'ila ya naɗa masu sarki da zai yi mulki a kansu.
  • Wani Abiya ɗaya ne daga cikin firistocin haikali a zamanin Sarki Dauda.
  • Abiya sunan ɗaya daga cikin 'ya'ya maza na Sarki Yerobowam ne.
  • Abiya kuma sunan wani babban firist ne da ya dawo Yerusalem tare da Zerubabel daga bautar talala a Babila.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 15:03
  • 1 Sama'ila 08:1-3
  • 2 Tarihi 13:19
  • Luka 01:05

Abiyata

Gaskiya

Abiyata babban firist ne domin al'ummar Isra'ila a zamanin Sarki ‌Dauda.

  • Sa'ad da Sarki Saul ya kashe firistoci, Abiyata ya kubce ya gudu wajen ‌Dauda a jeji.
  • Abiyata da wani firist mai suna Zadok sun bauta wa ‌Dauda da aminci dukkan kwanakin sarautarsa.
  • Bayan mutuwar Dauda, Abiyata ya taimaki Adoniya ƙoƙarin ya zama sarki maimakon Suleman.
  • Sabili da wannan, Sarki Suleman ya cire Abiyata daga ƙungiyar firistoci.

(Hakanan duba: Zadok, Saul (Tsohon Alƙawari), Dauda, Suleman, Adoniya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:32-34
  • 1 Sarakuna 01:07
  • 1 Sarakuna 02:22-23
  • 2 Sama'ila 17:15
  • Markus 02:25-26

Abna

Gaskiya

Abna da Sarki Saul 'ya'yan wa da ƙane ne a cikin Tsofon Alƙawari.

  • Abna shi ne shugaban rundunar mayaƙan Saul, shi ne ya gabatar da saurayi Dauda ga Saul bayan da Dauda ya kashe gagon nan Golayat.
  • Bayan mutuwar Sarki Saul, Abna ya zaɓi Isboshet ɗan Saul ya zama sarki a Isra'ila, sa'ad da aka zaɓi Dauda ya zama sarki a Yahuda.
  • Daga baya, Yowab shugaban rundunar mayaƙan Dauda, ya yiwa Abna mummunan kisan maƙirci.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 26:26-28
  • 1 Sarakuna 02:5-6
  • 1 Sarakuna 02:32
  • 1 Sama'ila 17:55-56
  • 2 Sama'ila 03:22

Absalom

Gaskiya

Absalom ɗan Sarki Dauda na uku ne. Shi sananne ne domin kyaun jamalinsa da kuma zafin rai.

  • Sa'ad da aka yi wa ƙanwar Absalom Tama fyaɗe ta wurin ɗan'uwansu, Amnon, wanda suke uba ɗaya, Absalom ya shirya ya sa a kashe Amnon.
  • Bayan an kashe Amnon, Absalom ya gudu zuwa gundumar Geshu (inda mahaifiyarsa Ma'aka ta fito) ya kuma zauna a can har shekara uku. Sa'an nan Sarki Dauda ya aika ya komo zuwa Yerusalem, amma bai bari Absalom ya shigo gabansa ba har shekara biyu.
  • Absalom ya juyar da waɗansu mutane gãba da Sarki Dauda ya bida tawaye gãba da shi.
  • Mayaƙan Dauda suka yi yaƙi gãba da Absalom suka kashe shi. Dauda ya yi baƙinciki da haka ya faru.

(Hakanan duba: Geshur, Amnon)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:1-3
  • 1 Sarakuna 01:06
  • 2 Sama'ila 15:02
  • 2 Sama'ila 17:1-4
  • 2 Sama'ila 18:18
  • Zabura 003:1-2

Adamu

Gaskiya

Adamu mutum ne na fari da Allah ya hallita. Da shi da matarsa Hauwa'u an yi su cikin surar Allah.

  • Allah ya hallici Adamu daga turɓaya ya hura masa rai a cikinsa.
  • Sunan Adamu ya yi kama da kalmar Ibraniyanci "jar dauɗa" ko "ƙasa."
  • Sunan nan "Adamu" ɗaya yake da waɗannan kalmomi a Tsohon Alƙawari "'yan adam" ko "talikai."
  • Dukkan mutane zuriyar Adamu da Hauwa'u ne.
  • Adamu da Hauwa'u sun yiwa Allah rashin biyayya. Wannan ya raba su da Allah kuma yasa zunubi da mutuwa suka shigo cikin duniya.

(Hakanan duba: mutuwa, zuriya, Hauwa, siffar Allah, rayuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 02:14
  • Farawa 03:17
  • Farawa 05:01
  • Farawa 11:05
  • Luka 03:38
  • Romawa 05:15

Afisos, mutumin Afisos, Afisawa

Gaskiya

Afisos wani daɗaɗɗen birnin Girkawa ne wajejen garin da yau ake kira Turkiya.

  • A kwanakin masu bi na farko, Afisos ita ce cibiyar Asiya, wadda take ƙaramin lardi ne na Roma a wancan lokacin.
  • Sabo da inda birnin yake, wanan birnin ya zama da muhimmanci a fannin kasuwanci da zirga zirga.
  • An san wani sanannen wurin bautar gunkiyar Artemis (Diyana) da ke a Afisus.
  • Bulus ya zauna ya kuma yi aiki a Afisus fiye da shekaru biyu, daga bisani ya naɗa Timoti ya jagoranci sababbin masu bi a can.
  • Littafin Afisawa na cikin Sabon Alƙawari, wasiƙa ce wadda Bulus ya rubuta zuwa ga masu bi a Afisos.

(Hakanan duba: Asiya, Bulus, Timoti)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:32
  • 1 Timoti 01:3
  • 2 Timoti 04:11-13
  • Ayyukan Manzanni 19:1
  • Afisawa 01:1

Afolos

Gaskiya

Afolos Bayahude ne daga birnin Alezandariya a Masar wanda yake da baiwar koyar da mutane musamman akan Yesu.

  • Afolos yana da ilimi sosai game da Litattafan Ibraniyawa kuma yana da baiwar iya magana.
  • Ya karantu a ƙarƙashin Kiristoci biyu a Afisa masu suna Akila da Bilkisu.
  • Bulus ya jaddada cewa da shi da Afolos, da kuma wasu masu wa'azi da malamai, suna aiki da manufa ɗaya wato taimakon mutane su gaskata da Yesu.

(Hakanan duba: Akuila, Afisawa, Firissila, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 01:13
  • 1 Korintiyawa 16:12
  • Ayyukan Manzanni 18:25
  • Titus 03:13

Ahab

Gaskiya

Ahab mugun sarki ne wanda ya yi mulki bisa masarautar arewa ta Isra'ila daga 875 zuwa 854 BC.

  • Sarki Ahab ya sa mutanen Israr'ila suka yi sujada ga gumaku.
  • Annabi Iliya ya fuskanci Ahab ya gaya masa za a yi mugun fari shekara uku da wata shida sakamakon hukuncin zunuban da Ahab ya sa Isra'ila ta aikata.
  • Ahab da matarsa Yezebel sun yi waɗansu mugayen abubuwa da yawa, har ma da amfani da ikon da suke da shi su kashe mutane marasa laifi.

(Hakanan duba: Ba'al, Iliya, Yezebel, masarautar Isra'ila, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:1-2
  • 1 Sarakuna 20:1-3
  • 2 Tarihi 21:06
  • 2 Sarakuna 09:08

Ahasurus

Gaskiya

Ahasurus sarki ne wanda yayi mulki bisa tsohuwar masarauta ta Fasiya tsawon shekaru ashirin.

  • Wannan lokacin ne da Yahudawa da aka kwashe zuwa bautar talala a Babila, suka zo ƙarƙashin mulkin Fasiya.
  • Wani suna na wannan sarki shi ne Zazas.
  • Bayan ya kori matarsa cikin hasala, Sarki Ahasurus daga baya ya zaɓi wata mace Bayahudiya mai suna Esta ta zama sabuwar matarsa da kuma sarauniya.

(Hakanan duba: Babila, Esta, Itiyofiya, hijira, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 09:01
  • Esta 10:1-2
  • Ezra 04:7-8

Ahaz

Gaskiya

Ahaz mugun sarki ne wanda ya yi mulki bisa masarautar Yahuda daga 732 zuwa 716 BC. Wannan kimamin shekaru 140 ne kafin lokacin da aka kwashe mutane da yawa daga Isra'ila da Yahuda zuwa bautar talala a Babila.

  • Sa'ad da yake mulkin Yahuda, Ahaz yana da bagadi da aka gina shi domin yin sujada ga gumakun Asiriyawa, wanda yasa mutane suka juya daga Allah na gaskiya guda ɗaya, Yahweh.
  • Sarki Ahaz yana da shekara 20 sa'ad da ya soma mulki akan Yahuda, ya yi mulki shekara 16.

(Hakanan duba: Babila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 08:35-37
  • 2 Tarihi 28:01
  • 2 Sarakuna 16:20
  • Hosiya 01:01
  • Ishaya 01:1
  • Ishaya 07:04
  • Matiyu 01:9-11

Ahaziya

Gaskiya

Ahaziya sunan sarakai biyu ne: ɗaya ya yi mulki bisa masarautar Isra'ila, ɗayan ya yi mulki akan masarautar Yahuda.

  • Sarkin Yahuda Ahaziya ɗan Sarki Yehoram ne. Ya yi sarauta shekara ɗaya (841 BC) sai Yehu ya kashe shi. Ƙaramin ɗan Yowash daga bisani ya ɗauki gurbinsa a matsayin sarki.
  • Sarki Isra'ila Ahaziya ɗan Ahab ne. Y a yi mulki shekaru (850 - 49 B.C.). Ya mutu ne ta wurin rauni da ya samu sa'ad da ya faɗi ƙasa a fadarsa sai ɗan'uwansa Yoram ya zama sarki.

(Hakanan duba: Yehu, Ahab, Yerobuwam, Yowash)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 22:39-40
  • 2 Tarihi 22:02
  • 2 Tarihi 25:23-24
  • 2 Sarakuna 11:02

Ahiya

Gaskiya

Ahiya sunan mazaje ne da dama a Tsohon Alƙawari. Ga wasu sunayen mazajen.

  • Ahiya sunan wani firist ne a zamanin Saul.
  • Wani mutum mai suna Ahiya magatakarda ne a lokacin da Sarki Suleman yake sarauta.
  • Ahiya sunan wani annabi ne daga Shilo wanda ya yi anabci cewa al'ummar Isra'ila zata rabu ta zama masarauta biyu.
  • Mahaifin Sarki Ba'asha na Isra'ila shi ma ana kiransa Ahiya.

(Hakanan duba: Ba'asha, Shilo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 15:27-28
  • 1 Sarakuna 21:21-22
  • 1 Sama'ila 14:19
  • 2 Tarihi 10:15

Ai

Gaskiya

A lokatanTsohon Alƙawari, Ai sunan wani garin Kan'aniyawa ne kudu da Betel ratan kilo mita 8 arewa maso yamma da Yeriko.

  • Bayan ya ci Yeriko, Yoshuwa ya bida Isra'ilawa a kai harin ga Ai. Amma nan da nan aka buga su domin Allah bai ji daɗinsu ba.
  • Wani Ba'isra'ile mai suna Akan ya saci ganima daga Yeriko sai Allah ya umarta a kashe shi da iyalinsa. Sa'annan ne Allah ya taimaki Isra'ilawa suka ci mutanen Ai da yaƙi.

(Hakanan duba: Betel, Yeriko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 02:27-30
  • Farawa 12:8-9
  • Farawa 13:3-4
  • Yoshuwa 07:03
  • Yoshuwa 08:12

aidin, lambun aidin

Gaskiya

A kwanakin can farko aidin aidin shi ne yankin da ke da lambu inda Allah ya sa mutum na farko da mace ta farko su rayu.

  • Aidin inda Adamu da Hauwa suka zauna wani sashe ne kawai na aidin.
  • Ainahin wurin babu tabbas akan cewa ga daidai inda yake, amma rafuffukan Yuferetis da na tigris suna miƙa masu ruwa.
  • Kalmar nan aidin an samo ta ne daga Ibraniyanci wadda ke nufin "jin matuƙar farin ciki a ciki."

(Hakanan duba: Adamu, Rafin Yufiretis, Hauwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 28:11-13
  • Farawa 02:7-8
  • Farawa 02:10
  • Farawa 02:15
  • Farawa 04:16-17
  • Yowel 02:3

Akila

Gaskiya

Akila Ba-yahuden Kirista ne daga lardin Fontus, wata yankin ƙasa kudancin gaɓas da BaƙinTekun.

  • Akila da Bilkisu sun zauna a Roma, Italiya na ɗan tsawon lokaci, amma sai sarkin Roma, Kladiyus ya tilasta wa dukkan Yahudawa su bar Roma.
  • Bayan wannan Akila da Bilkisu suka tafi Koranti, inda suka gamu da manzo Bulus.
  • Suka yi aikin saƙa gwadon rumfar ɗaki tare da Bulus, sun kuma taimake shi wajen aikin yaɗa bishara.
  • Da Akila da Bilkisu sun koya wa masu bi game da gaskiya akan Yesu; ɗaya daga cikin waɗanda suka bada gaskiya wani ne mai baiwar koyarwa ana ce da shi Afolos.

(Hakanan duba: Afolos, Korint, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 16:19-20
  • 2 Timoti 04:19-22
  • Ayyukan Manzanni 18:02
  • Ayyukan Manzanni 18:24

Amalek, Ba'amaleke, Amalekawa

Gaskiya

Amalekawa makiyaya ne da suka zauna a kudancin Kan'ana, daga hamadar Negeb zuwa ƙasar Arebiya. Wannan jinsin mutane sun fito ne daga zuriyar Isuwa.

  • Amalekawa maƙiyan Isra'ila ne sosai tun daga lokacin da Isra'ila suka zo da farko suka zauna a Kan'ana.
  • Wani lokaci idan an ce "Amalek" ana nufin dukkan Amalekawa.
  • A wani yaƙi gãba da Amalekawa, da Musa ya ɗaga hannuwansa sama, Isra'ilawa suka dinga cin yaƙi. Sa'ad da ya gaji kuma hannuwansa suka fara saukowa ƙasa, sai suka fara samun rashi. Sai Haruna da Hur suka taimaki Musa riƙe hannunsa sama har saida Isra'ilwa suka ragargaza Amalekawa.
  • Da Sarki Saul da Sarki Dauda sun sha kai hare-haren yaƙi wa Amalekawa.
  • Bayan cin nasara sau ɗaya akan Amalekawa, Saul ya yiwa Allah rashin biyayya ta wurin ɗaukar wasu ganima da kuma ƙin kashe sarkin Amalekawa kamar yadda Allah ya umarta masa ya yi.

(Hakanan duba: Arabiya, Dauda, Isuwa, Negeb, Saul (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 04:43
  • 2 Sama'ila 01:08
  • Fitowa 17:10
  • Littafin Lissafi 14:23-25

Amaziya

Gaskiya

Amaziya ya zama sarki bisa masarautar Yahuda lokacin da aka kashe mahaifinsa, Sarki Yowash.

  • Sarki Amaziya ya yi sarauta bisa Yahuda shekara ashirin da tara, daga 796 BC zuwa 767 BC.
  • Sarki ne nagari, amma bai lalatar da tuddan wurare inda ake wa gumaku sujada ba.
  • A ƙarshe Amaziya ya karkashe dukkan mazaje waɗanda suka sa hannu cikin kisan mahaifinsa.
  • Ya buga 'yan tawayen Idomiyawa ya dawo da su ƙarƙashin mulkin sarautar Yahuda.
  • Ya ƙalubalenci Sarki Yehowash na Isra'ila da yaƙi amma aka ci shi. Wasu sassan ganuwar Yerusalem suka rushe kuma aka sace kayayyakin azurfa da zinariya na haikali.
  • Bayan shekaru da dama Sarki Amaziya ya juya daga bin Yahweh kuma waɗansu mutane a Yerusalem suka ƙulla maƙarƙashiya suka kashe shi.

(Hakanan duba: Yowash, Idom)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:10-12
  • 1 Tarihi 04:34
  • 2 Tarihi 25:9-10
  • 2 Sarakuna 14:10

Amnon

Gaskiya

Amnon shi ne babban ɗan Sarki Dauda daga matarsa Ahinowam.

  • Amnon ya yiwa 'yar'uwarsa Tamar wadda suke uba ɗaya fyaɗe, ita kuma 'yar'uwar Absalom ce.
  • Saboda wannan ne, Absalom ya shirya maƙarƙashiya gãba da Amnon ya kashe shi.

(Hakanan duba: Dauda, Absalom)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:1-3
  • 2 Sama'ila 13:02
  • 2 Sama'ila 13:7-9

Amon, Ba'amoniya, Amoniyawa

Gaskiya

"Mutanen Amon" ko Amoniyawa wasu jinsin mutane ne a Kan'ana. Sun fito ne daga zuriyar Ben-ami, wanda yake ɗan Lot ta wurin karamar ɗiyarsa.

  • Wannan suna "Ba'amoniya" na nufin musamman ta macen Amoniyawa. Za a iya bada fassara haka a maimako "mace Ba'amoniya."
  • Amoniyawa sun zauna gabas da Kogin Yordan kuma maƙiyan Isra'ila ne.
  • A wani karo, Amoniyawa suka yiwo hayar wani annabi ana ce da shi Bal'amu domin ya la'anta Isra'ila, amma Allah bai yarda masa ba.

(Hakanan duba: la'ana, Kogin Yodan, Lot)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 19:1-3
  • Ezekiyel 25:02
  • Farawa 19:38
  • Yoshuwa 12:1-2
  • Littafin Alƙalai 11:27
  • Zefaniya 02:08

Amos

Gaskiya

Amos annabin Isra'ilawa ne wanda ya yi zamani da Sarki Uziya na Yahuda.

  • Kafin a kiraye shi ya zama annabi, Amos tun farko makiyayi ne manomin ɓaure yana zaune a ƙarƙashin mulkin Yahuda.
  • Amos ya yi annabci gãba da wadatacciyar masarautar arewa ta Isra'ila game da rashin adalcin da suke musguna wa mutane.

(Hakanan duba: ɓaure, Yahuda, masarautar Isra'ila, makiyayi, Uziya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 01:01

Amoz

Gaskiya

Amoz mahaifin annabi Ishaya ne.

  • Sau ɗaya kaɗai aka ambace shi a Littafi Mai Tsarki sa'ad da aka ce da Ishaya "ɗan Amoz."
  • Wannan suna daban yake da sunan annabi Amos yakamata kuma a rubuta shi daban.

(Hakanan duba: Amos, Ishaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 19:02
  • Ishaya 37:1-2
  • Ishaya 37:21-23

Anas

Gaskiya

Anas babban firist ne na Yahudawa a Yerusalem na tsawon shekara 10, daga AD 6 zuwa AD 15. Sa'an nan gwamnatin Romawa ta cire shi daga matsayin manyan firistoci, koda shi ke ya ci gaba da zama tsayayyen shugaba a cikin Yahudawa.

  • Anas surikin Kefas ne, zaɓaɓɓen babban firist a lokacin hidimar Yesu.
  • Bayan manyan firistoci sun yi murabus, sukan riƙe sunan muƙaminsu tare da wasu ayyukan hidima na matsayinsu. Saboda haka ne ake ce da Anas babban firist a zamanin firistancin Kefas da waɗansu.
  • A lokacin da ake shar'anta shi a gaban shugabannin Yahudawa, an kawo Yesu da fari a gaban Anas domin ayi masa tambayoyi.

(Hakanan duba: babban firist, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:5-7
  • Yahaya 18:22-24
  • Luka 03:02

Andarawus

Gaskiya

Andarawus yana ɗaya daga cikin mutum goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa da shi .

  • ‌Dan 'uwan Andarawus shi ne Siman Bitrus. Dukkan su biyu masunta ne.
  • Da Bitrus da Andarawus suna kamun kifi ne a Tekun Galili sa'ad da Yesu ya kiraye su su zama almajiransa.
  • Kafin Bitrus da Andarawus su gamu da Yesu, sun yi almajiranci a wajen Yahaya Mai yin Baftisma.

(Hakanan duba: manzo, almajiri, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Yahaya 01:40
  • Markus 01:17
  • Markus 01:29-31
  • Markus 03: 17-19
  • Matiyu 04:19
  • Matiyu 10:2-4

Antiyok

Gaskiya

Antiyok sunan garuruwa biyu ne a Sabon Alƙawari. Daya na Siriya kusa da bakin ruwan da ake ce da shi Tekun Baharmaliya. Dayan yana Roma ne a lardin Fisidiya, kusa da birnin Kolossiya.

*‌ Wata ƙaramar ikilisiya a Antiyok ta Siriya ita ce wurin da aka fara kiran masu gaskatawa da Yesu "Kiristoci." Wannan coci tana da himmar aika masu bishara wajen Al'ummai.

  • Shugabannin ikilisiyar Yerusalem suka aika da wasiƙa zuwa ga masu bada gaskiya a iklisiya ta Antiyok a Siriya domin su taimake su su sani ba sa buƙatar su bi dokokin Yahudawa kafin su zama Kirista.
  • Bulus da Barnabas da Yahaya Markus suka tafi Antiyok a Fisidiya su yi bishara. Wasu Yahudawa daga wasu biranen suka zo suka tada hargitsi da ƙoƙarin su kashe Bulus. Amma mutane da yawa, Yahudawa da Al'ummai suka saurari koyarwar kuma suka gaskata da Yesu.

(Hakanan duba: Barnabas, Kolosse, Yahaya Markus, Bulus, lardi, Roma, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 03:10-13
  • Ayyukan Manzanni 06:5-6
  • Ayyukan Manzanni 11:19-21
  • Ayyukan Manzanni 11:26
  • Galatiyawa 02:11-12

Araba

Gaskiya

"Araba" a cikin Tsohon Alƙawari yawancin lokaci wata babbar hamada ce da kuma filayen wurare dake da kwarurruwa kewaye da Kogin Yordan daya zarce kudu zuwa arewacin ƙurewar Jan Teku.

  • Isra'ilawa sun yi tafiya cikin yankin hamadan nan a kan haryarsu daga Masar zuwa ƙasar Kan'ana.
  • Shi kuma "Tekun Araba" za a iya fassara shi zuwa, "tekun dake cikin yankin hamada ta Araba." Wannan teku yawancin lokaci ana ce da shi "Tekun Gishiri" ko "Mataccen Teku."
  • Wannan kalma "araba" zai iya yiwuwa yawancin lokaci ana nufin kowacce irin hamadar yanki.

(Hakanan duba: jeji, Tekun Iwa, Hogin Yodan, Kan'ana, Tekun Gishiri, Masar)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 23:24-25
  • 2 Sarakuna 25:4-5
  • 2 Sama'ila 02:29
  • Irmiya 02:4-6
  • Ayuba 24:5-7
  • Zakariya 14:10

Aram, Ba'aramiye, Aramiyawa, Aramiyanci, Aram ta Damaskus

Gaskiya

Aram sunan mutum biyu ne a Tsohon Alƙawari. kuma sunan wata yankin ƙasa ce arewa maso gabas da Kan'ana, inda Siriya take a yau.

  • Mutanen dake zaune a Aram an sansu da suna "Aramiyawa" suna faɗar "Aramiyanci.
  • Ɗaya daga 'ya'yan Shem ana kiransa Aram. Wani mutum kuma ana ce da shi Aram dangi ne na Rebeka. Mai yiwuwa ne yankin nan na Aram ya sami wannan suna daga ɗaya daga cikin mutanen nan biyu.
  • Daga baya aka san Aram da sunan Girik wato "Siriya."
  • Wannan suna "Faddan Aram" ma'anarsa "sararin Aram" ana samunsa a arewacin Aram.
  • Wasu 'yan'uwan Ibrahim sun zauna a birnin Haran, dake "Faddan Aram." ‌
  • A cikin Tsohon Alƙawari wani lokaci "Aram" da "Faddan Aram" na nufin yanki guda.
  • Wannan suna "Aram Naharayim" na nufin "Aram na Koguna Biyu." Wannan yanki yana arewacin sashin Mesofotamiya dake gabashin "Faddan Aram."

(Hakanan duba: Mesofotamiya, Fadan Aram, Rebeka, Shem, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:17-19
  • 2 Sama'ila 08:06
  • Amos 01:5
  • Ezekiyel 27:16
  • Farawa 31:19-21
  • Hosiya 12:12
  • Zabura 060:1

Ararat

Gaskiya

A cikin Littafi Mai Tsarki, "Ararat" suna ne da aka ba wata ƙasa, wani mulki da kuma manyan tsaunuka a jere.

  • "‌Ƙasar Ararat" watakila tana cikin inda yanzu shi ne arewa maso gabas na ɓangaren ƙasar Turkaniya wato Toki.
  • An fi sanin Ararat da sunan tsaunin da Jirgin Nuhu ya sauka a kai bayan da ruwayen babbar ambaliya suka fara janyewa.
  • A zamanin yanzu, tsaunin da ake kira "Tsaunin Ararat" yawancin lokaci ana zaton shi ne wurin da "tsaunikan Ararat" na Littafi Mai Tsarki suke.

(Hakanan duba: akwati, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 19:35-37
  • Farawa 08:4-5
  • Ishaya 37:38
  • Irmiya 51:27

Arebiya, Ba'arebiye, Arebiyawa

Gaskiya

Arebiya ita ce babbar ƙasa duk duniya wadda ruwa ya kusan kewaye ta, kusan 3,000,000 kilomitas zagayen ta. Tana kudu maso gabas da Isra'ila, tana iyaka da Jan Teku, da Teku Arebiya da kuma Gacin Fasiya.

  • Sunan nan " Ba'arebiye" ana nufin wani mutum dake zaune a Arebiya ko wani abu da aka haɗa shi da Arebiya.
  • Mutane na fari da suka zauna a Arebiya sune jikokin Shem. Wasu mazaunan kuma har da ɗan Ibrahim wato Isma'ila da zuriyarsa, da kuma zuriyar Isuwa.
  • Yankin hamadar da Isma'ilawa suka yi yawo shekara 40 tana nan ne cikin Arebiya.
  • Bayan da Bulus ya zama mai bada gaskiya ga Yesu, ya tafi ya yi 'yan shekaru a hamadar Arebiya.
  • A cikin wasiƙarsa zuwa ga Kiristoci a Galatiya Bulus ya faɗi cewa Tsaunin Sinai tana cikin Arebiya.

(Hakanan duba: Isuwa, Galatiyawa, Isma'ila, Shem, Sinai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 10:14-15
  • Ayyukan Manzanni 02:11
  • Galatiyawa 01:15-17
  • Galatiyawa 04:24-25
  • Irmiya 35:24-26
  • Nehemiya 02:19-20

Asa

Gaskiya

Asa sarki ne da ya yi mulki bisa sarautar Yahuda shekara arba'in, daga 913 - 873 BC.

  • Sarki Asa sarki ne nagari wanda ya cire gumaku da yawa na maƙaryatan alloli yasa Isra'ilawa su soma yiwa Yahweh sujada.
  • Yahweh ya ba Sarki Asa nasara a yaƙe-yaƙensa gãba da waɗansu al'ummai.
  • Daga baya a mulkinsa, Sarki Asa ya daina dogara ga Yahweh ya kuwa kama wata cuta wadda a ƙarshe ta kashe shi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:14-16
  • 1 Sarakuna 15:7-8
  • 2 Tarihi 14:03
  • Irmiya 41:09
  • Matiyu 01:07

Asaf

Gaskiya

Asaf Ba'lebi ne da baiwar waƙa shi ne ya wallafa muryoyi domin zabura ta Sarki Dauda. Shi ma kansa ya rubuta nasa zaburar.

  • Sarki Dauda ya naɗa Asaf ya zama ɗaya daga cikin mutum uku mawaƙa waɗanda suke bada waƙoƙin sujada a haikali. Wasu waƙoƙin annabtai ne.
  • Asaf ya tarbiyar da 'ya'yansa suka kuma ɗauki wannan nawaiya, ta kaɗa kayan waƙoƙi da yin annabci cikin haikali.
  • Wasu kayan kaɗe-kaɗe na waƙoƙi sun haɗa da su, sarewa, garaya, ƙaho, da molaye.
  • Zabura 50 da 73-83 ance daga Asaf suke. mai yiwuwa waɗansu daga cikin waƙoƙin nan marubutansu daga cikin iyalinsa ne.

(Hakanan duba: zuriya, garaya, sarewa, annabi, zabura, ƙaho)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:39-43
  • 2 Tarihi 35:15
  • Nehemiya 02:08
  • Zabura 050:1-2

Asha

Gaskiya

Asha ɗan Yakubu na takwas ne. Zuriyarsa tana ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila wanda kuma ake kira "Asha."

  • Mahaifiyar Asha ita ce Zilfa, baranyar La'aitu.
  • Ma'anar sunansa "farinciki, ko "mai albarka."
  • Asha kuma sunan yankin ƙasar da aka ba kabilar Asha ne lokacin da Isra'ilawa suka shiga ƙasar alƙawari.

(Hakanan duba: Isra'ila, kabulu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:1-2
  • 1 Sarakuna 04:16
  • Ezekiyel 48:1-3
  • Farawa 30:13
  • Luka 02:36-38

Ashdod, Azotus

Gaskiya

Ashdod ɗaya daga cikin shahararrun birane biyar na Filistiyawa ne. Ashdod na kudu maso yamma da Kan'ana kusa da Tekun Baharmaliya, dai-dai rabin tafiya tsakanin biranen Gaza da Yoffa.

  • Haikalin gunkin allahn Filistiyawa Dagon a Ashdod yake.
  • Allah ya hukunta mutanen Ashdod ainun da Filistiyawa suka sace akwatin alƙawari suka aje shi a haikalin tsafinsu a Ashdod.
  • Da Girik sunan birnin nan Azotus ne. Yana ɗaya daga cikin biranen da mai wa'azi, Filib ya shaida masu bishara.

(Hakanan duba: Ekron, Gat, Gaza, Yoffa, Filibiya, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 05:1-3
  • Ayyukan Manzanni 08:40
  • Amos 01:8
  • Yoshuwa 15:45-47
  • Zakariya 09:06

Ashera, ginshiƙin Ashera, ginshiƙan Ashera, Ashtoret, Ashtoretai

Gaskiya

Ashera sunan wata allahiya ce wadda mutanen Kan'ana suke mata sujada a lokacin Tsohon Alƙawari. "Ashtoret" wataƙila wani suna ne na "Ashera" ko kuma sunan wata allahiyar daban da tayi kusa da tata.

  • Wannan kalmar "ginshiƙan Ashera" ana nufin wasu sassaƙaƙƙun siffofi ne na itace ko sassaƙaƙƙun itatuwa da aka yi domin su wakilci wannan allahiya.
  • ‌Ginshiƙan Ashera yawancin lokaci ana kafa su kusa da bagadin gunkin nan Ba'al, wanda ake tunanin shi ne mijin Ashera. Wasu jinsin mutane suna wa Ba'al sujada sun ɗauke shi allahn rana kuma Ashera ko Ashtoret allahiyar wata.
  • Allah ya umarci Isra'ilawa su lalata duk sassaƙaƙƙun siffofi na Ashera.
  • Wasu shugabannin Isra'ilawa kamar su Gidiyon, Sarki Asa, da Sarki Yosiya sun yi biyayya da Allah suka shugabanci mutane a lallatar da waɗannan gumaku.
  • Amma wasu shugabannin Isra'ilawa kamar Sarki Suleman, Sarki Manasse, da Sarki Ahab basu kawar da ‌ginshiƙan Ashera ba amma suka iza mutane su yiwa waɗannan gumaku sujada.

(Hakanan duba: allahn ƙarya, Ba'al, Gidiyon, siffa, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:04
  • 2 Sarakuna 21:03
  • Ishaya 27:9
  • Littafin Alƙalai 03:7-8
  • Mika 05:14

Ashkelon

Gaskiya

A lokacin Littafi Mai Tsarki, Ashkelon wani babban birnin Filistiya ne a gaɓar Tekun Baharmaliya. Har wa yau tana nan a Isra'ila.

  • Ashkelon ɗaya ce daga cikin shahararrun birane biyar na Filistiyawa tare da Ashdod, Ikron, Gat, da Gaza.
  • Isra'ilawa basu ci dukkan mutanen Ashkelon a yaƙi ba, koda shike masarautar Yahuda ta mallaki ƙasar tuddansu.
  • Ashkelon ta kasance ƙarƙashin Filistiyawa ɗaruruwan shekaru.

(Hakanan duba: Ashdod, Kan'ana, Ekron, Gat, Gaza, Filistiyawa, Baharmaliya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 06:17-18
  • Amos 01:8
  • Irmiya 25:19-21
  • Yoshuwa 13:2-3
  • Littafin Alƙalai 01:18-19
  • Zakariya 09:05

Asiriya, Ba'asiriye, Asiriyawa, Daular Asiriya

Gaskiya

Asiriya al'umma ce ƙaƙƙarfa lokacin da Isra'ilawa ke zaune a ƙasar Kan'ana. Daular Asiriya ƙungiyoyin wasu al'ummai ne da sarkin Asiriya ya yi mulkinsu.

  • Al'ummar Asiriya ta zauna ne a yankin da yanzu shi ne arewacin Iraƙi.
  • Asiriyawa sun yaƙi Isra'ilawa a lokuta daban-daban bisa ga tarihi.
  • A shekara ta 722 BC, Asiriyawa suka cinye mulkin Isra'ila gabaɗaya suka tilasta wa Isra'ilawa da yawa su tafi Asiriya da zama.
  • Ragowar Isra'ilawa suka shiga auratayya da baƙin da Asiriyawa suka kawo cikin Isra'ila daga Samariya. Zuriyar mutanen da suka auri baƙi sune daga baya aka kira su Samariyawa.

(Hakanan duba: Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:11
  • Farawa 25:17-18
  • Ishaya 07:16-17
  • Irmiya 50:17
  • Mika 07:11-13

Asiya

Gaskiya

A lokacin LIttafi Mai Tsarki, "Asiya" sunan wani lardi ne na mulkin Roma. Wurin yana yamma da ƙasar da yanzu ake ce da ita Toki ko Turkaniya.

  • Bulus ya yi tafiya a Asiya yana yaɗa bishara a birane da yawa. Wasu daga cikin biranen sune Afisa da Kolosse.
  • Domin kada a sami ruɗanya da Asiya ta wannan zamanin, zai zamana tilas a fassara ta haka, " lardin Asiya a zamanin dã ta Roma" ko "Lardin Asiya."
  • Dukkan ikilisiyoyi da aka ambata a Wahayin Yahaya suna daga lardin Asiya ta Roma.

(Hakanan duba: Roma, Bulus, Afisawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 16:19-20
  • 1 Bitrus 01:1-2
  • 2 Timoti 01:15-18
  • Ayyukan Manzanni 06:8-9
  • Ayyukan Manzanni 16:07
  • Ayyukan Manzanni 27:1-2
  • Wahayin Yahaya 01:4-6
  • Romawa 16:05

Ataliya

Gaskiya

Ataliya muguwar matar Yehoram sarkin Yahuda ce. Ita jikar mugun Sarki Omri na Isra'ila ne.

  • ‌Ɗan Ataliya wato Ahaziya ya zama sarki bayan Yehoram ya rasu.
  • Sa'ad da ɗanta Ahaziya ya rasu, Ataliya ta shirya ta kashe dukkan sauran iyalin sarki.
  • Amma ɗan ƙaramin jikan Ataliya Yowash wata antinsa ta ɓoye shi ta cece shi daga mutuwa. A ƙarshe ya zama sarkin Yahuda.

(Hakanan duba: Ahaziya, Yehoram, Yowash, Omri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 22:02
  • 2 Tarihi 24:6-7
  • 2 Sarakuna 11:03

Atazazas

Gaskiya

Atazazas sarki ne da ya yi sarauta bisa ƙasar Fasiya daga misalin 464 zuwa 424 BC.

  • A mulkin Atazazas, Isra'ilawa daga Yahuda suna bautar talala a Babila wadda take ƙarƙashin mulkin Fasiya a lokacin.
  • Atazazas ya yaddar wa Ezra firist da wasu shugabannin Yahudawa su bar Babila su koma Yerusalem su koya wa Isra'ilawa Shari'ar Allah.
  • Daga baya a wannan lokaci, Atazazas ya yardar wa Nehemiya mai ƙoƙon shayarwarsa a fãda ya koma Yerusalem ya bida Yahudawa domin a sake gina garu kewaye da birnin.
  • Saboda Babila tana ƙarƙashin mulkin Fasiya, Atazazas wani lokaci ana kiransa "sarkin Babila."
  • A lura cewa Atazazas daban yake da Zazas (Ahasurus).

(Hakanan duba: Ahasurus, Babilon, mai ƙoƙon shayarwa, Ezra, Nehemiya, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 04:7-8
  • Ezra 07:1-5
  • Nehemiya 02:01
  • Nehemiya 13:6-7

Ayuba

Gaskiya

Ayuba mutum ne da aka yi bayaninsa a Littafi Mai tsarki a matsayin marar aibi mai adalci ne kuma a gaban Allah. Anfi saninsa domin jurewarsa a cikin bangaskiyarsa ga Allah a cikin lokuttan wahala mai tsanani.

  • Ayuba yayi zama a ƙasar Uz, wadda ke wani waje gabas da ƙasar Kan'ana, watakila kusa da lardin Idomiyawa.
  • Anyi tunanin cewa yayi rayuwa a zamanin Isuwa da Yakubu saboda ɗaya daga cikin abokan Ayuba shi "Batimaniye ne," wanda wata ƙungiyar mutane ce da aka yiwa suna bisa ga sunan jikan Isuwa.
  • Littafin Ayuba a Tsohon Alƙawari ya zance game da yadda Ayuba da wasu suka dubi wahalarsa. Ya kuma bada yadda Allah a matsayin mahaliccin kowa da mai mulkin ko'ina ya kalli al'amarin.
  • Bayan dukkan bala'o'in, daga bisani Allah ya warkar da Ayuba ya kuma sake ba shi 'ya'ya da dukiya.
  • Littafin Ayuba na cewa ya tsufa sosai sa'ad da ya mutu.

(Hakanan duba: Ibrahim, Isuwa, ruwan ambaliya wato tsufana, Yakubu, Nuhu, ƙungiyar mutane)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 14:12-14
  • Yakubu 05:9-11
  • Ayuba 01:01
  • Ayuba 03:05

Azariya

Gaskiya

Azariya sunan mutane ne da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Wani Azariya an fi saninsa da sunansa na Babila, Abenego. Shi yana ɗaya daga cikin Isra'ilawa da yawa daga Yahuda waɗanda sojojin Nebukadnezza suka kama suka kai Babila da zama. Azariya da 'yan'uwansa Isra'ilawa Hananiya da Mishayel suka ƙi su yi wa sarkin Babila sujada, sai yasa aka jefa su cikin tanderun wuta don a hukunta su. Amma Allah ya kare su basu ƙone ba ko kaɗan.
  • Uziya sarkin Yahuda an san shi da sunan nan "Azariya."
  • Wani Azariya a cikin Tsohon Alƙawari babban firist ne.
  • A lokacin annabi Irmiya, wani mutum ana ce da shi Azariya ya tunzura Isra'ilawa su yi rashin biyayya ga Allah ta wurin barin ƙasarsu.

(Hakanan duba: Babila, Daniyel, Hananiya, Mishayel, Irmiya, Uziya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:38
  • 1 Sarakuna 04:02
  • 2 Tarihi 15:01
  • Daniyel 01:6-7
  • Irmiya 43:02

Ba'al

Gaskiya

Ma'anar "Ba'al" shi ne "ubangiji" ko "maigida" kuma sunan babban gunkin da Kan'aniyawa suke bautawa ne.

  • Akwai kuma allolin gida da mahaɗin sunayensu "Ba'al" ne, kamar "Ba'al na Feyo." Wani lokaci dukkan waɗannan alloli ana ce da su "Ba'aloli."
  • Wasu mutane sunayensu na da wannan kalma "Ba'al" a ciki.
  • Akwai mugayen halaiya a cikin sujada ga Ba'al kamar su yin hadaya da yara da kuma amfani da karuwai.
  • A lokatai daban-daban a tarihinsu, Isra'ilawa suma suka dulmiya cikin yiwa Ba'al sujada, suka bi tafarkin al'ummai matsafa dake kewaye da su.
  • A lokacin sarautar Ahab, annabin Allah Iliya ya kawo ƙalubale domin ya tabbatar wa mutane cewa babu Ba'al, kuma Yahweh ne kaɗai Allahn gaske. Sakamakon haka, aka hallakar da dukkan annabawan Ba'al sai kuma mutane suka fara yiwa Yahweh sujada.

(Hakanan duba: Ahab, Ashera, Iliya, allahn ƙarya, karuwa, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 16:31
  • 1 Sama'ila 07:3-4
  • Irmiya 02:7-8
  • Littafin Alƙalai 02:11
  • Littafin Lissafi 22:41

Ba'amoriye, Amoriyawa

Gaskiya

Amoriyawa ƙungiyar ƙarfafan mutane ne waɗanda suka fito daga zuriyar jikan ɗan Nuhu Kan'ana.

  • Ma'anar sunansu "Mai tsayi" mai yiwuwa ana nufin yankin duwatsu inda mazauninsu yake ko kuma saboda an san su dogaye ne a tsayi.
  • Amoriyawa sun zauna a yankin kowanne ɓarayin Kogin Yordan. Mazaunan birnin Ai Amoriyawa ne.
  • Allah ya ambaci "zunubin Amoriyawa" waɗanda suka haɗa da bautar gumaku da duk irin zunubin dake tafe da wannan.
  • Yoshuwa ya shugabanci hallakar da Amoriyawa, kamar yadda Allah ya umarce su suyi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 02:09
  • Ezekiyel 16:03
  • Farawa 10:16
  • Farawa 15:14-16
  • Yoshuwa 09:10

Ba'asha

Gaskiya

Ba'asha ɗaya daga cikin mugayen sarakunan Isra'ila ne, wanda ya tunzura Isra'ilawa su yi sujada ga alloli.

  • Ba'asha shi ne sarki na uku na Isra'ila kuma ya yi sarauta shekara ashirin da huɗu, lokacin da Asa ke sarauta a Yahuda.
  • Shi hafsan sojoji ne wanda ya zama sarki ta wurin kashe sarki Nadab dake kan gadon sarauta a lokacin.
  • A lokacin sarautar Ba'asha an yi yaƙe-yaƙe da yawa tsakanin mulkin Isra'ila dana Yahuda, musamman da Sarki Asa na Yahuda.
  • Sabili da zunuban Ba'asha masu yawa Allah ya cire shi daga sarauta ta wurin mutuwarsa.

(Hakanan duba: Asa, allahn ƙarya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 15:17
  • 2 Sarakuna 09:09
  • Irmiya 41:09

Babel

Gaskiya

Babel babban birni ne a yankin da ake ce da shi Shina a kudancin Mesofotamiya. Daga bisani aka kira Shina Babiloniya.

