Key Terms

'ya'ya, yaro ko yarinya

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da shi yawancin lokaci a yi magana akan mutum marar shekaru da yawa, duk da jariri. Kalman nan "'ya'ya" na nufin suna da yawa ana kuma amfani da ita wajen bada misalai.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, al'majirai da mabiya ana kiransu "'ya'ya."
  • Sau da yawa wannan kalma "'ya'ya" ana amfani da it wajen kiran zuriyar mutum akan ce da su 'ya'yansa.
  • Wannan furci "'ya'yan wani abu" ana nufin halaiyar'ya'yan yadda take. Ga misali:
  • 'ya'yan haske
  • 'ya'ya masu biyayya
  • 'ya'yan shaiɗan
  • Wannan furci "'ya'ya" zai iya zama game da mutane waɗanda 'ya'yan ruhaniya ne. Misali, "'ya'yan Allah" wato mutanen Allah tawurin bangaskiya cikin Yesu.

Shawarwarin Fassara

  • Wannan kalma "yara" yakamata a fassarata a matsayin "zuriya" sa'ad da ana nufin jikokin mutum ko tattaɓa kunnensa.
  • Bisa ga yadda zai shiga cikin rubutu "'ya'yan wani abu" za a iya fassara shi haka, "mutane waɗanda ke da halaye kamar" ko "mutane masu yi kamar."
  • Idan yayiwu, wannan furci "'ya'yan Allah" za a iya juya shi a sauƙaƙe, tunda muhimmin kan magana a cikin Littafi Mai Tsarki shi ne Allah Ubanmu na sama. Wasu fassarar tare da waɗannan sune, "mutanen Allah" ko "'ya'yan Allah na ruhaniya."
  • Lokacin da Yesu ya kira almajiransa "yara" wannan ma za a iya fassara shi haka, "aminaina abokai" ko "ƙaunatattun almajiraina."
  • Wannan furci, 'ya'yan alƙawari" za a iya fassara shi haka, "mutanen da suka karɓi abin da Allah ya alƙawarta masu."

(Hakanan duba: zuriya, alƙawari, ɗa, ruhu, gaskatawa, ƙaunatacce)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:28
  • 3 Yahaya 01:04
  • Galatiyawa 04:19
  • Farawa 45:11
  • Yoshuwa 08:34-35
  • Nehemiya 05:05

'ya'yan Allah, yaran Allah

Ma'ana

Kalmar "'ya'yan Allah" kalma ce da aka yi ta amfani da ita tana kuma da ma'anoni da yawa.

  • A Sabon Alƙawari, kalmar "'ya'yan Allah" na nufin dukkan masu bada gaskiya ga Yesu an kuma fassara ta da "yaran Allah" tun da ya kunshi maza da mata.
  • Amfani da wannan kalma na nuna dangantaka da Allah kamar yadda dangantaka tsakanin ɗan mutane da ubansa take, da kuma dukkan damar da take ta samun zama 'ya'ya.
  • Waɗansu mutane kan fassara kalmar "'ya'yan Allah" da aka samu a cikin Farawa 6 da mala'ika da suka faɗi - miyagun ruhohi ko iskokai. Waɗansu kuma sukan yi tunanin ikon siyasa na masu mulki ko kuma zuwa zuriyar Shitu.
  • A Sabon Alƙawari, kalmar "'ya'yan Allah" na nufin dukkan masu bada gaskiya cikin Yesu kuma ana fassara shi da "'ya'yan Allah" tun da ya ƙunshi maza da mata.
  • Amfani da wannan kalmar na nuna dangantaka da Allah da take kamar dangantakar 'ya'ya da mahaifinsu, da kuma dukkan damar kasancewa 'ya'ya.
  • Laƙabin "Ɗan Allah" abu ne na daban: yana nufin Yesu, wanda yake maɗakaicin Ɗan Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Inda "'ya'yan Allah" ana nufin masu bi cikin Yesu, za a iya fassara shi da "'ya'yan Allah"
  • A cikin Farawa 6:2 da 4 hanyoyin fassara "'ya'yan Allah" sun haɗa da " mala'iku" "ruhohi." "shugaban dukkan halittu, ko "aljanu."
  • A ƙara kuma ganin sashen "ɗa."

(Hakanan duba: mala'ika, aljani, ɗa, Ɗan Allah, mai mulki, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 06:02
  • Farawa 06:04
  • Ayuba 01:06
  • Romawa 08:14

'yancin haihuwa

Ma'ana

Wannan kalma "'yancin haihuwa" a cikin Littafi Mai Tsarki na nufin girmamawa, sunan iyali, da tarin dukiya da aka saba ba wa ɗan fari a cikin iyali.

  • 'yancin haihuwar ɗan fari da ake ba shi sun haɗa har da riɓi biyu na gãdon mahaifi.
  • ‌Ɗan sarki na fari akan bashi 'yancin haihuwa na yin sarauta bayan mahaifinsa ya mutu.
  • Isuwa ya sayar da 'yancin haihuwasa na ɗan fari ga ƙanensa Yakubu. Saboda haka, Yakubu ya gaji albarkar ɗan fari maimakon Isuwa.
  • 'Yancin haihuwa na ɗan fari ya haɗa da bangirma da ake samu na lisafta farkon zuriya daga ɗan fari na tushen iyalin nan.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fasara "'yancin haihuwa" zasu haɗa da "hakkin ɗan fari da dukiya ta ɗan fari" ko "girman iyali" ko "zarafi da gãdon ɗan fari."

(Hakanan duba: ɗan fãri, gãdo, zuriya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 05:01
  • Farawa 25:34
  • Farawa 43:33
  • Ibraniyawa 12:14-17

a cikin Kristi, a cikin Yesu, a cikin Ubangiji, a cikin sa

Ma'ana

Kalmar nan "a cikin Kristi" ana danganta su ne da yanayin yin bayanin dangantaka da Yesu Kristi ta wurin bada gaskiya a cikinsa.

  • Waɗansu kalmomi masu nasaba da wannan sun haɗa da "a cikin Kristi Yesu, a cikin Yesu Kristi, a cikin Ubangiji Yesu, cikin Ubangiji Yesu Kristi."
  • Wata ma'ana ta "a cikin Kristi" zata haɗa da "domin ku na Almasihu ne" ko "da yake ya danganta ne ga yadda kake danganta da Yesu."
  • Waɗannan kalmomin masu nasaba da wanan kalmar suna da ma'ana iri ɗaya da yin imani da Yesu da kuma zama almajirinsa.
  • A lura: a waɗansu lokutan ana magana ne kan smun irin abin da Kristi ya samu, wannan amfanin da ake samu ta wurin imani da Yesu. Zama da ɗaukaka cikin Yesu na nufin ka yi murna cikin Kristi da kuma yabon Allah kan abin da yayi cikin Kristi, A gaskata Yesu wannan na nufin mu dogara gare shi a matsayin mai cetonmu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, akwai hanyoyi da za a fassara "a cikin Kristi" da "a cikin Ubangiji" to sun haɗa da:
  • "wanda yake na Kristi"
  • "saboda kun yi imani da Kristi"
  • "saboda Kristi ya cece mu"
  • "cikin hidima ga Ubangiji"
  • "dogaro ga Ubangiji"
  • "sabo da abin da Ubangiji ya yi"
  • Mutanen da suka yi "imani da Yesu Kristi" ko "suka yi imani da abin" Yesu ya yi ko ya koyar kuma suna dogara gare shi domin ya cece su saboda hadayarsa akan giciye da ta biya hakin laifofinmu. Waɗansu harsunan na da waɗansu na da waɗansu kalmomi na fassara wannan kalmar "yin imani da" "samun rabo a cikin" ko "dogara gare shi."

(Hakanan duba: Kristi, Ubangiji, Yesu, imani, bangaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:05
  • 2 Korintiyawa 02:17
  • 2 Timoti 01:01
  • Galatiyawa 01:22
  • Galatiyawa 02:17
  • Filimon 01:06
  • Wahayin Yahaya 01:10
  • Romawa 09:01

a tuba, tube-tube, tubabbe, tuba

Ma'ana

Kalmomin "a tuba" da "tuba" na nuna juyawa daga barin zunubi a kuma juya ga Allah.