  • Wannan birnin Babel jikan ɗan Ham da ake ce da shi Nimrod ya kafa ta, wanda ya yi mulkin yankin Shina.
  • Mutanen Shina suka yi girman kai suka shirya su gina hasumiya mai tsayi da zai kai sama. Daga baya wannan wuri aka san shi da "Hasumiyar Babila."
  • Saboda mutane maginan hasumiyar suka ƙi su warwatsu kamar yadda Allah ya umarta, sai ya dama harsunansu har suka kasa fahimtar junansu. Wannan ya tilasta masu su tashi su bar gun su tafi su zauna a wurare daban-daban dukkan bangon duniyan nan.
  • Tushen ma'ananr kalmar nan "Babel" shi ne "rikirkicewa," an bada sunan lokacin da Allah ya rarraba ko ya dama harsunan mutane.

(Hakanan duba: Babila, Ham, Mesofotamiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:8-10
  • Farawa 11:09

Babila, Babiloniya, Babiloniye, Babiloniyawa

Gaskiya

Birnin Babila shi ne babban birnin ƙasar Babila ta dã, wanda shima ɓangaren Mulkin Babila ne.

  • Babila ta kasance a gaɓar Kogin Yufiretis, a wajen da aka gina Hasumiyar Babila shekaru aru aru da suka wuce.
  • Wani lokaci wannan kalma "Babila" na nufin dukkan ƙasar Mulkin Babila. Misali, "sarkin Babila" ya yi mulkin dukkan ƙasar, ba birnin kaɗai ba.
  • Babiloniyawa ƙarfafan ƙunguyoyin mutane ne da suka hari sarautar Yahuda suka riƙe mutanen cikin bautar talala a Babiloniya har shekaru 70.
  • Wani sashen wannan ƙasa ana kiransa "Kaldiya" mazaunan wurin ana ce da su "Kaldiyawa." Saboda haka ne wannan kalma "Kaldiya" yawancin lokaci ana kira Babiloniya da shi.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kalmar nan "Babila" ana amfani da ita a kamanta wurare, mutane, da kuma yanayin tunanin mutane game da bautar gumaka da wasu halayen zunubi.
  • Wannan faɗar "Babila Babba" ko "babban birnin Babila" na nufin birni ko al'umma dake da girma, mai wadata, masu zunubi, kamar yadda tsohon birnin Babila na dã yake.

(Hakanan duba: Babel, Kaldiya, Yahuda, Nebukadnezza)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:01
  • 2 Sarakuna 17:24-26
  • Ayyukan Manzanni 07:43
  • Daniyel 01:02
  • Ezekiyel 12:13
  • Matiyu 01:11
  • Matiyu 01:17

Bahibite, Hibitiyawa

Gaskiya

Hibitiyawa su ne ɗaya daga cikin manyan ƙungiyoyin mutane da ke zama a ƙasar Kan'ana.

  • Dukkan waɗannan ƙungiyoyin, sun haɗa da Hibitiyawa, sun kasance ne daga Kan'ana, wanda ya kasance jikan Nuhu.
  • Shekem Bahibite ya yiwa Dina 'yar yakubu fyɗe, ɗan'uwanta kuma ya kashe Hibitiyawa da yawa a matsayin ramako.
  • Lokacin da Yoshuwa ya jagoranci Isra'ilawa su mallaki ƙasar Kan'ana, Isra'ilawa sun yi kasadar ƙulla ƙawance da Hibitiyawa a memakon mamaye su.

(Hakanan duba: Kan'ana, Hamor, Nuhu, Shekem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 08:7-8
  • Fitowa 03:7-8
  • Farawa 34:2
  • Yoshuwa 09:1-2
  • Littafin Alƙalai 03:1-3

Bahitte, Hittiyawa

Gaskiya

Hittiyawa su ne zuriyar Ham ta wurin ɗansa Kan'ana. Sun zama babbar daula da ke a wurin da yau ake kira Turkiyya da kuma arewacin Filistiya.

  • Ibrahim ya kawo ɗan yankin mallaka daga Efron Bahitte domin ya bisne marigayiyar matarsa Sera a cikin kogo a can.
  • Iyayen Isuwa sun damu a lokacin da Isuwa ya auro matan Hittiyawa guda biyu.
  • Ɗaya daga cikin manyan jarumawan Dauda sunansa Yuriya Bahitte.
  • Waɗansu daga cikin bãƙi da Suleman ya auro Hittiyawa ne. Waɗannan bãƙin mata suka karkatar da zuciyar Suleman daga Allah sabo da allohlin ƙarya da suka bautawa
  • Har kusan kullum Hittiyawa sun kasance barazana ga Isra'ilawa, a zahirance da kuma a ruhaniyance.

(Hakanan duba: zuriya, Isuwa, bãƙo, Ham, maɗaukaki, Suleman, Uriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 09:20-21
  • Fitowa 03:7-8
  • Farawa 23:11
  • Farawa 25:10
  • Yoshuwa 01:4-5
  • Nehemiya 09:8
  • Littafin Lissafi 13:27-29

Bal'amu

Gaskiya

Bal'amu wani ba'al'ummen annabi ne wanda Sarki Balek ya yi hayarsa ya la'anta Isra'ila sa'ad da suka kafa zango a Kogin Yordan a arewacin Mowab, sa'ad da suke shirin shiga ƙasar Kan'ana.

  • Bal'amu yana daga birnin Feto, wanda ya kasance wajen Kogin Yufiretis, wajen mil 400 daga ƙasar Mowab.
  • Sarkin Midiyawa, Balek ya tsorata da ƙarfin Isra'ilawa da yawansu shi ne ya yiwo hayar Bal'amu ya la'anta su.
  • Da Bal'amu ke tafiya wurin Isra'ila, mala'ikan Allah ya tsaya akan hanyarsa sai jakin Bal'amu ya tsaya. Allah kuma ya ba jakin iya magana ga Bal'amu.
  • Allah bai bari Bal'amu ya la'anta isra'ilawa ba maimakon haka ya umarce shi ya sa masu albarka.
  • Daga baya, Bal'amu ya kawo mugunta akan Isra'ilawa ya tunzura su suyi sujada ga gunkin Ba'al-feyo.

(Hakanan duba : albarka, Kan'ana, la'ana, jaki, Kogin Yufiretis, Kogin Yodan, Midiyan, Mowab, Feyo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:16
  • Maimaitawar Shari'a 23:3-4
  • Yoshuwa 13:22-23
  • Littafin Lissafi 22:05
  • Wahayin Yahaya 02:14

Barabas

Gaskiya

Barabas ɗan kurkuku ne a Yerusalem lokacin da aka kama Yesu.

  • Barabas ɗan fashi ne wanda ya yi laifin kisan kai da tawaye gãba da gwamnatin Roma.
  • Sa'ad da Fontus Bilatus ya bada zaɓi ya saki Barabas ko Yesu, mutane suka zaɓi Barabas.
  • Sai Bilatus ya saki Barabas ya tafi baratacce, amma ya yanke wa Yesu hukuncin kisa.

(Hakanan duba: Bilatus, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 18:40
  • Luka 23:19
  • Markus 15:07
  • Matiyu 27:15-16

Barnabas

Gaskiya

Barnabas ɗaya ne daga cikin Kiristoci na farko da suka kasance tare da manzanni.

  • Barnabas Ba'isra'ile ne na kabilar Lebi kuma daga tsibirin Sifuros.
  • Sa'ad da Shawulu (Bulus) ya zama Kirista, Barnabas ya matsa wa masu bada gaskiya su karɓe shi a matsayin ɗan'uwa mai gaskatawa.
  • Barnabas da Bulus sun yi tafiya tare wajen yaɗa bishara mai daɗi game da Yesu cikin birane daban-daban.
  • Sunansa Yosef, amma ana kiransa "Barnabas," ma'ana "ɗan ƙarfafawa."

(Hakanan duba: Kirista, Saifuros, labari mai daɗi, Lebi, Bulus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:36
  • Ayyukan Manzanni 11:26
  • Ayyukan Manzanni 13:03
  • Ayyukan Manzanni 15:33
  • Kolosiyawa 04:10-11
  • Galatiyawa 02:9-10
  • Galatiyawa 02:13

Bartalomiyo

Gaskiya

Bartalomiyo ɗaya ne daga cikin almajiran Yesu guda sha biyu.

  • An aiki Bartalomiyo tare da sauran manzanni, su tafi su yaɗa bishara su yi al'ajibai cikin sunan Yesu.
  • Yana kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka ga Yesu ya koma sama.
  • Bayan 'yan sati da dama da faruwar wannan, yana tare da sauran manzanni a Yerusalem ranar Fentikos sai Ruhu Mai Tsarki ya sabko masu.

(Hakanan duba: manzo, labari mai daɗi, Ruhu Mai Tsarki, al'ajibi, Fentikos, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Luka 06:14-16
  • Markus 03:17-19

Baruk

Gaskiya

Baruk sunan mutane ne da dama a Tsohon Alƙawari.

  • Wani Baruk (ɗan Zabbal) ya yi aiki da Nehemiya wajen gyara garun Yerusalem.
  • Kuma lokacin Nehemiya, wani Baruk kuma (ɗan Kol-Hoze) yana ɗaya daga cikin shugabanni da suka zauna a Yerusalem bayan an gyara garunta.
  • Wani Baruk daban (ɗan Neriya) mataimaki ne ga annabi Irmiya, wanda ya taimake shi cikin ayyuka iri-iri kamar su rubuta saƙonni da Allah ya ba Irmiya sa'annan ya karanta wa mutane.

(Hakanan duba: manzo, Irmiya, Yerusalem, Nehemiya, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 32:12
  • Irmiya 36:04
  • Irmiya 43:1-3

Bashan

Gaskiya

Bashan wani yankin ƙasa ne gabas da Tekun Galili. Shi ne mamaye wajen da yau ake ce da shi Siriya da kuma Tuddan Golan.

  • A Tsohon Alƙawari birnin mafaka da ake ce da shi "Golan" a wannan yankin Bashan yake.
  • Bashan ƙasa ce mai armashi sananniya domin itatuwan riminta da makiyayar dabbobi.
  • A Farawa 14 an rubuta cewa Bashan wurin yaƙi ne tsakanin sarakuna da yawa da al'ummarsu.
  • A lokacin da Isra'ilawa suke yawo a jeji bayan fitowarsu daga Masar, sun ƙwace wani ɓangaren yankin Bashan.
  • Bayan shekaru da dama, Suleman ya samo kayayyaki daga wannan yanki.

(Hakanan duba: Masar, rimi, Tekun Galili, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:13
  • Amos 04:01
  • Irmiya 22:20-21
  • Yoshuwa 09:10

Bashti

Gaskiya

A cikin lIttafin Tsohon Alƙawari na Esta, Bashti matar Ahaserus, sarkin Fasiya ce.

  • Sarki Ahaserus ya kori Sarauniya Bashti sa'ad da ta ƙi yin biyayya da umurninsa zuwa nuna kyaunta ga bugaggun bãƙinsa.
  • Ta dalilin haka kuwa, aka yi neman sabuwar sarauniya da haka aka zaɓi Esta ta zama sabuwar matar sarki.

(Hakanan duba: Ahaserus, Esta, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Esta 01:9-11
  • Esta 02:1-2
  • Esta 02:17-18

Batsheba

Gaskiya

Batsheba matar Yuriya ce, shi sojane a rundunar Sarki Dauda. Bayan mutuwar Yuriya, ta zama matar Dauda, da kuma mahaifiyar Suleman.

  • Dauda ya yi zina da Batsheba sa'ad da take auren Yuriya.
  • Da Batsheba ta ɗauki cikin yaron Dauda, Dauda ya sa aka kashe Yuriya a yaƙi.
  • Sa'an nan Dauda ya auri Batsheba sai suka haifi ɗansu.
  • Allah ya hukunta Dauda saboda zunubinsa yadda ya sa ɗan ya mutu bayan 'yan kwanaki da haihuwa.
  • Bayan wannan, Batsheba ta haifi wani ɗan, Suleman, wanda ya girma ya zama sarki a madadin Dauda.

(Hakanan duba: Dauda, Suleman, Yuriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:4-5
  • 1 Sarakuna 01:11
  • 2 Sama'ila 11:03
  • Zabura 051:1-2

Belzebul

Gaskiya

Belzebul wani suna ne na Shaiɗan ko mugun ruhu. Wani lokaci ana rubuta shi haka "Belzebub."

  • Wannan suna ma'anarsa "ubangijin ƙudaje" ma'ana "mai mulki akan mugayen ruhohi." Amma ya fi kyau a fassara wannan kalma da yadda aka rubuta ta da farko maimakon a fassara ma'anarsa.
  • Za a iya fassara ta kuma haka "Belzebul mugun ruhu" domin a tabbatar ko wanene ake ambata.
  • Wannan suna yana da dangantaka da sunan gunkin nan "Ba'al-zebub" na Ekron.

(Hakanan duba: aljani, Ekron, Shaiɗan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 11:15
  • Markus 03:22
  • Matiyu 10:25
  • Matiyu 12:25

Benaiya

Gaskiya

Benaiya sunan mutane ne da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Benaiya ɗan Yehoyida ɗaya daga cikin jarumawan Dauda ne. ‌Ƙwararren mayaƙi ne da aka sa shi shugaban matsaran Dauda.
  • Lokacin da ake naɗa Suleman sarki, Benaiya ya taimake shi tumbuke maƙiyansa. Daga bisani ya zama hafsan rundunar mayaƙan Isra'ila.
  • Wasu mazaje a cikin Tsohon Alƙawari masu suna Benaiya har da Lebiyawa uku: da firist, da mawaƙi, da wani zuriyar Asaf.

(Hakanan duba: Asaf, Yehoyida, Balebi, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 04:36
  • 1 Sarakuna 01:08
  • 2 Sama'ila 23:20-21

Benyamin

Gaskiya

Benyamin shi ne autan da aka haifa wa Yakubu da shi da matarsa Rahila. Ma'anar sunansa "ɗan hannun damana."

  • Da shi da wansa Yosef sune kaɗai 'ya'yan Rahila, wacce ta rasu bayan haihuwar Benyamin.
  • Zuriyar Benyamin suka zama ɗaya daga cikin kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
  • Sarki Saul yana daga kabilar Benyamin ta Isra'ila.
  • Manzo Bulus ma yana daga kabilar Benyamin.

(Hakanan duba: Isra'ila, Yakubu, Yosef (Tsohon Alƙawari), Bulus, Rahila, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:1-2
  • 1 Sarakuna 02:08
  • Ayyukan Manzanni 13:21-22
  • Farawa 35:18
  • Farawa 42:04
  • Farawa 42:35-36
  • Filibiyawa 03:4-5

Beriya

Gaskiya

A lokacin Sabon Alƙawari, Beriya (ko Berowa) birni ne mai wadata a kudu maso gabas da Makidoniya, kusan kilo mita 80 kudu da Tassalonika.

  • Bulus da Silas sun gudu zuwa Beriya bayan abokansu Kiristoci sun taimake su suka kubce daga wasu Yahudawa waɗanda suka tada tarzoma a Tassalonika.
  • Da mutanen Beriya suka ji Bulus yana wa'azi, suka bincike Nassi su tabbatar cewa abin da yake gaya masu gaskiya ne.

(Hakanan duba: Makidoniya, Bulus, Silas, Tassalonika)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 17:11
  • Ayyukan Manzanni 17:13-15
  • Ayyukan Manzanni 20:04

Bet Shemes

Gaskiya

Bet Shemes sunan wani birnin Kan'aniyawa ne kimamin kilomita 30 yamma da Yerusalem.

  • Isra'ilawa suka kama Bet Shemes a lokacin da Yoshuwa yake shugabanci.
  • Bet shemes birni ne da aka keɓe domin firistoci Lebiyawa su zauna.
  • Lokacin da Filistiyawa suke mayar da akwatin alƙawari da suka kama zuwa Yerusalem, Bet shemes shi ne birnin da suka fara tsayawa da shi.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, Kan'ana, Yerusalem, Yoshuwa, Balebi, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:09
  • 1 Sama'ila 06:09
  • Yoshuwa 19:20-21
  • Littafin Alƙalai 01:33

Betani

Gaskiya

Garin Betani yana gabashin gangaren Tsaunin Zaitun, misalin mil 2 gabas da Yerusalem.

  • Betani tana kusa da hanyar da ta bi tsakanin Yerusalem da Yariko.
  • Yawancin lokaci Yesu yakan ziyarci Betani inda abokansa na kusa su La'azaru, Marta da Maryamu suke zama.
  • Anfi sanin Betani musamman da wurin da Yesu ya tada La'azaru daga matattu.

(Hakanan duba: Yeriko, Yerusalem, La'azaru, Marta, Maryamu ('yar'uwar Marta), Tsaunin Zaitun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 01:26-28
  • Luka 24:50-51
  • Markus 11:01
  • Matiyu 21:15-17

Betel

Gaskiya

  • Betel birni ne da yake arewa da Yerusalem a ƙasar Kan'ana. Dã ana ce da shi "Luz."
  • Bayan ƙarɓar alƙawarin Allah na farko, Ibram (Ibrahim) ya gina wa Allah bagadi kusa da Betel. Sunan wurin dama ba Betel bane a lokacin, amma aka saba kiransa Betel wanda aka fi sanin sa da shi.
  • lokacin da yake guje wa ɗan'uwansa Isuwa, Yakubu ya dakata kusa da birnin nan ya kwanta a ƙasa ya yi barci. Da yake barci, sai ya yi mafarki aka nuna masa mala'iku suna hawa sama suna sauka a bisa wani tsani da ya kai sama.
  • Wannan birni ba shi da suna "Betel" sai da Yakubu ya ba shi wannan suna. Domin a gane sosai, wasu masu fassara za su fassara shi su ce "Luz" (daga baya an kira shi Betel) a surorin da aka yi magana akan Ibrahim, da kuma lokacin da Yakubu ya isa can (kafin ya sauya sunan).
  • An faɗi Betel sau da yawa a Tsohon Alƙawari kuma wuri ne da muhimman abubuwa suka faru.

(Hakanan duba: Ibrahim, bagadi, Yakubu, Yerusalem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 12:8-9
  • Farawa 35:01
  • Hosiya 10:15
  • Littafin Alƙalai 01:23

Betlehem, Ifrata

Gaskiya

Betlehem ƙanƙanen birni ne a cikin ƙasar Isra'ila, kusa da birnin Yerusalem. An kuma san shi da sunan nan "Ifrata" wanda watakila sunansa kenan tun farko.

  • Ana kiran Betlehem "birnin Dauda" tunda yake a can aka haifi Sarki Dauda.
  • Annabi Mika ya ce Almasihu zai zo daga "Betlehem Ifrata."
  • Aka cika wannan anabci, sa'ad da aka haifi Yesu a Betlehem bayan shekaru da yawa.
  • Ma'anar sunan nan Betlehem shi ne "gidan gurasa" ko "gidan abinci."

(Hakanan duba: Kaleb, Dauda, Mika)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 35:16
  • Yahaya 07:42
  • Matiyu 02:06
  • Matiyu 02:16
  • Rut 01:02
  • Rut 01:21

Betuwel

Gaskiya

Betuwel ɗan ɗan'uwan Ibrahim ne wanda ana ce da shi Naho.

  • Betuwel mahaifin Rebeka da Laban ne.
  • Akwai kuma wani gari da ake ce da shi Betuwel, wanda watakila yana Yahuda ta kudu ne, ba nisa daga garin Biyasheba.

(Hakanan duba: Biyasheba, Laban, Naho, Rebeka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 04:30
  • Farawa 28:02

Bilatus

Gaskiya

Bilatus gwamnan lardin Yudiya ta Roma ne wanda ya zartar wa Yesu hukuncin mutuwa.

  • Saboda Bilatus ne gwamna, yana da 'yanci ya yanke wa masu laifi hukuncin mutuwa.
  • Shugabannin Yahudawa suna so Bilatus ya gicciye Yesu, saboda haka suka yi ƙarya cewa Yesu mai laifi ne.
  • Bilatus ya lura cewa Yesu ba shi da laifi, amma yana jin tsoron taro kuma yana so ya faranta masu rai, saboda haka ya umarci sojojinsa su gicciye Yesu.

(Hakanan duba: gicciye, gwamna, laifi, Yudiya, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:27-28
  • Ayyukan Manzanni 13:28
  • Luka 23:02
  • Markus 15:02
  • Matiyu 27:13
  • Matiyu 27:58

birnin Dauda

Gaskiya

Wannan furci "birnin Dauda" wani suna ne domin Yerusalem da Betlehem.

  • Yerusalem ita ce inda Dauda ya zauna sa'ad da yayi mulkin Isra'ila.
  • Betlehem ita ce inda aka haifi Dauda.

(Hakanan duba: Dauda, Betlehem, Yerusalem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:1-2
  • 2 Sama'ila 05:6-7
  • Ishaya 22:8-9
  • Luka 02:04
  • Nehemiya 03:14-15

Bitrus, Simon Bitrus, Kefas

Gaskiya

Bitrus yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu guda goma sha biyu. Shi shugaba ne mai mahimmanci a ikilisiya ta farko,

  • Kafin Yesu ya kira shi ya zama almajirinsa, sunan Bitrus Siman ne.
  • Daga baya Yesu ya kira shi "Kefas," ma'ana "dutse" a harshen Aramaik. Ma'anar sunan Bitrus "dutse" a harshen Grik.
  • Allah ya yi aiki ta wurin Bitrus ya warkar da mutane ya kuma yi wa'azin labari mai daɗi akan Yesu.
  • Litattafai biyu a cikin Sabon Alƙawari wasiƙu ne da Bitrus ya rubuta domin ya ƙarfafa ya kuma koyar da 'yan'uwa masu bada gaskiya.

(Hakanan duba: almajiri, manzanni)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08;25
  • Galatiyawa 02:6-8
  • Galatiyawa 02:12
  • Luka 22:58
  • Markus 03:16
  • Matiyu 04:18-20
  • Matiyu 08:14
  • Matiyu 14:30
  • Matiyu 26:33-35

Biyasheba

Gaskiya

A lokacin Tsohon Alƙawari, Biyasheba wani birni ne mil 45 kudu maso yamma da Yerusalem a cikin hamada da yanzu ana ce da ita Negeb.

  • Hamadar dake kewaye da Biyasheba shi ne jejin da Hajaratu da Isma'ila suka yi yawo bayan Ibrahim ya sallame su daga rumfunansa.
  • Ma'anar sunan wannan birni shi ne "rijiyar da aka yi rantsuwa." An bashi wannan suna sa'ad da Ibrahim ya yi rantsuwa zai hukunta mazajen Sarki Abimelek domin sun ƙwace ɗaya daga cikin rijiyoyin Ibrahim.

(Hakanan duba: Abimelek, Ibrahim, Hajaratu, Isma'ila, Yerusalem, rantsuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 03:20
  • 2 Sama;ila 17:11
  • Farawa 21:14
  • Farawa 21:31
  • Farawa 46:01
  • Nehemiya 11:30

Bo'aza

Gaskiya

Bo'aza Ba'isra'ile ne shi ne kuma mijin Rut, mahaifin kakan Sarki Dauda, da kuma zuriyar Yesu Almasihu.

  • Bo'aza yayi rayuwa a zamanin da akwai mahukunta cikin Isra'ila.
  • Shi dangin wata mata ce Ba'isra'ila mai suna Na'omi wadda ta komo Isra'ila bayan mijinta da 'ya'yanta maza sun mutu a Mowab.
  • Bo'aza ya fanshi gwauruwa surukar Na'omi, Rut tawurin aurenta kuma ya ba ta bege da miji da 'ya'ya.
  • Ana duban Bo'aza a misalin hoton yadda Yesu ya ƙwato mu kuma ya fanso mu daga zunubi.

(Hakanan duba: Mowab, fansa, Rut)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:12
  • 2 Tarihi 03:17
  • Luka 03:30-32
  • Matiyu 01:05
  • Rut 02:04

Bulus, Saul

Gaskiya

Bulus shugaba ne na ikilisiya ta farko wanda Yesu ya aike shi ya kai wannan labari mai daɗi zuwa ga wasu ƙungiyoyin mutane da yawa.

  • Bulus Bayahude ne wanda an haife shi cikin birnin Tarsus ta Roma, ya kuma zauna a can domin ɗan ƙasar Roma ne.
  • Tun farko ana kiran Bulus da sunansa na Yahudanci, Saul.
  • Saul ya zama shugaban addinin Yahudawa ya danƙe Yahudawa da suka zama Kirista domin yana tsammani suna nuna rashin bangirma ga Allah ta wurin gaskantawa da Yesu.
  • Yesu ya bayyana kansa ga Saul a wani haske mai makantarwa ya gaya masa ya dena cutar da Kiristoci.
  • Saul ya bada gaskiya ga Yesu sai ya fara koyar da 'yan'uwansa Yahudawa akan Yesu.
  • Daga baya, Allah ya aiki Saul ya koyar da mutanen daba Yahudawa bane akan Yesu, ya kuma fara kafa ikilisiyoyi a birane daban-daban a lardunan mulkin Roma. A wannan lokaci ne aka fara kiransa da sunansa na Romanci "Bulus."
  • Bulus kuma ya rubuta wasiƙu domin ya ƙarfafa ya kuma koyar da Kiristocin dake cikin ikkilisiyoyi a biranen nan. Yawancin wasiƙun nan suna cikin Sabon Alƙawari.

(Hakanan duba: Kirista, shugabannin yahudawa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korantiyawa 01:03
  • Ayyukan Manzanni 08:03
  • Ayyukan Manzanni 09:26
  • Ayyukan Manzanni 13:10
  • Galatiyawa 01:01
  • Filimon 01:08

Damaskus

Gaskiya

Damaskus shi ne babban birnin Siriya. Har yanzu yana nan a wurin da yake a cikin kwanakin Littafi mai tsarki.

  • Damaskus na ɗaya daga cikin tsofafufin birane da har yanzu ake zama a cikin duniya
  • A cikin kwanakin Ibrahim, Damaskus ita ce babbar cibiyar masarautar Aram(yanzu tana ƙasar da ake kira Siriya).
  • A cikin dukkan Tsohon Alƙawari, akwai ayoyi da yawa da ke magana kan cunɗanya tsakanin mazaunan Damaskus da mutanen Isra;ila.
  • Ananbce-anabce da yawa na littafi mai tsarki sun yi anabcin hallakarwar Damaskus. Ana tsammanin an cika wannan anabcin a lokacin da Asiriya ta hallakar da birnin a kwanakin tsohon Alƙawari, ko kuma ace akwai tsammanin kammala ƙarasa rushe wannan birni anan gãba.
  • A cikin Sabon Alƙawari Saul Bafarisiye (wanda aka sani da suna Bulus) yana akan hanyarsa domin kamo masubi a birnin Damaskus a lokacin da yesu ya gamu da shi ya kuma sa shi ya zama mai bi.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 24:23-24
  • Ayyukan Manzanni 09:1-2
  • Ayyukan Manzanni 09: 03
  • Ayyukan Manzanni 26:12
  • Galatiyawa 01:15:-17
  • Farawa 14:15-16

Dan

Gaskiya

Dan shi ne ɗa na biyar a cikin 'ya'yan Yakubu goma sha biyu kuma yana cikin kabilun Isra'ila goma sha biyu.Yankin da kabilar Dan ke zama yana yankin arewacin Kan'ana kuma ana kiran Kan'ama da wannan sunan.

  • A kwanakin Ibram, akwai birnin da ake kira Dan yana yamma da Urshalima.
  • A waɗansu shekaru can baya sai al'ummar Isra'ila ta shiga ƙasar alƙawari,da kuma wani garin na da ban mai suna Dan wanda ke misalin tazarar mil 60 a arewacin Urshalima,
  • Kalmra "Daniyawa na ma'anar zuriyar Dan" waɗanda suma zuriyarsa ne.

(Hakanan duba: Kan'ana, Yerusalem, kabilu sha biyu na Isra'il)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 12:35
  • 1 Sarakuna 04:25
  • Fitowa 01:1-5
  • Farawa 14:14
  • Farawa 30:06

Daniyel

Gaskiya

Daniyel annabi ne Bais'ile ne wanda a matsayinsa na matashi aka kwashe su zuwa bauta har tsawon shekaru 70 ta wurin sarkin Babila mai suna Nebubkadnezar a wajejen shekaru 600 kafin zuwan Almasihu.

  • A wanan lokacin an kame Isra'ilawa da yawa daga Yahuda zuwa bauta a Babila har tsawon shekaru 70.
  • An laƙabawa Daniyel suna Belteshazzar.
  • Daniyel mai daraja ne matashi kuma mai adalci wanda ya yi biyyaya da Allah
  • Allah ya ba Daniyel damar iya fassarar mafarkai da yawa ko kuma wahayi domin sarakuna Babila.
  • Sabo da gwanintarsa da kuma halinsa na daraja, aka ba Daniyel babban aikin shugabanci ko matsayi a cikin mulkin daular Babiloniyawa
  • Bayan shekaru da yawa daga baya, maƙiyan Daniyel suka zura sarkin Babila mai suna Dariyus ya yi doka wadda ta hana bautar kowa sai dai sarki shi kaɗai. Daniyel ya ci gaba da addu'a ga Allah, domin haka aka kama shi aka jefa shi cikin kogon zakoki. Amma Allah ya kuɓutar da shi bai ji ko da ƙwarzanen ciwa ba.

Wuraren da ake samuunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel :01:6-7
  • Daniyel 05: 29
  • Daniyel 07:28
  • Ezekiyel 14:12-14
  • Matiyu 24:15

Dariyos

Gaskiya

Dariyos sunan sarakuna ne da yawa a yankin Fasiya. Ana tsammanin kalmar "Dariyos" ta sarauta ce sarauta ce ba wai suna ba.

  • "Dariyos Bamade" ne ya yi ta fargabar jefa annabi Daniyel a cikin kogon zakoki a matsayin horo domin bauta wa Allah.
  • "Dariyos Bafasiye" ya sa hannu a aikin sake gina haikali a Yerusalem a kwanakin Ezra da Nehemiya.

(Hakanan duba: Fasiya, Babila, Daniyel, Ezra, Nehemiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 04:4-6
  • Haggai 01:01
  • Nehemiya 12:22
  • Zakariya 01:01

Dauda

Gaskiya

Dauda shi ne sarki na biyu a Isra'ila ya kuma ƙaunaci Allah. Shi ne babban marubucin littafin Zabura.

  • Tun Dauda na ƙaramin yaro yana kiwon tumakin iyalansu, Allah ya zaɓe shi ya zama sarkin Isra'ila na gaba.
  • Dauda ya zama gwarzon mayaƙi ya kuma jagoranci Isra'ila zuwa yaƙi gãba da maƙiyansu. Ya yi nasara da Goliya hakan kuma sananne ne sosai.
  • Sarki Saul ya so ya kashe shi, amma Allah ya kare shi, ya naɗa shi sarki bayan mutuwar Saul.
  • Dauda ya yi wani zunubi mai ban takaici, amma ya tuba Allah kuma ya gafarta masa.
  • Yesu Masihi, ana kiransa "Ɗan Dauda" domin shi zuriyar sarki Dauda ne.

(Hakanan duba: Goliyat, Filistiyawa, Saul (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 17:12 -13
  • 1 Sama'ila 20:34
  • 2 Sama'ila 05: 02
  • 2 Timoti 02:08
  • Ayyukan Manzanni 02: 25
  • Ayyukan Manzanni 13:22
  • Luka 01:32
  • Markus 02:26

Delila

Gaskiya

Delila wata mata ce 'yar falasɗinu wadda Samsin ya ƙaunata sosai, amma ita ba matarsa ba ce.

  • Delila ta fi ƙaunar kuɗi fiye da Samsin.
  • Filistiyawa suka ba Delila cin hanci suns faɗa mata yadda za ta sa ya yi rauni. Lokacin da ƙarfinsa ya tafi, filistiyawa suka kama shi.

(Hakanan duba: rashawa, Filistiyawa, Samsin)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Alƙalai 16:4-5
  • Littafin Alƙalai 16:6-7
  • Littafin Alƙalai 16:10
  • Littafin Alƙalai 16:18

Ekron, Ekroniyawa

Gaskiya

Ekron shi ne babban birnin Filistiyawa, wanda ke da nisan mil tara daga tekun Baharmaliya.

  • Haikalin allahn ƙarya Ba'alzebub ya kasance a Ikron.
  • A lokacin da Filistiyawa suka ƙwace sanduƙin Alƙawari sun kai shi zuwa Ashdod daga baya suka matsar da shi zuwa Gat daga can kuma zuwa Ikro sabo da Allah ya yi ta gallazar mutanen da rashin lafiya da mutuwa a duk birnin da aka kai sandiƙin Alƙawari. Daga baya suka yarda su aikar da shi zuwa Isra'la.
  • Lokacin da Sarki Ahaziya ya faɗo daga benen gidansa ya ji wa kansa rauni, ya yi zunubi sabo da ya je ya tuntuɓi allahn ƙarya Ba'alzebub na Ikron akan cewa ko zai mutu ko kuwa zai rayu daga wanan rauni nasa. Sabo da zunubinsa, Yahweh ya ce zai mutiu.

(Hakanan duba: Ahaziya, sanduƙin alƙawari, Ashdod, Ba'alzebub, allahn ƙarya, Gat, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 05:10
  • Yoshuwa 13:2-3
  • Alƙalai 01:18-19
  • Zakariya 09:5

Elam, Elamawa

Gaskiya

Elam ɗan Shem ne kuma jikan Nuhu.

  • Zuriyar Elam su ake kira "Elamawa" sun kuma zauna a wani yanki da ake kira "Elam"
  • Wanan yanki na Elam yanakudu maso gabas da kogin Tigiris wanda a yanzu haka yana yammacin Iran ne.

(Hakanan duba: Nuhu, Shem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:17-19
  • Ayyukan Manzanni 02:9
  • Ezra 08:4-7
  • Ishaya 22:06

Elisha

Gaskiya

Elisha annabi ne a Isra'ila a lokutan sarakuna da yawa na Isra'ila: Ahab, Ahaziya, Yehoram, Yehu, Yehoahaz, da Yehoash.

  • Allah ya ce da annabi Iliya ya shafe Elisha a matsayin annabi.
  • Da aka ɗauke Iliyata karusar iska Elisha ya zama annabin Allah na Isra'ila.
  • Elisha ya yi mu'ujuzai da yawa, da suka haɗa da warkar da mutum daga Siriya wanda ke da ciwon kuturta, ya kuma tayar da ɗan wata mata daga Shunem.

(Hakanan duba: Iliya, Na'aman, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 19:15-16
  • 2 Sarakuna 03:15
  • 2 Sarakuna 05:8
  • Luka 04:25

Eliyakim

Gaskiya

Eliyakim sunan mutane biyu ne a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Wani mutum mai suna Eliyakim shi ne babban mai kula da fada a ƙarƙashin sarki Hezikiya.
  • Wani sunan Eliyakim suna ne na ɗan sarki Yosiya wanda saikin Masar Neko ya naɗa shi sarkin Yahuda.

(Hakanan duba: Hezikiya, Yehoaikim, Yosiya, Fira'auna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:18
  • 2 Sarakuna 18:26
  • 2 Sarakuna 18:37
  • 2 Sarakuna 23:34-35

Eliyeza

Gaskiya

Eliyeza sunan da dama maza a cikin Littafi Mai Tsarki.

  • Eliyeza shi ne ɗa na uku ga ɗan'uwan Musa Haruna. Bayan Haruna ya mutu, sai Eliyeza ya zama babban firist a Isra'ila.
  • Hakanan Eliyeza sunan ɗaya daga cikin "jarumawan Dauda" ne.
  • Wani Eliyeza ɗin kuma yana ɗaya daga cikin ubanni na Yesu.

(Hakanan duba: Haruna, babban firist, Dauda, mai girma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 24:3
  • Littafin Alƙalai 20:27-28
  • Littafin Lissafi 26:1-2
  • Littafin Lissafi 34:16-18

Elizabet

Gaskiya

Elizabet ita ce mahaifiyar Yahaya mai baftisima. Sunan mijinta Zakariya.

  • Zakariya da Elizabet basu taɓa haihuwa ba, amma a cikin tsufansu, Allah ya yiwa Zakariya da Elizabet cewa za su sami ɗa.
  • Allahya riƙe alƙawarinsa, bada daɗewa ba Zakariya da Elizabet suka sami, ta kuma haifi ɗa. Suka sa masa suna Yahaya.
  • Elizabet kuma dangin Maryamu uwar Yesu ce.

(Hakanan duba: Yahaya (mai Baftisima), Zakariya (Sabon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 01:5
  • Luka 01:24-25
  • Luka 01:41

En Gedi

Gaskiya

En Gedi sunan wani birni ne a a saharar Yahuda kudu maso gabas da Yerusalem.

  • En Gedi na kusa da tafkin Tekun Gishiri.
  • Ɗaya sashe na sunansa na nufin "maɓulɓula" wato ƙoramar da ruwa ke fitowa daga cikin birni zuwa teku.
  • An san En Gedi da ƙyaƙƙyawan kuringa da kuma ƙasa mai dausayi, zai iya yiwuwa sabo da yadda ruwa ke kwarara a wurin ne daga ƙoramar ruwa.
  • A kwai mafaka a En Gedi inda Dauda ya gudu a lokacin da sarki Saul ke fafarar sa.

(Hakanan duba: Dauda, jeji, maɓulɓula, Yahuda, hutu, Tekun Gishiri, Saul (Tsohon Alƙawari), mafaka, kuringa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 20:2
  • Waƙar Suleman 01:12-14

Enok

Gaskiya

Enok sunan mutane biyu ne a Tsohon Alƙawari.

  • Ɗaya Enok ɗin daga zuriyar Set yake. Shi ne baban kakan Nuhu.
  • Wanan Enok ɗin ya yi dangataka ta ƙut da ƙut da Allah kuma lokacin da ya kai shekaru 365 Allah ya ɗauke shi zuwa sama da ransa.
  • Ɗaya Enok ɗin shi ne ɗan Kayinu.

(Hakanan duba: Kayinu, Set)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:3
  • Farawa 05:18-20
  • Farawa 05:24
  • Yahuza 01:14
  • Luka 03:36-38

Esta

Gaskiya

Esta bayahudiya ce da ta zama sarauniya a masauratar Fasiya a lokacin da Babiloniyawa suka kame Yahudawa.

  • Littafin Esta ya bada labarin yadda Ista ta zama matar sarkin fasiya, sarki Ahasurus da kuma yadda Allah ya more ta ta ceci mutanenta.
  • Esta mareniya ce wadda ɗan'uwan mahaifinta mutum mai tsoron Allah Modakai ya goya.
  • Biyayyarta ga wanan uban goyo nata ya temake ta ta zama da biyayya ga Allah.
  • Esta ta yi biyayya ga Allah ya sa ta kasadar ranta domin ta ceci mutanenta, Yahudawa.
  • Tarihin Esta yana nuna yadda Allah mai iko dukkake sarrafa duk abubuwan da ke faruwa a cikin tarihi, musamman kan yadda yake kare mutanensa da kuma yin aiki a cikin waɗanda ke yi masa biyayya.

(Hakanan duba: Ahasurus, Babila, Modakai, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Esta 02:7
  • Esta 02:15
  • Esta 07:1
  • Esta 08:2

Ezekiyel

Gaskiya

Ezekiyel annabi ne na Allah a lokacin bauta lokacin da aka kwashe Yahudawa da yawa ta hanun sojojin babila.

  • Fiye da shekaru ashirin, shi da matarsa suka zauna a Babila kusa da kogi Yahudawa kuma suka riƙa zuwa wurin su saurare shi lokacin da yake faɗar saƙon Allah.
  • Bayan waɗansu abubuwa Ezekiyel ya yi anabci game da rushewar da kuma komowar Yerusalem da kuma haikali.
  • Hakanan ya yi anabci game da mulki mai zuwa na Almasihu.

(Hakanan duba: Babila, Kristi, bauta, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 01:3
  • Ezekiyel 24:24

Ezra

Gaskiya

Ezra wani firist ne na Isra'ilawa a cikin shari'ar yahudawa da ke ƙunshe da tarihi na Isra'ilawa da komawar su Yerusalem da Babila inda Isra'ila ta yi bauta na tsawon shekaru saba'in.

  • Ezra ya rubutawani sashe na tarihin Yahudawa a cikin littafi Mai Tsarki a cikin littafin Ezra. ta yiwu ya rubuta littafin Nehemiya, tun da yake waɗannan littattafan guda biyu tushensu ɗaya ne tun can farko.
  • Bayan Ezra ya dawo Yerusalem ya sake kafa shari'a, tunda yake Isra'ila sun dena kiyaye Asabaci sun kuma yi aurataiya da mata masu bautar gumaka.
  • Ezra kuma ya taimaka domin sake gina haikali, wanda babilawa suka rushe a lokacin da suka kame Yerusalem.
  • A kwai muatane biyu da ake kiran su da suna Ezra waɗanda aka baiyana a cikin Tsohon Alƙawari.

(Hakanan duba: Babila, bauta, Yerusalem, shari'a, Nehemiya, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 07:06
  • Nehemiya 08:1-3
  • Nehemiya 12:01

Fadan Aram

Gaskiya

Fadan Aram sunan wani yanki ne inda iyalin Ibrahim suka zauna kafin su tafi ƙasar Kan'ana. Ma'anar sunan nan "filin Aram" ne.

  • Lokacin da Ibrahim ya bar Haran ta Fadan Aram domin ya tafi ƙasar Kan'ana, yawancin iyalinsa sun tsaya a baya a Haran.
  • Bayan shekaru da yawa, Bawan ibrahim ya tafi Fadan Aram domin ya sama wa Ishaku mata daga cikin yan'uwansa a can ya kuwa sami Rebeka, jikar Betuwel.
  • Yakubu ɗan su Ishaku da Rebeka, shima ya tafi Fadan Aram ya auro 'ya'ya mata biyu na Laban ɗan'uwan Rebeka dake zaune a Haran.
  • Aram, da Fadan Aram, da Aram-Nahariyam, dukka dama yanki guda ne da yanzu a zamanin nan ita ce ƙasar Siriya.

(Hakanan duba: Ibrahim, Aram, Betuwel, Kan'ana, Haran, Yakubu, Laban, Rebeka, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 28:02
  • Farawa 35:09
  • Farawa 46:12-15

Faran

Gaskiya

Faran wata hamada ce ko jeji gabas da Masar kudu kuma da ƙasar Kan'ana. Akwai kuma Tsaunin Faran, wanda mai yiwuwa wani sunan ne kuma na Tsaunin Sinai.

  • Baiwar nan Hajaratu da ɗanta Isma'il suka tafi suka zauna a jejin Faran bayan Saratu ta umarci Ibrahim ya sallame su.
  • Da Musa ya fitar da Isra'ilawa daga Masar, sun wuce ta cikin jejin Faran.
  • Daga Kadesh Barniya ne dake cikin jejin Faran, Musa ya aiki magewaya goma sha biyu su tafi su leƙo ƙasar Kan'ana su kawo rahoto.
  • Jejin Zin yana arewa da Faran kuma jejin Sin na kudu da Faran.

(Hakanan duba: Kan'ana, jeji, Masar, Kadesh, Sinai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsaarki:

  • 1 Sarakuna 11:18
  • 1 Sama'ila 25:1
  • Farawa 21:19-21
  • Littafin ‌Lissafi 10:11-13
  • Littafin ‌Lissafi 13:3-4

Fasiya, Fasiyawa

Gaskiya

Fasiya ƙasa ce wadda ita ma ta zama babbar mulki mai iko wadda Sairus Mai Girma ya kafa a shekara ta 550 BC. ‌Ƙ‌asar Fasiya tana kudu maso gabas da Babiloniya da kuma Asiriya a yankin da yau ake ce da shi Iran.

  • Mutanen Fasiya ana ce da su "Fasiyawa."
  • A ƙarƙashin dokar Sarki Sairus, aka 'yantar da Yahudawa daga bautar talala a Babila aka yardar masu su tafi gida, kuma aka sake gina haikali a Yerusalem, da kuɗin da mulkin Fasiya ya tanada.
  • Sarki Atazazas shi ne mai mulkin sarautar Fasiya lokacin da Ezra da Nehemiya suka koma Yerusalem domin su sake gina ganuwoyin Yerusalem.
  • Esta ta zama sarauniyar mulkin Fasiya lokacin data auri Sarki Ahasurus.

(Hakanan duba: Ahasurus, Atazazas, Asiriya, Babila, Sairus, Esta, Ezra, Nehemiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 36:20
  • Daniyel 10:13
  • Esta 01:3-4
  • Ezekiyel 27:10

Fenihas

Gaskiya

Fenihas sunan mutum biyu ne a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Wani firist mai suna Fenihas yana ɗaya daga cikin jikokin Haruna maza. Yayi gãba sosai da bautar gumaku a Isra'ila.
  • Fenihas ya ceci Isra'ilawa daga annobar da Yahweh ya aika domin ya hukunta su domin sun auri matan Midiyawa suka yi wa allolinsu sujada.
  • Fenihas ya tafi tare da sojojin Isra'ilawa sau da yawa domin su hallaka Midiyawa.
  • Wani Fenihas da aka ambata a Tsohon Alƙawari ɗaya ne daga cikin mugayen 'ya'yan Eli firist a zamanin annabi Sama'ila.
  • Fenihas da ɗan'uwansa Hofni an kashe dukkan su biyun sa'ad da Filistiyawa suka kai wa Isra'ila hari suka sace Akwatin Alƙawari.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, Kogin Yodan, Midiyawa, Filistiyawa, Sama'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 04:04
  • Ezra 08:02
  • Yoshuwa 22:13-14
  • Littafin ‌Lissafi 25:6-7

Feriziyawa

Gaskiya

Feriziyawa suna ɗaya daga cikin kabilun da suke cikin ƙasar Kan'ana. Ba mu da isasshen sani game da waɗannan mutane ko su wane ne kakanninsu ko kuma wane yankin Kan'ana suka zauna a ciki.

  • An ambaci Feriziyawa sau da dama a cikin Tsohon Alƙawari a Littafin Alƙalai, inda aka rubuta cewa Feriziyawa sun yi auratayya da Isra'ilawa suka kuma yaudare su zuwa ga yin sujada ga allolin ƙarya.
  • Muyi la'akari cewa iyalin Ferez, da ake kiran su "Feriziyawa" ƙungiyar mutane ne daban da Feriziyawa. Zai yiwu dole a banbanta rubuta sunayensu domin a fayyace su sosai.

(Hakanan duba: Kan'ana, gumaka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 09:20-21
  • 2 Tarihi 08:7-8
  • Fitowa 03:16-18
  • Farawa 13:07
  • Yoshuwa 03:9-11

Feyo, Tsaunin Feyo, Ba'al Feyo

Gaskiya

Wannan magana "Feyo" da "Tsaunin Feyo" ana ambaton wani tsauni ne dake arewa maso gabas da Tekun Gishiri, a yankin Mowab.

  • Wannan suna "Bet Feyo" sunan wani birni ne, da aka kafa watakila akan tsaunin ko kusa da shi. A nan ne Musa ya rasu bayan da Allah ya nunan masa ‌Ƙasar Alƙawari.
  • "Ba'al Feyo" gunkin Mowabawa ne da suke yi masa sujada akan Tsaunin Feyo. Isra'ilawa suma sun fara yiwa wannan gunki sujada Allah kuma ya hukunta su akai.

(Hakanan duba: Ba'al, gunki, Mowab, Tekun Gishiri, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin ‌Lissafi 23:28-30
  • Littafin ‌Lissafi 31:16-17
  • Zabura 106:28 -29

Filib, mai bishara

Gaskiya

A Ikilisiyar Kirista ta farko a Yerusalem, Filib yana ɗaya daga cikin shugabanni bakwai da aka zaɓa su lura da matalauta Kiristoci masu buƙatu musamman gwauraye.

  • Allah ya yi amfani da Filib ya shaida bishara ga mutane da yawa a garuruwa daban-daban a lardunan Yudiya da Galili, har da wani mutumin Itiyofiya da ya gamu da shi a hanyar jeji zuwa Gaza daga Yerusalem.
  • Bayan shekaru da yawa, Filib yana zama a Siseriya sa'ad da Bulus da abokansa suka sauka a gidansa akan hanyarsu zuwa Yerusalem.
  • Yawancin masu tauhidin Littafi Mai Tsarki sun ɗauka Filib mai bishara daban yake da manzon Yesu mai wannan suna. Wasu yare zasu so su banbanta waɗannan mutane biyu ta wurin sauya rubutun sunayensu domin a fayyace sosai su mutanen nan biyu sun banbanta.

(Hakanan duba: Filib (manzo))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:5-6
  • Ayyukan Manzanni 08:06
  • Ayyukan Manzanni 08:13
  • Ayyukan Manzanni 08:31
  • Ayyukan Manzanni 08:36
  • Ayyukan Manzanni 08:40

Filib, manzo

Gaskiya

Manzo Filib yana ɗaya daga cikin asalin almajiran Yesu guda goma sha biyu. Shi ɗan garin Betsaida ne.

  • Filib ya kawo Nataniyel ga Yesu.
  • Yesu ya tambayi Filib yadda za a sama wa taron mutane sama da 5000 abinci.
  • A cin jibin Idin ‌Ƙetarewa wanda Yesu ya ci da almajiransa, ya yi masu magana akan Allah Ubansa. Filib ya tambayi Yesu ya nuna masu Uban.
  • Wasu yare za su so su rubuta sunan wannan Filib daban da wancan Filib (mai bishara) domin a guje wa ruɗami.

(Hakanan duba: Filib (mai bishara))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:14
  • Yahaya 01:44
  • Yahaya 06:06
  • Luka 06:14
  • Markus 03:17-19

Filifai, Filibiyawa

Gaskiya

Filifai babban birni ne da Roma ta mallaka yana cikin Makidoniya a arewacin tsohuwar Giris.

  • Bulus da Sila sun tafi Filifai suyi wa'azin Yesu ga mutanen.
  • Lokacin da suke a Filifai, aka kama Bulus da Sila amma Allah ya yi abin al'ajibi ya kuɓutar da su.
  • Littafin Sabon Alƙawari na Filibiyawa wasiƙa ce da Bulus ya rubuta wa Kiristoci dake cikin ikilisiya ta Filifai.
  • A yi lura wannan birni daban yake da Siseriya Filifai dake arewa maso gabas da Isra'ila kusa da Tsaunin Hermon.

(Hakanan duba: Siseriya, Kirista, ikkilisiya, Masidoniya, Bulus, Silas)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:1-2
  • Ayyukan Manzanni 16:11
  • Matiyu 16:13-16
  • Filibiyawa 01:01

Filistiya

Gaskiya

Filistiya sunan wani babban yanki ne a ƙasar Kan'ana, an kafa shi a gaɓar Tekun Baharmaliya.

  • Wannan yanki yana wuri mai yalwar amfani a gaɓar filin da ya kai Yoffa arewa zuwa Gaza a kudu. Wajen kilomita 64 a tsawo a faɗi kuma kilomita 16.
  • Filistiyawa ne suka zauna a Filistiya su ƙungiyar mutane ne masu ƙarfi waɗanda kullum abokan gabar Isra'ilawa ne.

(Hakanan duba: Filistiyawa, Gaza, Yoffa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 10:9-10
  • Yowel 03:04
  • Zabura 060:8-9

Filistiyawa

Gaskiya

Filistiyawa wasu ƙungiyar mutane ne da suka zauna a yankin Filistiya a gaɓar Tekun Baharmaliya. Ma'anar sunansu "mutanen teku."

  • Akwai manyan biranen Filistiya guda biyar: Ashdod, Ashkelon, Ekron, Gat, da Gaza.
  • Birnin Ashdod yana arewacin sashen Filistiya, birnin Gaza kuma yana kudunta.
  • Alƙali Samson shahararren mayaƙi ne gãba da Filistiyawa, ya yi amfani da mafificin ƙarfi daga Allah.
  • Sarki Dauda yawancin lokaci yakan kai yaƙi ga Filistiyawa, har da lokacin da yake saurayi ya buge mayaƙin Filistiya, Goliyat.

(Hakanan duba: Ashdod, Ashkelon, Dauda, Ekron, Gat, Gaza, Goliyat, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 18:9-11
  • 1 Sama'ila 13: 04
  • 2 Tarihi 09:25-26
  • Farawa 10:11-14
  • Zabura 056:1-2

Fir'auna, sarkin Masar

Gaskiya

A zamanin dã, sarakunan da suka yi mulki a Masar ana ce da su Fir'aunnoni.

  • Gaba ɗaya duka, fir'aunoni sama da 300 suka yi sarautar Masar fiye da shekaru 2,000.
  • Waɗannan sarakunan Masar masu iko ne da wadata.
  • Da yawa cikin waɗannan fir'aunonin an faɗe su a cikin Littafi Mai Tsarki.
  • Yawancin lokaci wannan muƙamin ana amfani da shi a maimakon suna. Idan haka ya faru akan fara rubutawa da babban harufa kamar haka, "Fir'auna."

(Hakanan duba: Masar, sarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:9-10
  • Ayyukan Manzanni 07:13
  • Ayyukan Manzanni 07:21
  • Farawa 12:15
  • Farawa 40:07
  • Farawa 41:25

Firisilla

Gaskiya

Firisilla da mijinta Akila Kiristoci ne Yahudawa waɗanda suka yi aiki da manzo Bulus a aikinsa na bishara.

  • Firisilla da Akila sun baro Roma saboda mai mulki ya tilasta wa Kiristoci su tashi daga nan.
  • Bulus ya haɗu da Akila da Firisilla a Koranti. Su masu saƙa rumfar gida ne, sai ya haɗa kai da su cikin wannan aiki.
  • Da Bulus ya bar Koranti zai tafi Siriya Firisilla da Akila suka tafi tare da shi.
  • Daga Siriya, su ukun suka tafi Afisa. Da Bulus ya bar Afisa, Firisilla da Akila suka dakata a gun suka ci gaba da aikin yaɗa bishara a can.
  • Sun koyar da wani mutum mai suna Afolos a Afisa wanda ya bada gaskiya ga Yesu kuma shi mai baiwar iya magana ne da karantarwa.

(Duba kuma: gaskatawa, Kirista, Korint, Afisos, Bulus, Roma, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa16:19-20
  • 2 Timoti 04:19-22
  • Ayyukan Manzanni 18:01
  • Ayyukan Manzanni 18:24

Fonishiya, Sarofonishiyawa

Gaskiya

A zamanin dã, Fonishiya al'umma ce mai wadata tana kafe a Kan'ana a gaɓar Tekun Baharmaliya arewa da Isra'ila.

  • Fonishiya ta kasance a yankin ƙasar dake yamma na wanda a yau ita ce ƙasar Lebanon.
  • A lokacin Sabon Alƙawari, cibiyar Fonishiya Taya ce. Wania kuma muhimmin birnin Fonishiya shi ne Sidon. Fonishiya na kusa da Siriya, saboda haka mutane daga wannan yankin ana ce da su "Sarofonishiyawa.
  • Fonishiyawa sanannun masassaƙa ne gwanaye suna amfani da itacen sida dake da yawa a ƙasarsu, domin kuma suna yin launin shunayya mai tsada, suna kuma da baiwar tafiya fatauci akan ruwa. Gwanaye kuma a gina kwale-kwalen ruwa.
  • Wani rubutu na tun farko mutanen Fonishiyawa ne suka ƙagoshi. An yi amfani da shi. Harufofin rubutunsu ya bazu ko'ina saboda cuɗanyarsu da ƙungiyoyin mutane da yawa ta wurin kasuwancinsu.

(Hakanan duba: sida, shunayya, Sidon, Tyre)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 11:19-21
  • Ayyukan Manzanni 15:3-4
  • Ayyukan Manzanni 21:02
  • Ishaya 23:10-12

Fontus

Gaskiya

Fontus wani lardin Roma ne a lokacin mulkin Roma da Ikilisiya ta farko. An kafa ta ne a kudancin gaɓar Baƙin Teku, a arewacin yankin da yanzu ita ce ƙasar Turkaniya ko Toki.

  • Kamar yadda yake a rubuce a littafin Ayyukan Manzanni, mutane da suke daga lardin Fontus suna Yerusalem sa'ad da Ruhu Mai Tsarki ya fara zuwa ga manzanni a Ranar Fentikos.
  • Wani mai bada gaskiya mai suna Akila ya zo ne daga Fontus.
  • Lokacin da Bitrus yake rubuta wa Kiristoci dake warwatse cikin wurare daban-daban na yankin nan, Fontus na ɗaya daga cikin yankunan daya ambata.

(Hakanan duba: Akila, Fentikos)

Wuraren da za ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:1-2
  • Ayyukan Manzanni 02:09

Fotifa

Gaskiya

Fotifa wani mahimmin hakimi ne na fir'aunan Masar a lokacin da aka sayar da Yosef bawa ga wasu Ishma'ilawa.

  • Fotifa ya sayi Yosef daga Ishma'ilawa ya zaɓe shi ya lura da gidansa.
  • Da aka laƙa wa Yosef ƙarya, Fotifa ya jefa Yosef a kurkuku.

(Hakanan duba: Masar, Yosef (Tsohon Alƙawari), Fir'auna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 37:34-36
  • Farawa 39:02
  • Farawa 39:14

Gad

Gaskiya

Gad na ɗaya daga cikin 'ya'yan Yakubu. Hakanan ana kiran Yakubu Isra'ila.

  • Iyalan Gad sun zama ɗaya daga cikin kabilu goma na Isra'ila.
  • Wani mutum kuma da ake kira Gad annabi ne da ya tunkari Dauda a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne sabo da zunubinsa na yin ƙidayar mutanen Isra'ila.
  • Sunayen waɗannan biranen su ne Ba'algad da Migdalgad dukkansu suna kalmomi biyu a asalin fassara ta farko ana rubuta su kamar haka "Ba'al Gad" da "Migdal Gad."

(Hakanan duba: ƙirga, annabi, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:18
  • Fitowa 01:1-5
  • Farawa 30:11
  • Yoshuwa 01:12
  • Yoshuwa 21: 38

Galatiya, Galatiyawa

Gaskiya

A cikin lokacin Sabon Alƙawari Galatiya ta zama babban lardin Roma a yankin tsakiyar ɓangaren da yanzu ake kira ƙasar Turkiyya.

  • Wani ɓangare na Galatiya ya yi iyaka da Baƙin Teku, wanda yake a ɓangaren arewa. Hakanan tana da iyaka da lardin Asiya, Bitiniya, Kafadosiya, Silisiya da Famfiliya.
  • Manzo Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa Kristocin da ke zama a lardin Galatiya. Wanan wasiƙar tana cikin Sabon Alƙawari ita ake kira "Galatiyawa."
  • Ɗaya daga cikin dalilan da suka sa Bulus ya rubuta wasiƙa zuwa ga Galatiyawa shi ne domin ya ƙara jaddada bisharar ceto ta wurin alheri ne ba ta wurin ayuka ba.
  • Yahudawa Masu bi a can cikin kuskure suna koyawa al'ummai masu bi cewa ya zama wajibi ga waɗanda suka bada gaskiya su kiyaye waɗansu shari'u na Yahudawa.

(Hakanan duba: Asiya, imani, Silisiya, labari mai daɗi, Bulus, ayuka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 16:1-2
  • 1 Bitrus 01:1-2
  • 2 Timoti 04:9-10
  • Ayyukan Manzanni 16:6-8
  • Galatiyawa 01:1

Galili, Bagalile, Galilawa

Gaskiya

Galili shi ne yanki mafi yawa a arewacin Isra'ila, yana kudu da Samariya. "Bagalile" shi ne mutumin da ke zama a Galili ko mazaunin Galili.

  • Galili da Samariya da Yudiya su ne manyan lardunan Isra'ila a kwanakin Sabon Alƙawari.
  • Galili tana iyaka da "Tekun Galili" daga gabas.
  • Yesu ya yi rayuwa da kuma girma a garin Nazaret ta Galili.
  • Mafi yawa daga cikin ayukan Yesu da koyarwarsa ya yi su ne a yankin Galili.

(Hakanan duba: Nazaret, Samariya, Tekun Galili)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09:32
  • Ayyukan Manzanni 13:31
  • Yahaya 02:1-2
  • Yahaya 04:3
  • Luka 13:3
  • Markus 03:7
  • Matiyu 02:22-23
  • Matiyu 03:13-15

Gat, Bagatiye, Bagatiyawa

Gaskiya

Gat na ɗaya daga cikin manyan birane biyar na Filistiyawa. Yana nan a arewacin Ekron da kuma gabashin Ashdod da Ashkelon.

  • Gwarzon yaƙin Filistiyawa Goliyat daga birnin Gat yake.
  • A lokacin Sama'ila, Filistiyawa suka sace sanduƙin alƙawari daga Isra'ila suka kai shi haikalin gunkinsu na arna a Ashdod. Daga bisani suka matsar da shi zuwa Gat daga nan sai suka kai shi Ekron. Amma Allah ya hori mutanen biranen da cututtuka sabo da haka suka ɗauke shi suka sake komar da shi Isra'ila.
  • Lokacin da Dauda ke guduwa daga wurin sarki Saul, ya gudu zuwa Gat ya zauna a can na ɗan wani lokaci da matansa biyu da 'ya'yansa shidda da kuma mazajen da ke tare da shi.

(Hakanan duba: Ashdod, Ashkelon, Ekron, Gaza, Goliyat, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 02:39
  • 1 Sama'ila 05:8-9
  • 2 Tarihi 26:6-8
  • Yoshuwa 11:21-22

Gaza

Gaskiya

A kwanakin littafi Mai Tsarki, Gaza ita ce wuri mafi wadata a biranen Filistiyawa garin na gaɓar Tekun Baharmaliya kusa mil 38 a kudancin Ashdod. Yana ɗaya daga cikin manyan biranen Filistiyawa biyar.

  • Sabo da yanayin wurin da take Gaza ta zama wurinsaukar jiragen ruwa inda ayukan kasuwanci ke wakana a tsakanin ƙungiyoyin ƙasashe mabambanta.
  • A yau birnin Gaza har yanzu shi ne mafi muhimmanci a tashoshin jiragen ruwa a wanan yanki, wanda yake a gaɓar Tekun Baharmaliya wanda ke da iyaka da Isra'ila a bangon arewa da kuma gabashi, da kuma Masar a yankin kudu.
  • Gaza shi ne birnin da Filistiyawa suka kai Samsin bayan da suka kame shi.
  • Filibus mai bishara ya yi tafiya a yankin sahara zuwa Gaza a lokacin da ya sadu da bãbã na Habasha.

(Hakanan duba: Ashdod, Filibus, Filistiyawa, Habasha, Gat)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:24-25
  • Ayyukan Manzannni 08:26
  • Farawa 10:19
  • Yoshuwa 10:40-41
  • Littafin Alƙalai 06:3-4

Gerar

Gaskiya

Gerar wani birni ne a yankin ƙasar Kan'ana, yana a kudu maso yamma da Hebron da kumaarewa maso yamma da Biyasheba.

  • Sarki Abimelek shi ne mai mulkin Gerar a lokacin da Ibrahim da Saratu suka zauna a can.
  • FIlistiyawa sune suka mamaye yankin Gerar a lokacin da Isra'ilawa ke zama a Kan'ana.

(Hakanan duba: Abimelek, Biyasheba, Hebron, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 14:12-13
  • Farawa 20:1-3
  • Farawa 26:1
  • Farawa 26:6

Geshur, Geshuriyawa

Gaskiya

A lokacin Sarki Dauda, Geshur wata 'yar ƙaramar masarauta ce wadda ke wajejen gabashin Tekun Galili a tsakanin ƙasashen Isra'ila da Aram.

  • Sarki Dauda ya auri Ma'aka ɗiyar Geshur Sarki, ta haifa masa ɗa mai suna, Absalom.
  • Bayan ya kashe ɗan'uwansa Amnon da suke 'yan turaka Absalom ya gudu zuwa arewa maso gabas daga Yerusalem zuwa Geshur, kusan nisan mil 140. Ya zauna a can na tsawon shekaru uku.

(Hakanan duba: Absalom, Amnon, Aram, Tekun Galili)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:23
  • 2 Sama'ila 03:2-3
  • Maimaitawar Shari'a 03:14
  • Yoshuwa 12:3-5

Getsemani

Gaskiya

Getsemani wani lambu ne na itatuwan zaitun a gabashin Yerusalem a hayin kwarin Kidron kusa kuma da Dutsen Zaitun.

  • Lambun Getsemani wuri ne da Yesu da almajiransa kan je su kaɗaitu su huta ware da taron mutane.
  • A lambun Getsemani ne Yesu a yi addu'a cikin matuƙar ɓacin rai kafin a kama shi a can ta hannun shugabannin Yahudawa.

(Hakanan duba: Yahuza Iskariyoti, Kwarin Kidron, Dutsen Zaitun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Markus 14:32
  • Matiyu 26:36

Gibeya

Gaskiya

Gibeya wani birni ne a arewacin Yerusalem da kuma kudancin Betel.

  • Gibeya na cikin yankin kabilar Benyamin.
  • Ya kasance wani babban fagen daga tsakanin Benyamawa da Isra'ila.

(Hakanan duba: Benyamin, Betel, Yerusalem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 10:26-27
  • 2 Sama'ila 21:6
  • Hosiya 09:9
  • Littafin Alƙalai 19:12-13

Gibiyon, Bagiyone, Gibiyoniyawa

Gaskiya

Gibiyon Gari ne da ke a kusan mil 13 arewa maso yamma na Yerusalem. Mutanen da ke zama a Gibiyon Gibiyoniyawa ne.

  • Da Gibiyoniyawa suka ji yadda Isra'ilawa suka rurrushe biranen Yeriko da Ai sai suka furgita.
  • Sai Gigiyoniyawa suka zo wurin shugabannin Isra'ila a Gilgal sia suka nuna kamar sun zo daga wata ƙasa ne mai nisa.
  • Suka yaudari shugabannin Isra'ila suka ƙulla yarjejeniya da Gibiyoniyawa cewa za su ba su Kariya ba kuma za su kashe su ba.

(Hakanan duba: Gilgal, Yeriko, Yerusalem)

Wuraen da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 08:29
  • 1 Sarakuna 03:4-5
  • 2 Sama'ila 02:12-13
  • Yoshuwa 09:3-5

gidan Dauda

Gaskiya

Batun nan "gidan Dauda" na nufin iyali zuriyar sarki Dauda.

  • Wannan ma za'a iya fassara ta a matsayin "zuriyar Dauda" ko "iyalin Dauda" ko kabilar Sarki Dauda."
  • Saboda da Yesu zuriyar Dauda ne, shi ɗaya ne daga "gidan Dauda."
  • A waɗansu lokutan "gidan Dauda" ko iyalin Dauda" tana nufin mutanen da ke cikiniyalin Dauda da ke raye.
  • A sauran waɗansu lokutan wannan yana fin yin magana ne gaba ɗaya domin ambaton zuriya haɗe ma da waɗanda suka mutu.

(Hakanan duba: Dauda, zuriya, hausa, Yesu, sarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 10:19
  • 2 Sama'ila 03:06
  • Luka 01:69-71
  • Zabura 122:05
  • Zakariya 12:07

Gidiyon

Gaskiya

Gidiyon mutumin Isra'ila ne wanda aka yi renonsa domin ya ceci Isra'ilawa daga maƙiyansu.

  • A wancan lokacin na Gidiyon ke raye, mutanen da ake kira Midiyanawa suna ta kai wa Isra'ilawa hari suna kuma lalatar da amfanin gonakinsu.
  • Ko da yake Gidiyon na jin tsoro Allah ya more shi domin ya jagoranci Isra'ilawa su yi yaƙi gãba da Midiyanawa su kuma yi nasara da su.
  • Gidiyon ya yi biyayya da Allah ta wurin rushe bagadan allohlin ƙarya Ba'al da Ashera.
  • Ba wai jagorancin Isra'ila kawai ya yi ba su yi nasara da maƙiyansu amma har ya ƙarfafa su su yi biyayya da Allah su kuma bauta wa Yahweh, tilon Allah na gaskiya.

(Hakanan duba: Ba'al, Ashera, kuɓutarwa, Midiyan, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 11:32-34
  • Littafin Alƙalai 06:11
  • Littafin Alƙalai 06:23
  • Littafin Alƙalai 08: 17

Gileyad, Bagileye, Gilediyawa

Gaskiya

Gileyad sunan wani yanki ne mai duwatsu a gabashin Kogin Yodan inda kabilar Isra'ila na gidan Gad da Ruben da Manasse suka zauna.

  • Wanan yankin shi ne kuma ake kira "ƙasa mai duwatsu ta Gileyad" ko "dutsen Gileyad."
  • Haka nan Gileyad ya kasance sunaye na mutane da yawa a cikin Tsohon Al‌ƙawari. Ɗaya daga cikinsu shi ne jikan Manasse. Wani Gileyad ɗin kuma shi nemahaifin Yefta.

(Hakanan duba: Gad, Yefta, Manasse, Ruben, kabilun Isra'ila goma sha biyu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:22
  • 1 Sama'ila 11:1
  • Amos 01:3
  • Maimaitawar Shari'a 02:36-37
  • Farawa 31:21
  • Farawa 37:25-26

Gilgal

Gaskiya

Gilgal sunan wani gari ne a arewacin Yeriko shi ne kuma wuri na farko da Isra'ilawa suka yi zango bayan sunƙetare Kogin Yodan domin shiga Kan'ana.

  • A Gilgal ne Yoshuwa ya jera duwatsu sha biyu waɗanda ya kwaso daga busasshen Kogin Yodan.
  • Gilgal shi ne birnin da Iliya da Elisha suka bari a lokacin da suka ƙetare Yodan a lokacin da za'a fyauce Iliya zuwa sama.
  • Akwai wurare da yawa da ake kira "Gilgal" a cikin Tsohon Alƙawari.
  • Kalmar nan "gilgal" ma'anarta ita ce "kewayen dutse" wato ana nufin wurin da aka kewaye da dutse aka gina bagadi.
  • A cikin Tsohon Al‌ƙawari, wanan sunan har kullum yakan baiyana a matsayin "gilgal." Wanan zai iya nuna cewa ba wai wani wuri ne ba kawai, sai dai bayani ne game da wanirin wuri.

(Hakanan duba: Iliya, Elisha, Yeriko, Kogin Yodan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 07:15-17
  • 2 Sarakuna 02:1-2
  • Hosiya 04:15
  • Littafin Alƙalai 02:1

Girgashiyawa

Gaskiya

Girgashiyawa mutane ne da ke zama kusa da Tekun Galili a ƙasar Kan'ana.

  • Su zuriyar Ham ne ɗan Kan'ana domin haka su ne aka fi sani Kan'aniya."
  • Allah ya yi alƙawari zai temaki Isra'ilawa su yi nasara da Girgashiyawa da sauran mutanen Kan'aniyawa.
  • Kamar sauran mutane, Girgashiyawa masu bautar allolin ƙarya suna yin mummunar rayuwa a matsayin wani ɓangare na sujada.

(Hakanan duba: Kan'ana, Ham, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:14
  • Maimaitawar Shari'a 07:1
  • Farawa 10:16
  • Yoshuwa 03:9-11
  • Yoshuwa 24:11-12

Girkanci, Bagirke

Gaskiya

A kwanakin Sabon Alƙawari, Girka wani lardi ne na daular Roma.

  • Kamar ƙasar da ake kira Girka a yau, tana can ne kusa da iyakokin Tekun Baharmaliya, da Tekun Aijiyan da Tekun loniya.
  • Manzo Bulus ya yi ta biranen Girka ya kuma kafa majami'u a biranen Korint, Tassalonika da Filifiya mai yiwuwa da sauran waɗansu.
  • Mutanen da suka zo daga Girka su ake kira Girkawa kuma harshen su shi ne "Girkanci". Hakanan mutane daga sauran lardunan Roma suma suna magana da harshen "Girkanci".

(Hakanan duba: Korint, Al'ummai, Girkawa, Ibraniyawa, Filifiya, Tassalonika)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 08:21
  • Daniyel 10:20-21
  • Daniyel 11:1-2
  • Zakariya 09:13

Girkanci, magana da harshen Girkanci

Gaskiya

Kalmar nan "Girkanci" tana nufin harshen da ake magana da shi a ƙasar Girka. Girka, hakaka nan kalmar zata iya zama da ma'anar mutuminda ya zo daga Girka. Hakanan ana magana da harshen Girkanci a dukkan Daular Roma. Kalmar nan "Girkanci" tana nufin "magana da harshen Girkanci."

  • Tun da yake waɗanda ba Yahudawa ba ne a Daular Roma na magana da harshen Girka, har kullum akan kira al'ummai da "Girkawa" a cikin Sabon Alƙawari musamman in ana batun wanda ba Bayahude ne ba.
  • Kalmar nan "Yahudawan Girka" tana nufin Yahudawan da ke magana da harshen Girka saɓanin "Ibraniyancin Yahudawa" waɗanda ke magana da Ibraniyanci, ko kuma Aremiyanci.
  • Waɗansu hanyoyi da za'a fassara "Girkanci" sun haɗa da, "masu magana da harshen Girka" ko "masu bin al'adun Girkawa" ko kuma "Girkawan kansu."
  • Idan ana magana a kan wanda ba Bayahude ba ne, Girka zata iya zama "al'ummai."

(Hakanan duba: Aram, Al'ummai, Girka, Ibraniyawa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:1
  • Ayyukan Manzanni 09:29
  • Ayyukan Manzanni 11:20
  • Ayyukan Manzanni 14:1-2
  • Kolosiyawa 03:11
  • Galatiyawa 02:3-5
  • Yahaya 07:35

Golgota

Gaskiya

"Golgota" sunan wani wuri ne inda aka gicciye Yesu. Sunansa ya zo ne daga kalmar Aremiyanci wadda ke nufin "Wurin Ƙoƙon Kai."

  • Golgota tana bayan garun birnin Yerusalem, can kusa kusa. Tana nan ne gangaren Dutsen Zaitun.
  • A waɗansu tsofaffin fassarori na juyin Littafi Mai Tsarki na turanci, an fassara Golgota da "Kalfari" wadda aka samo daga Latin wadda ke nufin "ƙoƙon kai."
  • Juyi da yawa na Littafi Mai Tsarki na amfani da kalmar da ta yi kama da "Golgota" tun da yake an riga an baiyana kalmar a wurin.

(Hakanan duba: Aram, Tsaunin Zaitun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 19: 17
  • Markus 15:22
  • Matiyu 27:33

Goliyat

Gaskiya

Goliyat wani ƙaton soja ne a cikin sojojin Filistiyawa wanda Dauda ya kashe.

  • Goliyat ya kai a ƙalla mita biyu zuwa uku na tsawo. Har kullum akan kira shi da gago sabo da shi ƙato ne sosai.
  • Ko da yake Goliyat na da makaman da suka fi na Dauda sosai, Allah ya ba Dauda ƙarfi da ƙwarewa ya yi nasara da Goliyat.
  • An aiyana Isra'ilawa akan sun yi nasara kan Filistiyawa a sakamakon nasarar Dauda bisa Goliyat.

(Hakanan duba: Dauda, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 20:4-5
  • 1 Sama'ila 17:4-5
  • 1 Sama'ila 21:8-9
  • 1 Sama'ila 22: 9-10

Gomora

Gaskiya

Gomara wani birni ne a kwari mai dausayi na kusa da Sodom, inda ɗan ɗan'uwan Ibrahim Lotu ya zaɓi ya zauna.

  • Ba'a san ainahin inda Gomara da Sodom suke ba, amma akwai bayanai da ke nuna cewa sun kasance ne kai tsaye kudu da Tekun Gishiri kusa da kwarin Siddim.
  • Akwai sarakuna da yawa da ke yaƙi a yankin da Sodom da Gomora suka kasance.
  • Lokacin da aka kame iyalin Lotu acikin rikici tsakanin Sodom da waɗansu birane, Ibrahim da mazajensa sun kuɓutar da su.
  • Ba da jimawa ba bayan wanan, Allah ya hallakar da Sodom da Gomora sabo da aikin muguntar mutanen da ke zama a can.

(Hakanan duba: Ibrahim, Babila, Lotu, Tekun Gishiri, Sodom)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:6
  • Farawa 10:19
  • Farawa 14:1-2
  • Farawa 18:21
  • Ishaya 01:9
  • Matiyu 10:15

Goshen

Gaskiya

Goshen sunan wani yanki ne mai albarka a yankin Kogin Nilu a yankin gabashin Masar.

  • A lokacin da Yosef ya zama shugaba a Masar, mahaifinsa da 'yan'uwansa da iyalinsu sun je sun zauna a Goshen domin tsira daga yunwa a Kan'ana.
  • Su da zuriyarsu sun zauna yadda ya kamata a Goshen har fiye da shekaru 400, amma a wancan lokacin aka tilasta su aikin bauta ta hanun sarkin Masar.
  • Daga ƙarshe Allah ya aiko Musa ya temaki mutanen Isra'ila su fita daga ƙasar Goshen su tsira daga bauta.

(Hakanan duba: Masar, yunwa, Musa, Kogin Nilu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 08:22-24
  • Farawa 45:11
  • Farawa 47:2
  • Farawa 50:7-9
  • Yoshuwa 10:40-41

Habakuk

Gaskiya

Habakuk annabi ne na Tsohon Alƙawari wanda ya yi rayuwa a wajejen lokacin da Sarki Yehoa'ikim ke mulkin Yahuda. Shima annabi Irmiya yana da rai a dai-dai wanan lokacin.

  • Annabin shi ne ya rubuta littafin Habakuk a wajejen 600 BC a lokacin da Babilawa suka mamaye Yerusalem suka kwashe mutanen Yahuda da yawa zuwa bauta.
  • Yahweh ya ba Habakuk anabci game da yadda "Kaldiyawa" (Babilawa) za su zo su mamaye mutanen Yahuda.
  • Ɗaya daga cikin fittacen jawabin Habakuk shi ne: "Adalin mutum zai rayu ta wurin bangaskiya."

(Hakanan duba: Babila, Yehoa'ikim, Irmiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Habakuk 01:2

Habila

Gaskiya

Habila ɗa na biyu ne ga Adamu da Hauwa'u.‌ Shi ƙanen Kayinu ne.

  • Habila makiyayi ne.
  • Habila ya yi hadayar wasu dabbobinsa baiko ga Allah.
  • Allah ya gamsu da Habila da baye-bayensa.
  • Kayinu ɗan farin su Adamu da Hawa'u shi ne ya kashe Habila.

(Hakanan duba: Kayinu, hadaya, makiyayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 04:02
  • Farawa 04:09
  • Ibraniyawa 12:24
  • Luka 11:49-51
  • Matiyu 23:35

Haggai

Gaskiya

Haggai annabi ne na Yahuda bayan Yahudawa sun dawo gida daga zaman bautar talala daga Babila.

  • A kwanakin da Haggai ke yin anabci, Sarki Uzziya na sarautar Yahuda.
  • Shima annabi Zakariya yana yin annabci a dai-dai wanan lokacin.
  • Haggai da Zakariya suka gargaɗi Yahudawa da su sake gina haikali, wanda Babilawa suka ragargaje a ƙarƙashin mulkin Sarki Nebukkadnezar.

(Hakanan duba: Babila, Yahuda, Nebukadnezar Uzziya, Zakariya (Tsohon Al‌ƙ‌awari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 05:1-2
  • Ezra 06:13-15

Hajara

Gaskiya

Hajara Bamasariya ce wadda ta zama baiwa ga Saratu.

  • Lokacin da saratu bata sami haihuwa ba, ta bada Hajaratu baiwarta ga mijinta Ibram ta haifa masa 'ya'ya.
  • Hajara ta yi juna biyu ta haifar wa Ibram Isma'ila.
  • Allah ya ya lura da Hajaratu a lokacin da take cikin ƙunci a cikin jeji ya kuma yi alƙawarinsawa zuriyarta albarka.

(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, Isma'ila, Saratu, baiwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:25
  • Farawa 16:1-4
  • Farawa 21:9
  • Farawa 25:12

Ham

Gaskiya

Ham shi ne ɗa na biyu a cikin 'ya'yan Nuhu guda uku.

  • Lokacin da ruwan tsufana ya rufe dukkan duniya, Ham tare da 'yan'uwansa na tare da Nuhu a cikin jirgi tare da matayensu.
  • Bayan ruwan tsufana, akwai wani sha'ani inda Ham ya zama da rashin girmamawa ga mahaifinsa, Nuhu. A sakamakon haka Nuhu ya lla'anta ɗan Ham Kan'ana da dukkan zuriyarsa, waɗanda daga bisani ake kiran su Kan'aniyawa.

(Hakanan duba: jirgi, Kan'ana, rashin girmamawa, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 05:32
  • Farawa 06:10
  • Farawa 07:13-14
  • Farawa 10:1
  • Farawa 10:20

Hamat, Hamitiyawa, Lebo Hamat

Gaskiya

Hamat wani birni ne mai muhimmanci a arewacin Siriya, arewa da ƙasar Kan'ana. Hamitiyawa zuriyar Nuhu ne ɗan Kan'ana.

  • Wanan suna "Lebo Hamat" mai yiwuwa yana nufin dutse ne da ake wucewa ta kusa da shi a kusa da birnin Hamat.
  • Waɗansu fassarori suna fassara "Lebo Hamat" da "mashigizuwa Hamat."
  • Sarki Dauda ya yi nasara da sarkin maƙiyansa wato Sarki Tou na Hamat, hakan ya sa suka zama da zamantakewa mai kyau.
  • Hamat na ɗaya daga ciki gidan ajiya na Suleman inda ake adana kayayyakin masarufi.
  • Ƙasar Hamat ita ce inda aka kashe Sarki Zedekiya ta hanun Sarki Nebukadnezzar da kuma wurin da aka kame Sarki Yehoahaz ta hanun Sarkin Masar.
  • Kalmar nan "Hamitiye" za'a iya fassara ta da "mutumin Hamat."

(Hakanan duba: Babila, Kan'ana, Nebukadnezzar, Siriya, Zedekiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:3-4
  • 2 Sama'ila 08:9
  • Amos 06 :1-2
  • Ezekiyel 47:15-17

Hamor

Gaskiya

Hamor mutumin Kan'ana ne da zama a birnin Shekem a lokacin da Yakubu da iyalinsa ke zama kusa da Sukkot. Shi mutumin Hibitiye ne.

  • Yakubu ya sayi filin maƙabarta daga 'ya'yan Hamor.
  • A lokacin da suke a can, ɗan Hamor mai suna Shekem ya yiwa ɗiyar Yakubu mai suna Dinatu fyaɗe.
  • 'Yan'uwan Dinatu suka ɗauki fansa a kan iyalin Hamor suka kashe mazaje a birnin Shekem.

(Hakanan duba: Kan'ana, Hibitiye, Yakubu, Shekem, Sukkot)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:14-16
  • Farawa 34:2
  • Farawa 34:21
  • Yoshuwa 24:32-33
  • Littafin Alƙalai 09:28

Hananiya

Gaskiya

Hananiya suna ne na mutane mabambanta da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Ɗaya Hananiyan Ba'isra'ile ne da a ka kame zuwa bauta a Babila wanda a ka canjawa suna "Shadrak."
  • An ba shi matsayi a matsayin mai hidima a gidan sarauta sabo da ƙwarewarsa da kuma halinsa mai martaba.
  • A lokacin da a ka jefa Hananiya (Shadrak) da sauran abokansa biyu a cikin tanderun wuta sabo da sun ƙi bautawa sarkin Babila. Allah ya nuna ikonsa ta wurin kare su daga wutar.
  • Wani mutum kuma mai suna Hananiya an lissafa shi a cikin zuriyar Sarkin Suleman.
  • Wani Hananniya na da bam shi ne wani annabin ƙarya a kwanakin annabi Irmiya.
  • Wani mutum kuma mai suna Hananiya firist ne wanda ya jagoranci gangamin murna a kwanakin Nehemiya.

(Hakanan duba: Azariya, Babila, Daniyel, annabin ƙarya, Irmiya, Mishayel)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 01:6-7
  • Daniyel 02:17-18
  • Irmiya 28:1
  • Irmiya 28:5-7
  • Irmiya 28:15:17

Hannatu

Gaskiya

Hannatu ita ce mahaifiyar annabi Sama'ila. Ita ɗaya ce daga cikin matan Elkana guda biyu.

  • Hannatu bata iya samun damar haihuwa ba, wanda abin ya zama abin baƙin ciki a gare ta.
  • A cikin haikali, Hannatu ta yi addu'a da gaskiya domin Allah ya bata ɗa tare da alƙawarin zata miƙa wanan ɗa a bautar Allah.
  • Allah ya amsa addu'arta da kuma yaron nan Sama'ila ya yi girma sai ta kawo shi ya yi hidima a cikin haikali.
  • Bayan haka Allah ya ba Hannatu waɗansu 'ya'ya bayan Sama'ila.

(Hakanan duba: ɗaukan ciki, Sama'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 01:1-2
  • 1 Sama'ila 02:1

Haran

Gaskiya

Haran ƙanen Ibram ne, mahaifin Lotu kuma.

  • Hakanan Haran sunan wani gari ne da Ibram da iyalinsa suka zauna sa'ad da suke akan hanyarsu ta zuwa Ur zuwa ƙasar Kan'ana
  • Wani mutum kuma mai suna Haran shi ne ɗan Kalib.
  • Mutum na uku ɗmai suna Haran shi ne ɗan zureiyar Lebiyawa.

(Hakanan duba: Ibrahim. Kalib, Kan'ana, Lebiyawa, Lotu, Tera, Ur)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 19:19:12
  • Ayyukan Manzanni 07:1-3
  • Farawa 11:31
  • Farawa 27:43-45
  • Farawa 27:43-45
  • Farawa 28:10-11
  • Farawa 29:4-6

Haruna

Gaskiya

Haruna wan Musa ne. Allah ya zaɓi Haruna ya zama babban firist na farko domin mutanen Isra'ila.

  • Haruna ya taimaki Musa a wajen yiwa Fir'auna magana ya saki Isra'ilawa su tafi 'yantattu.
  • Sa'ad da Isra'ilawa ke tafiya cikin jeji, Haruna ya yi zunubi ta wurin ƙera wa mutane gunki domin suyi masa sujada.
  • Allah kuma ya zaɓi Haruna da zuriyarsa su zama (firist) firistoci domin mutanen Isra'ila.

(Hakanan duba: firist, Musa, Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 23:14
  • Ayyukan Manzanni 07:38-40
  • Fitowa 28:1-3
  • Luka 01:05
  • Littafin Lissafi 16:45

Hauwa

Gaskiya

Wanan ita ce mace ta farko. Ma'anar sunanta shi ne "rai" ko "rayuwa."