  • A "tuba" na nufin wani ya canza tunanin zuciyarsa.
  • A Littafi Mai Tsarki, "tuba" na nufin a juyo daga tunani da ayyuka na mutuntaka na zunubi, a kuma juyo zuwa ga tunani da ayyukan Allah.
  • Yayin da mutane suka tuba daga zunubansu, Allah na gafarta masu ya kuma taimaka masu su fara yi masa biyayya.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "tuba" za a iya fassarawa da kalma ko faɗa dake ma'anar "juyawa (ga Allah)" ko "juyawa daga zunubi zuwa kuma ga Allah" ko "juyawa zuwa ga Allah, nesa da zunubi."
  • Yawanci kalmar "tuba" za a iya fassarawa da amfani da aikatawa "ka tuba." Ga misali, "Allah ya bayar da tuba ga Isra'ila" za a iya fassarawa haka "Allah ya ba Isra'ila ikon su tuba."
  • Wasu hanyoyin da za a fassara "tuba" zasu haɗa da "juyawa daga zunubi" ko "juyawa ga Allah kuma nesa da zunubi."

(Hakanan duba: gafartawa, zunubi, juyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 03:19-20
  • Luka 03:3
  • Luka 03:8
  • Luka 05:32
  • Luka 24:47
  • Markus 01:14-15
  • Matiyu 03:03
  • Matiyu 03:11
  • Matiyu 04:17
  • Romawa 02:04

adalci, marar adalci, rashin adalci, barata,baratarwa

Ma'ana

"Adalci" da "barata" na nufin nuna kirki ga mutane bisa ga shari'ar Allah. Shari'un 'Yan'adam dake nuna matsayin Allah na halin karamci zuwa ga wasu suma ana iya kiransu adalci.

  • Zama mai "adalci" shine kayi aikin kirki kuma karamci ga wasu. Yana kuma nuna gaskiya da rikon amana kayi abin da ke dai-dai a gaban Allah.
  • Aikata "aikin adalci" na ma'ana ka ɗauki mutane da kirki, da nagarta, kuma dai-dai bisa ga shari'ar Allah.
  • Karɓar "hukunci" shine ayi maka adalci ƙarƙashin shari'a, ko dai shari'a ta kiyaye ka ko ka sami horo ta wurin karya shari'a.
  • Wasu lokutta kalmar "hukunci" na iya ma'ana "adalci" ko "bin shari'ar Allah."

Kalmar "marar adalci" da "rashin adalci" na nufi nuna rashin kirki ga mutane da halin cutarwa.

  • "Rashin adalci" shine yin wani abin cutarwa ga wani wanda bai cancanta ba. Yana nufin aikata rashin adalci ga mutane.
  • Rashin adalci kuma na nufin nuna halin karamci ga wasu mutane yayin da ake nuna halin wulaƙanci ga wasu.
  • Wanda ke nuna halin marar adalci shine wanda ke nuna "sonkai" ko "bambanci" domin baya karamta mutane a matsayi dai-dai.

Kalmar "barata" da "baratarwa" na nufin maida mai laifi ya zama marar laifi. Allah ne kaɗai zai iya baratar da mutane da gaske.

  • Sa'ad da Allah ya baratar da mutane, yana gafarta zunubansu ya mai da kamar ma basu yi laifi ba. Yana baratar da masu zunubi waɗanda suka tuba suka sa dogararsu ga Yesu ya cece su daga zunubansu.
  • "Baratarwa" na nufin abin da Allah yayi sa'ad da ya gafartawa wani taliki zunubansa ya kuma furta wannan taliki mai adalci ne a idanunsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, wasu hanyoyin fassara "adalci" sun haɗa da "halin tsarki" da "karamci."
  • Kalmar "barata" ana iya fassara ta a matsayin "karamtawa" ko "sakamakon cancanta."
  • Yin "adalci" ana iya fassarawa "nuna karamci" ko "nuna halin adalci."
  • A cikin wasu nassosin, "barata" na iya fassaruwa a matsayin "adalci" ko "sahihanci."
  • Ya danganta da nassin, "rashin barata" ana iya fassarawa a "rashin kirki" ko "nuna sonkai" ko "rashin adalci."
  • Kalmar "marar adalci" ana iya fassara ta a "marasa kirki" ko "mutane marasa adalci" ko "mutanen dake nuna rashin karamci ga wasu" ko "mutane marasa adalci" ko "mutane marasa biyayya ga Allah."
  • Sauran hanyoyin fassara "rashin barata" suna iya haɗawa da, "rashin karamci" ko "rashin kirki."
  • Wasu hanyoyin fassara "barata" suna iya haɗawa da "a furta wani taliki cewa mai adalci ne" ko "a sa wani ya zama mai adalci."
  • Kamar "baratarwa" ana iya fassarawa "a furta mutum mai adalci ne" ko "zama mai adalci" ko "sanya mutane su zama masu adalci."
  • Furcin "sakamakon baratarwa" ana iya fassarawa "saboda Allah ya baratar da mutane da yawa" ko "wanda ya zama sakamakon Allah ya sa mutane da yawa sun zama masu adalci."
  • Furcin "domin baratarwarmu" ana iya fassarawa " domin Allah ya iya maida mu masu adalci."

(Hakanan duba: gafartawa, laifi, shar'antawa, adalci, adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 44:16
  • 1 Tarihi 18:14
  • Ishaya 04:3-4
  • Irmiya
  • Ezekiyel 18:16-17
  • Mika 03:8
  • Matiyu 05:43-45
  • Matiyu 11:19
  • Matiyu 23:23-24
  • Luka 18:03
  • Luka 18:08
  • Luka 18:13-14
  • Luka 21:20-22
  • Luka 23:41
  • Ayyukan Manzanni 13:38-39
  • Ayyukan Manzanni 28:04
  • Romawa 04:1-3
  • Galatiyawa 03:6-9
  • Galatiyawa 03:11
  • Galatiyawa 05:3-4
  • Titus 03:6-7
  • Ibraniyawa 06:10
  • Yakubu 02:24
  • Wahayin Yahaya 15:3-4

aikata laifi, ci gaba da laifi, laifi

Ma'ana

Kalmar "laifi"na nufin karya doka, sharaɗi, tsarin nagarta. Ayita "laifi" na nufin a aika "laifi."

  • A misali, ayi "laifi" za a iya bayyanawa haka "a gitta layi," wat , a tsallake taƙaicewa ko iyaka da aka tsara domin jin daɗin wani da wasu.
  • Kalmar "laifi," "zunubi," "lalata" da "aikata laifi" dukka sun haɗa da ma'anar aiwatar da abin gãba da nufin Allah da rashin biyayya da dokokinsa.

Shawarwarin Fassara:

  • "Aikata laifi" za a iya fassarawa haka "zunubi" ko "rashin biyayya" ko "tawaye."
  • Idan wata aya ko nassi ya yi amfani da kalmomi biyu dake ma'anar "zunubi" ko "karya doka" ko "aikata laifi," yana da muhimmanci, idan mai yiwuwa ne, ayi amfani da hanyoyi daban-daban a fassara waɗannan kalmomi. Sa'ad da Littafi Mai Tsarki ya yi amfani da kalmomi biyu ko fiye da haka dake da ma'ana shigen iri ɗaya a cikin nassin ɗaya, yawanci dalilin shi ne domin a jaddada abin da aka riga aka faɗa ko a nuna muhimmancinsa.

(Hakanan duba: zunubi, aikata laifi, lalata)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 04:06
  • Daniyel 09:24-25
  • Galatiyawa 03:19-20
  • Galatiyawa 06:1-2
  • Littafin Lissafi 14:17-19
  • Zabura 032:01

akwati

Ma'ana

Akwati wani sassaƙaƙƙen adaka ne dogo da aka yi shi da katako domin ya riƙe ko ya kare wani abu. Akwati zai iya zama babba ko ƙarami ya danganta da abin da ake amfani da shi.

  • A Littafi Mai Tsarki na Turanci, wannan kalma "akwati" anyi amfani da shi a matsayin wani babban sassaƙaƙƙen jirgi ne da Nuhu ya gina domin ya tsira daga ambaliyar da ta ci duniya dukka. Gindin akwatin kamar faranti yake yana da jinka da kuma bango.
  • Wasu hanyoyin da za a fassara wannan kalma zasu haɗa da, "kwale-kwale mai girma sosai" ko "kwale-kwale" ko "jigin kaya na ruwa" ko "babban jirgi mai siffar akwati."
  • Akwai kalmar Ibraniyanci da ake amfani da ita a kwatanta wannan babban jirgi kalmar guda ce da aka yi amfani da ita domin kwando ko akwati da aka sa ɗan jariri Musa lokacin da mahaifiyarsa ta sa shi a bisa Kogin Nilu ta ɓoye shi. Yawancin lokaci ana fassara shi a ce "kwando."
  • A cikin faɗar "akwatin alƙawari" ana amfani da wata kalmar Ibraniyanci daban da "jirgi." Wannan ana fassara shi ya zama "akwati" ko "adaka" ko "abin ajiya a ciki."
  • Sa'ad da za a zaɓi kalmar fassara "akwati" yana da muhimmanci a kowanne rubutu ayi la'akari da yadda girman abin yake da kuma abin da ake amfani da shi.