  • Allah ya yi mace daga Haƙarƙarin da ya ciro daga Adamu.
  • An hallici Hauwa ta zama "mataimakiya" ga Adamu ta zo ta taimaki Adamu cikin aikin lambu a aikin da Allah ya ba shi ya yi.
  • Shaiɗan ya jarafci Hauwa (da siffar maciji) ita ce ta fara yin zunubi ta wurin cin 'ya'yan itacen da Allah ya ce kada a ci.

(Hakanan duba: Adamu, rai, Shaiɗan)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 02 12
  • 2 Korintiyawa 11:3
  • Farawa 03:20
  • Farawa 04:2

Hebron

Gaskiya

Hebron birni ne da ke a tudu, tuddai masu duwatsu kusan mil 20 a kudu da Yerusalem.

  • An gina birnin ne a wajejen 2000 BC a kwanakin Ibram. An ambace shi a lokuta da yawa a cikin bada tarihin Tsohon Alƙawari.
  • Hebron ya taka muhimmiyar rawa a cikin rayuwar Sarki Dauda. Da 'ya'yansa da yawa har ma da Absalom a can aka haife shi.
  • Wanan birni an rushe shi a wajejen ƙarni na 70 ta hanun Romawa.

(Hakanan duba: Absalom)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 02:10-11
  • Farawa 13:18
  • Farawa 23:1-2
  • Farawa 35:27
  • Farawa 37:12-14
  • Littafin Alƙalai 01:10
  • Littafin Lissafi 13:22

Herod, Herod Antifas

Gaskiya

A kwanakin rayuwar Yesu, Herod Antifas shi ne ke mulkin ɓangaren Daular Roma wadda ta haɗa da lardin Galili.

  • Kamar mahaifinsa Herod Babba, Antifas a waɗansu lokutan akan kira shi da "Sarki Herod" koda yake shi ba cikakkaken sarki.
  • Herod Antifas shi ne ya mulki kusan kashi ɗaya bisa huɗu na lardin Isra'ila, domin shima akan kira shi da suna "Herod Tetrak." "Tetrak" sunan matsayi ne na mutumin da ke mulkin kashi ɗaya bisa huɗu na ƙasa.
  • Herod Antifas shi ne ya bada umarni a kashe Yahaya mai Baftisima ta wurin fille masa kai.
  • Herod Antifas ne ya tambayi Yesu kafin a giciye shi.
  • Sauran Herododin a cikin Sabon Alƙawari su ne ɗan Antifas (Agirifa) da kuma jikansa (Agirifa na biyu) wanda ya yi sarauta a kwanakin manzannin.

(Hakanan duba: gicciyewa, Herod Babban, Yahaya (mai Baftisima), sarki, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 03:1-2
  • Luka 03:20
  • Luka 09:9
  • Luka 13:32
  • Luka 23:9
  • Markus 06:20
  • Matiyu 14:2

Herod, Herod Babba

Gaskiya

Herod Babba ne ke mulkin Yahudiya a lokacin da aka haifi Yesu. Shi ne na farko daga cikin shugabannin Idom da aka ba suna Herod waɗanda suka yi mulki akan waɗansu ɓangarorin Daular Roma.

  • Magajinsa ya tubaya shiga Yahudanci aka rene shi a matsayin Bayahude.
  • Cesar Agustus ya bashi suna "Sarki Herod" duk da yake shi ba sarki ba ne na gaske. Ya yi mulki bisa Yahudawa har shekaru talatin da uku.
  • Herod Babba ya yi fice sabo da ƙayatattun gine-gine da ya umarta ayi da kuma sake gina haikalin Yahudawa a Yerusalem.
  • Wannan Herod ɗin yana da baƙin hali ya kuma sa an kashe mutane da yawa. A lokacin da ya ji cewa an haifi "sarkin Yahudawa" a Betlehem, ya umarta a kashe dukkan jarirai maza a cikin garin.
  • 'Ya'yansa Herod Antifas da Herod Filibus da jikansa Herod Agrifa suma sun zama shugabannin Roma. Ɗan jikansa Herod Agrifa na biyu da aka (kira "Sarki Agrifa") ya yi mulkin dukkan Yahudiya.

(Hakanan duba: Herod Antifas, Yudiya, sarki, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Matiyu 02:3
  • Matiyu 02:12
  • Matiyu 02:16
  • Matiyu 02:20
  • Matiyu 02:22

Herodiyas

Gaskiya

Herodiyas matar Herod Antifas ce a cikin Yahudiya a kwanakin Yahaya mai Baftisima.

  • Herodiyas dã ita matar ɗan'uwan Herod Antifas ɗan'uwan Filibus, amma daga bisani sai ta auri Herod Antifas ba bisa shari'a ba.
  • Yahaya mai Baftisima ya tsautawa Herod da Herodiyas sabo da aurensu da baya bisa doka. Sabo da wannan, Herod ya sa Yahaya a kurkuku sabo da Herodiyas daga bisani ya fille masa kai.

(Hakanan duba: Herod Antifas, Yahaya (mai Baftisima))

Wuraren da ake samunsa a Litttafi Mai Tsarki:

  • Luka 03:19
  • Markus 06:17
  • Markus 06:22
  • Matiyu 14:4

Hezekiya

Gaskiya

Hezekiya shi ne sarki na sha uku a cikin sarautar Yahuda. Shi sarki ne da yada dogara da kuma kuma yi wa Allah biyayya.

  • Ba kamar mahaifinsa Ahab ba, wanda ya zama mugun sarki, Hezekiya sarki ne nagari wanda ya rushe dukkan wuraren sujada na gumaka a Yahuda.
  • A wani lokaci ya yi rashin lafiya sosai har ya kusa mutuwa, ya yi addu'a da gaskiya ga Allah domin ya kuɓutar da ransa. Allah ya amsa addu'arsa ya bar shi ya ƙara yin shekaru goma sha biyar.
  • A matsayin alama ta cewa wannan zai faru, Allah ya yi mu'ujjuza na komar da rana baya.
  • Hakanan Allah ya amsa addu'ar Hezekiya ta ceton ransa daga sarki Sennakerib na Asiriya, wanda ke kai masu hari.

(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, allahn ƙarya, Yahuda, Sennakerib)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:13-14
  • 2 Sarakuna 16:19-20
  • Hosiya 01:1
  • Matiyu 01:9-11
  • Littafin Misalai 25:1-3

Hilkiya

Gaskiya

Hilkiya babban firist ne a kwanakin mulkin Sarki Yosiya.

  • A lokacin da ake gyaran haikali, Hilkiya babban firist ya samo Littafin Shari'a ya kuma bada umarni a kaiwa Sarki Yosiya.
  • Bayan da aka karanta masa Littafin Shari'a, Yosiya ya damu ya kuma sa mutanen Yahuda su sake bautawa Yahweh su kuma sake yin biyayya ga shari'unsa
  • Wani mutum kuma mai suna Hilkiya shi ne ɗan Eliyakim ya kuma yi aiki a fãda a lokacin Sarki Hezekiya.

(Hakanan duba: Eliyakim, Hezekiya, babban firist, Yosiya, Yahuda, shari'a, sujada, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 18:18

Horeb

Gaskiya

Tsaunin Horeb wani suna ne na Tsaunin Sinai, wurin da Allah ya ba Musa allunan dutse tre da dokoki goma.

  • Tsaunin Horeb ana kiran sa "tsaunin Allah."
  • Horeb shi ne wurin da Musa ya ga kurmi na cin wuta a lokacin da yake kiwon tumaki.
  • Tsaunin Horeb shi ne wurin da Allah ya baiyana alƙawarinsa ga Isra'ilawa ta wurin ba su allunan dutse ɗauke da dokokinsa a kansu.
  • Shi ne wurin da can baya Alllah ya ce da Musa ya bugi dutse domin ya samar wa da Isra'ilawa ruwa a lokacin da suke watangaririya a sahara.
  • Ba a san ainahin dai-dai inda wannan tsauni yake ba, amma yana nan ne dai a yankin Sinai.
  • Zai iya yiwuwa cewa Horeb shi ne ainahin sunan tsaunin saboda haka "Tsaunin Sinai" na nufin cewa "tsauni da ke a Sinai," wato yana nuna cewa Horeb tana nan ne a jeji Sinai.

(Hakanan duba: yarjejeniya, Isra'ila, Musa, Sinai, Dokoki Goma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:9-11
  • 2 Tarihi 05:9-10
  • Maimaitawar Shari'a 01:02
  • Fitowa 03:1-3
  • Zabura 106:19

Hosheya

Gaskiya

Hosheya sunan wani sarki ne na Isra'ila da kuma sunan mutane da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Hosheya ɗan Ala sarkin Isra'ila ne na tsawon shekaru tara a waɗansu kwanaki na sarauta Ahaz da Hezekiya, sarakunan Yahuda.
  • Yoshuwa ɗan Nun da sunansa Hosheya ne. Musa ya canza sunan Hosheya zuwa Yoshuwa kafin a aike tare da mutane sha ɗaya su leƙi asirin ƙasar Kan'aniyawa.
  • Bayan mutuwar musa, Yoshuwa ya jagoranci mutanen Isra'ila domin su mallaki ƙasa kan'ana.
  • Akwai wani mutum na dabam mai suna Hosheya ɗan Azaziya ɗaya kuma daga cikin shugabannin Ifraimawa.

(Hakanan duba: Ahaz, Kan'ana, Ifraim, Hezekiya, Yoshuwa, Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 27:20
  • 2 Sarakuna 15:30
  • 2 Sarakuna 17:03
  • 2 Sarakuna 18:01
  • 2 Sarakuna 18:09

Hosiya

Gaskiya

Hosiya annabi ne na Isra'ila wanda ya rayu ya kuma yi anabci a wajejen shekaru 750 kafin zuwan Kristi.

  • Hidimarsa ta kai shekaru masu yawa har zuwa mulkokin sarakuna da yawa, kamar su Yerobowam, Zakariya, Yotam, Ahaz, Hosheya, Uzziya, da Hezekiya.
  • Allah ya ce da Hosiya ya auri karuwa mai suna Gomar ya kuma ci gaba da ƙaunar ta, duk da yake bata da aminci a gare shi.
  • Wannan na nuna ƙaunar Allah ga mutanensa marasa aminci, wato Isra'ila
  • Hosiya ya yi anabci gãba da mutanen Isra'ila sabo da zunubansu, yana rinjayo su su juyo daga bautar gumaka.

(Hakanan duba: Ahaz, Hezekiya, Hosheya, Yerobowam, Yotam, Uzziya, Zakariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Hosiya 01:1-2
  • Hosiya 01:3-5
  • Hosiya 01:6-7

Ibrahim, Ibram

Gaskiya

Ibram mutumin Kaldiya ne daga birnin Ur wanda Allah ya zaɓe shi ya zama kakan Isra'ilawa. Allah ya sauya sunansa zuwa "Ibrahim."

  • Ma'anar "Ibram" shi ne "mahaifi da aka ɗaukaka."
  • Ma'anar "Ibrahim" shi ne, "mahaifin masu yawa."
  • Allah ya yiwa Ibrahim alƙawari zai sami zuriya masu yawa, da za su zama babbar al'umma.
  • Ibrahim ya gaskanta Allah ya kuma yi masa biyayya. Allah ya bi da Ibrahim ya tashi daga Kaldiya zuwa ƙasar Kan'ana.
  • Lokacin da suke zama a ƙasar Kan'ana, sa'ad da suka tsufa tukuf, Ibrahim da matarsa Saratu suka sami ɗa, shi ne Ishaku.

(Hakanan duba: Kan'ana, Kaldiya, Saratu, Ishaku)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 03:08
  • Farawa 11:29-30
  • Farawa 21:04
  • Farawa 22:02
  • Yakubu 02:23
  • Matiyu 01:02

Idom, Ba'idome, Idomawa, Idomiya

Gaskiya

Idom shi ne ƙarin sunan Isuwa. A yankin da ya zauna an san wurin da suna "Idom" daga bisani kuma ana kiransa "Idomiya"Idomawa kuma su ne zuriyarsa.

  • Yankin Idom ya sassauya a lokuta masu yawa, yankin yana kudancin Isra'ila ne, sannu kan hankali kuma ya kai kudancin Yahuda.
  • A kwanakin Sabon Alƙawari, Idom ta kai har rabin kufdancin lardin Yahudiya. Girkawa suka kira shi "idomiya"
  • Ma'anar wanan suna Idom shi ne "ja" wanda ke nufin an rufe Isuwa da jar suma a lokacin da aka haife shi. Ko kuma tana nufin 'yar jar miyar taushe da ta sa Isuwa ya sayar da matsayinsa na ɗan fari.
  • A cikin Tsohon Alƙawari ƙasar Idom akan yawan ambatonta a matsayin abokiyar gabar Isra'ila.
  • Dukkan Littafin Obadiya baki ɗaya yana magana ne game da hallakar Idom. Sauran littatafan annabawan Tsohon Alƙawari suma sun yi magana gãba da Idom.

(Hakanan duba: magafci, matsayin haihuwa, Isuwa, Obadiya, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 25:30
  • Farawa 32:3
  • Farawa 36:01
  • Ishaya 11:14-15
  • Yoshuwa 11:16-17
  • Obadiya 01:02

Ifirat, Ifirata, Ifiratiye, Ifratiyawa

Gaskiya

Ifirata sunan birni ne a yankin arewacin Isra'ila. Wanan garin tsohon sunansa shi ne "Betlehem" ko "Ifrata Betlehem."

  • Ifirata sunan ɗaya daga cikin 'ya'yan Kalibu ne. Birnin Ifrata ana tsammanin ya sami suna ne daga gare shi.
  • Mutumin da ya zo daga birnin Ifirata Shi ne ake kira "Ba'ifirate."
  • Bo'aza, kakan baban Dauda ba'Ifirate ne.

(Hakanan duba: Betlehem, Bo'aza, Kaleb, Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


Ifraim, Ba'ifraime, Ifraimiyawa

Gaskiya

Ifraim shi ne ɗa biyu ga Yosef. Zuriyarsa ita ake kira Ifraimiyawa, suna ɗaya daga cikin kabilan Isra'ila sha biyu.

  • Kabilar Ifraim na ɗaya daga cikin kabilu goma da ke arewacin Isra'ila.
  • A waɗansu lokutan a cikin Littafi Mai Tsarki in an ambaci Ifraim ana magana ne akan ɗaukacin yankin arewacin Isra'ila.
  • Yankin Ifraim yanki ne mai duwatsu ko tuddai, bisa ga bayanai akan ce da ita "ƙasa mai duwatsu ta Ifraim" ko "duwatsun Ifraim."

(Hakanan duba: mulkin Isra'ila, kabilun Isra;ila goma sha biyu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:66-69
  • 2 Tarihi 13:4-5
  • Ezekiyel 37:16
  • Farawa 41:52
  • Farawa 48:1-2
  • Yahaya 11:54

Ikoniyom

Gaskiya

Ikoniyom wani birni ne a tsakiyar kudancin wurin da yau ake kira Turkiya.

  • A cikin aikin fita bishara na Bulus, shi da Barnabas sun je Ikoniyom bayan Yahudawa sun tilasta masu su bar birnin Antiyok.
  • Yahudawa marasa bada gaskiya da al'umai a Ikoniyom suka shirya su jejjefe Bulus da abokan aikinsa, amma suka kuɓuce zuwa birnin Listra da ke kusa.
  • Bayan wannan da mutanen Antiyok da na Ikoniyom suka zo Listra suka zuga mutane su jejjefe Bulus.

(Hakanan duba: Barnabas, Listra, dutse)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 03:10-13
  • Ayyukan Manzanni 14:1
  • Ayyukan Manzanni 14:19-20
  • Ayyukan Manzanni 16:1-3

Iliya

Gaskiya

Iliya ɗaya ne daga cikin mafiya muhimmaci a cikin annabawan Yahweh. Iliya ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakunan Isra'ila da na Yahuda masu Yawa tare da sarki Ahab.

  • Allah ya yi mu'ujuzai da yawa ta hannun ilya, wanda ya haɗa da tayar da yaron da ya mutu.
  • Iliya ya tsautawa sarki Ahab sabo da bautar allolin ƙarya na Ba'al.
  • Ya ƙalubalanci annabawan Ba'al zuwa gwaji wanda ya nuna Yahweh shi ne kaɗai Allah na gaskiya.
  • A ƙarshen rayuwar Iliya Allah ya ɗauke shi sama tun yana raye ta wata hanya mai ban mamaki.
  • Bayan ɗaruruwan shekaru Iliya tare da Musa sun baiyana tare da Yesu a kan dutse, sun kuma yi magana game da zuwan Yesu da shan wuyarsa da kuma mutuwarsa a Yerusalem.

(Hakanan duba: mu'ujuza, annabi, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 17:1
  • 2 Sarakuna 1:3-4
  • Yakubu 5:16-18
  • Yahaya 01:19-21
  • Yahaya 01:24-25
  • Markus 09:5

Irmiya

Gaskiya

Irmiya annabin Allah ne a masarautar Yahuda. Littafin Irmiya a Tsohon Alƙawari yana ɗauke da anabce-anabcensa.

  • Kamar yawancin annabawa, sau da yawa Irmiya na gargaɗin mutanen Isra'ila cewa Allah zai hukuntasu saboda zunubansu.
  • Irmiya yayi anabci cewa Babiloniyawa za su ƙwace Urshalima, yasa wasu mutanen Yahuda suka ji haushi. Sai suka sanya shi cikin wata rijiya mai zurfi, busasshiya suka barshi nan ya mutu. Amma sarkin Yahuda ya umarci bayinsa su je su ceto shi daga rijiyar.
  • Irmiya ya rubuta cewa yayi fatan a ce ma idanunsa su zama "maɓulɓular hawaye," domin ya bayyana zurfin ɓacin ransa bisa kangara da wahalhalun mutanensa.

(Hakanan duba: Babila, Yahuda, annabi, kangara, rijiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 35:25
  • Irmiya 01:02
  • Irmiya 11:01
  • Matiyu 02:18
  • Matiyu 16:13-16
  • Matiyu 27:10

Ishaku

Gaskiya

Ishaku shi ne tilon ɗa ga Ibrahim da kuma Saratu. Allah ya yi alƙawari zai ba su ɗa duk da yake sun tsufa sosai.

  • Sunan nan Ishaku ma'anarsa ita ce "ya yi dariya." Sa'ad da Allah ya faɗa wa Ibrahim cewa Saratu za ta haifi ɗa Ibrahim ya yi dariya domin dukkansu sun tsufa sosai. Can wani lokaci ma, Saratu ta yi dariya bayan ta ji wannan labari.
  • Amma Allah ya cika alƙawarinsa an kuma haifi Ishaku ga Ibrahim da Saratu a kwanakin tsufansu.
  • Allah ya faɗawa Ibrahim cewa yarjejeniyar da ya yi da shi za ta zama har ga Ishaku da zuriyoyinsa har abada.
  • Lokacin da Ishaku yake saurayi, Allah ya gwada bangakiyar Ibrahim ta wurin umrataar sa ya miƙa Ishaku hadaya.
  • Ɗan Ishaku Yakubu yana da 'ya'ya maza goma sha biyu waɗanda daga bisani ake kira kabilu goma sha biyu na Isra'ila.

(Hakanan duba: Ibrahim, zuriya, har abada, cika, Yakubu, Saratu, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:28-29
  • Farawa 25:9-11
  • Farawa 25:19
  • Farawa 26:1
  • Farawa 26:08
  • Farawa 28:1-2
  • Farawa 31:18
  • Matiyu 08:11-13
  • Matiyu 22:32

Ishaya

Gaskiya

Ishaya annabin Allah ne da ya yi anabci a kwanakin mulkin sarakuna huɗu na Yahuda, wato Uzziya, Yotam, Ahaz da Hezekiya.

  • Ya rayu ne a Yerusalem a lokacin da Asiriyawa ke kaiwa birnin hari a kwanakin mulkin Hezekiya.
  • Littafin Ishaya a cikin Tsohon Al‌ƙawari na ɗaya daga babban litattafan a cikin Littafi Mai Tsarki.
  • Ishaya ya rubuta anabce-anabcen da waɗansun su suka cika tun yana raye.
  • Ishaya an san shi musamman kan anabcinsa da ya yi game da Mesaya wanda ya cika shekaru 700 bayan anabcin a lokacin da Yesu ke raye a duniya.
  • Yesu da almajiransa sun yanko aya daga anabcin Ishaya domin su koyar da mutane game da Mesaya.

(Hakanan duba: Ahaz, Asiriya, Kristi, Hezekiya, Yotam, Yahuda, annabi, Uzziya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 20:1-3
  • Ayyukan Manzanni 28:26
  • Ishaya 01:1
  • Luka 03:4
  • Markus 01:01
  • Markus 07:06
  • Matiyu 03:03
  • Matiyu 04:14

Ishma'il, Ba'Ishma'ile, Ishma'ilawa

Gaskiya

Ishma'il ɗan Ibrahim ne da Hajara baiwa daga Masar. Akwai sauran Mutane a cikin Tsohon Alƙawari da ke da suna Ishma'il.

  • Ma'anar sunan nan Ishma'il ita ce "Allah na ji."
  • Allah ya yi alƙawarin yiwa Ishma'il ɗan Ibrahim albarka, amma ba shi ba ne ɗan da Allah ya yiwa Ibrahim alƙawari ba.
  • Allah ya kare Hajara da Ishma'il lokacin da aka tura su daji.
  • A lokacin da Ishma'il ke cikin dajin Faran, ya auri ɗiyar masarawa.
  • Ishma'il ɗan Netaniya hafsan soja ne daga Yahuda wanda ya jagoranci ƙungiyar mutane su kashe gwabna wanda sarkin Babila, Nebukadnezza ya naɗa.
  • Akwai waɗansu maza huɗu dake Ishma'il a cikin Tsohon Alƙawari.

(Hakanan duba: Ibrahim, Babila, yarjejeniya, jeji, Masar, Hajara, Ishaku, Nebukadnezza, Faran, Saratu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:28-31
  • 2 Tarihi 23:01
  • Farawa 16:12
  • Farawa 25:9-11
  • Farawa 25:16
  • Farawa 37:25-26

Isra'ila, Ba'isra'ile, Isra'ilawa, Yakubu

Gaskiya

Yakubu shi ne ƙaramin ɗan tagwai na Ishaku da Rebeka.

  • Ma'anar sunan Yakubu shi ne "ya kama diddige" wanda wata faɗar ce dake ma'ana "ya yi cuta." Yayin da ake haihuwar Yakubu, yana riƙe da diddigen Isuwa ɗan'uwansa tagwai.
  • Shekaru da yawa daga bisani, Allah ya canza sunan Yakubu zuwa "Isra'ila," wanda ke ma'ana "ya yi gwagwarmaya da Allah."
  • Yakubu mai dabara ne da ruɗi. Ya sami hanyoyin da ya ɗauke albarkar ɗan fãri ya kuma gaji zarafofi daga yayansa, Isuwa.
  • Isuwa yaji haushi ya kuma yi shirin kashe shi sai Yakubu ya bar garinsa. Amma daga bisani bayan shekaru Yakubu ya dawo da matansa da 'ya'yansa zuwa ƙasar Kan'ana inda Isuwa ke zama, kuma iyalansu suka zauna cikin salama kurkusa da juna.
  • Yakubu yana da 'ya'ya maza sha biyu. Zuriyarsu ne suka zama kabilu sha biyu na Isra'ila.
  • Akwai wani mutum kuma daban mai suna Yakubu da aka lissafa a matsayin mahaifin Yosef a rubutun tarihin zuriya a cikin Matiyu.

(Hakanan duba: Kan'ana, ruɗa, Isuwa, Ishaku, Rebeka, kabilar sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:11
  • Ayyukan Manzanni 07:46
  • Farawa 25:26
  • Farawa 29:1-3
  • Farawa 32:1-2
  • Yahaya 04:4-5
  • Matiyu 08:11-13
  • Matiyu 22:32

Issaka

Gaskiya

Issaka shi ne ɗa na biyar ga Yakubu. Mahaifiyarsa ita ce Liya.

  • Ƙasar Issaka na da iyaka da ƙasashen Naftali, Zebulun, Manasse, da Gad.
  • Tana nan dab da kudancin Tekun Galili.

(Hakanan duba: Gad, Manasse, Naftali, kabilar Isra'ila sha biyu, Zebulun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 01:1-5
  • Ezekiyel 48:23-26
  • Farawa 30:18
  • Yoshuwa 17:10

Istifanus

Gaskiya

Akan tuna da Istifanus domin shi ne mutum na farko da aka fara kashewa a masu bi na farko, wato shi ne na farko da aka kashe saboda bangaskiyar Almasihu. zahirin rayuwarsa da mutuwarsa an rubuta shi a littafin Ayyukan manzanni.

  • Ikilisiyar farko a Yerusalem ta zaɓi Istifanus don ya yi hidima ga kiristoci a matsayin dikin ta wurin samar da abinci ga gwauraye da sauran kiristoci masu buƙata.
  • Yahudawa da yawa sun zarki Istifanus da yin maganar găbă da Allah da kuma shari'un Musa.
  • Istifanus cikin gabagaɗi ya fito ya faɗi gaskiya game da Yesu shi ne Almasihu, ya fara da tarihin yadda Allah ya jagoranci mutanen Isra'ila.
  • Shugabanni Yahudawa suka ji haushin Istifanus suka zartar masa da hukuncin jifa da duwatsu har ya mutu a bayan gari.
  • Zartar da hukuncinsa ya zama da hannun Shawulu na Tarsus, wanda daga baya ya zama manzo Bulus.
  • Ansan Istifanus sosai da maganarsa ta ƙarshe da ya yi kafin ya mutu, "ya Ubangiji kada ka ɗora masu zunubin nan", wanda ya nuna ƙaunar da yake da ita domin waɗansu.

(Hakanan duba: zaɓa, dikin, Yerusalem, Bulus, dutse, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:05
  • Ayyukan Manzanni 06:09
  • Ayyukan Manzanni 06:10-11
  • Ayyukan Manzanni 06:12
  • Ayyukan Manzanni 07:56
  • Ayyukan Manzanni 11:19
  • Ayyukan Manzanni 22:20

Isuwa

Gaskiya

Isuwa ɗaya ne daga cikin tagwan 'ya'yan Ishaku da Rebeka. Shi ne aka fara haifa musu. Ɗan'uwansa shi ne Yakubu.

  • Isuwa ya sayar da matsayinsa na ɗan fari ga Yakubu sabo da abinci.
  • Tun da Isuwa shi ne na farko, ya kamata mahaifinsu Ishaku ya ba shi wata albarka ta musamman. Amma Yakubu ya yaudari Ishaku har ya ba shi albarka a memakon Isuwa. Da farko ya yi fushi har ya so kashe Yakubu, amma daga bisani ya gafarta masa.
  • Isuwa yana da 'ya'ya da yawa da jikoki, waɗannan zuriya su ne suka zama babbar al'uma da ke zama a Kan'ana.

(Hakanan duba: Idom, Ishaku, Yakubu, Rebeka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 25:26
  • Farawa 25:29-30
  • Farawa 26:34
  • Farawa 27:11-12
  • Farawa 32:5
  • Ibraniyawa 12: 17
  • Romawa 09:13

Itiofiya, Ba'Itiofiye

Gaskiya

Itiofiya ƙasa ce a Afrika tana kudu da Masar, tana da kan iyaka da kogin Nilu daga yamma kuma tana iyaka da jan teku daga gabas. Mutumin da ya zo daga Itiofiya sunansa "Ba'Itiofiye."

  • Tsohuwar Itiofiya tana can kudu da Masar, kuma ta haɗa ƙasashe da yawa da yau ake kiransu Afrika, kamar su Sudan, Habasha, Somaliya, Kenya, Uganda, Janhuriyar Afrika ta tsakiya, da kuma Chadi.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, a waɗansu lokutan ana kiran Itiofiya "Kush" ko " Nubiya."
  • Ƙasashen Itiofiya "Kush" da Masar akan yi yawan ambatonsu tare a cikin Littafi Mai Tsarki, mai yiwuwa domin suna kusa da juna ne, kuma tushen iyayensu zai iya zama ɗaya.
  • Allah ya aiki Filibus mai bishara zuwa jeji inda ya yi bishara game da Yesu tare da bãbã na Habasha.

(Hakanan duba: Kush, Masar, bãbã, Filib)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:27
  • Ayyukan Manzanni 08:30
  • Ayyukan Manzanni 08:32-33
  • Ayyukan Mnzanni 08:36-38
  • Ishaya 18:1-2
  • Nahum 03:9
  • Zafaniya 03:9-11

Jibira'ilu

Gaskiya

Jibira'ilu sunan ɗaya daga cikin mala'ikun Allah ne. An ambaci sunansa sosai, a cikin Tsohon Alƙawari da kuma Sabon Alƙawari.

  • Allah ya aiko Jibra'ilu ya faɗawa annabi Daniyel ma'anar wahayin da ya gani.
  • Ɗaya lokacin kuma shi ne a sa'ad da Daniyel ke addu'a, mala'ika Jibira'ilu ya hura masa sai ya yi anabci akan abin da zai faru nan gaba. Daniyel ya baiyana shi a matsayin "balagaggen namiji"
  • A cikin Sabon Alƙawari an rubuta cewa Jibira'ilu ya ziyarci Zakariya cewa matarsa Elizabet wadda ta tsufa za ta haifi ɗa, mai suna Yahaya.
  • Watanni shida bayan wanan, aka aiki Jibira'ilu wurin Maryam ya ce da ita Allah zai yi mu'ujuza ta wurin ta za ta yi juna biyu ta haifi ɗa zai kuma zama "Ɗan Allah." Jibira'ilu yace da Maryam ta ba ɗanta suna "Yesu."

(Hakanan duba: mala'ika, Daniyel, Elizabet, Yahaya (mai baftisima) Maryam, annabi, Ɗan Allah, Zakariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 08:15-17
  • Daniyel 09:21
  • Luka 01:19
  • Luka 01:26

Kadesh, Kadesh-Barniya, Meriba Kadesh

Gaskiya

Sunayen Kadesh, Kadesh-Barniya, Meriba Kadesh dukkansu na magana game da wani birni mai muhimmanci a tarihin Isra'ila wanda ke a sashen kudancin Isra'ila, kusa da lardin Idom.

  • Birnin Kadesh wani kurmi ne, wurin da akwai ruwa da ƙasa mai albarka a tsakiyar hamada mai suna Zin.
  • Musa ya aiki 'yan leƙen asirin ƙasa sha biyu zuwa ƙasar Kan'ana daga Kadesh Barniya.
  • Isra'ila kuma sunyi sansani a Kadesh a lokacin yawonsu cikin jeji.
  • A Kadesh Barniya ne Miriyam ta mutu.
  • A Meriba Kadesh ne Musa ya yi rashin biyayya da Allah ya kuma bugi dutsen domin ya samar wa Isra'ilawa ruwa, a maimakon yiwa dutsen magana kamar yadda Allah ya gaya masa.
  • Sunan "Kadesh" ya fito ne daga wata kalmar Ibraniyawa mai ma'ana "tsarki" ko "keɓaɓɓe."

(Hakanan duba: hamada, Idom, tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 48:28
  • Farawa 14:7-9
  • Farawa 16:14
  • Farawa 20:1-3
  • Yoshuwa 10:40-41
  • Littafin Lissafi 20:1

Kafarnihum

Gaskiya

Kafarnihum ƙauyen kamun kifi ne arewa maso yamma da gacin Tekun Galili.

  • Yesu ya zauna a Kafarna'um duk lokacin da yake koyarwa a Galili.
  • Almajiransa da yawa 'yan Kafarnihum ne.
  • Yesu ya yi al'ajibai da yawa a wannan birni har ma ya dawo wa wata 'yar yarinya da rai.
  • Kafarnihum yana ɗaya daga cikin birane uku da Yesu ya kwaɓe su domin mutanenta sun ƙi shi basu gaskata da maganarsa ba. Ya yi masu kashedi Allah zai hore su saboda rashin bangaskiyarsu.

(Hakanan duba: Galili, Tekun Galili)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 02:12
  • Luka 04:31
  • Luka 07:1
  • Markus 01:21
  • Markus 02:02
  • Matiyu 04:12-13
  • Matiyu 17:24-25

Kai'afas

Gaskiya

Kai'afas shi ne babban firist na Isra'ila a lokacin Yahaya mai Baftisma da Yesu.

  • Kai'afas yana da hannu sosai a shari'a da kisan da aka yiwa Yesu.
  • Manyan firistoci Anas da Kai'afas suna nan a lokacin da ake tuhumar Bitrus da Yahaya da aka kama su bayan sun warkar da wani gurgun mutum.
  • Ka'afas shi ne wanda ya ce ya gwamace mutum ɗaya ya mutu domin dukkan al'umma maimakon dukkan al'umma ta hallaka. Allah ya sa ya faɗi wannan saboda ya zama anabcin yadda Yesu zai mutu ya ceci mutanensa.

(Hakanan duba: Anas, babban firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:5-7
  • Yahaya 18:12
  • Luka 03:02
  • Matiyu 26: 3-5
  • Matiyu 26:57-58

Kaldiya, Ba'kaldiye

Gaskiya

Kaldiya wani yanki ne a kudancin Mesafotamiya ko Babiloniya. Mazaunan wannan yanki ana kiransu Kaldiyawa.

  • Birnin Ur, inda Ibrahim ya fito yana cikin Kaldiya. Yawancin lokaci ana kiransa Ur ta Kaldiyawa."
  • Sarki Nebukanezar ɗaya ne daga cikin Kaldiyawa da yawa da suka yi sarauta akan Babiloniya.
  • Bayan shekaru da yawa, wajen shekarata 600 BC, wannan kalma "Ba'kaldiye" ta zama sananniya da "Babiloniye."
  • A cikin littafin Daniyel, wannan kalma "Ba'kaldiye" ana nufin wasu ƙungiyar mutane ne musamman waɗanda ƙwararrun masana ne da suke bincike taurari.

(Hakanan duba: Ibrahim, Babila, Shina, Ur)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:4-5
  • Ezekiyel 01:01
  • Farawa 11:27:28
  • Farawa 11:31-32
  • Farawa 15:6-8
  • Ishaya 13:19

Kaleb

Gaskiya

Kaleb ɗaya ne daga cikin Isra'ilwa goma sha biyu 'yan leƙen asirin ƙasa waɗanda Musa ya aika su dubo ƙasar Kan'ana.

  • Da shi da Yoshuwa suka gaya wa mutane su dogara ga Allah ya taimake su su buge Kan'aniyawa.
  • Da Yoshuwa da Kaleb ne kaɗai a tsararsu da aka bar su su shiga ‌Ƙasar Alƙawari ta Kan'ana.
  • Kaleb ya roƙa a ba shi ƙasar Hebron da shi da iyalinsa. Ya sani Allah zai taimake shi ya ci mutanen dake zaune a wurin.

(Hakanan duba: Hebron, Yoshuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 04:13
  • Yoshuwa 14:6-7
  • Littafin Alƙalai 01:12
  • Littafin Lissafi 32:10-12

Kan'ana, Bakan'aniye, Kan'aniyawa

Gaskiya

Kan'ana ɗan Ham ne, ɗaya daga cikin 'ya'yan Nuhu. Kan'aniyawa sune zuriyar Kan'ana.

  • Kalman nan "Kan'ana" ko "ƙasar Kan'ana" ana nufin ƙasar nan dake tsakanin Kogin Yodan da Tekun Baharmaliya. Itace ta tafi kudu ta kai iyaka da Masar tayi yamma zuwa iyaka da Suriya.
  • Wannan ƙasa mazaunanta dã Kan'aniyawa ne, da kuma wasu yarurrukan mutane da dama.
  • Allah ya yi alƙawari zai bada ƙasar Kan'ana ga Ibrahim da zuriyarsa, Isra'ilawa.

(Hakanan duba: Ham, Ƙasar Alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 13:19-20
  • Fitowa 03:7-8
  • Farawa 09:18
  • Farawa 10:19-20
  • Farawa 13:07
  • Farawa 47:02

Kana

Gaskiya

Kana ƙauye ne ko kuma gari a lardin Galili, wajen mil tara yamma da Nazaret.

  • Kana garin Nataniyel ne, ɗaya daga cikin sha biyun.
  • Yesu ya je bikin ɗaurin aure a Kana a can ya yi al'ajibinsa na farko sa'ad da ya maida ruwa ya zama ruwan inabi.
  • Wani lokaci bayan wannan, Yesu ya dawo Kana ya gamu da wani shugaba daga Kafarnahum wanda ya roƙi warkarwa domin ɗansa.

(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 02:1-2
  • Yahaya 04:46-47

Karmel, Tsaunin Karmel

Gaskiya

Tsaunin Karmel yana cikin jerin wasu tsaunuka dake gaɓar Tekun Baharmaliya arewa da Filin Sharon. ‌Ɗaya daga cikin tsaunukan mafi tsayi ya kai mita 546.

  • Akwai kuma wani gari da ake kira "Karmel" yana cikin Yahuda, kudu da Tekun Gishiri.
  • Wani mawadacin mai mallaƙar ƙasa Nabal da matarsa Abigel sun zauna kusa da garin Karmel inda Dauda da mutanensa suka taimaka a tsare masu sausayar tumakin Nabal.
  • A bisa Tsaunin Karmel, Iliya ya ƙalubalanci annabawan Ba'al a wata gasa domin a tabbata cewa Yahweh ne kaɗai Allah na gaskiya.
  • Domin ƙarin haske cewa wannan ba wai tsauni ɗaya ba ne, za a iya fassara "Tsaunin Karmel" haka, "tsaunin dake kan jerin tsaunukan Karmel" ko "jerin tsaunukan Karmel."

(Hakanan duba: Ba'al, Iliya, Yahuda, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:18-19
  • 1 Sama'ila 15:12
  • Irmiya 46:18
  • Mika 07:14-15

Kayinu

Gaskiya

Kayinu da ƙanensa Habila sune 'ya'ya maza na Adamu da Hauwa'u da aka faɗi a Litttafi Mai Tsarki.

  • Kayinu manomi ne wanda ya noma kayan abinci Habila kuwa makiyayin tumaki ne.
  • Kayinu ya kashe ɗan'uwansa Habila a cikin hasalar ƙyashi, saboda Allah ya karɓi hadayar Habila, amma bai karɓi hadayar Kayinu ba.
  • Horon da Allah ya bashi shi ne ya kore shi daga gonar Iden ya gaya masa ƙasa baza ta ƙara bashi ammfani ba.
  • Allah ya sa lamba a goshin Kayinu wadda alama ce Allah zai kare shi daga kisa daga mutane sa'ad da yake yawo barkatai.

(Hakanan duba: Adamu, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:12
  • Farawa 04:02
  • Farawa 04:09
  • Farawa 04:15
  • Ibraniyawa 11:4
  • Yahuda 01:11

Kedar

Gaskiya

Kedar ɗan Ishma'ila ne na biyu. Shima birni ne mai muhimmanci, wanda ake kyautata zaton an bashi suna bisa ga sunan mutumin.

  • Birnin Kedar yana sashen arewacin Arabiya kusa da kudancin kan iyakar Falestin. A cikin lokuttan Littafi Mai Tsarki, an san shi saboda ƙasaitarsa da kyaunsa.
  • Zuriyar Kedar suka zama babbar ƙungiyar mutane da suma ake kiransu "Kedar."
  • Furcin "rumfunan Kedar masu duhu" yana nufin rumfunan gashin baƙaƙen awaki da mutanen Kedar suke zama a ciki.
  • Waɗannan mutane na Kedar masu kiwon tumaki ne da awaki. Suna kuma amfani da raƙuma wajen ɗaukar kaya.
  • A Littafi Mai Tsarki, furcin "ɗaukakar Kedar" na nufin ƙasaitar wannan birni da mutanensa.

(Hakanan duba: Arabiya, akuya, Ishma'ila, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Waƙar Suleman 01:05

Kedesh

Gaskiya

Kedesh birnin Kan'aniyawa ne wanda Isra'ilawa suka ƙwace sa'ad da suka shiga ƙasar Kan'ana.

  • Wannan birni na sashen arewacin Isra'ila, a cikin kason ƙasar da aka bayar ga kabilar Naftali.
  • Kedesh na ɗaya daga cikin biranen da aka zaɓa a matsayin wurin da Lebiyawa firistoci zasu zauna, tunda basu da wata ƙasa da take ta kansu.
  • An kuma keɓe shi a matsayin "birnin mafaka."

(Hakanan duba: Kan'ana, Hebron, Lebiyawa, Naftali, firist, mafaka, Shekem, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:72
  • Yoshuwa 19:37
  • Littafin Alƙalai 04:10

Keretiyawa

Gaskiya

Keretiyawa mutane ne waɗanda wataƙila wasu ɓangaren Filistiyawa ne. Kuma ana rubuta su haka, "Keretiyawa."

  • Da Keretiyawa da Feletiyawa wasu ƙungiyar mayaƙa ne daga rundunar Sarki Dauda waɗanda musamman amintattun matsaransa ne.
  • Benaya, ɗan Yehoaida ɗan ƙungiyar shirye shiryen Dauda ne, shi ne shugaban Keretiyawa da Feletiyawa.
  • Keretiyawa suka tsaya tare da Dauda lokacin da dole ya gudu daga Yerusalem saboda tawayen Absalom.

(Hakanan duba: Absalom, Benaiya, Dauda, Filistiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Zakariya 02:05

Kogin Nilu, Kogin Masar, Nilu

Gaskiya

Nilu wani dogon kogi ne da fãɗi a arewa maso gabas ta Afirka. An fi saninsa musamman babban kogin Masar.

  • Kogin Nilu ya gangara arewa ta tsakiyar Masar zuwa cikin Tekun Baharmaliya.
  • Amfani sukan yi girma sosai a ƙasar nan mai tãki a kowanne gefen Kogin Nilu.
  • Yawancin Masarawa suna zama kusa da Kogin Nilu tun da shi ne mai bada ruwa domin kayan abinci.
  • Isra'ilawa sun zauna a ƙasar Goshen, wadda take da armashi domin tana gaɓar Kogin Nilu.
  • Da Musa yake ɗan jariri, iyayensa sun saka shi cikin kwando a ciyayin iwa na Nilu domin su ɓoye shi daga mutanen Fir'auna.

(Hakanan duba: Masar, Goshen, Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 08:08
  • Farawa 41:1-3
  • Irmiya 46:08

Kogin Yodan, Yodan

Gaskiya

Kogin Yodan kogi ne dake malalowa daga arewa zuwa kudu, ya kuma yi kan iyakar gabashin ƙasar da ake kira Kan'ana.

  • A yau, Kogin Yodan ya raba Isra'ila a yammacinta daga Yodan a gabas.
  • Kogin Yodan ya malala ta Tekun Galili daga nan kuma ya tsiyaye kansa cikin Mataccen Teku.
  • Sa'ad da Yoshuwa ya bida Isra'ilawa zuwa cikin Kan'ana, sai da suka bi ta Kogin Yodan. Zurfinsa yafi na yadda za'a bi ta cikinsa kawai, amma Allah ta wurin al'ajibi ya tsaida kogin daga malalowa saboda suyi tafiya bisa gadon kogin.
  • Yawanci a cikin Littafi Mai Tsarki ana kiran Kogin Yodan "Yodan."