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, kwando)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 03:20
  • Fitowa 16:33-36
  • Fitowa 30:06
  • Farawa 08:4-5
  • Luka 17:27
  • Matiyu 24:37-39

akwatin alƙawari, akwatin Yahweh

Ma'ana

Waɗannan sunaye manufarsu akwati adakar katako ne musamman, da aka dalaye da zinariya, a cikinsa akwai allunan duwatsu guda biyu waɗanda aka rubuta Dokoki Goma a bisansu. A cikinsa kuma akwai sandar Haruna da kuma tukunyar manna.

  • Kalmar nan "akwati" za a iya fassarata haka "akwati" ko "adaka" ko "abin yin ajiya a ciki."
  • Abin da ke cikin wannan adakar yana tuna wa Isra'ilawa alƙawarin Allah da ya yi da su.
  • Kasancewar Allah yana bisa akwatin alƙawari a wuri mafi tsarki a masujada, inda ya yi magana da Musa a madadin Isra'ilawa.
  • Lokacin da akwatin alƙawari yake wuri mafi tsarki na masujada, babban firist ne kaɗai zai kusanci akwatin, sau ɗaya a shekara a Ranar Kaffara.
  • Juyi na Turaci da dama suna fassara "dokokin alƙawari" su ce da ita "shaida." Wannan maganana nufin Dokokin nan Goma shaida ne ko suna shaida alƙawarin Allah da mutanensa. Ana kuma fassarata ta haka "alƙawarin shari'a."

(Hakanan duba: akwati, alƙawari, kaffara, wuri mai tsarki, shaida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 06:15
  • Fitowa 25:10-11
  • Ibraniyawa 09:05
  • Littafin Alƙalai 20:27
  • Littafin Lissafi 07:89
  • Wahayin Yahaya 11:19

al'ajibi, al'ajibai, mamaki, mamakai, alama, alamu

Ma'ana

"Al'ajibi wani abin ban mamaki ne da ba shi yiwuwa saiko Allah ya sa shi ya faru.

  • Ga misalan al'ajibai da Yesu ya yi, ya tsauta wa hadari ya yi tsit, ya warkar da wani mutum makaho.
  • A wasu lokaci ana ce da abubuwan ban mamaki "al'ajibai" domin suna sa mutane su cika da mamaki.
  • Wannan kalmar "mamaki" yawancin lokaci ana faɗar haka ne idan ayyukan ikon Allah suka bayyana, kamar yadda ya hallici sammai da duniya.
  • Za a iya kiran "alamu" al'ajibai domin ana amfani da su a matsayin shaida cewa Allah ne mai iko dukka wanda yake da dukkan mulki ko'ina.
  • Wasu al'ajiban ayyukan Allah ne na fansa, misali yadda ya kuɓutar da Isra'ilawa daga bauta a Masar da yadda ya tsare Daniyel daga cutarwar zakoki.
  • Wasu al'ajiban ayyukan hukunci ne na Allah, misali yadda ya aiko da ambaliyar ruwa a zamanin Nuhu da lokacin da ya kawo mugayen annobai a ƙasar Masar a zamanin Musa.
  • Yawancin al'ajiban Allah na warkaswar jikin mutane ne marasa lafiya da mayar da rai ga mutanen da suka mutu.
  • An nuna ikon Allah a cikin Yesu sa'ad da ya warkar da mutane, ya sa yana yi suka natsu, tafiya akan ruwa, da tada matattu. Waɗannan duk al'ajibai ne.
  • Allah kuma ya taimaki annabawa da manzanni suyi al'ajiban warkarwa da wasu abubuwa waɗanda sai ta wurin ikon Allah za a iya yin su.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara "al'ajibai" ko "mamakai" za a iya haɗawa da waɗannan "abubuwa marasa yiwuwa da Allah ke yi" ko "ayyukan Allah masu ƙarfi" ko "ayyukan Allah na ban mamaki."
  • Wannan furci da aka cika amfani da shi "alamu da al'ajibai" za a iya fassarawa haka "sanarwa da al'jibai" ko "al'ajibai na ban mamaki da suka nuna yadda Allah mai girma ne."
  • A yi lura wannan ma'anar alama mai ban mamaki daban take da alamar dake sanarwa ko bada shaida domin wani abu. Su biyun suna kusa da juna a ma'ana.

(Hakanan duba: iko, annabi, manzo, alama)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tasalonikawa 02:8-10
  • Ayyukan Manzanni 04:17
  • Ayyukan Manzanni 04:22
  • Daniyel 04:1-3
  • Maimaitawar Shari'a 13:01
  • Fitowa 03:19-22
  • Yahaya 02:11
  • Matiyu 13:58

alama, alamomi, tabbaci, tunatarwa

Ma'ana

Alama abu ne, ko aiki da kan yaɗa abu mai ma'ana.

  • "Tunatarwa" alamomi ne da kan "tunasar" da mutane ta wurin taimakonsu su tuna wani abu, masamman abin da akayi alƙawari:
  • Bakangizon da Allah ya halitta a sararin sama alama ne don tunawa jama'a cewa ya yi alƙawari ba zai ƙara hallaka duniya da ruwa ba.
  • Allah ya umarci Isra'ilawa da su yiwa'ya'yansu kaciya alamar alƙawarinsa da su.
  • Alama kan tona ko ta nuna wani abu:
  • Mala'ika ya ba makiyaya alamar da za ta taimakesu su san jaririn da aka haifa mai ceto a Betlehem.
  • Yahuda ya simbaci Yesu alamar da shugabannin addini za su gane Yesu domin su kama shi.
  • Alamomi kan tabbatar da abin da yake na gaskiya:
  • Mu'ujizan da annabawa da manzanni sukayi alamomi ne da suka nuna cewa suna faɗar saƙon Yahweh ne.
  • Mu'ujizan da Yesu ya aiwatar suka tabbatar da cewa gaskiya shi ne Almasihu.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, "alama" za a iya fassara ta da "shaida" ko "allon alama" ko "maki" ko "tabbaci" ko " ko"shaida" ko "nuni".
  • "Nuna alama da hannuwa" za a iya fassara shi da "motsi da hannu" ko "nuni da hannu" ko "yin nuni."
  • A waɗansu yarurrukan, za a iya samun kalma ɗaya domin "alama" da take tabbatar da wani abu da kuma wata kalma daban "alama" da take nufin mu'ujiza.

(Hakanan duba: mu'ujiza, manzanni, Almasihu, alƙawari, kaciya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:18-19
  • Fitowa 04:8-9
  • Fitowa 31:12-15
  • Farawa 01:14
  • Farawa 09:12
  • Yahaya 02:18
  • Luka 02:12
  • Markus 08:12
  • Zabura 089:5-6

alantaka

Ma'ana

Kalmar nan "allantaka" tana njufin duk wani abu da ya ƙunshi Allah ko kuma yake game Allah.

  • Waɗansu hanyoyi da ake moron wannan sun haɗa da "hukuncin Allah" " Allah,"fasalin Allah" "ikon Allah" da ɗaukakar Allah."
  • A wani wuri a cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da alantaka domin a nuna wani abu game da alloli na ƙarya.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara kalmar nan "allantaka" sun haɗa da "mallakar Allah"ko "daga Allah" ko kuma "abin da ya shafi Allah" ko kuma halaiyar Allah."
  • Misali, "hukumar Allah" zata iya "zama mulkin Allah" ko sarautar da ta zo daga Allah."
  • Kalmar nan "ɗaukakar Allah" za'a iya fassara ta da cewa ɗaukakar da ta zo dzga Allah, ko ɗaukakar da Allah yake da ita."
  • Waɗansu fassarorin za su iya nufin cewa wanan na nufin duk wani batu da ake yi game da allahn ƙarya shi ne alantaka.

(Hakanan duba: hukuma, gunki, ɗaukaka, Allah, hukunci, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 10:3-4
  • 2 Bitrus 01:04
  • Romawa 01:20

albarka, mai albarka, sa albarka

Ma'ana

A sã wa wani mutum ko wani abu "albarka" ma'anar shi ne a sã abu mai kyau da abubuwan amfani su faru ga mutumin nan ko wannan abin da ake săwa albarka.

  • Ma'anar sã wa wani mutum albarka furta marmarin abu mai kyau da kuma amfani ne ya faru ga mutumin nan.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, yawancin lokaci mahaifi zai furta ƙaiyadadden albarka akan yaransa.
  • Sa'ad da mutane suka "albarkaci" Allah ko suka nuna son a albarkaci Allah, wannan ya nuna suna yabon sa.
  • Wannan kalma "albarka" wani lokaci ana amfani da ita a tsarkake abinci kafin a ci ko domin godiya da kuma yabon Allah domin abincin.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan an sã "albarka" za a iya fassara shi ya zama "ayi tanadi mai ɗunbun yawa domin" ko "ayi alheri da tagomashi ga."
  • "Allah ya kawo babbar albarka ga" za a iya juya shi haka, "Allah ya bada kyawawan abubuwa da yawa ga" ko "Allah yayi tanadi jingim domin" ko "Allah ya sa abubuwa masu kyau su faru."
  • "An albarkace shi" za a iya juya shi haka "Zai sami babbar riba" ko "zai ɗanɗana abubuwa masu kyau" ko "Allah zai sa ya wadata."
  • "Mai albarka ne mutumin da" za a iya fasara shi haka "Zai zama da kyau ƙwarai ga mutum wanda."
  • Furci kamar wannan "albarka ga Ubangiji" za a iya fasarata "Bari a yabi Ubangiji" ko "Yabi Ubangiji" ko "Na yabi Ubangiji."
  • A lokacin da aka sã wa abinci albarka, za a iya fassara wannan haka, "a gode wa Allah domin abinci" ko "a yabi Allah domin ya basu abinci" ko "a tsarkake abincin ta wurin yabon Allah domin sa.

(Hakanan duba: yabo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 10:16
  • Ayyukan Manzanni 13:34
  • Afisawa 01:03
  • Farawa 14:20
  • Ishaya 44:03
  • Yakubu 01:25
  • Luka 06:20
  • Matiyu 26:26
  • Nehemiya 09:05
  • Romawa 04:09

alheri, mai alheri

Ma'ana

Kalmar nan "alheri" tana magana ne akan temako ko wata albarka da aka ba wani wanda bai wajebce shi ba. Kalmar nan "mai alheri" tana nufin wani ne wanda ya nuna alheri ga waɗansu.

  • Alherin Allah zuwa ga masu zunubi kyauta ce da aka samu ba tare da an biya ba.
  • Hakan nan batun nan alheri yana nuna yin kirki ga wani da kuma gafartawa wani wahda ya yi maka abu mara dacewa, ko abubuwa na cutarwa.
  • Bayanin nan "samun alheri" bayani ne dake nufin karɓar temako da kuma jiƙai daga Allah. Sau da yawa ya haɗa da ma'anar cewa Allah na jin daɗin wani yana kuma temakonsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi da za'a iya fassara "alheri" sun haɗa da "halin kirki na Allah" ko "jinƙan Allah" ko "halin gafara da kirki na Allah domin masu zunubi" ko "jinƙan mai kirki,"
  • Haka nan za'a iya fassara "mai alheri" da "cike da alheri" ko "kirki" ko "jinƙai" ko "nuna cikakken halin kirki."
  • Batun nan "ya sami alheri a fuskau Allah" za'a iya fassara shi "ya sami jinƙai daga wurin Allah" ko "Allah ya yimasajinƙai ta wurin temako" ko "Allah ya yi masa tagomashinsa" ko "Allah ya ji daɗin sa ya temake shi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:33
  • Ayyukan Manzanni 06:8
  • Ayyukan Manzanni 14:4
  • Kolosiyawa 04:6
  • Kolosiyawa 04:18
  • Farawa 43:28-29
  • Yakubu 04:7
  • Yahaya 01:16
  • Filibiyawa 04:21-23
  • Wahayin Yahaya 22:20-21

aljani, mugun ruhu, ƙazamin ruhu

Ma'ana

Duk waɗannan ana ɗaukan su a sheɗanu, waɗanda suke ruhohi ne da ke hamaiya da nufin Allah.

  • Allah ya hallici mala'iku su bauta masa. sa'ad da sheɗan ya tayar wa Allah, waɗansu mala'iku suma suka yi tayarwar sai aka turo su daga sama. an yi imani cewa aljinnu da mugayen ruhuhi su ne waɗannan "faɗaɗɗun mala'iku"
  • A waɗansu lokutan waɗannan aljanun ana kiran su "ƙazaman ruhohi" ma'ana "marasa tsarki"ko "miyagu" ko "mara sa tsarki."
  • Sabo aljanunu na bauta wa sheɗan, sukan yi miyagun abubuwa. A waɗansu lokutan sukan zauna zauna cikin mutane suna sarrafa su.
  • Aljanu na da da iko fiye da mutane, amma ba su kai ikon Allah ba.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "aljani" za'a iya fassara ta da "mugun ruhu."
  • Kalmar nan ƙazamin ruhu za 'a iya fassara ta da "ruhuhi mara sa tsafta" ko "gulɓatattun ruhohi" ko mugun ruhu."
  • A tabbatar cewa kalmar nan da aka fasssara ta a wannan hanya ta bambanta ba a yi amfani da kalmar sheɗan ba wajen fassarar aljani.
  • Haka nan ana so ayi la'akari da wannan kalma ta "aljani" kan yadda ake moronta a harhsen ƙasar.

(Hakanan duba: aljani ya buge, Shaiɗan, allahn ƙarya, mala'ika, mugu, tsaftata)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yakubu 02:19
  • Yakubu 03:5
  • Luka 04: 36
  • Markus 03:22
  • Matiyu 04:24

alƙawari

Ma'ana

Alƙawari wani shiri ne da ake ƙullawa tsakanin ƙungiyoyi biyu wanda ɗayansu ko dukka biyunsu dole su cika.

  • Wannan shiri zai iya zama tsakanin mutum ɗai ɗaya, ko tsakanin ƙungiyoyin mutane, ko tsakanin Allah da mutane.
  • Sa'ad da mutane suka yi alƙawari da juna, sukan yi alƙawari za su yi wani abu, kuma dole su yi shi.
  • Misali alƙawarai na mutane ya haɗa da su alƙawarin aure, alƙawarin kasuwanci, da yarjejeniya tsakanin ƙasashe.
  • A wasu alƙawaran, Allah ya yayi alƙawari ya cika nasa bangaren ba tare da biɗar sãkawa daga mutum ba. Misali, lokacin da Allah ya tsaida alƙawarinsa da ɗan adam, yayi alƙawari ba zai ƙara hallaka duniya da ambaliyar da zata gama duniya dukka ba, wannan alƙawari bata da ɓangaren da mutane za su cika.
  • A wasu alƙawaran, Allah yayi alƙawarin zai cika nasa ɓangaren idan dai mutane za su yi masa biyayya su cika nasu bangaren alƙawarin.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga yadda za a yi amfani da shi a rubutu, ga yadda za a fasara wannan kalma, "shirin da dole a cika shi" ko "ƙulla shiri" ko "jingina" ko "ɗaukar kwangila."
  • Wasu yarurukan mai yiwuwa suna da wasu maganganu maimakon alƙawari wanda ya danganta bisa ga ɗaya daga cikin ƙungiyar ko su dukka biyu ƙungiyoyin suka yi alƙawari dole su cika. Idan alƙawarin gefe guda ne, za a iya fasara shi haka, "alƙawari" ko "jingina."
  • A tabbatar fassarar wannan kalma bata yi kamar mutane ne suka fara yinta ba. A dukkan alƙawarai tsakanin Allah da mutane, Allah ne ya fara kawo alƙawarin.

(Hakanan duba: alƙawari, alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 09:12
  • Farawa 17:07
  • Farawa 31:44
  • Fitowa 34:10-11
  • Yoshuwa 24:24-26
  • 2 Sama'ila 23:5
  • 2 Sarakuna 18:11-12
  • Markus 14:24
  • Luka 01:73
  • Luka 22:20
  • Ayyukan Manzanni 07:08
  • 1 Korintiyawa 11:25-26
  • 2 Korintiyawa 03:06
  • Galatiyawa 03:17-18
  • Ibraniyawa 12:24

alƙawari, alƙawarai, alƙawarta

Ma'ana

Alƙawari rantsuwa ce za a yi wani abu. Sa'ad da wani ya yi alƙawarin wani abu, yana nunawa ya bada kai ya yi wannan abu.