(Hakanan duba: Kan'ana, Tekun Gishiri, Tekun Galili)

Wuraren da ake samunsa a Lttafi Mai Tsarki:

  • Farawa 32:9-10
  • Yahaya 01:26-28
  • Yahaya 03:25-26
  • Luka 03:3
  • Matiyu 03:06
  • Matiyu 04:14-16
  • Matiyu 04:14-16
  • Matiyu 19:1-2

Kogin Yufiretis, Kogi

Gaskiya

Yufiretis suna ne na ɗaya daga cikin koguna huɗu dake malala ta cikin Lambun Aidin. Shi ne kogin da ake yawan ambato a cikin Littafi Mai Tsarki.

  • Kogin Yufiretis na yau yana a yankin gabas ta tsakiya shi ne dogo da kuma kogi mafi muhimmanci a yankin Asiya.
  • Tare da ƙogin Tigris kan iyakar Yuferetis yana nan a wata ƙasa mai suna Mesofotomiya.
  • Tsohon birnin Ur inda Ibrahim ya baro yana bakin kogin Yuferetis ne.
  • Wanan kogin shi ya zama iyakokin ƙasar da Allah ya yi alƙawari zai ba Ibrahim (Farawa 15:18).
  • Waɗansu lokutan ana fin kiran Yufiretis "Kogi" ne kawai.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:7-9
  • 2 Tarihi 09:25-26
  • Fitowa 23:30-33
  • Farawa 02:13-14
  • Ishaya 07:20

Kolosiya, Kolosiyawa

Gaskiya

A lokacin Sabon Alƙawari, Kolosiya birni ne cikin lardin Roma da ake ce da ita Firijiya, wata gundumar ƙasa ce da yanzu ita ce kudu maso yamma ta ƙasarTurki. Mutanen Kolosiyawa sune mazaunan Kolosiya.

  • Wannan birni misalin mil 100 take daga Tekun Baharmaliya, Kolosiya tana kan muhimmiyar turba ta kasuwanci a tsakanin birnin Afisa da Kogin Ifrates.
  • Sa'ad da Bulus yake a kurkuku a Roma, ya rubuta wa "Kolosiyawa" wasiƙa domin ya gyara wasu koyarwar ƙarya da ke cikin masu bada gaskiya a Kolosiya.
  • Sa'ad da ya rubuta wannan wasiƙa, Bulus bai rigaya ya ziyarci wannan ikilisiya ba, amma ya ji akan waɗanda suka bada gaskiya a nan daga wurin abokin aikin sa, Ifafras.
  • Wataƙila Ifafras shi ne Krista ma'aikaci wanda ya fara kafa ikilisiya a Kolosiya.
  • Littafin Filimon wasiƙa ce ta Bulus zuwa ga ubangidan wani bawa a Kolosiya.

(Hakanan duba: Afisawa, Bulus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 01:03

Kora, Bakore, Korawa

Gaskiya

Kora sunan mutane uku ne a Tsohon Alƙawari.

  • Ɗaya daga cikin 'ya'yan Isuwa an sa masa suna Kora. Ya zama shugaba a gundumarsa.
  • Kora kuma wani zuriyar Lebi ne ya kuma yi hidima a rumfar sujada a matsayin firist. Ya zama mai kishin Musa da Haruna ya kuma jagoranci mutane suyi tawaye gãba da su.
  • Mutum na uku mai suna Kora an lissafa shi a zuriyar Yahuda.

(Hakanan duba: Haruna, hukuma, Kaleb, zuriya, Isuwa, Yahuda, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:34-37
  • Littafin Lissafi 16:1-3
  • Littafin Lissafi 16:25-27
  • Zabura 042:1-2

Korint, Korintiyawa

Gaskiya

Korint birni ne a ƙasar Giris, kusan mil 50 yamma da Atens. Korintiyawa sune mutanen da suka zauna a Korint.

  • A Korint aka kafa ɗaya daga cikin ikilisiyoyin Krista na farko.
  • Litattafan Sabon Alƙawari, 1 Korintiyawa da 2 Korintiyawa wasiƙu ne da Bulus ya rubuta wa Kristocin dake zaune a Korint.
  • A tafiyarsa ta farko ta Bishara, Bulus ya zauna a Korint kimamin watanni 18.
  • Bulus ya haɗu da Akila da Bilkisu lokacin da yake a Korint.
  • Wasu shugabannin ikilisiyoyi da suka shafi Korinti har da Timoti, da Titus, da Afolos, da Silas.

(Hakanan duba: Afolos, Timoti, Titus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 01:03
  • 2 Korintiyawa 01:23-24
  • 2 Timoti 04:19-22
  • Ayyukan Manzanni 18:01

Korniliyos

Gaskiya

Korniliyos Ba'al'umme ne ko kuma a ce ba Ba'yahuden mutum bane, shi hafsa ne a rundunar mayaƙan Roma.

  • Yakan yi addu'a kullum ga Allah yana kuma bayarwa ga matalauta hannu sake.
  • Da Korniliyos da iyalinsa suka ji manzo Bulus ya shaida bishara, sai suka zama masu bada gaskiya ga Yesu.
  • Mutanen gidan Korniliyos sune mutanen farko daba Yahudawa ba da suka zama masu bada gaskiya.
  • Wannan ya nuna wa mabiyan Yesu cewa, ya zo ne ya ceci dukkan mutane, har ma da al'ummai,

(Hakanan duba: manzo, gaskatawa, Ba'al'umme, labari mai daɗi, Girik, hafsan soja)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 10:01
  • Ayyukan Manzanni 10:08
  • Ayyukan Manzanni 10:18
  • Ayyukan Manzanni 10:22
  • Ayyukan Manzanni 10:24
  • Ayyukan Manzanni 10:26
  • Ayyukan Manzanni 10:30

Krit, Kritawa

Gaskiya

Krit tsibiri ce kudu da gaɓar Gris. Ba'karite mutum ne dake zaune a wannan tsibirin.

  • Manzo Bulus ya zo wannan tsibirin Krit lokacin tafiyarsa zuwa bishara.
  • Bulus ya bar abokin aikinsa Titus a Krit ya koya wa Kristoci ya kuma taimaka ya sa shugabanni domin ikilisiyar dake can.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:11
  • Ayyukan Manzanni 27:08
  • Amos 09:7-8
  • Titus 01:12

Kush

Gaskiya

Kush babban ɗan Ham ne wanda shi ma ɗa ne ga Nuhu. Shi kaka ne ga Lamirudu. 'Yan'uwansa biyu maza ana ce da su Masar da Kan'ana.

  • A lokacin Tsohon Alƙawari, "Kush" sunan wani babban yanki ƙasa ne kudu da Isra'ila. Mai yiwuwa ne an ba ƙasan nan sunan ɗan Ham Kush.
  • Tsohon yankin Kush ya maye ƙasa mai yawa da wataƙila a lokatai da dama ya haɗa har da ƙasashen zamanin yanzu kamar su Sudan, Masar, Itiyofiya, da ma wataƙila, Saudi Arabiya.
  • Akwai wani mutum kuma da ake ce da shi Kush an faɗe shi a cikin Zabura. Shi kuma Ba'benyami ne.

(Hakanan duba: Arebiya, Kan'ana, Masar, Itiyofiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:8-10
  • Ezekiyel 29:10
  • Farawa 02:13
  • Farawa 10:6-7
  • Irmiya 13:23

Kwarin Kidron

Gaskiya

Kwarin Kidron wani kwari ne mai zurfi a waje da birnin Yerusalem, a tsakanin ganuwarsa ta gabas da Tsaunin zaitun.

  • Zurfin kwarin yafi ƙafa 1,000 tsawonsa kuma yafi kamu 32.
  • Sa'ad da Sarki Dauda ke gudu daga ɗansa Absalom, ya bi ta cikin Kwarin Kidron domin ya kai Tsaunin Zaitun.
  • Sarki Yosiya da Sarki Asa na Yahuda sun bada umarni cewa wuraren tuddai na bagadan allolin ƙarya a rushe su a kuma ƙone; an zubar da tokarsu a cikin Kwarin Kidron.
  • A zamanin mulkin Sarki Hezekaya, Kwarin Kidron shi ne wurin da firistoci ke zubar da dukkan abu marar tsarki wanda suka fitar daga haikali.
  • Muguwar sarauniya Ataliya an kashe ta ne a kwarin saboda miyagun abubuwa da ta aikata.

(Hakanan duba: Absalom, Asa, Ataliya, Dauda, allahn ƙarya, Hezekaya, wuraren tuddai, Yosiya, Yahuda, Tsaunin Zaitun)

  • Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:
  • Yahaya 18:01

La'azaru

Gaskiya

La'azaru da 'yan'uwansa Mata, Maryamu da Marta, abokan Yesu ne na musamman. Yawanci Yesu na zama tare da su a Betani.

  • La'azaru dai anfi saninsa game da al'amarin yadda Yesu ya tada shi daga mutuwa bayan an bizne shi cikin kabari kwanaki da yawa.
  • Shugabannin Yahudawa suka fusata da Yesu kuma suka yi kishin ganin cewa ya yi wannan al'ajibi, suka kuma nemi hanyar kashe Yesu da La'azaru gabaɗaya.
  • Yesu kuma ya yi misali da wani matalaucin mabaraci da wani mutum mai arziki inda mabaracin an kira shi da suna "La'azaru."

(Hakanan duba: mabaraci, shugabannin Yahudawa, Marta, Maryamu, tadawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 11:11
  • Yahaya 12:1-3
  • Luka 16:21

Laban

Gaskiya

A cikin Tsohon Alƙawari, Laban kawu ne kuma suruki ne ga Yakubu.

  • Yakubu ya yi zama a gidan Laban a Fadan Aram kuma ya yi kiwon tumakinsa da Awaki a matsayin biyan dukiyar auren 'ya'yan Laban.
  • Yakubu dai wadda ya zaɓa itace Rahila ɗiyar Laban ta zama matarsa.
  • Laban ya ruɗi Yakubu ya sa ya auri babbar ɗiyarsa Liya da farko kafin ya bashi Rahila a matsayin mata.

(Hakanan duba: Yakubu, Naho, Liya, Rahila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 24:30
  • Farawa 24:50
  • Farawa 27: 43
  • Farawa 28:1-2
  • Farawa 29:05
  • Farawa 29:13
  • Farawa 30:26
  • Farawa 46: 16-18

Lamek

Gaskiya

Lamek suna ne na mutum biyu da aka ambata a cikin Littafin Farawa.

  • Lamek na farko da aka ambata zuriyar Kayinu ne. Da fahariya ya gaya wa matansa biyu cewa ya kashe mutum saboda ya yi masa rauni.
  • Lamek na biyu zuriyar Set ne. Kuma shima mahaifin Nuhu ne.

(Hakanan duba: Kayinu, Nuhu, Set)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 04:18-19
  • Farawa 04:24
  • Farawa 05:25
  • Farawa 05:29
  • Farawa 05:31
  • Luka 03:36

Lebanon

Gaskiya

Lebanon wata yankin ƙasa ce mai kyaun duwatsu a gaɓar Tekun Baharmaliya, arewa da Isra'ila. A lokacin Littafi Mai Tsarki wannan yanki kurmi ne cunkus da rimayen itatuwa kamar su sida da sifures.

  • Sarki Suleman ya aika ma'aikata Lebanon su saro itatuwan sida domin amfani da su a ginin haikalin Allah.
  • Lebanon ta dã da mazaunanta mutanen Fonisiya ne, ƙwararru a gine-ginen jiragen ruwa da ake amfani da su wajen kasuwanci masu armashi.
  • Birane Taya da Sidon suna cikin Lebanon. A waɗannan birane a cikin su ne aka fara amfani da rinin shunayya.

(Hakanan duba: sida, sifires, fir, Fonisiya)

Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:32-34
  • 2 Tarihi 02:8-10
  • Maimaitawar Shari'a 01:7-8
  • Zabura 029:3-5
  • Zakariya 10:8-10

Lebi, Balebiye, Lebiyawa, Lebiyanci

Gaskiya

Lebi na ɗaya daga cikin 'ya'ya maza sha biyu na Yakubu, ko Isra'ila. Kalmar "balebiye" na nufin wani taliki wanda ke daga ɗaya daga cikin kabilar Isra'ilawa wanda kakansu Lebi ne.

  • Lebiyawa sune ke da nauyin lura da haikali da bida hidimomin addini, duk da baikon hadayu da addu'o'i.
  • Dukkan firistocin Yahudawa Lebiyawa ne, zuriya daga Lebi kuma fannin kabilar Lebi. (Ba dukkan Lebiyawa bane firistoci, duk da haka.)
  • Lebiyawa firistoci keɓaɓɓu ne kuma an naɗa su domin aiki na musamman na bautar Allah a cikin haikali.
  • Wasu mutane kuma biyu masu suna "Lebi" kakannin Yesu ne, kuma sunayensu na cikin rubutaccen tarihin zuriya a cikin bisharar Luka.
  • Almajirin Yesu kuma mai suna Matiyu ana kiransa Lebi.

(Hakanan duba: Matiyu, firist, hadaya, haikali, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsu a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 02:1-2
  • 1 Sarakuna 08:3-5
  • Ayyukan Manzanni o4:36-37
  • Farawa 29:34
  • Yahaya 01:19-21
  • Luka 10:32

Lebiyatan

Gaskiya

Kalmar "Lebiyatan" na nufin wata irin dabba mai girma sosai, wadda ta ƙaurace an kuma ambace ta a rubuce-rubucen farko na Tsohon Alƙawari, Litattafan Ayuba, Zabura, da Ishaya.

  • Lebiyatan wani halitta ne mai girman gaske, mai kamannin maciji, mai ƙarfi da tsauri kuma yana sa ruwan dake kewaye da shi ya "tafasa." Bayaninsa yana kama da dabbar da ake kira Dinaso.
  • Ishaya ya bayyana Lebiyatan a matsayin "maciji mai shawagi."
  • Ayuba yayi rubutu a matsayin wanda ke da ilimin Lebiyatan, ana kyautata zaton cewa zamanin rayuwarsa akwai dabbar.

(Hakanan duba: Ishaya, Ayuba, maciji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 03:08
  • Zabura 104:25-26

Listra

Gaskiya

Listra birni ne a zamanin dã cikin Asiya ‌Ƙarama da Bulus ya ziyarta a tafiyarsa ta bishara. An kafa mazauninta a yankin Likaoniya, wadda take yanzu a ƙasar Turkiya ko Toki ta wannan zamani'

  • Bulus da abokansa sun kubce zuwa Derbi da Listra da haka Yahudawan Ikoniyum suka kai masu hari.
  • A Listra Bulus ya gamu da Timoti, wanda ya zama abokin bishara da mai kafa ikilisiya.
  • Bayan da Bulus ya warkar da wani mutum gurgu a Listra, mutanen wurin suka yi ƙoƙarin su yiwa Bulus da Barnabas sujada kamar alloli, amma manzannin suka kwaɓe su suka hana su yin haka.

(Hakanan duba: mai bishara, Ikoniyum, Timoti)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 03:10-13
  • Ayyukan Manzanni 14:06
  • Ayyukan Manzanni 14:08
  • Ayyukan Manzanni 14:21-22

Liya

Gaskiya

Liya na ɗaya daga cikin matan Yakubu. Ita ce mahaifiyar goma daga cikin 'ya'ya maza na Yakubu kuma zuriyarsu sune goma daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila.

  • Mahaifin Liya shi ne Laban, wanda kuma shi ɗan'uwan Rebeka ne mahaifiyar Yakubu.
  • Yakubu bai ƙaunaci Liya ba kamar yadda ya ƙaunaci ɗaya matar tasa, Rahila, amma Allah ya albarkaci Liya a yalwace ta wurin ba ta 'ya'ya da yawa.
  • ‌Ɗan Liya Yahuda shi ne kakan Sarki Dauda da Yesu.

(Hakanan duba: Yakubu, Yahuda, Laban, Rahila, Rebeka, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 29:17
  • Farawa 29:28
  • Farawa 31:06
  • Rut 04:11

Lot

Gaskiya

Lot ɗan ɗan'uwan Ibrahim ne.

  • Shi ɗan Haran ne ɗan'uwan Ibrahim.
  • Lot ya tafi tare da Ibrahim zuwa ƙasar Kan'ana ya zauna a cikin birnin Sodom.
  • Lot shi ne kakan Mowabawa da Ammoniyawa.
  • Da sarakai maƙiya suka kai wa Sodom Hari suka kuma kama Lot, Ibrahim ya zo da ɗaruruwan mutane ya ƙwato Lot ya kuma karɓo kadarorinsa.
  • Mutane dake zaune a birnin Sodom mugaye ne, saboda haka Allah ya hallaka birnin. Amma da farko ya faɗa wa Lot da iyalinsa su bar birnin domin su kuɓuta.

(Hakanan duba: Ibrahim, Ammon, Haran, Mowab, Sodom)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:08
  • Farawa 11:27-28
  • Farawa 12:4-5

Luka

Gaskiya

Luka ya rubuta litattafai biyu na Sabon Alƙawari: bishara ta hannun Luka da Ayyukan Manzanni.

  • A cikin wasiƙarsa ga Kolosiyawa, Bulus ya ambaci Luka likita ne. Bulus kuma ya yi faɗi a kan Luka a cikin wasu wasiƙunsa guda biyu.
  • Ana tsammani Luka ɗan harshen Girik ne kuma Ba'al'umme ne wanda ya zo ga sanin Yesu. A cikin Bishararsa, Luka ya faɗi a wurare da dama cikin rubutunsa da suka shaida ƙaunar Yesu ga dukkan mutane, Yahudawa da Al'ummai.
  • Luka ya tafi tare da Bulus a cikin tafiyar bishararsa sau biyu ya taimake shi cikin aikinsa.
  • A wasu rubutun ikilisiya ta farko, aka ce an haifi Luka a Antiyok ta Asiriya.

(Duba kuma: Antiyok, Bulus, Asiriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:11-12
  • Kolosiyawa 04:12-14
  • Filimon 01:24

Ma'aka

Gaskiya

Ma'aka ɗaya ne daga cikin 'ya'yan ɗan'uwan Ibrahim, Naho. Wasu mutane ma a cikin Tsohon Alƙawari suna da wannan suna.

  • Birnin Ma'aka ko Bet Ma'aka an kafa ta nesa ne arewacin Isra'ila, a yankin da kabilar Naftali ta mallaka.
  • Muhimmin birni ne kuma abokan gãba sun hari birnin sau da yawa.
  • Ma'aka sunan mataye ne da yawa, har da mahaifiyar ɗan Dauda Absalom.
  • Sarki Asa ya cire kakarsa Ma'aka daga zama sarauniya domin ta girmama sujada ga allahiya Ashera.

(Hakanan duba: Asa, Ashera, Naho, Naftali, kabilu goma sha biyu na Isra'ila)

  • Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

Mahallici

Gaskiya

A taƙaice "Mahallici" wani ne da yake hallita ko ya yi abubuwa.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "Mahallici" ana amfani da ita a kira Yahweh, domin shi ne ya hallici komai da komai.
  • Yawancin lokaci a kan haɗa da waɗannan kalmomi "na sa" ko "na wa" ko "na ku."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "Mahallici" za a iya fassara ta haka "Mai Hallita" ko "Allah dake yin hallita" ko "Wanda ya yi komai da komai."
  • Wannan furci "mahallicinsa" za a iya fassara ta haka "Wannan da ya hallice shi" ko "Allah daya hallice shi."
  • Wannan furci "Mahallicin ka" da Mahallici na" za a iya basu fassara guda.

(Hakanan duba: hallici, Yahweh)

Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Hosiya 08:13-14

Maikayel

Gaskiya

Maikayel shi ne sarki cikin dukkan tsarkakan Allah, mala'ikun dake masa biyayya. Shi ne kaɗai mala'ikan da aka ambata musamman "babban mala'ika na Allah.

  • Wannan kalma "babban mala'ika" na nufin "mafi girma cikin mala'iku" ko "mala'ika mai mulki."
  • Makel mayaƙi ne dake yaƙar maƙiyan Allah yana kare mutanen Allah.
  • Ya bida Isra'ilawa yaƙi gãba da rundunar Fasiya. A ƙarshen zamani zai bida rundunonin Isra'ila a yaƙi na ƙarshe gãba da ikokin mugunta, kamar yadda Daniyel ya yi anabci.
  • Akwai mazaje da dama a Littafi Mai Tsarki masu suna Makel. Mazaje da yawa an ambacesu da sunan "ɗan Maikayel."

(Hakanen duba: mai'laka, Daniyel, manzo, Fasiya)

Wurarea da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 10:13
  • Daniyel 10:21
  • Ezra 08:08
  • Wahayin Yahaya 12:7-9

Malakai

Gaskiya

Malakai ɗaya ne daga cikin annabawan Allah zuwa ga mulkin Yahuda. Ya kasance misalin shekaru 500 kafin Almasihu ya zo duniya.

  • Malakai yayi annabci a lokacin da ake gina haikalin Isra'ilawa bayan komowarsu daga bautar talala a Babila.
  • Ezra da Nehemiya sun yi rayuwa a lokaci guda da Malakai.
  • Littafin Malakai shi ne littafi na ƙarshe a Tsohon Alƙawari.
  • Kamar dukkan annabawan Tsohon Alƙawari, Malakai ya matsa wa mutane su tuba daga zunubansu su juyo ga yin sujada ga Yahweh.

(Hakanan duba: Babila, kamamme, Ezra, Yahuda, Nehemiya, Annabi, tuba, juyowa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Malakai 01:01

Manasse

Gaskiya

Akwai mutane biyar da ake kiransu da sunan Manasse a cikin Tsohon Alƙawari:

  • Manasse sunan ɗan farin Yosef ne.
  • Manasse da ƙanensa Ifraim Yakubu mahaifin Yosef ya karbe su tankar 'ya'yansa wannan ya ba zuriyarsu 'yancin zama cikin kabilu goma sha biyu na Isra'ila.
  • Zuriyar Manasse ta zama ɗaya daga cikin kabilun Isra'ila.
  • Yawancin lokaci ana kiran kabilar Manasse "rabin kabilar Manasse" domin wani sashen kabilar ne suka zauna a cikin ƙasar Kan'ana yamma da Kogin Yodan. Sauran kabilar suka zauna a gabashin Yodan.
  • Guda daga cikin sarakunan Yahuda shi ma ana kiransa Manasse.
  • Sarki Manasse mugun sarki ne wanda ya bada 'ya'yansa hadayar ƙonawa ga gumaku.
  • Allah ya hukunta Sarki Manasse ya bari abokan gãba suka cafke shi. Daga baya Manasse ya juyo ya rushe bagadai inda ake sujada ga gumaku.

(Hakanan duba: bagadi, Dan, Ifraim, Ezra, gumaka, Yakubu, Yahuda, al'ummai, kabilu goma sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 15:09
  • Maimaitawar Shari'a 03:12-13
  • Farawa 41:51
  • Farawa 48:1-2
  • Littafin Alƙalai 01:27-28

Marta

Gaskiya

Marta mace ce daga Betani da ta bi Yesu.

  • Marta tana da 'yar'uwa Maryamu da ɗan'uwa ana ce da shi La'azaru, wanda shi ma mai bin Yesu ne.
  • Wata rana da Yesu ya ziyarce su a gida, Marta ta sa hankalinta kan girke-girke, Maryamu 'yar'uwarta kuwa ta zauna tana sauraron koyarwar Yesu.
  • Da La'azaru ya mutu, Marta ta cewa Yesu ta gaskanta shi ne Almasihu ‌Ɗan Allah.

(Hakanan duba: La'azaru, Maryamu ('yar'uwar Marta))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 11:02
  • Yahaya 12:1-3
  • Luka 10:39

Maryamu ('yar'uwar Marta)

Gaskiya

Maryamu macece daga Betani data bi Yesu.

  • Maryamu tana da 'yar'uwa da ake kira Marta da ɗan 'uwansu da ake ce da shi La'azaru wanda shi ma ya bi Yesu
  • A wani lokaci Yesu ya ce Maryamu ta zaɓi abu mafi kyau da ta zaɓa ta saurari koyarwarsa maimakon damuwar girka masa abinci kamar Marta.
  • Yesu ya komo wa La'azaru da rai shi ɗan 'uwan Maryamu ne.
  • Wani lokaci bayan wannan, lokacin da Yesu yake cin abinci a gidan wani mutum a Betani, Maryamu ta zuba masa turare mai tsada a ƙafafunsa domin ta yi masa sujada.
  • Yesu ya yabe ta da yin haka ya ce tana shirya shi ne domin jana'izarsa.

(Hakanan duba: Betani, frankinsens, La'azaru, Marta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 11:1-2
  • Yahaya 12:1-3
  • Luka10:38-39

Maryamu Magadalin

Gaskiya

Maryamu Magadalin tana ɗaya daga cikin mataye da yawa da suka bada gaskiya ga Yesu suka bishi cikin aikin bishara. An santa da wadda Yesu ya warkar da ita daga aljannu bakwai masu juyata.

  • Maryamu Magadalin da wasu matan sun taimaka wa Yesu da manzanninsa ta wurin tallafin da suka basu.
  • An kuma faɗi cewa tana ɗaya daga cikin mataye da suka fara ganin Yesu bayan ya tashi daga matattu.
  • Sa'ad da Maryamu tana tsaye a waje, taga Yesu yana tsaye a wurin ya kuma gaya mata ta je ta shaida wa sauran almajiran cewa yana da rai kuma.

(Hakanan duba: aljannu, taɓuwar aljannu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 08:1-3
  • Luka 24:8-10
  • Markus 15:39-41
  • Matiyu 27:54-56

Maryamu, uwar Yesu

Gaskiya

‌Maryamu matashiyar mace ce wadda take zaune a Nazaret wadda kuma aka alƙawarta wa wani mutum a aure mai suna Yosef. Allah ya zaɓi Maryamu ta zama mahaifiyar Yesu Almasihu,‌ Ɗan Allah.

  • Ruhu Mai Tsarki ta wurin al'ajibi ya sa Maryamu ta yi ciki tun tana budurwa.
  • Mala'ika ya gaya mata jaririn da zata haifa ‌Ɗan Allah ne kuma dole tasa masa suna Yesu.
  • Maryamu tana ƙaunar Allah ta kuma yabe shi domin alherin da ya yi mata.
  • Yosef ya auri Maryamu, amma ta kasance budurwa har sai da ta haifi jaririn.
  • Maryamu ta yi tunani mai zurfi game da abubuwan al'ajibi da makiyaya da shehuna suka faɗi game da jariri Yesu.
  • Maryamu da Yosef suka ɗauki ɗan jaririn nan Yesu garin su miƙa shi a haikali. Daga baya suka tafi da shi Masar domin su kubce wa shirin da Sarki Hiridus ya ƙulla ya kashe jaririn. A ƙarshe suka koma Nazaret.
  • Da Yesu ya yi girma, Maryamu tana tare da shi lokacin da ya canza ruwa ya zama ruwan inabi a wani ɗaurin aure a Kana.
  • Litattafan Bishara sun ce Maryamu tana a gindin gicciye lokacin da Yesu yake mutuwa. Ya gaya wa almajirinsa Yahaya ya lura da ita kamar mahaifiyarsa.

(Hakanan duba: Kana, Masar, Herod Babba, Yesu, Yosef (Sabon Alƙawari), ‌Ɗan Allah, budurwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 02:04
  • Yahaya 02:12
  • Luka 01:29
  • Luka 01:35
  • Markus 06:03
  • Matiyu 01:16
  • Matiyu 01:19

Masar, Bamasare, Masarawa

Gaskiya

Masar ƙasa ce a arewa maso gabashin Afirka, a yankin yamma maso kudu na Kan'ana. Bamasare shi ne mutumin da ya zo daga Masar.

  • A kwanakin can can baya Masar tana da iko sosai kuma ƙasa ce mai wadata.
  • A lokuta masu yawa a lokacin fda aka sami ƙaranci abinci a Kan'ana, ubannin Isra'ila kan je Masar domin ayen abinci domin iyalansu.
  • Isra'ila sun kasance bayi a Masar na tsawon shekaru mau yawa.

Yusufu da Maryamu sun gangara zuwa Masar tare da yaronsu Yesu domin tsira daga Herod Babba.

(Hakanan duba: Herodus Babba, Yosef (Tsohon Alƙawari), Kogin Nilu, ubanni)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 04:7-9
  • Ayyukan Manzanni 07:10
  • Fitowa 03:7
  • Farawa 41:29
  • Farawa 41:57
  • Matiyu 02:15

masarautar Isra'ila

Gaskiya

Inda aka sani da arewacin ƙasar Isra'ila shi ne ya zama mulkin Isra'ila sa'ad da kabilun Isra'ila sha biyu suka rabu zuwa masarautu biyu bayan mutuwar Suleman.

  • Masarautar Isra'ila a arewa nada kabilu sha biyu, masarautar Yahuda kuma a kudu nada kabilu biyu.
  • Babban birnin masarautar Isra'ila shi ne Samariya. Kilomita 50 ne daga Yerusalem, babban birnin masarautar Yahuda.
  • Dukkan sarakunan masarautar Isra'ila miyagu ne. Suka janye mutane zuwa bautar gumaka da allolin ƙarya.
  • Allah ya aiki Asiriyawa suka kai hari ga masarautar Isra'ila. Aka kama Isra'ilawa da yawa aka tafi dasu su zauna a Asiriya.
  • Asiriyawa suka kawo bãƙi su zauna da sauran mutanen masarautar Isra'ila. Waɗannan bãƙi suka shiga auratayya da Isra'ilawa, daga nan kuma zuriyarsu suka zama mutanen Samariya.

(Hakanan duba: Asiriya, Isra'ila, Yahuda, Yerusalem, masarauta, Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 35:18
  • Irmiya 05:11
  • Irmiya 09:26

Masidoniya

Gaskiya

A lokatan Sabon Alƙawari, Masidoniya wani lardin Roma ne wanda ke yamma da Giris ta zamanin dã.

  • Wasu mahimman biranen Masidoniya da Littafi Mai Tsarki ya faɗa sune Bereya, Filifai da Tasalonika.
  • Tawurin wahayi Allah ya ce wa Bulus ya yi wa'azin bishara a Masidoniya.
  • Bulus da abokan aikinsa suka tafi Masidoniya suka koya wa mutanen can game da Yesu suka kuma taimaki sabobbin tuba su yi girma cikin bangaskiyarsu.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki akwai wasiƙu da Bulus ya rubuta wa masu bada gaskiya a biranen Masidoniya kamar su Filifai da Tasalonika.

(Hakanan duba: gaskatawa, Biriya, bangaskiya, labari mai daɗi, Giris, Filifai, Tasalonika)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 01:6-7
  • 1 Tasalonikawa 04:10
  • 1 Timoti 01:01:3-4
  • Ayyukan Manzanni 16:10
  • Ayyukan Manzanni 20:1-3
  • Filibiyawa 04:14-17

Matiyu, Lebi

Gaskiya

Matiyu ɗaya daga cikin mazaje goma sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama manzanninsa. An san shi kuma da Lebi ɗan Alfiyas.

  • Lebi (Matiyu) mai karɓar haraji ne daga Kafarnahum kafin ya sadu da Yesu.
  • Matiyu ya rubuta bishara dake da sunansa.
  • Da akwai wasu mazaje masu sunan Lebi da yawa a Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: manzanni, Lebiyawa, mai karɓar haraji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 05:27
  • Luka 06:14-16
  • Markus 02:14
  • Markus 03:17-19
  • Matiyu 09:09
  • Matiyu 10:03

Mede, Medes, Mediya

Gaskiya

Mediya tsohuwar masarauta ce ta dã yamma da Asiriya da Babiloniya, kuma arewa da Elam da Fasiya. Mutanen da suka zauna a masarautar Mediya ana ce da su "Medes."

  • Mulkin Mediya ya haɗa da wasu yankin da yau ana ce da ita Turkaniya ko Toki, Iran, Siriya, Irak da Afganistan.
  • Mutanen Medes sun yi dangantaka da Fasiyawa mulkokin biyu suka haɗa ƙarfinsu suka cinye mulkin Babila.
  • Dariyus Ba'mede ya hari Babiloniya lokacin da annabi Daniyel yake zaune can.

(Hakanan duba: Asiriya, Babilon, Sairus, Daniyel, Dariyus, Elam, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 17:06
  • Ayyukan Manzanni 02:09
  • Daniyel 05:28
  • Esta 01:3-4
  • Ezra 06:1-2

Melkizedek

Gaskiya

A lokacin da Abram ya yi rayuwa, Melkizedek ne sarkin birnin Salem (daga baya "Yerusalem")

  • Ma'anar sunan Melkizedek shi ne "sarkin adalci" sunan naɗinsa "sarkin Salem" ma'anar kuwa "sarkin salama."
  • An kuma kira shi "firist na Allah Maɗaukaki."
  • An fara ambaton Melkizedek a Littafi Mai Tsarki da ya ba Abram waina da ruwan inabi bayan Abram ya tsirar da ɗan ɗan'uwansa Lot daga sarakuna masu ƙarfi. Abram ya ba Melkizedek ɗaya bisa goma na ganimar nasarar da ya ciwo.
  • A cikin Sabon Alƙawari, an ambaci Melkizedek wani mutum ne da bashi damahaifi ko mahaifiya. An kira shi firist da sarki da zai yi mulki har abada.
  • Sabon Alƙawari ya ce Yesu firist ne bisa ga "irin matsayi na Melkizedek." Yesu ba daga zuriyar Lebi yake ba kamar yadda firistocin Isra'ila suke. Firistancinsa daga Allah yake, kamar yadda na Melkizedek yake.
  • Bisa ga wannan furci a Littafi Mai Tsarki, Melkizedek mutum ne kuma firist wanda Allah ya zaɓa ya wakilci ko ya nuna Yesu a bisani, sarki na har'abada na salama da adalci da kuma namu babban firist.

(Hakanan duba: Ibrahim, har abada, babban firist, Yerusalem, Lebiyawa, firist, adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 14:18
  • Ibraniyawa 06:20
  • Ibraniyawa o7:17
  • Zabura 110:4

Memfis

Gaskiya

Memfis wata daɗaɗɗar cibiyar birni ce a Masar, a gaɓar Kogin Nilu.

  • Memfis ta kasance a Masar ta ‌gangare, kudu da mashigar Kogin Nilu, inda ƙasar ke da tãki da amfani kuma da yawa.
  • ‌Ƙasarta mai ma'armashi da mazauninta tsakanin Masar ta Tudu da Gangare yasa Memfis ta zama babban birnin Kasuwanci da dillanci.

(Hakanan duba: Masar, Kogin Nilu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Hosiya 09:06

Meshek

Gaskiya

Meshek sunayen mutane biyu ne a Tsohon Alƙawari.

  • Wani Meshek ɗan Yafet ne.
  • ‌Ɗ‌aya Meshek ɗin jikan Shem.
  • Meshek kuma sunan yankin ƙasa ne, wanda watakila aka bata sunan ɗaya daga cikin mazajen nan.
  • Yankin Meshek watakila ta kasance a sashin da yanzu ake ce da ita Turkaniya ko Toki.

(Hakanan duba: Yafet, Nuhu, Shem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:5-7
  • Ezekiyel 27:12-13
  • Farawa 10:2-5
  • Zabura 120:05

Mesofotamiya, Aram Naharayim

Gaskiya

Mesofotamiya ita ce yankin ƙasar dake tsakanin Tigris da Kogunan Yufiretis. Mazauninta a dã wajen yankin ƙasar da take Iraƙ ne yanzu.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, wannan yanki ana kirasa "Aram Naharayim."
  • Kalmar nan "Mesofotamiya" ma'anarta "tsakiyar rafuffuka." Wannan furci "Aram Naharayim" kuwa ma'anarta "Aram ta koguna biyu."
  • Ibrahim ya zauna a biranen Mesofotamiya ta Ur da Haran kafin ya tashi zuwa ƙasar Kan'ana.
  • Babila birni ne mai mahimmanci a Mesofotamiya.
  • Yankin da ake kira "Kaldiya" shi ma cikin Mesofotamiya yake.

(Hakanan duba: Aram, Babila, Kaldiya, Kogin Yuferitis)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:09
  • Ayyukan Manzanni 07:1-3
  • Farawa 24:10-11

Midiyan, Bamidiye, Midiyawa

Gaskiya

Midiyan ɗan Ibrahim ne ta wurin matarsa Ketura. Kuma wannan sunan wasu ƙungiyar mutane ne da wani yanki dake Hamadar Arebiya ta Arewa wajen kudu da ƙasar Kan'ana. Mutanen ƙungiyar nan ana kiransu "Midiyawa."

  • Lokacin da Musa ya bar Masar da fari, ya tafi zuwa yankin Midiyan inda ya gamu da 'ya'ya mata na Yetro ya taimake su shayar da tumakinsu. Daga bisani Musa ya auri ɗaya daga cikin 'ya'ya mata na Yetro.
  • An kai Yosef Masar ta wurin wata ƙungiyar Midiyawa masu cinikin bayi.
  • Bayan shekaru masu yawa Midiyawa suka kai wa Isra'ilawa hari suka washe su cikin ƙasar Kan'ana. Gidiyon ya bida Isra'ilawa suka ci sua yaƙi.
  • Yawanci kabilun Arebiya na wannan zamani zuriyar waɗannan ƙungiyar ne.

(Hakanan duba: Arabiya, Masar, tumaki, Gidiyon, Yetro, Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:30
  • Fitowa 02:16
  • Farawa 25:1-4
  • Farawa 36:34-36
  • Farawa 37:28
  • Littafin Alƙalai 07:1

Mika

Gaskiya

Mika annabin Yahuda ne wajen shekaru 700 kafin Almasihu, lokacin da annabi Ishaya yake hidima ga Yahuda. Wani mutum kuma mai suna Mika ya yi rayuwa a lokacin mahukunta.

  • Littafin Mika yana kusa da ƙarshen Tsohon Alƙawari.
  • Mika ya yi annabci akan rushewar Samariya ta wurin Asiriyawa.
  • Mika ya kwaɓi mutanen Yahuda saboda rashin biyayyarsu ga Allah ya yi masu kashedi cewa maƙiyansu zasu kawo masu hari.
  • Annabcinsa ya ƙare da saƙon bege cikin Allah, wanda yake da aminci kuma mai ceton mutanensa.
  • A littafi Alƙalai, an bada labarin wani mutum mai suna Mika yana zaune a Ifraim wanda ya yi gunki da azurfa. Wani matashi firist yazo ya zauna da shi ya sace gunkin da wasu abubuwa da dama ya tashi ya tsere da wasu ƙungiyar Danawa. A ƙarshe Danawan da firist ɗin suka zauna a birnin Layish suka kuma kafa wannan gunkin suka yi masa sujada.

(Hakanan duba: Asiriya, Dan, Ifraim, gunki, Ishaya, Yahuda, mahukunta, Lebiyawa, firist, annabi, Samariya, azurfa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 26: 18-19
  • Mika 01:1
  • Mika 06:02

Miriyam

Gaskiya

Miriyam yayar su Haruna ne da Musa.

  • Lokacin da Miriyam take yarinya matashiya, mahaifiyarta ta gargaɗe ta da ta duba jariri ƙanenta Musa dake cikin kwando a cikin iwa na Kogin Nilu. Da ɗiyar fir'auna ta tsinci jaririn taga tana buƙatar wani mutum da zai lurar mata da shi, Miriyam ta kawo mahaifiyarta ta karɓi renon.
  • Miriyam ta bida Isra'ilawa a rawar murna da godiya bayan sun kuɓuta daga Masarawa da suka tsallake Jan Teku."
  • Bayan shekaru da yawa da Isra'ilawa suka yita yawo a jeji, Miriyam da Haruna suka faɗi abu marar kyau akan Musa domin ya auri Ba'kushiyar mata.
  • Saboda tawayen maganar da suka yi gãba da Musa, Allah yasa Miriyam ta kamu da cutar kuturta. Daga baya Allah ya warkar da ita da Musa ya yi roƙo dominta.

(Hakanan duba: Haruna, Kush, roƙo domin, Musa, Kogin Nilu, Fir'auna, tawaye.)

Wuraren da ake samusa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:1-3
  • Maimaitawar Shari'a 24:8-9
  • Mika 06:04
  • Littafin ‌Lissafi 12:02
  • Littafin ‌Lissafi 20:01

Mishayel

Gaskiya

Mishayel sunan mutum uku ne a Tsohon Alƙawari.

  • Wani mutum da ake ce da shi Mishayel ɗan ɗan'uwan Harunan ne. Lokacin da Allah ya kashe 'ya'yan Haruna maza biyu bayan sun miƙa turare ta hanyar da Allah bai tsara masu ba, Mishayel da ɗan'uwansa aka basu hidimar ɗaukar gawawakin zuwa bayan sansanin Isra'ilawa.
  • Wani mutum kuma da ake ce da shi Mishayel ya tsaya a gefen Ezra lokaci da Ezra yake karanta littafin shari'a da aka binciko a gaban jama'a.
  • Lokacin da mutanen Isra'ila suke bautar talala a Babila, wani yaro matashi da ake kira Mishayel an kama shi shima kuma aka tilasta masa ya zauna a Babila. Babiloniyawa suka bashi suna, "Meshak." Da shi da abokansa, Azriya (shadrak) da Hananiya (Abednego), suka ƙi suyi sujada ga siffar sarki sai aka jefa su cikin tanderun wuta.

(Hakanan duba: Haruna, Azariya, Babila, Daniyel, Hananiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 01:6-7
  • Daniyel 02:17-18

Mizfa

Gaskiya

Mizfa sunan garuruwa ne da yawa da aka faɗesu a cikin Tsohon Alƙawari. ma'anar shi ne, "wurin dubawa" ko "soron dubawa."

  • Lokacin da Saul yake fafarar Dauda, ya bar iyayensa a Mizfa, a ƙarƙashin tsaron sarkin Mowab.
  • Wani birni da ake kira Mizfa an kafa shi tsakiyar kan iyakar mulkin Yahuda da Isra'ila. Babban wurin mayaƙa ne.

(Hakanan duba: Dauda, Yahuda, sarautar Isra'ila, Mowab, Saul (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 15:20-22
  • 1 Sama'ila 07:5-6
  • 1 Sama'ila 07:10-11
  • Irmiya 40:5-6
  • Littafin Alƙalai 10:17-18

Modakai

Gaskiya

Modakai Bayahuden mutum ne da ya zauna a ƙasar Fasiya. Shi ne mai lura da ɗiyar ɗan'uwansa Esta, wadda daga bisani ta zama matar sarkin Fasiya, Ahasurus.

  • Sa'ad da yake aiki a fadar masarauta, Modakai ya ji mutane na shirin su kashe sarki Ahasurus. Ya je ya fallasa wannan al'amari ran sarki ya tsira.
  • Bayan wannan, Modakai kuma ya gano shirin da ake yi domin a kashe dukkan Yahudawa a mulkin Fasiya. Ya ba Esta shawara ta roƙi sarki ya ceci mutanenta.

(Hakanan duba: Ahasurus, Babila, Esta, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Esta 02:06
  • Esta 03:06
  • Esta 08:02
  • Esta 10:02

Molek, Molok

Gaskiya

Molek sunan ɗaya daga cikin gumakun da Kan'aniyawa suke yiwa sujada. Wasu sukan rubuta shi haka "Molok" da "Molek."

  • Mutanen dake yiwa Molek sujada suna miƙa masa 'ya'yansu hadaya ta wurin wuta.
  • Wasu Isra'ilawa kuma sun yi wa Molek sujada maimakon Allah na gaskiya, Yahweh. Suka bi ayyukan mugunta na masu yiwa Molek sujada. har ma da miƙa 'ya'yansu hadaya.