  • Littafi Mai Tsarki ya rubuta alƙawarai da yawa da Allah ya yiwa mutanensa.
  • Alƙawarai mahimman ɓangare ne na yarjejeniyar da aka yi a cikin wa'adodi.
  • Yawancin lokaci alƙawari akan haɗa shi da rantsuwa domin a tabbatar za a yi wannan abin.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "alƙawari" za a iya fassarawa haka, "miƙa wuya" ko "tabbatarwa" ko "yarjejeniya."
  • Idan an yi "alƙawari za a yi wani abu" za a iya fassara ta haka, "ka tabbatar wa wani mutum cewa zaka yi wani abu ko "bada amincewa za a yi abu."

(Hakanan duba: wa'adi, rantsuwa, alƙawari)

  • Galatiyawa 03:15-16
  • Farawa 25:31-34
  • Ibraniyawa 11:09
  • Yakubu 01:12
  • Littafin ‌Lissafi 30:02

Allah

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "Allah" tana nufin rayayyen nan da ya hallici komai ba daga cikin komai ba. Allah yana nan a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki. Ainahin sunan Allah shi ne "Yahweh."

  • Allah na nan a kullum; ya kasance kafin komai ya kasance kuma zai ci gaba da kasancewa har abada.
  • Shi ne kaɗai Allah na gaskiya yana kuma da iko akan komai da ke cikin duniya.
  • Allah cike yake da adalci, mai matuƙar hikima, mai tsarki, marar zunubi, adali, mai jinƙai, da kuma ƙauna.
  • Shi Allah ne mai riƙe alƙawari, wanda ke cika alƙawarinsa a kullum.
  • An hallici mutane nedomin su bautawa Allah kuma shi kaɗai za su bautawa.
  • Allah ya baiyana sunansa da "Yahweh" wanda ke nuna "shi ne" ko "ni ne" ko "Wanda har kullum yana nan."
  • Hakanan Littafi Mai Tsarki yana koyar da mu game da "allolin" ƙarya waɗanda gumaka ne mara sa rai rai da mutane ke bautawa cikin kuskure.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin da za'a fassara "Allah" za haɗa da "Mahallici" ko "Siffa" ko Mai Iko."
  • Waɗansu hanyoyin da za'a yi fassarar "Allah" su ne "Mahallici Mai Iko Dukka" ko "Ubangijin Dukkan Hallita" ko "Madawwamin Mahallici."
  • Yi la'akari da yadda ake kiran Allah a naku harshen da ake fassara. Idan haka ne yana da muhimmanci a tabbatar cewa wanan kalma ta yi daidai da ɗabi'ar Allah na gaskiya da aka ambata a sama.
  • Harsuna da yawa kan mori babban baƙi na farko a rubuta suna Allah na gaskiya domin bambanta shi da allahn ƙarya.
  • Wata hanya kuma da zata sa wanan ya zama ikakke ita ce moron wata kalmar domin ambaton "Allah" da kuma "gunki."
  • Kalmar nan "zan zama Allahnsu za su zama mutanena" za'a iya fassara ta da "Ni Allah zan yi mulki bisa waɗanan mutane za su kuma yi mini sujada."

(Hakanan duba: hallita, allahn ƙarya, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, allahn ƙarya, Ɗan Allah, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 01:7
  • 1 Sama'ila 10:7-8
  • 1 Timoti 04:10
  • Kolosiyawa 01:16
  • Maimaitawar Shari'a 29:14-16
  • Ezra 03:1-2
  • Farawa 01:2
  • Hosiya 04:11-12
  • Ishaya 36:6-7
  • Yakubu 02:20
  • Irmiya 05:5
  • Yahaya 01:3
  • Yoshuwa 03:9-11
  • Littafin Makoki 03:43
  • Mika 04:5
  • Filibiyawa 02:6
  • Littafin Misalai 24:12
  • Zabura 047:9

Allah Uba, Uba na sama, Uba

Ma'ana

Kalmar nan "Allah Uba" da kuma "Uba na sama" tana nufin Yahweh, Allah na gaskiya. Wata kalma kuma da ma'ana iri ɗaya ita ce "Uba," wadda aka mora da yawa a lokacin da Yesu ke magana game da shi.

  • Allah ya kasance a matsayin Allah Uba da Allah Ɗa da kuma Allah Ruhu mai Tsarki. kowanen su kuma cikakken Allah ne kuma duk da haka su Allah ɗaya ne. Wanan shi ne asirin da mutum mara Ruhu Mai Tsarki ba zai gane ba.
  • Allah Uba ya aiko Allah Ɗa (Yesu) zuwa cikin duniyas shi kuma ya aiko da Ruhu Mai Tsarki ga mutanensa.
  • Duk wanda ya gaskata da Allah Ɗa ya zama ɗan Allah Uba kenan kuma Ruhu Mai Tsarki ya zo ya zauna cikin mutumin nan. Wanan kuma wani asiri ne da ba kowane mutm ne ya fahimce shi dukka ba.

Shawarwarin Fassara:

  • A fassara wanan kalma "Allah Uba," ya fi kyau a fassara "Uba" da kalmar da ta yi dai-dai da kalmar ke nufin uba na jiki a cikin harshen.
  • Kalmar nan "Uba na sama" za'a iya fassara ta da "Uba wanda ke cikin sama" ko "Uba Allah wanda ke cikin sama" ko "Allah Ubanmu daga sama."
  • Kuma hah kullum ana moron babban bãƙi ne rubuta uba i idan ana magana game da Allah.

(Hakanan duba: uba, Allah, sama, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, Ɗan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 08:4-6
  • 1 Yahaya 02:1
  • 1 Yahaya 02:23
  • 1 Yahaya 03:1
  • Kolosiyawa 01:1-3
  • Afisawa 05: 18-21
  • Luka 10:22
  • Matiyu 05:16
  • Matiyu 23:9

allah, allahn ƙarya, alloli, alliya, gunki, gumaka, mai bautar gumaka,masu bautar gumaka, matsafi, halin tsafi

Ma'ana

Wato allahn ƙarya wani abu ne da mutane ke bautawa, a memakon Allah na gaskiya. Kalmar nan "alliya" tana magana ne akan allah ta ƙarya mace.

  • Waɗannan allolin ƙarya basu. Yahweh ne kaɗai Allah.
  • A waɗansu lokuta mutane kaan siffata wani abu domin su bauta musu, ko su maishi alama ta waɗannan alloli nasu na ƙarya.
  • A lokuta da yawa aljanu kan ruɗi mutane da cewa waɗannan alloli na ƙarya da suke bautawa suna da iko.
  • Ba'al da Dagon da Molek uku ne daga cikin allolin ƙarya da yawa da aka bautawa a kwanakin Littafi Mai Tsarki.
  • Ashera da Artamis (Diyana) waɗansu alloli ne da muanen can can baya suka bautawa.

Gunki wani abu ne da mutane kan siffanta domin su bauta musu.Irin wanan shi ake kira "halin tsafi" in har ya kai ga bada girma ga abin da ba Allah na gaskiya ba.

  • Mutane kan siffata gunki domin ya wakilci allolin ƙarya da suke bautawa.
  • Waɗanan allolin ƙarya ba su; ba wani Allah in ba Yahweh ba.
  • A waɗansu lokuta aljannu kan yi aiki ta wurin gunki domin ya nuna kamar yana da wani iko, ko da yake bashi da shi.
  • Akan yi gunki ne da abubuwa masu daraja kamar zinariya,azurfa,tagulla ko kuma wani itace mai tsada.
  • "Mulki na matsafa" na nufin "mulki mutane masu bautar gumaka" ko mulkin mutane da ke bautar abubuwan duniya."
  • "Kalmar nan "siffar gunki" wani suna ne na "sassaƙaƙƙiyar siffa" ko "gunki."

Shawarwarin Fassara:

  • Ta iya yiwuwa akwai wata kalma domin "gunki" ko "allahn ƙarya" a cikin harshen ko a cikin maƙwabtan harshen.
  • Kalmar "gunki" za'a iya moron ta a matsayin allolin ƙarya.
  • A Harshen ingilishi ƙaramin harafi na "g" shi ake mora domin a nuna gomaka, sa'annan ayi amfani da babban harafin "G" domin nuna Allah na ƙwarai. Waɗansu harsunan ma haka suke yi.
  • Zaɓi na gaba shi ne akan mori wata kalmar ta da bam domin ambaton allohli na ƙarya.
  • Waɗansu harsunan suka ƙara kalma domin su bambanta ko allah na ƙarya namiji ne ko mace ce.

(Hakanan duba: Allah, Asherah, Ba'al, Molek, aljani, siffa, mulki, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 35:02 * Fitowa 32:1
  • Zabura 031:06 * Zabura 081:8-10
  • Ishaya 44:20
  • Ayyukan Manzanni 07:41
  • Ayyukan Manzanni 07:43
  • Ayyukan Manzanni 15:20
  • Ayyukan Manzanni 19:27
  • Romawa 02:22
  • Galatiyawa 04:8-9
  • Galatiyawa 05:19-21
  • Kolosiyawa 03:03
  • 1 Tasalonikawa 01:09

almajiri, almajirai

Ma'ana

Kalmar nan almajiri tana nufin mutum ne wanda ya ɗauki dogon lokaci tare da malami, yana koyo daga hali da kuma koyarwar malaminsa.

  • Mutanen da suka bi Yesu suna koyon da kuma sauraren koyarwarsa da kuma yin biyayya da su ana kiran su "almajirai."
  • Yahaya mai baftisima shima yana da almajirai.
  • A lokacin hidimar Yesu akwai almajirai da dama da suka bi shi suka saurari koyarwarsa.
  • Almajiran Yesu ya zaɓi almajirai goma sha biyu su kasance masu bin sa na kurkusa; waɗannan mutane su aka sani da "manzanni."
  • Almajiran Yesu sha biyu sun ci gaba da zama "almajiransa" ko "sha biyu."
  • Gab da tafiyar Yesu sama, ya ummarci almajiransa da su koya wa sauran mutane yadda suma za su zama almajiran Yesu.
  • Duk wanda ya yi imani da kuma biyayya ga koyarwarsa ana ki ransa almajirin Yesu.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar almajiri za'a iya amfani da ita a ambaci "mai bi" ko "ɗalibi" ko mai "koyo" ko "makoyi"
  • A tabbata cewa irin wanan fassarar kalmar ba wai makoyi da ke koyo a aji kawai take nufi ba.
  • Fassarar irin wanan kalma za ta zama da bambanci dafassarar kalmar "manzo."

(Hakanan duba: manzo, imani, Yesu, Yahaya (mai Baftisima), sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:1
  • Ayyukan Manzanni 09:26-27
  • Ayyukan Manzanni 11:26
  • Ayyukan Manzanni 14:22
  • Ayyukan Manzanni 13:23
  • Luka 06:40
  • Matiyu 11:03
  • Matiyu 26:33-35
  • Matiyu 27:64

amin, hakika, gaskiya

Ma'ana

Wannan furci "amin" kalma ce da ake amfani da ita a nanata ko a jawo hankali ga abin da wani ya faɗa. Yawancin lokaci ana amfani da ita a ƙarshen addu'a. Wani lokaci ana fassara shi ya zama "gaskiya."

  • Sa'ad da aka yi amfani da ita a ƙarshen addu'a, "amin" na nuna yarda da addu'ar ko kuma nuna marmarin nufin addu'ar ta cika.
  • Yesu a koyarwarsa, ya yi amfani da "amin" domin ya ƙarfafa gaskiyar abin daya faɗi. Yawancin lokaci kuma zai bi wannan da "ina kuma ce maku" domin ya gabatar da wata koyarwar wadda take game da ta bisani.
  • Sa'ad da Yesu ya yi amfani da "amin" wasu juyi a Turanci (har da ULB) sukan fassara shi zuwa "hakika" ko "gaskiya."
  • Wata kalma kuma mai ma'anar "gaskiya" ana fassara ta wani lokaci a ce "lallai" ko "tabbas" ana amfani da su domin a karfafa abin da mai maganan yake faɗi.

Shawarwarin Fassara:

  • A yi lura ko yaren dake yin fassara suna da wata kalma ko furci musamman da ake amfani da ita domin a jaddada wani abin da aka rigaya aka faɗa.
  • Sa'ad da aka yi amfani da ita a ƙarshen addu'a domin a tabbatar da abu, za a iya fassara "amin" zuwa "bari ya zama" ko "bari haka ya faru" ko "wannan gaskiya ne."
  • Sa'ad da Yesu ya ce, "gaskiya ina gaya maku," wannan ma za a iya juya shi zuwa, "I, gaskiya ina gaya maku" ko "wannan gaskiya ne, Ni kuma ina gaya maku."
  • Wannan furci, "gaskiya, gaskiya ina gaya maku" za a iya juya shi zuwa "Ina gaya maku akan gaskiya" ko "ina gaya maku wannan da himma" ko abin da nake gaya maku gaskiya ce"

(Hakanan duba: cikawa, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 27:15
  • Yahaya 05:19
  • Yahuda 01:24-25
  • Matiyu 26:33-35
  • Filimon 01:23-25
  • Wahayin Yahaya 22:20-21

amintacce, yin aminci, marar aminci, rashin aminci

Ma'ana

Zama da "aminci" ga Allah na nufin har kullum mu yi rayuwa bisa ga koyarwar Allah. Yana nufin mu zama da aminci gare shi ta wurin yi masa biyayya. Mataki ko yanayi na zama da aminci shi ne yin aminci."

  • Mutumin da ke da aminciza'a iya dogara da shi a ko da yaushe yakan riƙe alƙawaransa kuma har kullum yakan cika wajibansa ga sauran mutane.
  • Mutum mai aminci yakan jure a cikin yin aikin da aka danƙa masa, koma da abin na da tsawo kuma yana da wahala.
  • Aminci ga Allah shi ne nacewa kulum cikin yin abin da Allah ke so mu yi.
  • Kalmar nan "rashin aminci" tana nuna mutane waɗanda basu yin abin da Allah ya umarce su su yi. Yanayi ko mataki na zama marar aminci shi ake kira "rashin aminci."
  • An kira mutanen Isra'ila "marasa aminci" a lokacin da suka ci gaba da bautawa gumaka, da kuma a lokacin da suka yiwa Allah rashin biyayya ta waɗansu hanyoyi.
  • A cikin aure, wanda ya yi zina shi "marar aminci" ne ga matarsa ko ga maigidanta.
  • Allah ya yi amfani da kalmar rashin aminci domin ya nuna halin rashin biyayya na Isra'ila. Basu yin biyayya ga Allah ko kuma girmama shi.

Shawarwarin Fassara:

  • A wurare da yawa "aminci" ana fassara shi da kalmar "ladabi" ko "sadaukarwa" ko kuma "abin dogara."
  • A waɗansu wuraren, za'a iya fassara "aminci" da cewa hali ne na nacewa cikin yin biyayya da kuma imani da Allah,"
  • Hanyoyin da za'a iya fassara aminci sun haɗa da "juriya cikin imani" ko "ladabi" ko "zama abin dogaro" ko gaskatawa da kuma yin biyayya ga Allah."
  • Ya danganta ga wurin, "rashin aminci za'a iya fassara shi da "ƙin yin aminci" ko rashin yin "imani" ko "rashi biyayya" ko rashin "ladabi."
  • Ƙaulin nan "rashin aminci" za'a iya fassara shi da "mutane mara aminci (ga Allah)" ko "waɗanda ke yi wa Allah rashin biyayya" ko "mutanen da kan tayar wa Allah."
  • Kalmar nan "rashin aminci" za'a iya fassara ta da "halin rashin biyayya" ko "rashin aminci" ko "rashin imani ko biyayya."
  • A waɗansu harsunan, kalmar "rashin amnci" an danganta ta da kalmar "rashin bangakiya."

(Hakanan duba: zina, imani, rashin biyayya, bangaskiya, imani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 24: 49
  • Lebitikus 26:40
  • Littafin Lissafi 12:07
  • Yoshuwa 02:14
  • Littafin Alƙalai 02:16-17
  • 1 Sama'ila 02:09
  • Zabura 012:01
  • Littafin Misalai 11:12-13
  • Ishaya 01:26
  • Irmiya 09:7-9
  • Hosiya 05:7
  • Luka 12:46
  • Luka 16:10
  • Kolosiyawa 01:07
  • 1 Tasalonikawa 05:24
  • 3 Yahaya 01:05

amintaccen alƙawari, alƙawarin amana, ƙauna mai alheri, ƙauna marar ƙarewa

Ma'ana

Waɗannan kalmomi ana amfani da su a nuna niyyar Allah ya cika alƙawaran da yayi wa mutanensa.

  • Allah yayi wa Isra'ilawa alƙawarai a cikin wani tsararren shiri da ana kiransa "alƙawari."
  • "Amintaccen alƙawari" ko "alƙawarin aminci" na Yahweh yana bayyana yadda Yahweh mai cika alƙawaransa ne ga mutanensa.
  • Amincin Allah game da cika alƙawaransa yana nuna shi mai alheri ne ga mutanensa.
  • Wannan kalma "bada kai" wata kalma ce da ke nuna amincewa da dogara ga wani cewa zai yi abin da ya alƙawarta da abin da zai zama da riba ga wani.