(Hakanan duba: Kan'ana, mugunta, gunki, Allah, hadaya, gaskiya, sujada, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 11:07
  • 2 Sarakuna 23:10
  • Ayyukan Manzanni 07:10
  • Irmiya 32:33-35
  • Lebitikus 18:21

Mowab, Ba'mowabe, Ba'mowaba

Gaskiya

Mowab ɗan ɗiyar Lot ta fari ne. Ya kuma zama sunan ƙasar da shi da iyalinsa suka zauna. Wannan magana "Ba'mowabe" ana nufin mutumin da ya fito daga zuriyar Mowab ko kuma yana zaune a ƙasar Mowab.

  • ‌Ƙasar Mowab tana gabashin Tekun Gishiri.
  • Mowab tana kudu maso gabas da garin Betlehem inda iyalin Na'omi suka zauna.
  • Mutanen Betlehem suka kira Rut "Ba'mowaba" domin ita macece daga ƙasar Mowab. Wannan kalma za a iya fassarata a ce "mace Ba'mowaba" ko "mace daga Mowab."

(Hakanan duba: Betlehem, Yahudiya, Lot, Rut, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farwa 19:37
  • Farawa 36:34-36
  • Rut 01:1-2
  • Rut 01:22

Musa

Gaskiya

Musa annabi ne kuma shugaban mutanen Isra'ila tsawon shekaru sama da 40.

  • Da Musa yake ɗan jariri, iyayen Musa suka sa shi a cikin kwando a ciyayin iwa na Kogin Nilu domin su ɓoye shi daga fir'auna a Masar. 'Yar'uwar Musa Maryamu ita ce ta lura da shi a wurin. Ran Musa ya tsira sa'ad da ɗiyar Fir'auna ta same shi ta ɗauke shi ta kai shi fada domin ta girmar da shi a matsayin ɗanta.
  • Allah ya zaɓi Musa domin ya fitar da Isra'ilawa daga bauta a Masar ya kuma bishe su zuwa Ƙasar Alƙawari.
  • Bayan da Isra'ilawa suka kubce daga Masar da lokacin da suke yawo a jeji, Allah ya ba Musa duwatsu biyu da Dokoki Goma a rubuce a kansu.
  • Wajen ƙarshen rayuwarsa Musa ya hangi Kasar Alƙawari, amma bai shiga ya zauna a cikinta ba domin ya yiwa Allah rashin biyayya.

(Hakanan duba: Miriyam, ‌Ƙasar Alƙawari, Dokoki Goma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:04
  • Ayyukan Manzanni 07:30
  • Fitowa 02:10
  • Fitowa 09:01
  • Matiyu 17:04
  • Romawa 05:14

mutumin Allah

Gaskiya

Wannan furci "mutumin Allah" magana ce ta girmama annabin Yahweh. A kan kuma yi amfani da ita idan ana ambaton mala'ikanYahweh.

  • Sa'ad da ana magana a kan annabi, za a iya fassara wannan haka "mutumin dake na Allah" ko "mutumin da Allah ya zaɓa" ko "mutumin da yake bauta wa Allah."
  • Sa'ad da ana magana a kan mala'ika za a iya fassara wannan a ce "manzon Allah" ko "'mala'ikan ka" ko "wani taliki daga Allah da ya yi kama da mutum."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 23:12-14
  • 1 Sarakuna 12:22
  • 1 Sama'ila 09:9-11

Na'aman

Gaskiya

A cikin Tsohon Alƙawari, Na'aman shi ne shugaban rundunar mayaƙan sarkin Aram.

  • Na'aman yana da mummunan ciwon fatar jiki da ake kira kuturta da ba a iya warkarwa.
  • Wata baiwa Ba'yahudiya a cikin gidan Na'aman ta gaya masa, ya je ya roƙi annabi Elisha ya warkar da shi.
  • Elisha ya ce wa Na'aman ya yi wanka sau bakwai a Kogin Yodan. Da Na'aman ya yi biyayya, Allah ya warkar da shi daga cutar.
  • Sakamakon haka, Na'aman ya gaskanta da Allah kaɗai na gaskiya Yahweh.
  • Wasu mazaje biyu da ake kiransu Na'aman zuriyar ɗan Yakubu ne Benyamin.

(Hakanan duba: Aram, Kogin Yodan, kuturta, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Tarihi 08:6-7
  • 2 Sarakuna 05:01
  • Luka 04:27

nAdoniya

Gaskiya

Adoniya shi ne ɗan Sarki Dauda na huɗu cikin 'ya'ya maza.

  • Adoniya ya yi ƙoƙarin ya zama sarkin Isra'ila bayan mutuwar 'yan'uwansa maza Absalom da kuma Amnon.
  • Amma dai, Allah ya rigaya ya yiwa Suleman alƙawarin kursiyin Dauda, saboda haka aka hamɓare maƙarƙashiyar Adoniya aka ba Suleman kursiyin.
  • Da Adoniya ya sake neman ya naɗa kansa sarki karo na biyu, Suleman ya kashe shi.

(Hakanan duba: Dauda, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:


Naftali

Gaskiya

Naftali ɗan Yakubu na shida ne. Zuriyarsa ce ta zama kabilar Naftali wadda take ɗaya daga cikin kabilu goma sha biyu na Isra'ila.

  • Wani lokaci ana amfani da sunan Naftali domin a faɗi mazaunin kabilar.
  • ‌Ƙasar Naftali tana arewa da Isra'ila, tana kuma iyaka da kabilar Dan da Asha. Iyakar gabashinta yana yammacin gaɓar Tekun Kinneret.
  • An ambata kabilar a cikin Tsohon Alƙawari da kuma Sabon Alƙawari a Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: Asha, Dan, Yakubu, Tekun Galili, kabilu goma sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:15
  • Maimaitawar Shari'a 27:13-14
  • Ezekiyel 48:1-3
  • Farawa 30:08
  • Littafin Alƙalai 01:33
  • Matiyu 04:13

Naho

Gaskiya

Naho sunan mutum biyu ne 'yan'uwan Ibrahim, kakansa da ɗan'uwansa.

  • ‌Ɗ‌an'uwan Ibrahim Naho shi ne kakan matar Ishaku Rebeka.
  • Wannan magana "birnin Naho" mai yiwuwa "an ba birnin sunan Naho" ko "birnin da Naho ya zauna cikin sa" ko "birnin Naho."

(Hakanan duba: Ibrahim, Rebeka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:24-27
  • Farawa 31:53
  • Yoshuwa 24:02
  • Luka 03:34

Nahum

Gaskiya

Nahum annabi ne wanda ya yi wa'azi a lokacin da mugun Sarki Manasse ke sarauta bisa Yahuda.

  • Nahum ɗan garin Elkosh ne, wanda yake kusan mill 20 daga Yerusalem.
  • Littafin Nahum daga Tsohon Alƙawari ya rubuta anabtai game da hallakarwar Ninibe birnin Asiriyawa.

(Hakanan duba: Asiriya, Manasse, annabi, Ninebe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Nahum 01:01

Natan

Gaskiya

Natan annabin Allah ne mai aminci da ya kasance a lokacin da Dauda yake sarauta bisa Isra'ila.

  • Allah ya aiki Natan ya ta'azantar da Dauda bayan Dauda ya yi mummunan zunubi gãba da Yuriya.
  • Natan ya tsauta wa Dauda koda shike Dauda sarki ne.
  • Dauda ya tuba daga zunubinsa bayan Natan ya bayyana masa.

(Hakanan duba: Dauda, amintacce, annabi, Yuriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 17:1-2
  • 2 Tarihi 09:29
  • 2 Sama'ila 12:1-3
  • Zabura 051:01

Nazaret, Banazare

Gaskiya

Nazaret gari ne a yankin Galili a arewacin Isra'ila. Nazaret wajen kilomita 100 take daga Yerusalem, za a ɗauki kwana uku ko huɗu ana tafiya a ƙafa.

  • Yosef da Maryamu daga Nazaret suke, a nan ne kuma suka girmar da Yesu. Shi yasa aka san Yesu da "Banazare."
  • Yahudawa da yawa mazaunan Nazaret basu ga kwarjinin koyarwar Yesu ba domin ya girma a tsakanin su, sai suka yi zaton kamar su yake."
  • Watarana, Yesu yana koyarwa a Nazaret, Yahudawa suka yi ƙoƙarin su kashe shi domin ya ce shi ne Almasihu, ya kuma tsauta masu domin sun ƙi shi.
  • Furcin da Nataniyel ya yi da ya ji Yesu daga Nazaret yake ya nuna wannan birni bashi da daraja a idanun mutane.

(Hakanan duba: Almasihu, Galili, Yosef (Sabon Alƙawari), Maryamu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 26:9-11
  • Yahaya 01:43-45
  • Luka 01:26-29
  • Markus 16:5-7
  • Matiyu 02:23
  • Matiyu 21:9-11
  • Matiyu 26:71-72

Nebukadnezza

Gaskiya

Nebukadnezza sakin masarautar Babila ne wanda rundunar mayaƙansa mai ƙarfi ta ci ƙungiyar mutane da al'umma da yawa.

  • A ƙarƙashin shugabancin Nebukadnezza, rundunar Babiloniya ta kai hari ta kuma ci sarautar Yahuda a yaƙi, ta kwashe yawancin mutanen Yahuda zuwa Babila ga bauta. Kamammun aka tilas ta masu su zauna a can har shekara 70 wannan shi ne shekarun da ake kira "Kwashewa zuwa Babila."
  • ‌Ɗ‌aya daga cikin waɗanda aka kwasa, Daniyel ya fassara wasu daga cikin mafarkan sarki Nebukadnezza.
  • Wasu Isra'ilawa guda uku da aka kama, Hananiya, Mishayel, da Azariya, an jefa su cikin tanderun wuta da suka ƙi su rusuna wa wani gagarumin gunkin zinariya da Nebukadnezza ya yi.
  • Sarki Nebukadnezza mai taurin kai ne yana kuma yin sujada ga gumaka. Lokacin da ya ci Yahuda da yaƙi, ya sato kayayyakin zinariya da azurfa da yawa daga haikali a Yerusalem.
  • Saboda Nebukadnezza yana da giman kai ya kuma ƙi ya juyo daga bautar gumaku, Yahweh ya sa shi kaɗaici shekara bakwai, yana zaune kamar dabba. Bayan shekara bakwai, Allah ya maido da Nebukadnezza sa'ad da ya ƙasƙantar da kansa ya yabi Allah kaɗai na gaskiya, Yahweh.

(Hakanan duba: girman kai, Azariya, Babila, Hananiya, Mishayel)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:15
  • 2 Sarakuna 25:1-3
  • Daniyel 01:02
  • Daniyel 04:04
  • Ezekiyel 26:08

Negeb

Gaskiya

Negeb wani yankin hamada ne a kudancin Isra'ila, kudu maso yamma kuma da Tekun Gishiri.

  • Ainihin ma'anar kalmar shi ne "Kudu," wasu juyin Turanci sukan fassara shi haka.
  • Mai yiwuwa ne "Kudu" bata inda Hamadar Negeb take a yau.
  • Lokacin da Ibrahim ya zauna a cikin birnin Kadesh, yana cikin Negev ko a kudanci yankin.
  • Ishaku yana zaune a Negev lokacin da Rebeka ta taho ta gamu da shi ta zama matarsa.
  • Kabilar Yahudawa ta Yahuda da Simiyon sun zauna a kudancin yankin.
  • Babban birni mafi girma a Negeb ita ce Biyasheba

(Hakanan duba: Ibrahim, Biyasheba, Isra'ila, Yahuda, Kadesh, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 12:09
  • Farawa 20:1-3
  • Farawa 24:62
  • Yoshuwa o3:14-16
  • Littafin ‌Lissafi 13:17-20

Nehemiya

Gaskiya

Nehemiya Ba'isra'ile ne da dole ya tafi ƙasar Babiloniya sa'ad da Babiloniyawa suka kwashe mutanen Isra'ila da Yahuda zuwa bautar talala.

  • Lokacin da yake Mai shayarwa ga Sarkin Fasiya, Atazazas, Nehemiya ya roƙi sarki iznin ya koma Yerusalem.
  • Nehemiya ya bida Isra'ilawa a gina ganuwar Yerushalem wanda Babiloniyawa suka rushe.
  • Nehemiya yayi shekara goma sha biyu yana shugabanci a Yerusalem kafin ya koma fadar sarki.
  • Littafin Nehemiya a Tsohon Alƙawari ya bada labarin ayyukan Nehemiya na sake gina ganuwa da shugabantar da mutanen Yerusalem.
  • Akwai kuma wasu mutane masu sunan Nehemiya a Tsohon Alƙawari. Yawancin lokaci akan ƙara da sunan mahaifi domin a banbanta wane Nehemiyan ake magana a kai.

(Hakanan duba: Atazazas, Babila, Yerusalem, ɗa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 02:1-2
  • Nehemiya 01:02
  • Nehemiya 10:03
  • Nehemiya 12:46

Ninebe, Baninebe

Gaskiya

Ninebe ne babban birnin Asiriya. Baninebe shi ne wanda yake zaune a Ninebe.

  • Allah ya aiki annabi Yonah ya faɗakar da Ninebawa su juyo daga hanyoyin muguntarsu. Mutanen suka tuba Allah kuma bai hallaka su ba.
  • Daga baya Asiriyawa suka daina bauta wa Allah. Suka ci sarautar Isra'ila suka kwashe mutanen zuwa Ninebe.

(Hakanan duba: Asiriya, Yona, tuba, juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:11-14
  • Yona 01:03
  • Yona 03:03
  • Luka 11:32
  • Matiyu 12:41

Nuhu

Gaskiya

Nuhu mutum ne da ya yi rayuwa wajen sama da shekaru 4,000 da suka wuce, a lokacin da Allah ya aiko da ambaliyar ruwa da ya game duniya dukka ya hallaka dukkan mugayen mutane dake a duniya. Allah ya ce wa Nuhu ya gina wani makeken jirgi wanda shi da iyalinsa zasu zauna a ciki sa'ad da ruwa ya rufe fuskar duniya.

  • Nuhu adilin mutum ne wanda ya yi biyayya da Allah cikin dukkan abu.
  • Da Allah ya ce Nuhu ya gina makeken jirgi, Nuhu ya gina shi dai-dai yadda Allah ya gaya masa ya yi.
  • A cikin jirgin ne , aka kiyaye Nuhu da iyalinsa lafiya, daga baya 'ya'yansu da jikokinsu suka sake cika duniya da mutane.
  • Kowanne mutum da aka haifa tun daga lokacin ruwan tsufana zuriyar Nuhu ne.

(Hakanan duba: zuriya, jirgi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 05:30-31
  • Farawa 05:32
  • Farawa 06:08
  • Farawa 08:01
  • Ibraniyawa 11:7
  • Matiyu 24:37

Obadiya

Gaskiya

Obadiya wani annabi ne a Tsohon Alƙawari da ya yi annabci gãba da Idom, zuriyar Isuwa. Akwai kuma maza da yawa da ake kiran su Obadiya cikin Tsohon Alƙawari.

  • Littafin Obadiya shi ne mafi gajarta a cikin Tsohon Alƙawari ya kuma faɗi wani wahayi da Obadiya ya karɓo a mafarki daga Allah.
  • Ba a sani ba sosai sa'ad da Obadiya ya yi rayuwa ya kuma yi anabci. Mai yiwuwa a lokacin mulkin waɗannan ne: Yoram, Ahaziya, Yowash, da Ataliya sarakunan Yahuda. Annabi Daniyel, Ezekiyel da Irmiya watakila sun yi annabci a wannan lokacin su ma.
  • Watakila kuma Obadiya ya rayu har ya zuwa ƙarshen sarautar Sarki Zedekiya da kwashewa zuwa bautar talala a Babila.
  • Wasu mutane masu suna Obadiya sune, wani zuriyar Saul, ba Gadiye da ya zama ɗaya daga cikin mazajen Dauda, da wani wanda ya zama shugaban masu hidima a fadar Sarki Ahab, da wani hakimin sarki Yehoshafat, da wani wanda ya taimaka wurin gyara haikali a zamanin Sarki Yosiya, da kuma wani Balebi mai tsaron ƙofa a zamanin Nehemiya.
  • Mai yiwuwa marubucin littafin Nehemiya ɗaya ne daga cikin waɗannan mazaje.

(Hakanan duba: Ahab, Babila, Dauda, Idom, Isuwa, Ezekiyel, Daniyel, Gad, Yehoshafat, Yosiya, Lebi, Saul (Tsohon Alƙawari), Zedekiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:21
  • 1 Tarihi 08:38-40
  • Ezra 08:8-11
  • Obadiya 01:02

Omri

Gaskiya

Omri jarumin runduna ne da ya zama sarkin Isra'ila na shida.

  • Sarki Omri ya yi sarauta shekara goma sha biyu a birnin Tirza.
  • Kamar sauran sarakunan Isra'ila da suka sha gabansa, Omri mugun sarki ne wanda ya ƙara bida mutanen Isra'ila cikin bautar gumaka.
  • Omri kuma shi ne mahaifin Sarki Ahab.

(Hakanan duba: Ahab, Isra'ila, Yerobowam, Tirza)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 22:1-3

Rabba

Gaskiya

Rabba birni ne mafi muhimmanci na mutanen Ammoniyawa.

  • A lokacin yaƙi gãba da Ammoniyawa, Isra'ilawa na yawan kaiwa Rabba farmaki.
  • Dauda sarkin Isra'ila ya mamaye Rabba a matsayin ɗaya daga cikin nasararsa.
  • Birnin da aka san shi da sunan Amman Yodan yanzu dã nan Rabba take.

(Hakanan duba: Ammon, Dauda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 20:1
  • 2 Sama'ila 20:26
  • Maimaitawar Shari'a 03:11
  • Ezekiyel 25:3-5
  • Irmiya 49:1-2

Rahab

Gaskiya

Rahab mace ce wanda ta zauna a Yeriko da Isra'ila suka yaƙe su. Ita karuwa ce.

  • Rahab ta ɓoye Isra'ilawa biyu masu leƙen asirin Yeriko kafin Isra'ila suka yaƙe ta. Ta taimaka wa masu leƙen asirin domin su tsira zuwa sansanin Isra'ila.
  • Rahab ta zama mai bada gaskiya ga Yahweh.
  • Da ita da iyalinta an ware su ba a kashe su ba, a sa'ad da aka hallakar da Yeriko sai kuma suka zo suka yi zama tare da Isra'ilawa.

(Hakanan duba: Isra'ila, Yeriko, karuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 11:29-31
  • Yakubu 02:25
  • Yoshuwa 02:21
  • Yoshuwa 06:17-19
  • Matiyu 01:05

Rahila

Gaskiya

Rahila ɗaya daga cikin matan Yakubu ce. Ita da 'yar'uwarta Liya 'ya'yan Laban ne, kawun Yakubu.

  • Rahila ce mahaifiyar Yosef da Benyamin, waɗanda zuriyarsu suka zama biyu daga cikin kabilun Isra'ila.
  • Shekaru da dama, Rahila ba ta haifi 'ya'ya ba. Sa'an nan Allah ya sa ta haifi Yosef.
  • Bayan wasu shekaru, da ta haifi Benyamin, Rahila ta mutu, Yakubu kuma ya binne ta kusa da Betlehem.

(Hakanan duba: Betlehem, Yakubu, Liya, Yosef (Tsohon Alƙawari), Kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 29:06
  • Farawa 29:19-20
  • Farawa 29:30
  • Farawa 31:06
  • Farawa 33:1-3
  • Matiyu 02:18

Rama

Gaskiya

Rama wani tsohon birne ne a Isra'ila kilomita 8 daga Yerusalem. A wannan yankin ne kabilar Benyamin ke zama.

  • A Rama ne Rahila ta mutu bayan da ta haifi Benyamin.
  • Sa'ad da aka kwashe Isra'ilawa ga bauta, an kawo su Rama kafin aka wuce da su zuwa Babila.
  • Rama ne gidan mahaifiyar Sama'ila da mahaifinsa.

(Hakanan duba: Benyamin, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 27:27
  • 1 Sama'ila 02:11
  • 2 Tarihi 16:1
  • Irmiya 31:15
  • Yoshuwa 18:25-28
  • Matiyu 02:17-18

Ramot

Gaskiya

Ramot birni ne mai muhimmanci a cikin tsaunukan Giliyad kusa da Kogin Yodan. Ana kuma kiran sa da suna Ramot Giliyad.

  • Ramot gãdo ne na Isra'ilawa kabilar Gad an kuma keɓe shi birnin mafaka.
  • Sarki Ahab na Isra'ila da Sarki Yehoshafat na Yahuda sun yi yaƙi gãba da sarkin Aram a Ramot. An kashe Ahab a wannan yaƙi.
  • Akwai wani lokacin da, Sarki Ahaziya da Sarki Yoram suka yi yunƙurin su mallaki birnin Ramot daga sarkin Aram.
  • A Ramot Giliyad aka shafe Yehu sarki bisa Isra'ila.

(Hakanan duba: Ahab, Ahaziya, Gad, Yehoshafat, Yehu, Yoram, Kogin Yodan, Yahuda, mafaka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:73
  • 1 Sarakuna 22:03
  • 2 Tarihi 18:03
  • 2 Sarakuna 08:28-29

Rebeka

Gaskiya

Rebeka jikar Naho ce ɗan'uwan Ibrahim.

  • Allah ya zaɓi Rebeka ta zama matar Ishaku ɗan Ibrahim.
  • Rebeka ta baro yankin Aram Naharayim inda take da zama ta tafi tare da bawan Ibrahim zuwa yankin Negeb a inda Ishaku ke zama.
  • Rebeka bata haifi 'ya'ya ba har na tsawon lokaci, amma a ƙarshe Allah ya albarkace ta da 'yan biyu maza, Isuwa da Yakubu.

(Hakanan duba: Ibrahim, Aram, Isuwa, Yakub, Naho, Negeb)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 24:15
  • Farawa 24:45
  • Farawa 24:56
  • Farawa 24:64
  • Farawa 25:28
  • Farawa 26:08

Rehobowam

Gaskiya

Rehobowam ɗaya daga cikin 'ya'yan Sarki Suleman, ya kuma zama sarkin al'ummar Isra'ila bayan mutuwar Suleman.

  • A farkon shekarar mulkinsa, Rehobowam ya yi mulki da tsanani ga mutanensa, sai goma daga kabilar Isra'ila suka yi masa tawaye suka kafa "masarautar Isra'ila" a arewacin ƙasar.
  • Rehobowam ya ci gaba da zama sarki a gabashin masarautar Yahuda, wanda ke tare da kabilu biyun da suka rage, Yahuda da Benyamin.
  • Rehobowam ya zama mugun sarki wanda bai yi biyayya da Yahweh ba, amma ya yi sujada ga allolin ƙarya.

(Hakanan duba: masarautar Isra'ila, Yahuda, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:10
  • 1 Sarakuna 11:41-43
  • 1 Sarakuna 14:21
  • Matiyu 01:07

Rimon

Gaskiya

Rimon sunan wani mutum ne da kuma wurare dayawa cikin Littafi Mai Tsarki. Haka kuma sunan wani alla ce.

  • Wani mutum mai suna Rimon mutumin Benyamin daga birnin Birot a Zebulun. 'Ya'yan wannan mutumin ne suka kashe Ishboshet, ɗan Yonatan wanda ya zama gurgu.
  • Rimon gari ne dake gabashin Yahuda, a yankin da Benyamiyawa ke gãdonta.
  • "Dutsen Rimon" wuri ne na mafaka da ɓuya inda 'ya'yan Benyamin ke gudu su ɓuya a lokacin yaƙi don kada a hallaka su.
  • Rimon Ferez wuri ne da ba a sani ba cikin jejin Yahudiya.
  • Na'aman shugaban runduna na Siriya ya yi magana game da haikali na alla Rimon, inda sarkin Siriya ya yi sujada.

(Hakanan duba: Benyamin, Yahudiya, Na'aman, Siriya, Zebulun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tasrki:

  • 2 Sarakuna 05:18
  • 2 Sama'ila 04:5-7
  • Littafin Alƙalai 20:45-46
  • Littafin Alƙalai 21:13-15

Roma, Romawa

Gaskiya

A kwanakun Sabon Alƙawari, birnin Roma ya zama mazaunin Daular Romawa. Nan ne babban birnin ƙasar Italiya.

  • Daular Romawa ta yi mulki bisa dukkan yankunonin dake kewaye da Tekun Baharmaliya, har da Isra'ila.
  • Kalmar "Romawa" na manufar dukkan yankuna da abin mallakar gwamnatin Rom har da 'yan ƙasa shugabannin Romawa.
  • An kai Manzo Bulus zuwa birnin Roma a matsayin ɗan kurkuku domin ya yi shelar bisharar sunan Yesu.
  • Littafin "Romawa" na Sabon Alƙawari wasiƙa ce da Bulus ya rubuta zuwa ga Kiristoci a Roma.

(Hakanan duba: labari mai daɗi, teku, Bilatus, Bulus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 01:15-18
  • Ayyukan Manzani 22:25
  • Ayyukan Manzanni 28:14
  • Yahaya 11:48

Ruben

Gaskiya

Ruben shi ne ɗan fari na Yakub. Mahaifiyarsa itace Liya.

  • Da 'yan'uwansa ke shirin su kashe ɗanɗan ƙaninsu Yosef, Ruben ya fishe ran usufu ta wurin gaya masu a maimakon haka su jefa shi can cikin rami.
  • Daga baya Ruben ya komo domin ya kuɓutar da Yusufu, amma sauran 'yan'uwansa sun riga sun sayar da shi ga zama bawa ga 'yan kasuwan da ke wucewa.
  • Zuriyar Ruben sun zama ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila.

(Hakanan duba: Yakubu, Yosef (Tsohon Alƙawari), Liya, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 29:32
  • Farawa 35:21-22
  • Farawa 42:22
  • Farawa 42:37

Rut

Gaskiya

Rut wata mace ce daga Mowab wadda ta yi rayuwa a lokacin da alƙalai ke jagorancin Isra'ila. Ta auri wani mutumin Isra'ila a Mowab a lokacin da iyalin sa suka koma nan sabili da yunwar da aka yi cikin Isra'ila a zamanin da alƙalai ke mulki a Isra'ila.

  • Mijin Rut ya mutu, bayan wani lokaci ta bar Mowab tare da surukuwarta Na'omi, wadda take komowa garinta, Betlehem a Isra'ila.
  • Rut ta yi aminci ga Na'omi ta kuma yi mazakuta ta wurin tanadin abinci dominta.
  • Rut ta auri Bo'aza Ba'Isra'ile ta kuma haifi ɗa wanda ya zama kakan sarki Dauda. Domin sarki Dauda kakan Yesu Almasihu ne haka kuma Rut.

(Duba kuma: Betlehem, Bo'aza, Dauda, alƙalai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Matiyu 01:05
  • Rut 01:3-5
  • Rut 03:09
  • Rut 04:06

Saifros

Gaskiya

Saifros wani tsibiri ne cikin Tekun Baharmaliya, misalin kilomita 64 kudu da ƙasar Turki ta zamanin yau.

  • Barnabas yana daga Saifros saboda haka mai yiwuwa ne ɗan'uwansa Yahaya Markus ma daga can yake.
  • Bulus da Barnabas sun yi wa'azi tare a tsibirin Saifros a farkon tafiyar su ta bishara. Yahaya Markus ya bisu domin ya taimaka masu a wannan tafiyar.
  • Bayan haka, Barnabas da Yahaya Markus suka sake ziyartar Saifros.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, an faɗi cewa Saifros na da arziƙin itatuwan rimi.

(Hakanan duba: Barnabas, Yahaya Markus, tekun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:36-37
  • Ayyukan Manzanni 13:05
  • Ayyukan Manzanni 15:41
  • Ayyukan Manzanni 27:04
  • Ezekiyel 27:6-7
  • Ishaya 23:10-12

Sairin

Gaskiya

Sairin birnin Girik ne a arewacin gaɓar Tekun Baharmaliya ta Afrika, dai dai kudu da tsibirin Krit.

  • A lokacin Sabon Alƙawari, da Yahudawa da Kristoci sun zauna a Sairin.
  • Wataƙila an fi sanin Sairin a cikin Littafi Mai Tsarki da wani mutum da ake kira Simon wanda ya ɗauki giciyen Yesu.

(Hakanan duba: Krit)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 11:19-21
  • Matiyu 27:32-34

Sairos

Gaskiya

Sairos Sarkin Fasiya ne wanda ya kafa mulkin Fasiya wajen shekara ta 550 BC, tawurin yaƙi. A tarihi an sanshi kuma da Sairos mai Girma.

  • Sarki Sairos ya ci birnin Babila da yaƙi, wannan ya zama sanadin sakin Isra'ilawa waɗanda aka riƙe su a ƙasar bauta.
  • An fi sanin Sairos da halinsa na tausayawa ga al'umman da suka ci da yaƙi. Saboda alherinsa ne zuwa ga Yahudawa aka sake gina haikalin Yerusalem bayan an kwasar su zuwa bautar talala.
  • Sairus ne yake sarauta lokacin da su Daniyel, Ezra da Nehemiya ke da rai.

(Hakanan duba: Daniyel, Dariyos, Ezra, Nehemiya, Fasiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 36:23
  • Daniyel 01:21
  • Ezra 05:13
  • Ishaya 44:28

Sama'ila

Gaskiya

Sama'ila annabi ne da kuma alƙali na ƙarshe na Isra'ila. Ya keɓe Saul da Dauda a matsayin sarakunan Isra'ila.

  • Sama'ila haifaffen ɗa ne na Elkana da Hannatu a cikin garin Rama.
  • Hannatu bakarariya ce, sai ta yi addu'a da naciya domin Allah ya bata ɗa. Sama'ila shi ne amsar addu'ar.
  • Hannatu ta yi alƙawari idan aka karɓi adu'arta, Allah ya ba ta ɗa namiji, aka ji rokon ta, zata miƙa ɗanta ga Yahweh.
  • Domin ta cika alƙawarinta ga Allah, lokacin da Sama'ila ke ɗan yaro, Hannatu ta aika da shi ya zauna ya kuma taimaki Eli a cikin haikali.
  • Allah ta tãda Sama'ila ya zama babban annabi.

(Hakanan duba: Hannatu, alƙali, annabi, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 01:19
  • 1 Sama'ila 09:24
  • 1 Sama'ila 12:17
  • Ayyukan Manzanni 03:24
  • Ayyukan Manzanni 13:20
  • Ibraniyawa 11:32-34

Samariya, Ba'samariye ko Ba'samariya

Gaskiya

Samariya sunan birni ne da zagayen yankinsa daga arewancin Isra'ila. Yankin na tsakanin kwarin Sharon daga yammansa da kuma Kogin Yodan daga kuma gabas da shi.

  • A Tsohon Alƙawari, Samariya shi ne babban birni na Masarautar Arewancin Isra'ila. Daga baya yankin kewaye da shi aka kira shi da suna Samariya.
  • Sa'ad da Asiriyawa suka mamaye Masarauta ta arewancin Isra'ila, sai suka ƙwace birnin Samariya suka tilasta wa yawancin Isra'ilawa na yankin arewanci su gudu, zuwa wasu birane cikin Asiriya.
  • Asiriyawa suka kawo bãƙi dayawa zuwa cikin yankin Samariya a madadin Isra'ilawa waɗanda aka kora.
  • Wasu daga cikin sauran Isra'ilawa da suka rage a wannan yankin suka auri bãƙin da suka shigo nan, zuriyarsu ana ce da su Samariyawa.
  • Yahudawa suka yi ƙyamar Samariyawa domin su ba cikakkun Yahudawa bane kuma domin kakanninsu sun yi sujada ga kazaman alloli.
  • A zamanin Sabon Alƙawari, yankin Samariya ya yi iyaka da yankin Galili daga arewacinsa da kuma yanki na Yahudiya daga gabas.

(Hakanan duba: Asiriya, Galili, Yahudiya, masarautar Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:1-3
  • Ayyukan Manzanni 08:05
  • Yahaya 04:4-5
  • Luka 09:51-53
  • Luka 10:33

Samsin

Gaskiya

Samsin na ɗaya daga cikin alƙalai, na Isra'ila. Ya fito daga kabilar Dan.

  • Allah ya baiwa Samsin karfi wanda ya fi na mutum, wanda ya yi amfani dashi domin ya yaƙi makiyan Isra'ila, Filistiyawa.
  • An sanya Samsin a ƙarƙashin alƙawari da ba zai aske gashin kansa ba ko kuma ya shã giya ko wani abin shã kumburarre. A duk sa'ad da yake kiyaye wannan alƙawari, Allah ya ci gaba da ikonta shi.
  • Daga nan ya saɓa wa alƙawarin da ya ɗauka ya bari aka aske gashin kansa, har Filistiyawa suka cafke shi.
  • Yayin da Samsin ke cikin bauta, Allah ya sake maido masa da ƙarfinsa ya kuma bashi damar ya hallakar da haikalin ƙazamin allah Dagon, tare da Filistiyawa masu yawan gaske.

(Hakanan duba: mai kuɓutarwa, Filistiyawa, kabilu goma sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 11:32-34
  • Littafin Alƙalai 13:25
  • Littafin Alƙalai 16:02
  • Littafin Alƙalai 16:31

Saratu, Saraya

Gaskiya

  • Saratu matar Ibrahim ce.
  • Sunanta na farko shi ne "Saraya," amma Allah ya canza shi zuwa "Saratu."
  • Saratu ta haifi Ishaku, ɗan da Allah ya alƙawarta ya bata da Ibrahim.

(Hakanan duba: Ibrahim, Ishaku)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 11:30
  • Farawa 11:31
  • Farawa 17:15
  • Farawa 25:9-11

Saul (Tsohon Alƙawari)

Gaskiya

Saul Ba'isra'ili ne wanda Allah ya zaɓa ya zama sarki na farko na Isra'ila.

  • Saul dogo ne kyakkyawa, kuma ƙaƙƙarfan soja. Shi ne irin mutumin da Isra'ila ke buƙata shi zama sarkinsu.
  • Koda yake da farko ya bi Allah, daga baya Saul ya cika da girman kai ya yi wa Allah rashin biyayya. Domin haka, Allah ya zaɓi Dauda domin ya ɗauki gurbin Saul a matsayin sarki sai kuma ya bari aka kashe Saul a yaƙi.
  • A cikin Sabon Alƙawari, akwai wani Bayahude mai suna Saul wanda ya zama Bitrus wanda kuma ya zama manzon Yesu Almasihu.

(Hakanan duba: sarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 10:1-3
  • 1 Sama'ila 09:01
  • 2 Sama'ila 01:1-2
  • Ayyukan Manzanni 13:22
  • Zabura 018:1

Sennakerib

Gaskiya

Sennakerib babban sarki ne mai iko a aAsiriya wanda ya sa Nineba ta zama da wadata, birni mai daraja.

  • Sarki Sennakerib sananne ne wajen yaƙi gãbã da Babila da kuma mulkin Yahuda.
  • Shi sarki ne mai girman kai da kuma yiwa Yahweh izgilanci.
  • Sennakerib ya kai wa Yerusalem Hari a lokacin sarki Hezekiya.
  • Yahweh ya la'anci sojojin Sennakerib suka hallaka.
  • Litattafan Tsohon Alƙawari na Sarakuna da Tarihinsu an rubuta su a lokacin mulkin Sennakerib.

(Duba kuma: Asiriya, Babila, Hezekiya, Yahuda, Izgili, Ninebe.)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 32:1
  • 2 Tarihi 32:16-17
  • 2 Sarakuna 18:13

Set

Gaskiya

A cikin littafin Farawa, Sst ne ɗan Adamu da Hauwa na uku.

  • Hauwa ta ce anbata shitu ne a madadin ɗanta Habila, wanda ɗan'uwansa Kayinu ya kashe.
  • Nuhu na ɗaya daga cikin zuriyar Set, don haka duk wanda ya rayu tun daga lokacin Ambaliyar nan ya zama ɗaya daga cikin zuriyar Set.
  • Set da iyalinsa ne mutanen farko da "suka fara kira ga sunan Ubangiji."

(Hakanan duba: Habila, Kayinu, zuriya, kakanni, tsufana, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 01: 01
  • Luka 03:36-38
  • Littafin Lissafi 24:17

Sharon, Sararin Sharon

Gaskiya

Sharon sunan fili ne, kasa mai dausayi a gefen Tekun Meditaraniya, kudu da Tsaunin Karmel. Ana kuma kiranta "Sararin Sharon."

  • Birane da yawa an ambace su a Littafi Mai Tsarki cewa suna Sararin Sharon tare da Yoffa, Lidda da Sisariya.
  • Akan iya fassara wannan kamar " sararin ana kiranshi Sharon" ko "Sararin Sharon".
  • Mutanen da suke zama a yankin sharon ana kirana su "Sharoniwa".

(Hakanan duba: Sisariya, Karmel, Yoffa, teku)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:16-17
  • Ayyukan Manzanni 09:35
  • Ishaya 33:9

Sheba

Gaskiya

A zamanin dã, Sheba tsohon yankin kasa ne da yake a wajen kudancin Arabiya.

  • Yankin ko ƙasar Sheba ta kasance kusa da wurin da yanzu kasashen Yemen da Itofiya suke.
  • Mazauni ne na zuriyar Ham.
  • Sarauniyar Sheba ta zo ta ziyarci sarki Suleman lokacin da taji labarin shahararsa da wadatarsa da hikimarsa.
  • Akwai kuma mutane da yawa da suke da suna "Sheba" an lissafasu a tushen Tsohon Alƙawari. Zai iya yiwuwa sunan wannan yanki ya samo asali ne daga ɗaya daga cikin waɗannan mutanen.
  • Birnin Biyasheba ne aka gajarta shi zuwa Sheba a wani lokaci cikin Tsohon Alƙawari.

(Hakanan duba: Arabiya, Biyasheba , Itofiya, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:8-10
  • 1 Sarakuna 10:1-2
  • Ishaya 60:6-7
  • Zabura 072:10

Shekem

Gaskiya

Shekem gari ne a Kan'ana da ke mil 40 arewa da Yerusalem. Shekem ma sunan mutum ne a Tsohon Alƙawari.

  • Garin Shekem shi ne inda Yakubu ya zauna bayan da suka sulhunta da ɗan'uwansa Isuwa.
  • Yakubu ya sayi gona daga hannun 'ya'yan Hamor Bahibiye a Shekem. Wannan gonar ta zamto wurin bizne iyalinsa da kuma inda 'ya'yansa suka bizne shi.
  • Ɗan Hamor Shekem ya yiwa 'yar Yakubu Dinatu fyaɗe, sakamakon haka ɗan Yakubu ya kashe dukkan mazajen garin Shekem.

Shawarwarin fassara:

  • Hamor

(Hakanan duba: Kan'ana, Isuwa, Hamor, Bahibiye, Yakubu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:14-16
  • Farawa 12:6-7
  • Farawa 33:19
  • Farawa 37:13

Shem

Gaskiya

Shem ɗaya daga cikin 'ya'yan Nuhu uku ne, da suka bishi zuwa cikin jirgi lokacin ambaliyar da ta shafe duniya wadda akayi bayaninta a cikin littafin Farawa.

  • Shem tsazon Ibrahim ne da zuriyarsa.
  • Zuriyar Shem an sansu da "Semiyawa"; suna yin yaren "Semitik" kamar Ibraniyanci da Larabci.
  • Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Shem ya rayu kusan shekaru 600.

(Hakanan duba: Ibrahim, Arabiya, Jirgi, ambaliya, Nuhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsaki:

  • Farawa 05:32
  • Farawa 06:10
  • Farawa 07:13-14
  • Farawa 10:1
  • Farawa 10:31
  • Farawa 11:10
  • Luka 03:36-38

Shilo

Gaskiya

Shilo katangar garin Kan'aniyawa ce wadda isra'ilawa suka ci da yaƙi ƙarƙashin shugabancin Yoshuwa.

  • Garin Shilo yana yamma da Kogin Yodan da kuma arewa maso gabas da birnin Betel.
  • Lokacin da Yoshuwa ke jagorantar Isra'ila, garin shilo ya kasance mahaɗar mutanen Isra'ila.
  • Kabilu sha biyu na Isra'ila sukan haɗu a Shilo su saurari Yoshuwa yana faɗa masu rabon kowa daga ƙasar Kan'ana.
  • Kafin a gina wani haikali a Yerusalem, a Shilo ne Isra'ilawa kan je su miƙa hadaya ga Allah.
  • Lokacin da Sama'ila yake ƙaramin yaro, mahaifiyarsa Hannatu ta ɗaukeshi ta kaishi ya zauna a Shilo don ya horu ta hannun Eli firist ya bautawa Yahweh.

(Hakanan duba: Betel, keɓewa, Hannatu, Yerusalem, Kogin Yodan, firist, hadaya, Sama'ila, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 02: 26-27
  • 1 Sama'ila 01:9-10
  • Yoshuwa 18: 1-2
  • Littafin Alƙalai 18:30-31

Shimei

Gaskiya

Shimei sunan mutane da yawa ne a Tsohon Alƙawari.

  • Shimei ɗan Gera daga kabilar Benyamin yake wanda ya la'anci Sarki Dauda ya jefe shi da duwatsu lokacin da yake gudu zuwa Yerusalem domin gujewa kisa daga ɗansa Absalom.
  • Akwai kuma Lebiyawa firistoci da yawa a Tsohon Alƙawari da ake kiransu Shimei.

(Hakanan duba: Absalom, Benyamin, Balebi, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:17
  • 1 Sarakuna 01:08
  • 2 Sama'ila 16:13
  • Zakariya 12:12-14

Shinar

Gaskiya

Shinar na nufin "kasa mai rafika biyu" kuma sunan yanki mai sarari ne a kudancin Mesofotamiya.

  • Anzo ansan Shinar da "Kaldiya" da "Babiloniya" dã".
  • Mutanen dã dake zaune a birnin Babel a Sararin Shinar sun gina hasumiya mai tsawo don su mai da kansu manyan mutane.
  • Tsara ta gaba, masu kakan yahudawa Ibrahim ya zauna a ƙasar Ur a wannan yanki, wanda a wannan lokacin ake kiran shi "Kaldiya."

(Hakanan duba: Ibrahim, Babel, Babila, Kaldiya, Mesofotamiya, kakanni, Ur)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:8-10
  • Farawa 14:01
  • Farawa 14:7-9
  • Ishaya 11:10-11
  • Zakariya 05:11

Sidon, Sidoniyawa

Gaskiya

Sidon shi ne babban ɗan Kan'ana. Akwai kuma gari da ake kira Sidon, da aka sawa suna bayan ɗan Kan'ana.

  • Garin Sidon yana ta arewa maso yamma da Isra'ila a wajen Tekun Baharmaliya a yankin da yanzu ƙasar Lebanon take.
  • Su kuma "Sidoniyawa" mutane ne da suke zama a tsohuwar Sidon da yankunan kewayanta.
  • A Littafi Mai Tsarki, Sidon tana da kusanci da garin Tyre, waɗannan garuruwa an sansu domin wadatarsu da kuma aikin lalatar mutanensu.

(Duba kuma: Kan'ana, Nuhu, Fonishiya, teku, Tyre.)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 12:20
  • Ayyukan Manzanni 27:3-6
  • Farawa 10:15-18
  • Farawa 10:19
  • Markus 03:7-8
  • Matiyu 11:22
  • Matiyu 15:22

Silas, Silbanus

Gaskiya

Silas shugaba ne a cikin masu bi na Yerusalem.