Shawarwarin Fasara:

  • Yadda aka fassara wannan kalma zai danganta ga yadda aka fassara waɗannan kalmomi "alƙawari" da "aminci."
  • Waɗansu hanyoyin fassara wannan kalma sune, "ƙauna mai aminci" ko "bada kai, ko "ƙauna mai jimiri" ko "ƙaunar da za a iya dogara da ita."

(Hakanan duba: alƙawari, aminci, alheri, Isra'ila, mutanen Allah, alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezra 03:11
  • Littafin Lissafi 14:18

annabi, annabawa, annabci, yin annabci, mai gani, annabiya

Ma'ana

"Annabi" mutum ne wanda yake faɗin saƙonnin Allah ga mutane. Mace mai yin haka ana kiranta "annabiya."

  • Yawancin lokaci annabawa sukan faɗakar da mutane su juyo daga zunubansu su yi biyayya ga Allah.
  • "Annabci" shi ne saƙon da annabi ke faɗi. "Yin annabci" shi ne faɗin saƙonnin Allah.
  • Yawancin lokaci saƙon annabci na haɗe da abin da zai faru a wani lokaci mai zuwa.
  • Annabci da yawa a cikin Tsohon Alƙawari sun rigaya sun cika.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, litattafan da annabawa suka rubuta, wasu lokuta ana kiransu "annabawa."
  • Misalin wannan furci, "littafin shari'a da annabawa" hanya ce ta ambaton dukkan nassin Yahudawa, waɗanda aka sansu a matsayin "Tsohon Alƙawari."
  • Wata tsohuwar magana game da annabi shi ne "mai gani" ko "mutumin dake gani."
  • Wani lokaci "mai gani" na nufin maƙaryacin annabi ko wani dake aikata sihiri.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "annabi" za a iya fassarawa haka "mai magana ga Allah" ko "mutumin da yake magana domin Allah" ko "mutumin dake faɗar saƙonnin Allah."
  • Za a iya fassara "mai gani" haka, "mutumin dake ganin wahayi" ko "mutumin dake hangen lokaci mai zuwa daga Allah."
  • Wannan magana "annabiya" za a iya fassarawa haka "mace mai faɗi domin Allah" ko "mace mai magana domin Allah" ko "mace wadda take faɗin saƙonnin Allah."
  • Wasu hanyoyin fassara "annabci" za su zama kamar haka, "saƙo daga Allah" ko "saƙon annabi."
  • Wannan magana "yin annabci" za a iya fassarawa haka, "faɗin maganganu daga Allah" ko " a faɗi saƙon Allah."
  • Wannan misali a cikin furci, "shari'a da annabawa" za a iya fassarawa haka, "litattafan shari'a dana annabawa" ko "dukkan abin da aka rubuta game da Allah da mutanensa, har da shari'ar Allah, da abin da annabawansa suka yi wa'azi a kai."
  • Idan ana ambaton annabi (mai gani) na gunki, zai zamana dole a fassara wannan haka "maƙaryacin annabi (mai gani) ko "annabi (mai gani) na gunki" ko "annabin Ba'al," a misali.

(Hakanan duba: Ba'al, sihiri, gunki, maƙaryacin annabi, cika, shari'a, wahayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:14-16
  • Ayyukan Manzanni 03:25
  • Yahaya 01:43-45
  • Malakai 04:4-6
  • Matiyu 01:23
  • Matiyu 02:18
  • Matiyu 05:17
  • Zabura 051:01

Asabaci

Ma'ana

Kalmar "Asabaci" na nufin rana ta bakwai cikin mako, wadda Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe ta ranar hutu kada a yi wani aiki.

  • Bayan Allah ya gama hallitar duniya cikin kwana shida, sai ya huta a rana ta bakwai. Haka kuma, Allah ya dokaci Isra'ilawa da su keɓe rana ta bakwai a matsayin rana ta musamman don hutu da kuma yi masa sujada.
  • Dokar "a kiyaye ranar Asabaci da tsarki" na ɗaya daga cikin dokoki goma da Allah ya rubuta kan allon dutsen da ya baiwa Musa domin Isra'ilawa.
  • Bisa ga ƙidayar ranakun Yahudawa, ranar Asabaci daga faɗuwar ranar Jumma'a ne har zuwa Sati faɗuwar rana.
  • Wani lokacin a cikin Littafi Mai Tsarki Asabaci ana kiranta "Ranar Asabaci" a maimakon Asabaci.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan za a kuma iya fassarawa haka, "ranar hutawa" ko "ranar da ba a aiki" ko "ranar Allah ta hutawa."
  • Wasu juyin na amfani da manyan haruffa wajen rubuta wannan kalma domin a nuna rana ce ta musamman, kamar "Ranar Asabaci" ko "Ranar Hutawa."
  • Ayi la'akari da yadda ake fassara kalmar a yaren lardin ko na ƙasar.

(Duba kuma: hutu)

Wurarenda ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 31:2-3
  • Ayyukan Manzanni 13:26-27
  • Fitowa 31:14
  • Ishaya 56:6-7
  • Littafin Makoki 02:06
  • Lebitikus 19:03
  • Luka 13:14
  • Markus 02:27
  • Matiyu 12:02
  • Nehemiya 10:32-33

ayyuka, aiwatarwa, aiki,

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, "ayyuka," "aiwatarwa," dukkansu suna manufar abubuwan da Allah ko mutane ke aikatawa ne.

  • Kalmar "aiki" na nufin yin kwadago ko duk wani abin da ake yi domin yi wa wasu mutane hidima.
  • "Ayyukan" Allah da kuma "aikin hannuwansa" magana ce dake nufar dukkan abubuwan da yake yi ko ya rigaya ya aikata, har ma da hallitar duniya, ceton masu zunubi, tanadawa dukkan hallinsa da kuma adana dukkan duniya a matsayi ɗaya. Kalmomin "aiwatarwa" da kuma "ayyuka" ana amfani da su a bayyana al'ajiban Allah kamar "manyan ayyuka" ko "ayyukan mamaki."
  • Ayyuka da aikin da mutum ya yi na iya zama nagari ko mugu.
  • Ruhu Mai Tsarki na ikonta masubi domin su yi ayyuka nagari, waɗanda ake ce da su "iri mai kyau."
  • Mutane ba su samun ceto ta wurin aikata ayyuka nagari; ana cetonsu ta wurin bangaskiyarsu cikin Yesu.
  • "Aikin" mutum na iya zama abin da yake yi domin samun abin zaman gari ko domin yiwa Allah hidima. Littafi ma ya shaida Allah da "yin aikin."

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara "ayyuka" ko "aiwatarwa" zasu iya zama "ayyuka" ko "abubuwan da ake yi."
  • Sa'ad da ake nufin "ayyukan" Allah ko "aiwatarwa" da kuma "aikin hannuwansa," wannan faɗar za a kuma iya fassarawa haka "al'ajibai" ko "manyan ayyuka" ko "abubuwan ban mamaki da yake yi."
  • Faɗar "aikin Allah" za a iya fassarawa haka "abubuwan da Allah ke yi" ko "al'ajiban da Allah yake yi" ko "abubuwan ban mamaki da Allah yake yi" ko "kowanne abin da Allah ya aiwatar."
  • Kalmar "aiki" zai iya zama jimlar guda na "ayyuka" kamar a "kowanne aiki nagari" ko "kowanne aiwatarwa nagari."
  • Kalmar "aiki" zata iya samun ma'ana mai fãɗi na "hidima" ko "aikin hidima." A misali. Faɗar "aikinka cikin Ubangiji" za a kuma iya fassarawa a matsayin, "abin da kake yiwa Ubangiji."
  • Faɗar "ka gwada aikinka" za a iya fassarawa a matsayin "ka tabbata cewa abin da kake yi nufin Allah ne" ko "ka tabbata cewa abin da kake yi ya gamshi Allah."
  • Faɗar "aikin Ruhu Mai Tsarki" za a iya fassarawa a matsayin "ikontawar Ruhu Mai Tsarki" ko "hidimar Ruhu Mai Tsarki" ko "abubuwan da Ruhu Mai Tsarki yake yi."