  • Dattawan ikkilisiya na Yerusalem suka zaɓi Sila da Bulus da Barnaba su kai wasiƙa garin Antiyok.
  • Silas daga baya ya tafi tare da Bulus zuwa waɗansu garuruwa don su koyar game da Yesu.
  • An sa Bulus da Silas a kurkuku a birnin Filifai. Suka raira yabo ga Allah lokacin da suke a can wurin Allah kuma ya kuɓutar da su daga kurkukun. Yarin ya zama Kirista a ta dalilin shaidarsu.

(Hakanan duba: Antiyok, Barnabas, Yerusalem, Bulus, Filifai, kurkuku, shaida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 05:12
  • 1 Tasalonikawa 01:01
  • 2 Tasalonikawa 01:01
  • Ayyukan Manzanni 15:22

Silisiya

Gaskiya

Silisiya dã ƙaramar lardin Roma ce tana kudu maso arewacin ɓangaren da yanzu a zamanin nan ake ce da ita ƙasar Turki. Tana kan iyaka da Tekun Ajiyan.

  • Manzo Bulus ɗan ƙasar ne daga birnin Tarsus da ke cikin Silisiya.
  • Bulus ya kasance shekaru da dama a Silisiya bayan saduwarsa da Yesu a hanya zuwa Damaskus.
  • Waɗansu Yahudawa daga Silisiya suna cikin waɗanda suka ƙalubalanci Istifanus suka iza mutane su jejjefe shi har ga mutuwa.

(Hakanan duba: Bulus, Istifanus, Tarsus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:8-9
  • Ayyukan Manzanni 15:41
  • Ayyukan Manzanni 27:3-6
  • Galatiyawa 01:21-24

Simiyon

Gaskiya

A Littafi Mai Tsarki, akwai mutane da yawa da suke da suna Simiyon.

  • A Tsohon Alƙawari, ɗan Yakubu na biyu (Isra'ila) sunansa Simiyon. Maisifiyarsa kuwa sunanta Liya. Zuriyarsa ta kasance ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila.
  • Kabilar Simiyon ta mamaye yankin kudu na iyakar ƙasar alƙawari ta Kan'ana. ƙasarsa ta kasance kewaye da ƙasar da take ta Yahuda.
  • Lokacin da Yosef da Maryamu suka kawo jariri Yesu zuwa haikali a Yerusalem domin a miƙa shi ga Allah, wani tsohon mutum mai suna Simiyon ya yabi Yahweh domin ya yardar masa ya ga Almasihu.

(Hakanan duba: Kan'ana, Almasihu, keɓewa, Yakubu, Yahuda, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 29:33
  • Farawa 34:25
  • Farawa 42:35-36
  • Farawa 43:21-23
  • Luka 02:25

Simon Zilot

Gaskiya

Simon Zilot na ɗaya daga cikin almajirai goma sha biyu.

  • An ambaci Simon sau uku a jeren almajiran Yesu, amma kuma ba ayi cikakken bayani game da shi ba.
  • Simon na ɗaya daga cikin sha ɗayan da suka haɗu suka yi addu'a tare a Yerusalem bayan Yesu ya koma sama.
  • Kalmar "zilot " na iya zama Simon daga cikin iyalin "Zilotawa", ƙungiyar Yahudawa masu addini da suke da himma riƙe dokar Musa yayin da suke matuƙar tsayayya da gwamnatin Roma.
  • Ko, "zilot" na iya zama "himmatattu", ana maganar ƙwazon addinin Simon.

(Hakanan duba: Manzo, almajiri, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Luka 06:14-16
  • Markus 03: 17-19

Sinai, Tsaunin Sinai

Gaskiya

Tsaunin sinai tsauni ne da yake a kudancin wurin da yanzu ake kiranshi Tsibirin Sinai. Ana kuma kiranshi "Tsaunin Horeb."

  • Tsaunin Sinai ɓangare ne mafi girma a yankin jeji.
  • Isra'ilawa suka zo Tsaunin Sinai da suke tafiya daga Masar zuwa ‌Ƙasar Alƙawari.
  • Allah ya ba Musa Dokoki Goma a Tsaunin Sinai.

(Hakanan duba: jeji, Masar, Horeb, ‌Ƙasar Alƙawari, Dokoki Goma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:29-30
  • Fitowa 16:1-3
  • Galatiyawa 04:24
  • Lebitikus 27:34
  • Littafin Lissafi 01 :17-19

Siriya, Ashur

Gaskiya

Siriya ƙasa da take arewa maso gabas da Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, yanki ne ƙarƙashin mulkin masarautar Roma.

  • A lokacin Tsohon Alƙawari, Siriya ƙarfafan sojoji ne maƙiyan Isra'ilawa.
  • Na'aman shi ne shugaban sujojin Siriya wanda ya warke daga cutar kuturta ta hannun annabi Elisha.
  • Dayawan mazaunan Siriya kabilar Aram ne, wanda shima daga zuriyar Shem ne ɗan Nuhu.
  • Damaskos babban birnin Siriya, an ambace shi lokaci da dama a Littafi Mai Tsarki.
  • Saul ya tafi garin Damaskos da niyyar tsanantawa Kiristoci a can, amma Yesu ya tsai da shi.

(Hakanan duba: Aram, kwamanda, Damaskos, zuriya, Elisha, kuturta, Na'aman, tsanantawa, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:23
  • Ayyukan Manazanni 15:41
  • Ayyukan Manzanni 20:03
  • Galatiyawa 01: 21-24
  • Matiyu 04:23-25

Siseriya, Siseriya Filifai

Gaskiya

Siseriya birni ne mai mahimmanci a gaɓar Tekun Baharmaliya, kusan kilomita 39 kudu da Tsaunin Karmel. Siserriya Filifai birni ne dake arewa maso gabas da Isra'ila, kusa da Tsaunin Harmon.

  • Waɗannan birane an raɗa masu suna haka saboda Sizozin da suka yi mulkin Roma.
  • Siseriya ta gaɓar teku ta zama cibiyar birni ta lardin Roma na Yahudiya a lokacin da aka haifi Yesu,
  • Manzo Bitrus ya fara wa al'ummai wa'azi a Siseriya ne.
  • Bulus ya tashi daga Siseriya zuwa Tarsus a jirgin ruwa ya kuma wuce ta cikin birnin nan sau biyu a tafiyoyinsa na mai kai bishara.
  • Yesu da almajiransa sun yi tafiya a kewayen lardin nan na Siseriya Filifai cikin Siriya. Dukka biranen biyu an sa masu sunan nan don tunawa da Herod Filib.

(Hakanan duba: siza, al'ummai, teku, Kamel, Tsaunin Hamon, Roma, Tarsus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09:30
  • Ayyukan Manzanni 10:1-2
  • Ayyukan Manzanni 25:01
  • Ayyukan Manzanni 25:14
  • Markus 08:27
  • Matiyu 16:13-16

Siza

Gaskiya

Wannan kalmar "Siza" suna ne ko muƙami da sarakunan mulkin Roma da yawa suka yi amfani da shi. A cikin Littafi Mai Tsarki wannan sunan mutane uku ne da suka yi mulkin Roma.

  • Mai mulkin Roma na fari mai suna "Siza Agustus," shi ne wanda yake mulki a lokacin da aka haifi Yesu.
  • Bayan shekara talatin, lokacin da Yahaya mai yin baftisma ke yin wa'azi, Tiberiyas Siza ke riƙe da ragamar Mulkin Roma.
  • Tiberiyas Siza yake mulkin Roma lokacin da Yesu ya cewa mutane su ba Siza abin da ke na Siza su kuma ba Allah abin dake nasa.
  • Lokacin da Bulus ya ɗaukaka ƙara ga Siza, yana nufin mai mulkin Roma, Nero, wanda shima yana da wannan suna "Siza."
  • Sa'ad da aka yi amfani da sunan nan "Siza" shi kaɗai, za a iya fasara shi da ma'ana haka: "mai mulki" ko "mai mulkin Roma."
  • Sunaye kamar haka Siza Agustus ko Tiberiyas Siza, Za a iya rubuta "Siza" kusa da yadda yaren ƙasar za su rubuta ta.

(Hakanan duba: sarki, Bulus, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 25:06
  • Luka 02:01
  • Luka 20:23-24
  • Luka 23:02
  • Markus 12:13-15
  • Matiyu 22:17
  • Filibiyawa 04:22

Sodom

Gaskiya

Sodom gari ne a kudancin yankin Kan'ana inda ɗan'uwan Ibrahim Lot ya zauna da matarsa da 'ya'yansa.

  • Ƙasar da ta kewaye Sodom wurin mai kyau he, don haka Lot ya zaɓi ya zauna a wurin lokacin da yazo Kan'ana.
  • Takamaiman inda garin yake ba wanda ya sani domin Sodom da garin da yake kusa da shi Gomora dukka Yahweh ya hallakasu, a matsayin hukuncin mugun abin da mutanen suka yi.
  • Babban zunubin da mutanen Sodom suka aikata shi ne aikin luɗu.

(Hakanan duba: Kan'ana, Gomora)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:19
  • Farawa 13:12
  • Matiyu 10:15
  • Matiyu 11:24

Sukkot

Gaskiya

Sukkot sunan garuruwa biyu ne a Tsohon Alƙawari. Kalmar "sukkot" na nufin "wurin zama."

  • Gari na farko ana kiransa Sukkot yana gabas da Kogin Yodan.
  • Yakubu ya zauna a Sukkot tare da iyalinsa da garkunansa, ya gina masu wurin zama a nan.
  • Bayan shekaru ɗaruruwa, Gidiyon da jama'arsa suka tsaya a Sukkot lokacin da suke yaƙar Midiyanawa, amma mutanen wurin suka ƙi su basu abinci.
  • Sukkot na biyun yana arewacin Masar ne kuma a wannan wurin ne Isra'ilawa suka tsaya bayan sun haye Jan Teku lokacin da suke gujewa bauta a Masar.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 07:46
  • Fitowa 12:37-40
  • Yoshuwa 13:27-28
  • Littafin Alƙalai 08: 4-5

Suleman

Gaskiya

Suleman ɗaya daga cikin 'ya'yan sarki Dauda ne. Mahaifiyarsa ita ce Batsheba.

  • Lokacin da Suleman ya zama sarki, Allah ya ce masa ya roƙi duk abin da yake so. Sai Suleman ya roƙi hikima da zai iya mulkin jama'a da kyau da adalci. Allah ya yi farinciki da roƙon Suleman ya bashi hikima da wadata mai yawa.
  • Suleman ya zama sananne domin gina haikali a Yerusalem.
  • Koda yake Suleman ya yi mulki da hikima a shekarar farko ta mulkinsa, da ga baya ya yi rashin azancin auren matan bãƙi ya fara bautawa allolinsu.
  • Saboda rashin adalcin Suleman, bayan mutuwarsa Allah ya raba mulkin Isra'ila kashi biyu, Isra'ila da Yahuda. Waɗannan mulkokin sunyi ta yaƙar junansu.

(Hakanan duba: Batsheba, Dauda, Isra'ila, Yahuda, masarautar Isra'ila, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:47-50
  • Luka 12:27
  • Matiyu 01:7-8
  • Matiyu 06: 29
  • Matiyu 12:42

Taikikos

Gaskiya

Taikikos na ɗaya daga cikin masu hidimar bishara tare da Bulus.

  • Taikikos ya raka Bulus a ƙalla sau ɗaya yawace-yawacen watsa bishararsa a Asiya.
  • Bulus ya kwatanta shi a matsayin "ƙaunatacce" da "amintacce."
  • Taikikos ya ɗauki wasiƙun Bulus zuwa Afisos da Kolosse.

(Hakanan duba: Asiya, ƙaunatacce, Afisos, amintacce, bishara, mai hidima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:11-13
  • Kolosiyawa 04:09
  • Titus 03:12

Tamar

Gaskiya

Tamar sunan mata ne dayawa a Tsohon Alƙawari. Kuma sunan garuruwa ne da dama ko wurare a Tsohon Alƙawari.

  • Tamar surukar Yahuda ce. Ita ta haifi Ferez wanda yake kaka ga Yesu Almasihu.
  • Ɗaya daga cikin 'ya'yan sarki Dauda sunanta Tamar; ita 'yar'uwar Absalom ce. Ɗan'uwanta Amnon ya yi mata fyaɗe ya bar ta a yashe.
  • Absalom ma yana da 'ya sunanta Tamar.
  • Akwai gari mai suna "Hazezon Tamar" ɗaya yake da garin Engedi na yammancin Kogin Gishiri. Akwai kuma "Tamar Ba'al" akwai kuma gari da gabaɗaya ake kiransa "Tamar" wanda zai iya zama da banbanci da sauran garuruwa.

(Hakanan duba: Absalom, kakanni, Amnon, Dauda, kakanni, Yahuda, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:04
  • 2 Sama'ila 13:02
  • 2 Sama'ila 14:25-27
  • Farawa 38:6-7
  • Farawa 38: 24
  • Matiyu 01 :1-3

Tarshish

Gaskiya

Tarshish sunan mutane biyu ne a Tsohon Alƙawari. Kuma sunan gari ne.

  • Ɗaya daga cikin jikokin Yafet na da suna Tarshish.
  • Tarshish sunan wani mutum mai hikima ne na Sarki Ahasuros.
  • Birnin Tarshish birnin ne mai albarka birnin saffara, wanda jirage kan ɗauko kayayyaki masu amfani na saye da sayarwa ko kasuwanci.
  • Wannan birnin na da nasaba da Tyre da kuma waɗansu garuruwa da basu da nisa da Isra'ila, a iya cewa kudancin Sifen.
  • Annabin Tsohon Alƙawari Yona ya shiga jirgi a Tarshish don ya gudu a maimakon ya yi biyyaya da umarnin Allah ya je ya yiwa Nineba wa'azi.

(Hakanan duba: Esta, Yafet, Yona Nineba, Fonisiya, mallaka, masana)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 10:2-5
  • Ishaya 02:16
  • Irmiya 10:09
  • Yona 01:03
  • Zabura 048:07

Tarsus

Gaskiya

Tarsus gari ne mai albarka a lardin Roman ta yankin Silisiya, wanda yanzu yake kudancin Turkiya ko Toki.

  • Tarsus tana nan wajen babban kogi da kuma kusa da Tekun Baharmaliya, don haka yake yankin kasuwanci .
  • A wani lokaci shi ne babban birnin Silisiya.
  • A Sabon Alƙawari, an fi sanin Tarsus a matsayin mahaifar manzo Bulus.

(Hakanan duba: Silisiya, Bulus, lardi, teku)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09:11
  • Ayyukan Manzanni 09:30
  • Ayyukan Manzanni 11:25

Tasalonika, Batasalonike, Tasalonikawa

Gaskiya

A zamanin Sabon Alƙawari, Tasalonika shi ne babban birnin Masidoniya a tsohuwar daular Roma. Mutanen dake zama a wannan birni ake kira "Tasalonikawa."

  • Tasalonika birnin ne mai muhimmanci na bakin teku dake kan babbar hanyar da ta haɗe da Roma wajen daular Roma ta gabas.
  • Bulus, tare da Silas da Timoti, sun ziyarci Tasalonika a fitar su yawon bishara garo na biyu sakamakon haka kuma, ikilisiya ta kafi a wajen. Daga bisani, Bulus kuma ya ziyarci wannan birni a fitarsa yawon bishara karo na uku.
  • Bulus ya rubuta wasiƙu biyu zuwa ga Kiristocin dake Tasalonika. Waɗannan wasiƙu (1 Tasalonikawa da 2 Tasalonikawa) an haɗa dasu cikin Sabon Alƙawari.

(Hakanan duba: Masidoniya, Bulus, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 01:1
  • 2 Tasalonikawa 01:01
  • 2 Timoti 04:9-10
  • Ayyukan Manzanni 17:01
  • Filibiyawa 04:14-17

teku, Babban Teku, Tekun yamma, Baharmaliya

Gaskiya

A cikin Littafi Mai Tsarki, "Babban Teku" ko "tekun yamma" ana nufin ruwan nan da ake kira "Baharmaliya," shi ne babban ruwan da mutanen lokacin Littafi Mai Tsarki suka sani.

  • Baharmaliya tana iyaka da Isra'ila (gabas), Turai (arewa da yamma), da Afrika (kudu)
  • Wannan teku yana da mahimmanci a zamanin dã domin kasuwanci da tafiya saboda yana da gacin da ya shafi ƙasashe da yawa. Birane da kabilunda suke zaune a gaɓarsa sun azurta ƙwarai domin kwashe kaya daga wata ƙasa yafi sauƙi da jirgin ruwa.
  • Tunda Babban Teku yana yamma da Isra'ila, saboda haka ne ake ce da shi "Tekun yamma."

(Hakanan duba: Isra'ila, kabilu, azurta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 47:5-17
  • Ezekiyel 47:18-20
  • Yoshuwa 15:3-4
  • Littafin Lissafi 13:27-29

Tekun Galili, Tekun Kinneret, Tafkin Genesaret, Tekun Taiberiyas

Gaskiya

"Tekun Galili" tafki ne daga gabas da Isra'ila. A Tsohon Alƙawari ana kiranta da suna "Tekun Kinneret."

  • Ruwan wannan tafki na gangarowa zuwa kudu ta cikin Kogin Yodan zuwa Tekun Gishiri.
  • Kafarnahum, Betsaida, Genesaret, da kuma Taiberiyas sune garurukan dake daga bakin Tekun Galili a Sabon Alƙawari.
  • Yawancin ayyukan da Yesu ya aiwatar a lokacin rayuwarsa sun faru ne kurkusa da Tekun Galili.
  • Tekun Galili ana kiransa da suna "Tekun Taiberiyas" da kuma "Tafkin Genesaret."
  • Wannan kalma ana fassarata "Tafki a yankin Galili" ko "tafki kusa da Taiberiyas (Genesaret)."

(Hakanan duba: Kafarnihum, Galili, Kogin Yodan, Kogin Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 06:1-3
  • Luka 05:01
  • Markus 01:16-18
  • Matiyu 04:12-13
  • Matiyu 04:18-20
  • Matiyu 08:18-20
  • Matiyu 13:1-2
  • Matiyu 15:29-31

Tekun Gishiri, Tekun Mutuwa

Gaskiya

Tekun Gishiri (ko kuma jan teku) na tsakanin kudu da Isra'ila daga yammanci da kuma Mowab daga gabas da ita.

  • Kogin Yodan na gangarowa kudu zuwa cikin Tekun Gishiri.
  • Domin ya fi yawancin teku ƙanƙanta, ana iya ce da shi "Tafkin Gishiri."
  • Wannan teku na da wasu sinadarai masu yawa (ko gishiri) har babu wani abu mai rai dake iya zama ciki. Rashin dashe-dashe da dabbobi cikinsa ya sa ake kiransa da suna "Tekun Mutuwa."
  • A cikin Tsohon Alƙawari, wannan teku kuma ana ce da ita "Tekun Araba" da kuma "Tekun Negeb" domin yadda take kurkusa da lardunan Araba da Negeb.

(Hakanan duba: Ammon, Araba, Kogin Yodan, Mowab, Negeb)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 20:1-2
  • Maimaitawar Shari'a 03:17
  • Yoshuwa 03:14-16
  • Littafin Lissafi 34:1-3

Tekun Iwa, Jan Teku

Gaskiya

"Tekun Iwa" sunan tãrin ruwa ne dake tsakanin Masar da Arebiya. Yanzu ana kiransa da suna "Jan Teku."

  • Jan Teku na da tsawo matsattse ne kuma. Yana da girma fiye da tafki ko kogi, kuma ainihinTeku ya fi shi girma sosai.
  • Ya zama wa Isra'ilawa dole da su wuce ta Jan Teku lokacin da suke tserewa daga Masar. Allah ya aikata abin al'ajibi da ya sa ruwan teku ya rabe har mutane su iya tafiya bisa busasshiyar ƙasa.
  • Ƙasar Kana'an na daga Arewa da wannan teku.
  • Ana iya fassara wannan cewa "Tekun Iwa."

(Hakanan duba: Arabiya, Kan'ana, Masar)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:35-37
  • Fitowa 13:17-18
  • Yoshuwa 04:22-24
  • Littafin Lissafi 14:23-25

Tera

Gaskiya

Tera zuriyar Shem ne ɗan Nuhu. Shi ne mahaifin Ibram, Naho da Haran.

  • Tera yabar gidansa a Ur domin ya tafi ƙasar Kan'ana tare da ɗansa Ibram, jikansa Lot da matar Ibram wato Sarai.
  • A kan hanyar zuwa Kan'ana, Tera da iyalinsa suka zauna tsawon shekaru a birnin Haran a Mesofotamiya. Tera ya mutu a Haran yana da shekaru 205.

(Hakanan duba: Ibrahim, Kan'ana, Lot, Mesofotamiya, Naho, Sarah, Shem, Ur)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 11:31-32
  • 1 Tarihi 01:24-27
  • Luka 03:33-35

Timoti

Gaskiya

Timoti wani saurayi ne daga Listra. Daga bisani ya haɗu da Bulus a yawancin tafiye tafiyen bishararsa ya kuma taimaka wurin kiwon sabobbin tarurrukan masu bi.

  • Mahaifin Timoti mutumin Girik ne, amma da kakarsa Lois da mahaifiyarsa Yunis Yahudawa ne kuma masu bi cikin Almasihu.
  • Dattawa da Bulus suka zaɓi Timoti domin aikin hidima ta wurin ɗora masa hannuwansu da yi masa addu'a.
  • Litattafai biyu cikin Sabon Alƙawari (1 Timoti da 2 Timoti) wasiƙu ne da Bulus ya rubuta waɗanda suka bayar da jagora ga Timoti a matsayin shugaba saurayi a rukunin ikilisiyoyi.

(Hakanan duba: zaɓe, gaskatawa, ikilisiya Girik, mai hidima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 03:02
  • 1 Timoti 01:02
  • Ayyukan Manzanni 16:03
  • Kolosiyawa 01:01
  • Filimon 01:01
  • Filibiyawa 01:01
  • Filibiyawa 02:19

Tirza

Gaskiya

Tiza wani birnin Kan'ana ne mai muhimmanci da Isra'ilawa suka cafke. Suna ne kuma na ɗiyar Giliyad, zuriyar Manasse.

  • Birnin yana lardin da kabilar Manasse suka mamaye. Ana kautata zaton cewa birnin yana kamar mil goma daga arewacin birnin Shekem.
  • Shekaru daga bisani, na ɗan wani lokaci Tirza ya zama babban birnin tarayyar masarautar arewa ta Isra'ila, a zamanin mulkin sarakuna huɗu na Isra'ila.
  • Tirza kuma ya zamanto suna ne na ɗaya daga cikin jikokin Manasse mata. Suka roƙi a basu kasonsu na ƙasar tunda mahaifinsu ya mutu kuma bashi da 'ya'ya maza da zasu yi gãdonsa kamar yadda yake a al'ada.

(Hakanan duba: Kan'ana, gãdo, masarautar Isra'ila, Manasse, Shekem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Lissafi 27:1
  • Littafin Lissafi 36:11
  • Waƙar Suleman 06:4

Titus

Gaskiya

Titus Ba'al'umme ne. Ya sami horaswa daga Bulus na zama shugaba a cikin ikilisiyoyin farko.

  • Wasiƙar da Bulus ya rubuta wa Titus na ɗaya daga cikin litattafan Sabon Alƙawari.
  • A wannan wasiƙa Bulus ya umarci Titus da ya zaɓi dattawa domin ikilisiyoyin dake a tsibirin Krit.
  • A wasu wasiƙun nashi zuwa ga Kiristoci, Bulus ya ambaci Titus a matsayin wanda ke ƙarfafa shi yana kuma kawo masa farinciki.

(Hakanan duba: zaɓe, bangaskiya, ikilisiya, yanayi, Krit, dattijo, ƙarfafawa, umarni, hidima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:10
  • Galatiyawa 02:1-2
  • Galatiyawa 02:3-5
  • Titus 01:04

Tomas

Gaskiya

Tomas yana ɗaya daga cikin mazajen nan sha biyu da Yesu ya zaɓa da su zama almajiransa daga bisani kuma, manzanni. An kuma sanshi da suna "Didimos," wanda ke ma'ana "tagwaye."

  • Zuwa ƙarshen rayuwar Yesu, ya gaya wa almajiransa cewa zai tafi ya kasance tare da Uba zai kuma shirya wuri dominsu su kasance tare da shi. Tomas ya tambayi Yesu yadda zasu san hanyar zuwa wurin yayin da basu ma san inda zai tafi ba.
  • Bayan da Yesu ya mutu kuma ya dawo da rai, Tomas yace ba zai yadda da cewa Yesu yana kuma da rai ba sai indai zai gani ya kuma taɓa tabbunan inda aka yiwa Yesu rauni.

(Hakanan duba: manzanni, almajirai, Allah Uba, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Yahaya 11:15-16
  • Luka 06:14-16
  • Markus 03:17-19
  • Matiyu 10:2-4

Trowas

Gaskiya

Trowas birni ne a bakin teku wanda yake arewa ta yamma da gacin tsohon lardin Romawa na Asiya.

  • Bulus ya ziyarci Trowas a ƙalla sau uku a lokutan tafiye-tafiyensa zuwa larduka daban-daban domin wa'azin bishara.
  • A wani lokaci a Trowas, Bulus ya yi dogon wa'azi har zuwa cikin dare har wani saurayi kuma mai suna Yutikos barci ya kwashe shi yayin da yake sauraro. Saboda yana zaune ne bisa buɗaɗɗiyar taga, Yutikos ya yi doguwar faɗowa ƙasa ya kuma mutu. Ta wurin ikon Allah, Bulus ya tada wannan saurayi ya dawo da rai.
  • Sa'ad da Bulus yake Roma, Ya tambayi Timoti da ya kawo masa naɗaɗɗun litattafansa da alkyabbarsa da ya baro a Trowas.

(Hakanan duba: Asiya, wa'azi, lardi, ɗagawa, Roma, naɗaɗɗen littafi, Timoti)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 02:13
  • 2 Timoti 04:11-13
  • Ayyukan manzanni 16:08
  • Ayyukan manzanni 20:05

Tsaunin Hamon

Gaskiya

Tsaunin Hamon sunan tsauni ne wanda duk ya fi tsayi a Isra'ila kudu da ƙarshen jerin tsaunukan da suka somo daga Lebanon.

  • Ya kasance arewa da Tekun Galili, kuma akan iyakar arewa tsakanin Isra'ila da Siriya.
  • Wasu sunaye da wasu yarurruka sun ba Tsaunin Hamon sune "Tsaunin Siriyon" da "Tsaunin Seniya."
  • Tsaunin Hamon yana da ƙolƙoli uku. Mafi tsayin su misalin mita 2800 ne.

(Hakanan duba: Isra'ila, Tekun Galili, Siriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:23-24
  • Ezekiyel 27:4-5
  • Yoshuwa 11:16-17
  • Zabura 042:06
  • Waƙar Suleman 04:06

Tsaunin Zaitun

Gaskiya

Tsaunin Zaitun tsauni ne ko kuma a ce babban tudu da yake gabas da birnin Yerusalem. Tsayinsa kusan mita 787.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, wannan tsaunin wani lokaci ana ce da shi "tsaunin dake gabas da Yerusalem."
  • Sabon Alƙawari ya faɗi yadda sau da yawa Yesu da almajiransa sukan tafi Tsaunin Zaitun su yi addu'a ko kuma su huta.
  • An kama Yesu a Gonar Getsemani, wadda take kan Tsaunin Zaitun.
  • Za a iya fassara sunan nan haka "Tudun Zaitun" ko "Tsaunin Itacen Zaitun."

(Hakanan duba: Getsemani, zaitun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka:19:29
  • Luka 19:37
  • Markus 13:03
  • Matiyu 21:1-3
  • Matiyu 24:3-5
  • Matiyu 26:30

Tubal

Gaskiya

Akwai mutane da yawa a Tsohon Alƙawari da suke da suna "Tubal."

  • Wani mutum da ake kira Tubal yana ɗaya daga cikin 'ya'ya maza na Yafet.
  • Wani mutum da ake kira "Tubal-kayinu" ɗa ne ga Lamek kuma zuriyar Kayinu ne.
  • Tubal kuma suna wata ƙungiyar mutane ne wani annabawa Ishaya da Ezekiyel suka ambata.

(Hakanan duba: Kayinu, zuriya, Ezekiyel, Ishaya, Yafet, Lamek, ƙungiyar mutane, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:05
  • Ezekiyel 27:12-13
  • Farawa 10:2-5

Tyre, Tyrewa

Gaskiya

Tyre wani tsohon birni ne na Kan'aniyawa wanda yake a gaɓar Tekun Baharmaliya a cikin lardin da yanzu yake fanni ƙasar Lebanon ta yau. Mutanensa ana kiransu "Tyrewa."

  • Fannin birnin yana bisa tsibirin teku, wajen kilomita ɗaya daga sandararriyar ƙasa.
  • Saboda inda ya kasance da kuma sinadaransa masu yawa, kamar su itauwan sida, Tyre tana da masana'anta mai bunƙasa kuma tana da dukiya sosai.
  • Sarki Hiram na Tyre ya aika da katakai daga itatuwan sida da ƙwararrun ma'aikata da su taimaka wajen ginin fãdar Sarki Dauda.
  • Shekaru daga bisani, Hiram kuma ya aikawa da Sarki Suleman katakai da ƙwararrun ma'aikata da su taimaka wajen ginin haikali. Suleman ya biya shi da alkama mai yawan gaske da man zaitun.
  • Tyre yawanci an cika kwatanta shi da wani tsohon birni dake kusa da shi mai suna Sidon. Waɗannan sune birane mafi muhimmanci dake a lardi Kan'ana da ake kira Fonishiya.

(Hakanan duba: Kan'ana, sida, Isra'ila, teku, Fonishiya, Sidon)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 12:20
  • Markus 03:7-8
  • Matiyu 11:22
  • Matiyu 15:22

Ur

Gaskiya

Ur birni ne mai muhimmanci a kusa da Kogin Yufiretis a tsohon yankin Kaldiya, wadda ke harɗe da Mesofotamiya. Wannan yankin na a ƙasar da aka sani yau da suna Iraƙ.

  • Ibrahim ya fito ne daga birnin Ur kuma daga nan ne Allah ya kirawo shi ya fito ya tafi zuwa ƙasar Kana'an.
  • Haran, ɗan'uwan Ibrahim da kuma mahaifin Lot, ya mutu a Ur. Wannan na iya zama dalilin da ya sa Lot ya bar Ur ya tafi tare da Ibrahim.

(Hakanan duba: Ibrahim, Kan'ana, Kaldiya, Kogin Yufiretis, Haran, Lot, Mesofotamiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 11:27-28
  • Farawa 11:31

Uzziya, Azariya

Gaskiya

Uzziya ya zama sarkin Yahuda yana da shekaru sha shida ya kuma yi mulki shekaru 52, wannan shekaru ba a saba yin su bisa ƙaragar mulki ba. Uzziya ana kiransa da suna "Azariya" kuma.

  • Sarki Uzziya ya zama sananne a ƙwarewa ga sha'anin da kuma horo a yaƙi. Ya yi ganuwa domin kãre birni ya kuma yi makaman yaƙi ya ajiye su a bisa ganuwar domin a harba kibiyoyi da manyan duwatsu.
  • Sa'ad da Uzziya ke bautawa Ubangiji, sai ya wadata. Amma daga ƙarshen mulkinsa, duk da haka, sai girman kai ya shige shi sai kuma ya yi rashin biyayya ga Ubangiji ta yadda ya ƙona turare a cikin haikali, wanda firistocine kawai ke da izinin yin haka.
  • Saboda wannan zunubi, Uzziya ya kamu da ciwon kuturta wanda ya sa ya zauna nesa da sauran mutane har ƙarshen mulkinsa.

(Hakanan duba: Yahuda, sarki, kuturta, mulki, hasumiyar tsaro)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarkuna 14:21
  • Amos 01:01
  • Hosiya 01:01
  • Ishaya 06:1-2
  • Matiyu 01:7-8

Yafet

Gaskiya

Yafet yana ɗaya daga cikin 'ya'yan Nuhu uku.

  • A lokacin ambaliyar ruwa na duniya wato ruwan tsufana da ya rufe dniya bakiɗaya, Yafet da 'yan'uwansa maza biyu suna tare da Nuhu a cikin jirgi, duk da matayensu.
  • Ana jera sunayen 'ya'yan Nuhu kamar haka, "Shem, Ham, da Yafet." Wannan ya nuna cewa Yafet ne ƙaraminsu.

(Hakanan duba: jirgi, tsufana, Ham, Nuhu, Shem)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 01:04
  • Farawa 05:32
  • Farawa 06:10
  • Farawa 07:13-14
  • Farawa 10:1

Yahaya (mai Baftisma)

Gaskiya

Yahaya ɗa ne ga Zekariya da Elizabet. Tunda "Yahaya" suna ne da aka saba da shi, yawancin lokaci ana kiransa "Yahaya mai Baftisma" domin a bambanta shi da sauran mutanen da ake kira Yahaya, kamar Manzo Yahaya.

  • Yahaya annabi ne wanda Allah ya aiko domin ya shirya mutane su gaskata kuma su bi Almasihu.
  • Yahaya ya faɗi wa mutane su furta zunubansu, su kuma dena yin zunubi, domin su zama a shirya su karɓi Almasihu.
  • Yahaya yayi wa mutane da yawa baftisma a matsayin alamar ladama domin zunubansu kuma suna juyawa daga gare su.
  • Yahaya dai ana kiran sa "Yahaya mai Baftisma" saboda yayi wa mutane da yawa baftisma.

(Hakanan duba: baftisma, Zekariya (Sabon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 03:22-24
  • Luka 01:11-13
  • Luka 01:62-63
  • Luka 03:7
  • Luka 03:15-16
  • Luka 07:27-28
  • Matiyu 03:13
  • Matiyu 11:14

Yahaya (manzo)

Gaskiya

Yahaya na ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu kuma ɗaya daga cikin abokan Yesu na kurkusa.

  • Yahaya da ɗan'uwansa Yakubu 'ya'ya maza ne na wani mai sana'ar kamun kifi wato Su mai suna Zebedi.
  • A cikin bisharar daya rubuta game da rayuwar Yesu, Yahaya ya ambaci kansa a matsayin "Almajirin da Yesu ke ƙauna." Wannan na nuna cewa Yahaya wani muhimmin aboki ne na kurkusa da Yesu.
  • Manzo Yahaya ya rubuta litattafai biyar na Sabon Alƙawari: bishara ta Yahaya, wahayin Yesu Almasihu, da wasiƙu uku da aka rubuta wa sauran masubi.
  • A Lura da cewa manzo Yahaya daban yake da Yahaya mai Baftisma.

(Hakanan duba: manzo, bayyanawa, Yakubu (ɗan Zebedi), Yahaya (mai Baftisma), Zebedi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 02:9-10
  • Yahaya 01:19-21
  • Markus 03:17-19
  • Matiyu 01:1-3
  • Wahayin Yahaya 01:1-3

Yahaya Markus

Gaskiya

Yahaya Markus, wanda kuma aka fi sani da suna "Markus," yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi tafiya tare da Bulus a cikin tafiye-tafiyensa na bishara. Lallai an nuna cewa shine marubucin Littafin Bishara ta Markus.

  • Yahaya Markus ya raka ɗan'uwansa Barnabas tare da Bulus a fitarsu ta farko tafiya bishara.
  • Sa'ad da aka sanya Bitrus cikin kurkuku a Urshalima, masubi na wurin suka yi addu'a dominsa a cikin gidan mahaifiyar Yahaya Markus.
  • Markus ba manzo ba ne, amma ya sami koyarwa daga su Bulus da Bitrus ya kuma yi aiki tare da su cikin hidima.

(Hakanan duba: Barnabas, Bulus)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:11-13
  • Ayyukan Manzanni 12:24-25
  • Ayyukan Manzanni 13:05
  • Ayyukan Manzanni 13:13
  • Ayyukan Manzanni 15:36-38
  • Ayyukan Manzanni 15:39-41
  • Kolosiyawa 04:10-11

Yahuda

Gaskiya

Yahuda na ɗaya daga cikin manyan 'ya'ya maza na Yakubu. Mahaifiyarsa ita ce Liya. Ana kiran zuriyarsa "kabilar Yahuda."

  • Yahuda ne ya cewa 'yan'uwansa su saida ƙanensu Yosef a matsayin bawa a maimakon barinsa ya mutu a cikin rami mai zurfi.
  • Sarki Dauda da dukkan sarakunan da suka biyo bayansa zuriyar Yahuda ne. Yesu, ma, zuriyar Yahuda ne.
  • Sa'ad da mulkin Suleman ya ƙare kuma ƙasar Isra'ila ta rabu, masarautar Yahuda ita ce masarautar kudu.
  • A cikin Littafin Wahayin Yahaya na Sabon Alƙawari, an kira Yesu "Zaki na Yahuda."
  • Kalmomin "Bayahude" ko "Yahudiya" sun zo daga sunan "Yahuda ne."

(Hakanan duba: Yakubu, Bayahude, Yahuda, Yahudiya, kabilun Isra'ila sha biyu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:1-2
  • 1 Sarakuna 01:09
  • Farawa 29:35
  • Farawa 38:02
  • Luka 03:33
  • Rut 01:02

Yahuda ɗan Yakubu

Gaskiya

Yahuda ɗan Yakubu na ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu. Ayi la'akari da cewa shi ba ɗaya ba ne da Yahuda Iskariyoti.

  • Yawanci a cikin Littafi Mai tsarki, mutane masu suna iri ɗaya ana bambanta su ta wurin ambaton wanda ya haife su. A nan, an gane Yahuda a matsayin "ɗan Yakubu."
  • Wani mutumin kuma mai suna Yahuda shine ɗan'uwan Yesu.
  • Littafin Sabon Alƙawari mai suna "Wasiƙa ta Yahuda" ana kyautata zaton Yahuda ɗan'uwan Yesu ne ya rubuta shi, tunda marubucin ya bayyana kansa a matsayin "ɗan'uwan Yakubu." Yakubu shima wani ɗan'uwan Yesu ne.
  • Yana kuma iya yiwuwa littafin wasiƙa ta Yahuda wanda ya rubuta shi shine almajirin Yesu mai suna Yahuda, ɗan Yakubu.

(Hakanan duba: Yakubu (ɗan Zebedi), Yahuda Iskariyoti, ɗa, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Luka 06:14-16

Yahuda Iskariyot

Gaskiya

Yahuda Iskariyot yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu. Shine wanda ya bayar ko yashe da Yesu ga shugabannin Yahudanci.

  • Sunan "Iskariyot" na iya ma'anar "daga Keriyot," wanda kuma ke nuna cewa Yahuda yayi girma a wannan birnin.
  • Yahuda Iskariyot shine ma'ajin kudin manzannin kuma akai-akai yana sace wasu domin moriyar kansa.
  • Yahuda ya bayar da Yesu ta wurin gayawa shugabannin addini inda Yesu yake domin su kama shi.
  • Bayan da shugabannin addini sun yanke wa Yesu hukuncin mutuwa, Yahuda yayi danasanin cewa ya yashe da Yesu, sai ya maida kuɗin yashewar ga shugabannin Yahudanci daga nan ya kashe kansa.
  • Wani manzon kuma sunansa Yahuda, haka ma kamar ɗaya daga cikin 'yan'uwan Yesu. Ɗan'uwan Yesu shima ana kiransa "Yahuda."

(Hakanan duba: manzo, yashewa,shugabannin Yahudanci, Yahuda ɗan Yakubu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 06:14-16
  • Luka 22:47-48
  • Markus 03:19
  • Markus 14:10-11
  • Matiyu 26:23-25

Yahuda, mulkin Yahuda

Gaskiya

Kabilar Yahuda ita ce mafi girma a cikin kabilun Isra'ila. Masarautar Yahuda ta haɗa da kabilun Yahuda da Benyamin.

  • Bayan mutuwar Sarki Suleman, ƙasar Isra'ila ta rabu zuwa cikin masarautu biyu: Isra'ila da Yahuda. Masarautar Yahuda ita ce masarautar kudu, tana yamma da Tekun Gishiri.
  • Babban birnin masarautar Yahuda shi ne Yerusalem.
  • Sarakunan Yahuda guda takwas suka yi biyayya da Yahweh suka kuma bida mutane suyi masa sujada. Sauran sarakunan Yahuda miyagu ne suka kuma bida mutane suyi bautar gumaka.
  • Sama da shekaru 120 bayan da Asiriyawa suka kayar da Isra'ila (masarautar arewa), ƙasar Babila ta kayar da Yahuda. Babiloniyawa suka rushe birnin da haikalin, suka kuma ɗauki yawancin mutanen Yahuda zuwa Babila a matsayin 'yan talala.

(Hakanan duba: Yahuda, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 30:26-28
  • 2 Sama'ila 12:08
  • Hosiya 05:14
  • Irmiya 07:33
  • Littafin Alƙalai 01:16-17

Yahudiya

Gaskiya

Kalmar "Yahudiya" na nufin sashen ƙasa a tsohuwar Isra'ila. Wasu lokutta ana amfani da kalmar da matsastsitar manufa wasu lokuttan kuma da manufa mai fãɗi.

  • Wasu lokutta "Yahudiya" ana amfani da ita da manufa a matse a matsayin wani lardi dake a kudancin tsohuwar Isra'ila yamma da Mataccen Teku. Wasu fassarorin sun kira wannan lardi "Yahuda."
  • Wasu lokuttan "Yahudiya" ana amfani da ita da manufa mai fãɗi a matsayin dukkan lardunan tsohuwar Isra'ila, duk da Galili, Samariya, Feriya, Idumiya da Yahudiya (Yahuda).
  • Idan masu fassara suna so su fito da bambancin sosai, Yahudiya mai manufa da fãɗi za a iya fassarawa a matsayin "Ƙasar Yahudiya" tunda wannan ne fannin tsohuwar Isra'ila wadda kabilar Yahuda suka zaune tun asali.

(Hakanan duba: Galili, Idom, Yahuda, Yahuda, Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:14
  • Ayyukan Manzanni 02:09
  • Ayyukan Manzanni 09:32
  • Ayyukan Manzanni 12:19
  • Yahaya 03:22-23
  • Luka 01:05
  • Luka 04:44
  • Luka 05:17
  • Markus 10:1-4
  • Matiyu 02:01
  • Matiyu 02:05
  • Matiyu 02:22-23
  • Matiyu 03:1-3
  • Matiyu 19:01

Yakubu (ɗan Alfayos)

Gaskiya

Yakubu, ɗan Alfayos, yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu.

  • An bayar da sunansa a cikin jerin sunayen almajiran Yesu a cikin bisharun Matiyu, Markus, da Luka.
  • An kuma ambace shi a cikin littafin ayyukan manzanni a matsayin ɗaya daga cikin almajirai sha ɗaya da suka yi addu'a tare a Urshalima bayan da Yesu ya koma zuwa sama.

(Hakanan duba: manzo, almajiri, Yakubu (ɗan'uwan Yesu), Yakubu (ɗan Zebadi), sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 01:12-14
  • Luka 06:14-16
  • Markus 03:17-19
  • Markus 14:32-34
  • Matiyu 10:2-4

Yakubu (ɗan Zebedi)

Gaskiya

Yakubu, ɗa ga Zebedi, yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu. Yana da ƙane mai suna Yahaya wanda shima yana ɗaya daga cikin manzannin Yesu sha biyu.

  • Yakubu da ɗan'uwansa Yahaya suna sana'ar Su wato kamun kifi tare da mahaifinsu Zebedi.
  • Ana kiran Yakubu da Yahaya da wani suna "'Ya'yan Aradu," watakila saboda suna da saurin fushi.
  • Bitrus, Yakubu, da Yahaya sune almajiran Yesu na kurkusa kuma suna tare da shi a lokacin al'amuran mamaki kamar sa'ad da Yesu yana bisa dutse tare da Iliya da Musa da sa'ad da Yesu ya tada matattar ƙaramar yarinya da rai.
  • Wannan Yakubu daban ne da Yakubu wanda ya rubuta littafi a cikin Littafi Mai Tsarki. Wasu harsunan suna iya rubuta sunayen su daban saboda su bambanta tsakanin mutanen biyu.

(Hakanan duba: manzo, Iliya, Yakubu (ɗan'uwan Yesu), Yakubu (ɗan Alfayos), Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 09:28-29
  • Markus 01:19-20
  • Markus 01:29-31
  • Markus 03:17
  • Matiyu 04:21-22
  • Matiyu 17:1-2
  • Matiyu 17:1-2

Yakubu (ɗan'uwan Yesu)

Gaskiya

Yakubu ɗa ne ga Maryamu da Yosef. Yana ɗaya daga cikin 'yan'uwan Yesu da suke uwa ɗaya.

  • Sauran 'yan'uwan Yesu da suke uwa ɗaya sune Yosef, Yahuda, da Simon.
  • A lokacin kwanakin Yesu, Yakubu da 'yan'uwansa basu gaskata cewa Yesu shine Almasihu ba.
  • Daga bisani, bayan da Yesu ya tashi daga matattu, Yakubu ya gaskata da shi ya kuma zama shugaban Ikilisiyar Yerusalem.
  • Littafin Yakubu a Sabon Alƙawari wasiƙa ce Yakubu ya rubuta wa kiristocin da suka yi hijira zuwa wasu ƙasashe domin su gujewa tsanani.

(Hakanan duba: manzo, Almasihu, ikkilisiya, Yahuda ɗan Yakubu, tsanani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 01:18-20
  • Galatiyawa 02:9-10
  • Yakubu 01:1-3
  • Yahuda 01:1-2
  • Markus 09:1-3
  • Matiyu 13:54-56

Yebus, Bayebusiye, Yebusiyawa

Gaskiya

Yebusiyawa wata ƙungiyar mutane ce dake zaune a ƙasar Kan'ana. Su zuriya ne daga ɗan Ham Kan'ana.

  • Yebusiyawa suna zama a birnin Yebus, daga bisani aka canza sunansa zuwa Yerusalem sa'ad da sarki Dauda ya ci shi da yaƙi.
  • Melkizedek, sarkin Salem, kamar asalinsa Bayebusiye ne.

(Hakanan duba: Kan'ana, Ham, Yerusalem, Melkizedek)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:14
  • 1 Sarakuna 09:20-21
  • Fitowa 03:7-8
  • Farawa 10:16
  • Yoshuwa 03:9-11
  • Littafin Alƙalai 01: 20-21

Yefta

Gaskiya

Yefta mayaƙi ne daga Giliyad wanda kuma yayi hidima a matsayin alƙali bisa Isra'ila.

  • A Ibraniyawa 11:32, an yabi Yefta a matsayin muhimmin shugaba wanda ya kuɓutar da mutanensa daga maƙiyansu.
  • Ya ceto Isra'ilawa daga Ammoniyawa ya kuma bida mutanensa suka kayar da Ifraimawa.
  • Duk da haka Yefta, yayi wani wawan, garajen wa'adi ga Allah wanda ya zama sakamakon hadayar ɗiyarsa.

(Hakanan duba: Ammon, kuɓuta, Ifraim, Alƙali, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 11:32-34
  • Littafin Alƙalai 11:1-3
  • Littafin Alƙalai 11:35
  • Littafin Alƙalai 12:02

Yeho'akim

Gaskiya

Yeho'akim mugun sarki ne wanda yayi mulki bisa masarautar Yahuda, daga farkon wajen shekaru 608 kafin haihuwar Almasihu. Ɗan Sarki Yosiya ne. Da farko sunansa Eliyakim.

  • Fir'aunan Masar mai suna Neko ya canza sunan Eliyakim ya maida shi Yehoyakim ya kuma naɗa shi sarkin Yahuda.
  • Neko ya tilastawa Yehoyakim ya biya haraji ga Masar.
  • Sa'ad da sarki Nebukadnezar ya mamaye Yahuda daga bisani, Yehoyakim na ɗaya daga cikin waɗanda aka kama aka tafi dasu Babila.
  • Yehoyakim mugun sarki ne da ya karkatar da Yahuda daga bin Yahweh. Irmiya annabi yayi anabci gãba da shi.

(Hakanan duba: Babila, Eliyakim, Irmiya, Yahuda, Nebukadnezar)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 03:15-16
  • 2 Sarakuna 23:34-35
  • 2 Sarakuna 24:01
  • Daniyel 01:02
  • Irmiya 01:03

Yeho'ida

Gaskiya

Yeho'ida firist ne wanda ya taimaka ya ɓoye kuma ya kiyaye Sarki Ahaziya ɗan Yowash har sai da ya isa a furta shi sarki.

  • Yeho'ida ya shirya ɗaruruwan matsara su kiyaye Yowash ƙarami sa'ad da mutane ke shelar da shi sarki a haikali.
  • Yeho'ida ya bida mutane wurin kawar da dukkan bagadan allan ƙarya Ba'al.
  • Game da sauran rayuwarsa, Yeho'ida firist ya shawarci sarki Yowash ya taimake shi yayi biyayya da Allah kuma yayi mulkin mutane da hikima.
  • Wani mutum kuma mai suna Yeho'ida mahaifine ga Benaiya.

(Hakanan duba: Ahaziya, Ba'al, Benaiya, Yowash)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 11:04
  • 2 Sarakuna 12:1-3

Yehoram, Yoram

Gaskiya

"Yehoram" suna ne na sarakuna biyu a Tsohon Alƙawari. Dukka sarakuna biyun kuma an sansu da suna "Yoram."

  • Ɗaya Sarki Yehoram ɗin yayi mulki a masarautar Yahuda tsawon shekaru takwas. Shi ɗa ne ga Yehoshafat. Wannan sarkin ne aka fi sani da suna Yehoram.
  • Ɗayan Sarki Yehoram ɗin yayi mulki a masarautar Isra'ila tsawon shekaru sha biyu. Shi ɗa ne ga Sarki Ahab.
  • Sarki Yehoram na Yahuda yayi mulki a zamanin da annabawa Irmiya, Daniyel, Obadiya, da Ezekiyel suke annabci a masarautar Yahuda.
  • Sarki Yehoram kuma yayi mulki wasu lokutta sa'ad da Yehoshafat mahaifinsa yake mulki a bisa Yahuda.
  • A wasu juyin koyaushe suna amfani da sunan "Yehoram" sa'ad da ake ambaton wannan sarki na Isra'ila sa'an nan sunan "Yoram" domin sarkin Yahuda.
  • Wata hanyar ta bambanta kowanne a sarari shine wurin haɗawa da sunan mahaifinsa.

(Hakanan duba: Ahab, Yehoshafat, Yoram, Yahuda, masarautar Isra'ila, Obadiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 22:48-50
  • 2 Tarihi 21:03
  • 2 Sarakuna 11:1-3
  • 2 Sarakuna 12:18

Yehoshafat

Gaskiya

Yehoshafat suna ne na a ƙalla mutane biyu a Tsohon Alƙawari.

  • Wanda aka fi sani da wannan suna shine sarki Yehoshafat wanda shine na huɗu wurin mulki bisa masarautar Yahuda.
  • Ya maido salama tsakanin Yahuda da Isra'ila ya kuma rushe bagadan allolin ƙarya.
  • Wani Yehoshafat ɗin "marubuci ne" domin Dauda da Suleman. Aikinsa ya haɗa da rubuta takardu domin sarki ya sa hannu da rubuta tarihin muhimman al'amura da suka faru a masarautar.

(Hakanan duba: bagadi, Dauda, allan ƙarya, Isra'ila, Yahuda, firist, Suleman)

Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:10-12
  • 1 Sarakuna 04:17
  • 2 Tarihi 17:01
  • 2 Sarakuna 01:17
  • 2 Sama'ila 08:15-18
  • Matiyu 01:7-8

Yehoyakin

Gaskiya

Yehoyakin sarki ne da yayi mulki a masarautar Yahuda.

  • Yehoyakin ya zama sarki yana da shekaru 18. Yayi mulki wata ukku kacal, bayan haka sojojin Babiloniyawa suka kama shi suka tafi da shi Babila.
  • A lokacin gajeren mulkinsa, Yehoyakin yayi miyagun abubuwa irin waɗanda kakansa Sarki Manasse da mahaifinsa sarki Yehoyakim suka aikata.

(Hakanan duba: Babila, Yehoyakim, Yahuda, Manasse)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 36:8
  • 2 Sarakuna 24: 15-17
  • Esta 02: 06
  • Ezekiyel 01: 1-3
  • Irmiya 22:24
  • Irmiya 37: 01

Yehu

Gaskiya

Yehu suna ne na mutum biyu a Tsohon Alƙawari.

  • Yehu ɗan Hanani annabi ne a lokacin mulkin Sarki Ahab na Isra'ila da Sarki Yehoshafat na Yahuda.
  • Yehu ɗa (ko zuriyar) Yehoshafat hafsa ne a rundunar sojojin Isra'ila wanda kuma aka shafe ya zama sarki ta wurin umarnin annabi Elisha.
  • Sarki Yehu ya kashe miyagun sarakuna biyu, Sarki Yoram na Isra'ila da Sarki Ahaziya na Yahuda.
  • Sarki Yehu kuma ya kashe dukkan dangin sarki Ahab na dã ya kuma sa aka kashe muguwar sarauniya Yezebel.
  • Sarki Yehu ya rusar da dukkan wuraren sujadar Ba'al dake cikin Samariya ya kuma kashe dukkan annabawan Ba'al.
  • Sarki Yehu ya bautawa Allah na gaskiya shi kaɗai, Yahweh, kuma shine sarki bisa Isra'ila na tsawon shekaru ashirin da takwas.

(Hakanan duba: Ahab, Ahaziya, Ba'al, Elisha, Yehoshafat, Yehu, Yezebel, Yoram, Yahuda, Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 04:35
  • 1 Sarakuna 16:02
  • 2 Tarihi 19:1-3
  • 2 Sarakuna 10:09
  • Hosiya 01:04

Yeriko

Gaskiya

Yeriko birni ne mai iko a ƙasar Kan'ana. Yana yamma da Kogin Urdun kuma kudu da Tekun Gishiri.

  • Kamar yadda dukkan Kan'aniyawa suke yi, mutanen Yeriko suna bautar allolin ƙarya.
  • Yeriko shine birni na farko a ƙasar Kan'ana da Allah ya cewa Isra'ilawa su karɓe.
  • Sa'ad da Yoshuwa ya bida Isra'ilawa gãba da Yeriko, Allah yayi babban al'ajibi ta wurin taimakonsu su ci birnin.

(Hakanan duba: Kan'ana, Kogin Yodan, Yoshuwa, al'ajibi, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafin Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:78
  • Yoshuwa 02:1-3
  • Yoshuwa 07:2-3
  • Luka 18:35
  • Markus 10:46-48
  • Matiyu 20:29-31
  • Littafin Lissafi 22:1

Yerobowam

Gaskiya

Yerobowam ɗan Nebat shine sarki na farko na masarautar arewa ta Isra'ila wajen shekaru 900-910 kafin haihuwar Almasihu. Wani Yerobowam ɗin, ɗan Sarki Yehowash, yayi mulki bisa Isra'ila wajen shekaru 120 daga bisani.

  • Yahweh yaba Yerobowam ɗan Nebat anabci cewa zai zama sarki bayan Suleman kuma zai yi mulki bisa kabilu sha biyu na Isra'ila.
  • Sa'ad da Suleman ya mutu, kabilu goma na arewacin Isra'ila suka yi tawaye gãba da Rehobowam ɗan Suleman a maimako suka maida Yerobowam ya zama sarkinsu, suka bar Rehobowam a matsayin sarkin kabilu biyu kacal na kudu, Yahuda da Benyamin.
  • Yerobowam ya zama mugun sarki wanda ya bida mutanen Isra'ila suka kauce daga bautawa Yahweh a maimako kuma ya kafa masu gumakai domin suyi masu bauta. Dukkan sarakunan Isra'ila suka bi misalin Yerobowam kuma suka zama miyagu kamar yadda shima yake.
  • Wajen shekaru 120 daga bisani, wani sarki Yerobowam ɗin ya fara mulkin masarautar arewa ta Isra'ila. Wannan Yerobowam ɗa ne ga sarki Yehowash kuma ya zama mugu kamar dukkan sarakunan Isra'ila da suka kasance a baya.
  • Duk da muguntar Isra'ilawa, Allah yayi masu jinƙai ya taimaki wannan sarki Yerobowam ya ci ƙasa ya kuma kafa iyakoki domin lardinsu.

(Hakanan duba: allolin ƙarya, masarautar Isra'ila, Yahuda, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:16-17
  • 1 Sarakuna 12:02
  • 2 Tarihi 09:29
  • 2 Sarakuna 03:1-3
  • Amos 01:01

Yerusalem

Gaskiya

Yerusalem asalinsa tsohon birni ne na Kan'ana wanda daga bisani ya zama birni mafi muhimmanci a Isra'ila. Yana wajen kilomita 34 daga yamma da Tekun Gishiri kuma dai-dai arewa da Betlehem. Har wa yau shine babban birnin Isra'ila a yau.

  • Wannan suna "Yerusale"" an fara ambatonsa ne a cikin littafin Yoshuwa. Wasu sunayen wannan birni a Tsohon Alƙawari sun haɗa da "Salem", "birnin Yebus," da "Sihiyona." Dukka "Yerusalem" da "Salem," suna da tushen ma'anarsu na "salama."
  • Yerusalem asali tsararren wuri ne na Yebusiyawa da ake kira "Sihiyona" wanda Sarki Dauda ya ƙwato ya maida babban birninsa.
  • A Yerusalem ne Suleman ɗan Dauda ya gina haikali na farko a Yerusalem, bisa Tsaunin Moriya, wanda shine dutsen inda Ibrahim ya miƙa ɗansa Ishaku hadaya ga Allah. Aka sake gina haikalin a nan bayanda Babiloniyawa suka rushe shi.
  • Saboda haikalin na cikin Yerusalem, mayan bukukuwa na Yahudawa a nan ake shagalinsu.
  • Mutane sukan ce zamu "hau" zuwa Yerusalem tunda cikin duwatsu yake.

(Hakanan duba: Babila, Almasihu, Dauda, Yebusiyawa, Yesu, Suleman, haikali, Sihiyona)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 04:26-27
  • Yahaya 02:13
  • Luka 04:9-11
  • Luka 13:05
  • Markus 03:7-8
  • Markus 03:20-22
  • Matiyu 03:06
  • Matiyu 04:23-25
  • Matiyu 20:17

Yesse

Gaskiya

Yesse mahaifin Sarki Dauda ne kuma jikan Rut da Bo'aza.

  • Shi dai Yesse daga kabilar Yahuda yake.
  • Shi "Ifraimiye ne," wanda ke ma'anar ya fito ne daga garin Ifrata wato Betlehem.
  • Annabi Ishaya yayi anabci game da "toho" ko "reshe" da zai fito daga "jijiyar Yesse" ya kuma bayar da 'ya'ya. Wannan na maganar Yesu, wanda yake zuriyar Yesse.

(Hakanan duba: Betlehem, Bo'aza, zuriya, 'ya'ya, Yesu, sarki, annabi, Rut, kabilun Isra'ila sha biyu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:12
  • 1 Sarakuna 12:16
  • 1 Sama'ila 16:1
  • Luka 03:32
  • Matiyu 01:4-6

Yetro, Ruwel

Gaskiya

Sunayen "Yetro" da "Ruwel" dukka na mahaifin matar Musa ne, Ziffora. Akwai kuma wasu mutane biyu dake da suna "Ruwel" a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Sa'ad da Musa yake makiyayi a ƙasar Midiyan, ya auri ɗiyar mutumin Midiyan mai suna Ruwel.
  • Daga bisani Ruwel aka fara kiransa "Yetro, firist na Midiyan." Zai iya yiwuwa "Ruwel" sunan shi ne na dangi.
  • Sa'ad da Allah yayi magana da Musa daga cikin wuta a jeji, Musa yana kiwon tumakin Yetro ne.
  • Wani lokaci daga bisani, bayan Allah ya ceto Isra'ilawa daga Masar, Yetro ya fito zuwa wurin Isra'ilawa a jeji ya kuma ba Musa shawara mai kyau game da hukuncin al'amuran mutanen.
  • Ya gaskata da Allah sa'ad da yaji dukkan al'ajiban da Allah yayi domin Isra'ilawa a Masar.
  • Ɗaya daga cikin 'ya'ya maza na Isuwa an sa masa suna Ruwel.
  • An kuma faɗi wani mutum mai suna Ruwel a cikin jerin sunayen asalin Isra'ilawa da suka sake dawowa su zauna a Yahuda a ƙarshen bautar talalarsu a Babila.

(Hakanan duba : bautar talala, dangi, hamada, Masar, Isuwa, al'ajibi, Musa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 01:34-37
  • Fitowa 02:18-20
  • Fitowa 03:1-3
  • Fitowa 18:03
  • Littafin Lissafi 10:29

Yezebel

Gaskiya

Yezebel ita ce muguwar matar Sarki Ahab na Isra'ila.

  • Yezebel ta zuga Ahab da sauran Isra'ila suyi bautar gumaka.
  • Ta kuma kashe annabawan Allah da yawa.
  • Yezebel ta sanya mutum marar laifi mai suna Nabot a kashe shi saboda Ahab ya sãce garkar inabin Nabot.
  • A ƙarshe ita ma Yezebel aka kashe ta saboda dukkan miyagun abubuwan da ta aikata. Iliya yayi anabcin yadda zata mutu kuma haka ya faru dai-dai yadda ya furta.

(Hakanan duba: Ahab, Iliya, allan ƙarya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 16:31-33
  • 1 Sarakuna 19:1-3
  • 2 Sarakuna 09:07
  • 2 Sarakuna 09:31
  • Wahayin Yahaya 02:20

Yezriyel, Bayezriye

Gaskiya

Yezriyel wani birni ne mai muhimmanci a Isra'ila na kabilar Issaka, yana kudu maso yamma da Tekun Gishiri.

  • Birnin Yezriyel yana ɗaya daga cikin mahaɗar yamma na Sararin Megiddo, wanda kuma ake kira "Kwarin Yezriyel."
  • Sarakunan Isra'ila da yawa sunyi fãda-fãdarsu a cikin birnin Yezriyel.
  • Garkar inabin Nabot na kusa da fãdar Sarki Ahab a cikin Yezriyel. Annabi Iliya yayi anabci gãba da Ahab a wurin.
  • An kashe Yezebel muguwar matar Ahab a Yezriyel.
  • Muhimman al'amura da yawa sun faru a wannan birni, harda yaƙe-yaƙe da yawa.

(Hakanan duba: Ahab, Iliya, Issaka, Yezebel, fãda, Tekun Gishiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 04:12
  • 1 Sama'ila 25:43-44
  • 2 Sarakuna 08:28-29
  • 2 Sama'ila 02:1-3
  • Littafin Alƙalai 06:33

Yoffa

Gaskiya

A zamanin Littafi Mai Tsarki, birnin Yoffa muhimmi ne wajen kasuwancin gaɓar teku wanda ke dai-dai Tekun Meditareniyan, kudu da Sararin Sharon.

  • Tsohon birnin Yoffa yanzu aka fi sani da suna birnin Yaffa, wanda yanzu yake fannin birnin Tel Abib.
  • A Tsohon Alƙawari, Yoffa birni ne inda Yona ya shiga jirgi zuwa Tarshis.
  • A Sabon Alƙawari, wata mata kirista mai suna Tabita ta mutu a Yoffa, Bitrus kuma ya dawo da ita da rai.

(Hakanan duba: Teku, Yerusalem, Sharon, Tarshish)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09:37
  • Ayyukan Manzanni 10:08
  • Ayyukan Manzanni 11:4-6
  • Ayyukan Manzanni 11:11
  • Yona 01:03

Yona

Gaskiya

Yona annabin Ibraniyawa ne a Tsohon Alƙawari.

  • Littafin Yona ya faɗi labarin abin da ya faru sa'ad da Allah ya aiki Yona yayi wa'azi ga mutanen Nineba.
  • Yona ya ƙi tafiya Nineba a maimako ma ya shiga jirgi mai tafiya Tarshis.
  • Allah ya sanya wata babbar guguwar hadari ta sha ƙarfin jirgin.
  • Ya gaya wa mutanen dake tuƙin jirgin cewa yana gujewa daga Allah ne, sai ya bada shawarar a jefa shi cikin tekun. Sa'ad da suka yi haka sai guguwar hadarin ta tsaya.
  • Babban kifi ya haɗiye Yona, kuma ya kasance can cikin kifi har ranaku da dare uku.
  • Bayan haka, Yona ya tafi Nineba ya kuma yiwa mutanen wa'azi a can, sai suka juya daga zunubansu.

(Hakanan duba: rashin biyayya, Nineba, juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yona 01:03
  • Luka 11:30
  • Matiyu 12:39
  • Matiyu 16:04

Yonatan

Gaskiya

Yonatan suna ne na wajen mutane goma a Tsohon Alƙawari. Sunan na ma'anar "Yahweh ya bayar."

  • Babban abokin Dauda, Yonatan, shine Yonatan ɗin da aka fi sani da wannan suna a Littafi Mai tsarki. Wannan Yonatan shine babban ɗan Sarki Saul.
  • Sauran masu suna Yonatan da aka ambata a Tsohon Alƙawari sun haɗa da wani daga zuriyar Musa; ɗan ɗan'uwan Sarki Dauda; firistoci da yawa, wanda suka haɗa da ɗan Abiyata; da wani kuma marubuci a Tsohon Alƙawari wanda a gidansa aka kulle annabi Irmiya.

(Hakanan: Abiyata, Dauda, Musa, Irmiya, firist, Saul (Tsohon Alƙawari), marubuci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 01:41-42
  • 1 Sama'ila 14:1
  • 1 Sama'ila 20-02
  • 2 Sama'ila 01:3-5
  • 2 Sama'ila 01:3-5

Yoram

Gaskiya

Yoram ɗan Ahab sarki ne a Isra'ila. Wasu lokutta kuma ana kiransa "Yehoram."

  • Sarki Yoram na Isra'ila yayi mulki a lokaci guda da Sarki Yehoram na Yahuda.
  • Yoram mugun sarki ne da yayi bautar allolin ƙarya ya kuma sa Isra'ila suka yi zunubi.
  • Sarki Yoram na Isra'ila kuma yayi mulki a lokacin zamanin annabawa Iliya da Obadiya.
  • Wani mutumin kuma da aka kira da suna Yoram Sarkin Tou ta Hamat ne sa'ad da Dauda ke sarki.

(Hakanan duba: Ahab, Dauda, Iliya, Hamat, Yehoram, masarautar Isra'ila, Yahuda, Obadiya, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:10-12
  • 2 Tarihi 22:4-5
  • 2 Sarakuna 01:17
  • 2 Sarakuna 08:16

Yosef (Sabon Alƙawari)

Gaskiya

Yosef mahaifi ne ga Yesu a duniya ya kuma yi renon sa a matsayin ɗansa. Mutum ne mai adalci wanda aikinsa kafinta ne.

  • Yosef yayi tashen wata yarinya Bayahudiya mai suna Maryamu, yayin da suke tashen sai Allah ya zaɓe ta ta zama mahaifiyar Yesu Almasihu.
  • Wani mala'ika ya faɗi wa Yosef cewa Ruhu Mai Tsarki da aikin al'ajibi yasa Maryamu ta sami ciki, kuma jaririn Maryamu Ɗan Allah ne.
  • Bayan da aka haifi Yesu, sai wani mala'ika ya gargaɗi Yosef cewa ya ɗauki jaririn da Maryamu ya tafi Masar domin su gudu daga Herod.
  • Yosef da iyalinsa daga bisani sun yi zama a birnin Nazaret na Galili, inda yayi ta samun abin biyan buƙatu ta wurin sana'arsa ta kafinta.

(Hakanan duba: Almasihu, Galili, Yesu, Nazaret, Ɗan Allah, Budurwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 01:43-45
  • Luka 01:26-29
  • Luka 02:4-5
  • Luka 02:15-16
  • Matiyu 01:18-19
  • Matiyu 01:24-25
  • Matiyu 02:19-21
  • Matiyu 13:54-56

Yosef (Tsohon Alƙawari)

Gaskiya

Yosef shine ɗan Yakubu na sha ɗaya kuma ɗan fãri na mahaifiyarsa Rahila.

  • Yosef ƙaunataccen ɗan mahaifinsa ne.
  • 'Yan'uwansa suka yi kishinsa suka saida shi zuwa bauta.
  • A Masar, aka zargi Yosef da ƙarya aka kuma sa shi cikin kurkuku.
  • Duk da wahalhalunsa, Yosef ya tsaya da amincinsa ga Allah.
  • Allah ya kai shi ga matsayin iko na biyu a Masar ya kuma yi amfani da shi ya ceci mutane a lokacin da abinci yayi ƙaranci. Mutanen Masar, da iyalinsa, aka kiyaye su daga yunwa.

(Hakanan duba: Masar, Yakubu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 30:22-24
  • Farawa 33:1-3
  • Farawa 37:1-2
  • Farawa 37:23-24
  • Farawa 41:55-57
  • Yahaya 04:4-5

Yoshuwa

Gaskiya

Akwai mutane Isra'ilawa da yawa masu suna Yoshuwa a cikin Littafi Mai tsarki. Wanda aka fi sani shine Yoshuwa ɗan Nun mataimakin Musa wanda kuma daga bisani ya zama muhimmin shugaba na mutanen Allah.

  • Yoshuwa na ɗaya daga cikin 'yan leƙen asirin ƙasa da Musa ya aika su tafi binciken ƙasar Alƙawari.
  • Tare da Kaleb, Yoshuwa ya roƙi mutanen Isra'ilawa da suyi biyayya da umarnin Allah su shiga Ƙasar Alƙawari su kayar da Kan'aniyawa.
  • Shekaru da yawa daga bisani, bayan mutuwar Musa, Allah ya zaɓi Yoshuwa ya bida mutanen Isra'ila zuwa Ƙasar Alƙawari.
  • A yaƙi na farko kuma wanda aka fi sani gãba da Kan'aniyawa, Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka kayar da birnin Yeriko.
  • Littafin Yoshuwa a Tsohon Alƙawari ya faɗi yadda Yoshuwa ya bida Isra'ilawa suka ɗauki mallakar Ƙasar Alƙawari da yadda kuma ya ba kowacce kabilar Isra'ila fannin ƙasar domin su zauna.
  • An kuma ambaci Yoshuwa ɗan Yozadak a cikin litattafan Haggai da Zakariya; shi baban firist ne wanda ya taimaka aka sake gina ganuwoyin Urshalima.
  • Akwai kuma mutane da yawa masu suna Yoshuwa da aka ambata a cikin tarihohin asali da saura wurare a Littafi Mai Tsarki.

(Hakanan duba: Kan'ana, Haggai, Yeriko, Musa, Ƙasar Alƙawari, Zakariya (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 07:25-27
  • Maimaitawar Shari'a 03:21
  • Fitowa 17:10
  • Yoshuwa 01:03
  • Littafin Lissafi 27:19

Yosiya

Gaskiya

Yosiya sarki ne mai tsoron Allah da yayi mulki a bisa masarautar Yahuda na tsawon shekaru talatin da ɗaya. Ya bida mutanen Yahuda suka tuba suka yi biyayya da Yahweh.

  • Bayan an kashe mahaifinsa Sarki Amon, Yosiya ya zama sarki bisa Yahuda yana ɗan shekara takwas.
  • A cikin shekaru sha takwas na sarautarsa, Sarki Yosiya ya umarci Hilkiya babban firist ya sake gina haikalin Ubangiji. Yayinda wannan ke faruwa, sai aka samo litattafan shari'a.
  • Sa'ad da aka karantawa Yosiya litattafan Shari'ar, yayi ɓacin rai game da yadda mutanensa suka yi rashin biyayya ga Allah. Ya bada umarni a rushe dukkan wuraren bautar gumaka kuma a kashe firistocin allolin ƙarya.
  • Ya kuma umarci mutane su fãra yin shagalin bukin Ƙetarewa.

(Hakanan duba: allahn ƙarya, Yahuda, shari'a, Ƙetarewa, haikali)

  • 1 Tarihi 03:13-14
  • 2 Tarihi 33:24-25
  • 2 Tarihi 34:03
  • Irmiya 01:03
  • Matiyu 01:11

Yotam

Gaskiya

A cikin Tsohon Alƙawari, akwai mutane uku masu suna Yotam.

  • Wani mutum mai suna Yotam shine ɗan autan Gidiyon. Yotam ya taimaka aka kayar da yayansa Abimelek, wanda ya kashe dukkan sauran 'yan'uwansa maza.
  • Wani kuma mutumin mai suna Yotam sarki ne bisa Yahuda har tsawon shekaru sha shidda bayan mutuwar mahaifinsa Uzziya ko (Azariya).
  • Kamar mahaifinsa, Sarki Yotam yayi biyayya da Allah kuma sarki ne nagari.
  • Duk da haka, yadda bai kawar da wuraren bautar gumaka ba yasanya mutanen Yahuda daga bisani suka sake kaucewa daga Allah.
  • Yotam kuma yana ɗaya daga cikin kakannin da aka lissafa a cikin tarihin asalin Yesu Almasihu a cikin littafin Matiyu.

(Hakanan duba: Abimelek, Ahaz, Gidiyon, Uzziya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 26:21
  • 2 Sarakuna 15:05
  • Ishaya 01:1
  • Littafin Alƙalai 09:5-6

Yowab

Gaskiya

Yowab muhimmin shugaban sojoji ne na Sarki Dauda cikin dukkan zamanin mulkin Dauda.

  • Kafin Dauda ya zama sarki, Yowab dama yana ɗaya daga cikin amintattun mabiyansa.
  • Daga bisani, a lokacin mulkin Dauda a matsayin sarkin Isra'ila, Yowab ya zama hafsa na rundunar sojojin Sarki Dauda.
  • Yowab kuma ɗa ne ga Dauda, tunda mahaifiyarsa 'yar'uwar Dauda ce.
  • Sa'ad da Absalom ɗan Dauda ya bayar da shi ta wurin ƙoƙarin karɓe mulkinsa, Yowab ya kashe Absalom domin ya kiyaye sarki.
  • Yowab hazaƙaƙƙen mayaƙi ne ya kuma kashe mutane da yawa waɗanda suke maƙiyan Isra'ila.

(Hakanan duba: Absalom, Dauda)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 02:16-17
  • 1 Sarakuna 01:07
  • 1 Sama'ila 26:6-8
  • 2 Sama'ila 02:18
  • Nehemiya 07:11

Yowash

Gaskiya

Yowash suna ne na mutane da yawa a cikin Tsohon Alƙawari.

  • Wani Yowash mahaifi ne ga Gidiyon wanda ya kuɓutar da Isra'ilawa.
  • Wani Yowash ɗin kuma daga zuriyar Benyamin ne, ɗan'autan Yakubu.
  • Yowash wanda aka fi sani ya zama sarkin Yahuda yana ɗan shekara bakwai. Shi ɗa ne ga Ahaziya, sarkin Yahuda, wanda aka kashe.
  • Sa'ad da Yowash yana ɗan yaro, 'yar'uwar mahaifinsa ta cece shi daga mutuwa ta wurin ɓoye shi har sai da yayi girman da za'a iya naɗa shi sarki.
  • Yowash sarki ne nagari wanda da farko yayi biyayya da Allah. Amma bai kawar da wuraren tuddai ba, kuma Isra'ilawa suka sake komawa bautar gumaka.
  • Sarki Yowash yayi mulkin Yahuda a cikin wasu daga cikin shekarun da Sarki Yehowash yake mulkin Isra'ila. Waɗannan sarakuna daban suke da juna.

(Hakanan duba: Ahaziya, bagadi, Benyamin, allahn ƙarya, Gidiyon, wuraren tuddai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:10-12
  • 2 Tarihi 18:25-27
  • 2 Sarakuna 11:03
  • Amos 01:01
  • Littafin Alƙalai 06:11-12

Yowel

Gaskiya

Yowel annabi ne wanda ake kyautata zaton yayi rayuwa a lokacin mulkin Sarki Yowash na Yahuda. Akwai kuma wasu mutane da yawa a Tsohon Alƙawari da aka ba suna Yowel.

  • Littafin Yowel na ɗaya daga cikin gajerun litattafan anabci sha biyu a sashe na ƙarshe na Tsohon Alƙawari.
  • Abin da kawai aka sani game da rayuwar Yowel shine sunan mahaifinsa Fetuwel.
  • A cikin wa'azinsa a Fentikos, manzo Bitrus yayi sharhi daga littafin Yowel.

(Hakanan duba: Yowash, Yahuda, Fentikos)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 06:33-35
  • 1 Sama'ila 08:1-3
  • Ayyukan Manzanni 02:16
  • Ezra 10:43
  • Yowel 01:02

Yuriya

Gaskiya

Yuriya mutum mai adalci ne kuma ɗaya daga cikin ƙwararrun sojojin Sarki Dauda. An san shi da suna "Yuriya Bahitte."

  • Yuriya ba ƙyaƙƙyawar mata mai suna Batsheba.
  • Dauda ya aikata zina da matar Yuriya, sai kuma ta yi juna biyu da ɗan Dauda.
  • Domin ya rufe wannan zunubi, sai Dauda ya sa aka kashe Yuriya a filin dãgar yaƙi. Sai Dauda ya auri Batsheba.
  • Wani mutum mai suna Yuriya kuma firist ne a zamanin Sarki Ahaz.

(Hakanan duba: Ahaz, Batsheba, Dauda, Bahitte)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 15:05
  • 2 Sama'ila 11:03
  • 2 Sama'ila 11:26-27
  • Nehemiya 03:04

Zadok

Gaskiya

Zadok sunan wani babban firist ne mai muhimmanci a cikin Isra'ila a zamanin Sarki Dauda.

  • Da Absalom ya tayar wa Sarki Dauda, Zadok ya tsaya tare da Dauda ya kuma taimaka aka dawo da Akwatin Alƙawari zuwa Yerusalem.
  • Bayan wasu shekaru, yana nan sa'ad da aka shafe Solomon ɗan Dauda a matsayin sarki.
  • Akwai mutane biyu da aka kirasu da sunan Zadok suka taimaka wurin sake gina ganuwar Yerusalem a zamanin Nehemiya.
  • Zadok sunan kakan sarki Yotam ne.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, Dauda, Yotam, Nehemiya, mulki, Suleman)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 24:1-3
  • 1 Sarakuna 01:26-27
  • 2 Sama'ila 15:24:26
  • Matiyu 01:12-14

Zakariya (Sabon Alƙawari)

Gaskiya

A cikin Sabon Alƙawari, Zakariya Bayahuden firist ne wanda shi ne mahaifin Yahaya mai Baftisma.

  • Zakariya ya ƙaunaci Allah ya kuma yi masa biyayya.
  • Shekaru da dama Zakariya da matarsa, Elizabet, suka yi ta adu'a da naciya domin su sami ɗa, amma basu samu ba. Bayan da suka tsufa sosai, Allah ya amsa adu'arsu ya kuma basu ɗa.
  • Zakariya ya yi annabci da cewa ɗansa Yahaya shi ne zai furta ya kuma shirya hanyar Almasihu.

(Hakanan duba: Almasihu, Elizabet, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 01:5-7
  • Luka 01:21-23
  • Luka 01:39-41
  • Luka 03:1-2

Zakariya (Tsohon Alƙawari)

Gaskiya

Zakariya annabi ne wanda ya yi anabci a zamanin mulkin Sarki Dariyos na farko na Fasiya. Littafin Zakariya a Tsohon Alƙawari na ɗauke da annabce-anabsen Zakariya, da ya umarci waɗanda suka dawo daga bauta su sãke gina haikalin.

  • Annabi Zakariya ya yi zamaninsa ne lokaci ɗaya da Ezra, Nehemiya, Zerubabel da kuma Haggai. Yesu ya yi zancen sa a matsayin annabin da aka kashe a zamanin Tsohon Alƙawari.
  • Wani mai suna Zakariya ya zama mai kula da ƙofa a haikali a zamanin Dauda.
  • ‌Ɗaya daga cikin 'ya'yan Sarki Yehoshafat wanda ke da suna Zakariya ɗan'uwansa Yehoram ya kashe shi.
  • Zakariya ne sunan firist wanda mutanen Isra'ila suka jejjefe shi da duwatsu lokacin da ya yi masu kasheɗi wajen yiwa alloli sujada.
  • Sarki Zakariya ɗan Yerobowam ne ya kuma yi mulki bisa Isra'ila na tsawon wata shida kawai kafin aka kshe shi.

(Hakanan duba: Dariyos, Ezra, Yehoshafat, Yerobowam, Nehemiya, Zerubabel)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 05;1-2
  • Matiyu 23:34-36
  • Zakariya 01:1-3

Zakiyos

Gaskiya

Zakiyos mai karɓar haraji ne daga Yeriko wanda ya hau bisa itace domin ya ga Yesu wanda taro mai yawa suka kewaye shi.

  • Zakiyos ya sami canji na musamman bayan da ya gaskata da Yesu.
  • Ya tuba daga zunubinsa na cutar mutane ya kuma yi alƙawarin bãda rabin dukiyarsa ga talakawa.
  • Ya kuma yi alƙawarin maido wa mutane har riɓi huɗu kuɗin harajin da ya karɓa daga gare su fiye da kima.

(Hakanan duba: bangaskiya, alƙawari, tuba, zunubi, haraji, mai karɓar haraji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 19:02
  • Luka 19:06

Zebedi

Gaskiya

Zebedi mai sũ ne wato kamun kifi ne wanda aka san da shi sabili da 'ya'yansa, Yakubu da Yahaya, almajiran Yesu. Ana kiransu a cikin Sabon Alƙawari a matsayin "'ya'yan Zebedi."

  • 'Ya'yan Zebedi su ma masu sũ ne wato kamun kifi ne suna kuma aiki tare da shi su kama kifi.
  • Yakubu da Yahaya suka bar kamun kifi tare da mahaifinsu Zebedi suka kuma tafi tare da Yesu.

(Hakanan duba: almajiri, mai sũ ko kamun kifi, Yakubu (ɗan Zebedi), Yahaya (manzo))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 21:1-3
  • Luka 05:8-11
  • Markus 01:19-20
  • Matiyu 04:21-22
  • Matiyu 20:20
  • Matiyu 26:36-38

Zebulun

Gaskiya

Zebulun ne ɗa na ƙarshe da aka haifa wa Yakubu da Liya kuma yana ɗaya daga cikin kabilu sha biyu na Isra'ila.

  • Isra'ilawa na kabilar Zebulun aka basu ƙasa dake gab da Tekun Gishiri daga yamma.
  • Wani lokacin sunan "Zebulun" ana kiran sunan ƙasar da waɗannan kabilar Isra'ilawan ke zama.

(Hakanan duba: Yakubu, Liya, Tekun Gishiri, kabilu sha biyu na Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 01:1-5
  • Farawa 30:20
  • Ishaya 09:01
  • Littafin Alƙalai 04:10
  • Matiyu 04:13
  • Matiyu 04:16

Zedekiya

Gaskiya

Zedekiya, ɗan Yosiya, shi ne sarki na ƙarshe na Yahuda (597-587 B.C.). Akwai kuma dayawa masu suna Zedekiya cikin Tsohon Alƙawari.

  • Sarki Nebukadneza ya sanya Zedekiya sarki bisa Yahuda bayan ya kama Sarki Yehoyacin ya kuma ɗauke shi zuwa Babila. Daga baya Zedekiya ya yi tawaye don haka Nebukadneza ya kama shi ya kuma lallatar da dukkan Yerusalem.
  • Zedekiya, ɗan Kena'ana, annabin ƙarya ne a zamanin sarki Ahab na Isra'ila.
  • Wani mutum mai suna Zedekiya na ɗaya daga cikin waɗanda suka sa hannu na yarda ga Ubangiji a zamanin Nehemiya.

(Hakanan duba: Ahab, Babila, Ezekiyel, kasarautar Isra'ila, Yehoyacin, Irmiya, Yosiya, Yahuda, Nebukadnezza, Nehemiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:15-16
  • Irmiya 37:1-2
  • Irmiya 39:02

Zefaniya

Gaskiya

Zefaniya, ɗan Kushi, annabi ne wanda ya zauna a Yerusalem ya kuma yi anabci ̀̀̀a zamanin mulkin Sarki Yosiya. Ya yi rayuwa a zamani ɗaya da Irmiya.

  • Ya tsauta wa mutanen Yahuda domin sun yiwa allolin ƙarya sujada. Annabce-anabcensa an rubuta su cikin littafin Zefaniya a Tsohon Alƙawari.
  • Akwai mutane dayawa waɗanda aka kira su da sunan Zefaniya a Tsohon Alƙawari, yawancinsu firistoci ne.

(Hakanan duba: Irmiya, Yosiya, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 25:18
  • Irmiya 52:24-25
  • Zakariya 06:9-11
  • Zefaniya 01:03

Zerubabel

Gaskiya

Zerubabel sunan mutane biyu ne a cikin Tsohon Alƙawari.

  • ‌Ɗaya daga cikin waɗannan daga zuriyar Yehoyakim da Zedekiya ne.
  • Wani Zerubabel na daban, ɗan Shiltiyel, shi ne shugaban kabilar Yahuda a zamanin su Ezra da Nehemiya, sa'ad da Sairos sarkin Fasiya ya maido su daga bauta a Babila.
  • Zerubabel da Yoshuwa babban firist suna cikin waɗanda suka taimaka sãke gina haikali da bagadin Allah.

(Hakanan duba: Babila, Saifros, Ezra, babban firist, Yehoyakim, Yoshuwa, Yahuda, Nehemiya, Fasiya, Zedekiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 03:19-21
  • Ezra 02:1-2
  • Ezra 03:8-9
  • Luka 03:27-29
  • Matiyu 01:12

Zowa

Gaskiya

Zowa wani ɗan ƙaramin birni ne inda Lot ya tsere lokacin da Allah zai hallakar da Sodom da Gomora.

  • Da ana kiran birnin da suna "Bela" amma aka sãke mashi suna zuwa "Zowa" da Lot ya roƙi Allah da ya kãre wannan "ƙaramin" birni.
  • Ana kyautata zaton an gina Zowa ne a cikin kwarin Kogin Yodan ko kuma daga ƙarshen kudancin Tekun Mutuwa.

(Hakanan duba: Lot, Sodom, Gomora)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 34:1-3
  • Farawa 13:10-11
  • Farawa 14:1-2
  • Farawa 19:22
  • Farawa 19:23