(Hakanan duba: 'ya'yan itace, Ruhu Mai Tsarki, al'ajibi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:12
  • Ayyukan Manzanni 02:8-11
  • Daniyel 04:37
  • Fitowa 34:10-11
  • Galatiyawa 02:15-16
  • Yakubu 02:17
  • Matiyu 16:27-28
  • Mika 02:07
  • Romawa 03:28
  • Titus 03:4-5

Ba'al'umme, Al'ummai

Ma'ana

Kalmar nan "Ba'al'ume" tana nufin duk an da ba bayahude ba ne". Al'umai mutane ne da ba su cikin zuriyar Yakubu.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "marar kaciya" ana moron ta cikin salon magana domin ambaton al'ummai sabada da yawan su ba su yiwa 'ya'yansu maza kaciya kamar yadda Isra'ilawa ke yi.
  • Sabo da Allah ya zaɓi Yahudawa su zama mutanensa na musamman, sai suka ɗauki al'ummai kamar bare da ba za su taɓa zama mutanen Allah ba.
  • Ana kiran yahudawa "Isra'ilawa" ko "Ibraniyawa" a mabambanta lokuta cikin tarihi, kuma suna ganin kowa a matsayin "Ba'al'umme."
  • Za'a iya fassara al'ummai a matsayin waɗanda "ba Yahudawa ba" ko "ba Bayahude ba" ko "ba Ba'isra'ile ba" (Tsohon Alƙawari) ko kuma "ba Yahudu ba."
  • Bisa ga al'ada, Yahudawa ba su cin abinci ko kuma yin wata cuɗanya da al'ummai, wanda hakan ne ya fara kawo matsala a cikin ikkilisiyar farko.

(Hakanan duba: Isra'ila, Yakubu, Bayahude)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 09: 13-16
  • Ayyukan Manzanni 14:5-7
  • Galatiyawa 02:16
  • Luka 02:32
  • Matiyu 05:47
  • Matiyu 06:5-7
  • Romawa 11:25

Ba'sadusi, Sadusiyawa

Ma'ana

Sadusiyawa 'yan ƙungiyar siyasa ne na firistocin Yahudawa a zamanin Yesu Almasihu. Sun yadda da shugabancin Romawa basu kuma yadda akwai tashin matattu ba.

  • Dayawa daga cikin Sadusiyawa masu dukiya ne, mawadata ne cikin Yahudawa waɗanda ke riƙe da matsayi na shugabanci masu daraja kamar shugaban firist da babban firist.
  • Ayyukan Sadusiyawa ya kunshi kula da harabar haikali da kuma ayyukan firistoci kamar miƙa hadayu na baiko.
  • Sadusiyawa da Farisiyawa sun zuga shugabannin Romawa domin su gicciye Yesu.
  • Yesu ya yi magana gãba da waɗannan ƙungiyoyin addini domin son zuciyarsu da kuma munafuncinsu.

(Hakanan duba: shugabannin firistoci, majalisa, babban firist, munafuki, shugaban Yahudawa, Farisi, firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:03
  • Ayyukan Manzanni 05:17-18
  • Luka 20:27
  • Matiyu 03:07
  • Matiyu 16:01
  • Matiyu 16:01

bãbã, bãbãni

Ma'ana

A kusan kullum in ana magana akan kalmar nan bãbã ana nufin mutum ne da aka cirewa mazakuta. A wancan lokacin an yi amfani da kalmar wajen ambaton duk wani jami'in gwabnati, koma da waɗanda basu da wani lahani a jiki.

  • Yesu ya ce waɗansu bãbãnin haka aka haife su, ƙila sabo da lahani a fannin mazakutarsu, ko kuma sabo da rashin iya yin jima'i. Sauran suka zaɓi yin rayuwa irin ta bãbãni.
  • A kwanakin cancan baya bãbãni su ne masu yiwa sarki hidima, akan sa su su zama 'yan tsaro akan wurin zaman mata.
  • Waɗansu bãbãnin kuma manyan jami'ai ne na hukuma, irin su bãbã na Habasha, wanda ya sadu da manzo Filib a jeji.

(Hakanan duba: Filib)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 08:27
  • Ayyukan Manzanni 08:36
  • Ayyukan Manzanni 08:39
  • Ishaya 39:7-8
  • Irmiya 34:17-19
  • Matiyu 19:12

babban firist, shugabannin firistoci

Ma'ana

Kalmar nan "babban firist" tana nufin firist na musamman da aka sa ya yi hidimar babban firist na shekara ɗaya a matsayin shugaban dukkan firistocin Isra'ila. A lokacin Sabon Alƙawari, waɗansu sauran firistocin suma akan ɗauke su da muhimmanci sosai a cikin shugababannin addinin Yahudawa, tare da iko akan sauran firistocin da kuma mutane. Waɗannan su ne manyan firistoci.

  • Babban firist na da aikin na musamman. Shi kaɗai ke da damar shiga wuri mafi tsarki na rumfar sujada ko haukali domin miƙa hadaya sau ɗaya a shekara.
  • Isra'ilawa na da firistoci da yawa, amma babban firist ɗaya ne tak a lokaci guda.
  • Bayan babban firist ya yi ritaya, sukan riƙe sunan matsayinsu, tare da sauran waɗansu aikace-aikace na ofishi. Misali, Annas ya kasance babban firist a lokacin aikin firist na Kayafas da sauransu.
  • Manyan firistoci su ke da ɗawainiyar duk wani abu da ya shafi sujada a cikin haikali. Hakanan su ne ke kula da kuɗi da aka bayar a cikin haikali.
  • Manyan firistoci su ne suka fi girma da iko fiye da sauran firistoci. Babban firist ne kaɗai ya fi iko.
  • Shugabannin firistoci su ne suka zama waɗansu daga cikin manyan maƙiyan Yesu kuma suka matsa wa shugabannin Romawa da su kama shi su kashe shi.

Shawarwarin Fassara:

"Babban firist" za'a iya fassara shi da "firist mafi iko" ko " firist mafi girman matsayi."

  • Kalmar nan "manyan firistoci" za'a iya fassara ta da "shugabannin firistoci" ko "jogororin firistoci" ko "mahukuntan firistoci."

(Hakanan duba: Annas, Kayafas, firist, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 05:27
  • Ayyukan Manzanni 07:1
  • Ayyukan Manzanni 09:1
  • Fitowa 30:10
  • Ibraniyawa 06:19-20
  • Lebitikus 16:32
  • Luka 03:2
  • Markus 02:25-26
  • Matiyu 26:3-5
  • Matiyu 26:51-54

Bafarisiye, Farisawa

Ma'ana

Farisawa mahimman mutane ne ƙungiya kuma mai iko na shugabanin addinin Yahudawa a zamanin Yesu.

  • Da yawansu mawadatan tsaka-tsaka ne 'yan kasuwa wasunsu kuma firistoci ne.
  • Cikin dukkan shugabannin Yahudawa, Farisawa sune masu matsawa ayi biyayya da Shari'ar Musa da kuma wasu dokokin Yahudawa da al'adunsu.
  • Suna da damuwar su ga mutanen Yahudawa sun keɓe daga cuɗanya da al'umman dake kewaye da su. Sunan nan "Bafarisiye ya zo ne daga wannan magana "keɓewa."
  • Farisawa sun gaskata akwai rayuwa bayan an mutu; kuma sun gaskata akwai mala'iku da wasu hallitun ruhohi.
  • Farisawa da Sadusiyawa sun ƙalubalanci Yesu da Kiristocin fãri.

(Hakanan duba: majalisa, shugabannin Yahudawa, shari'a, Sadusiyawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 26:04
  • Yahaya 03:1-2
  • Luka 11:44
  • Matiyu 03:07
  • Matiyu 05:20
  • Matiyu 09:11
  • Matiyu 12:02
  • Matiyu 12:38
  • Filibiyawa 03:05

baftisma

Ma'ana

A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "baftisma" za a fassara ta haka "yiwa Kirista wanka a ruwa don a nuna an tsarkake shi daga zunubi an kuma haɗa shi ɗaya da Almasihu.

  • Banda kuma baftisma ta ruwa, Littafi Mai Tsarki ya yi maganar "baftismar Ruhu Mai Tsarki" da "baftisma da wuta."
  • Wannan kalma "baftisma" an sake yin amfani da ita a Littafi Mai tsarki domin a fassara shan matsananciyar wahala.

Shawarwarin Fassara:

  • Kiristoci sun banbanta a ra'ayi game da yadda za a yiwa mutum baftisma da ruwa. Mai yiwuwa zai fi kyau a fassara wannan kalma da yadda za a yi amfani da ruwan kawai.
  • Zai danganta ga nassin, kalmar "baftisma" za a iya fassara haka "a tsarkake," "a zuba a kan," ko lumawa" a ko (tsomawa) a ciki," "wankewa," ko "tsabtacewa a ruhaniya." A misali, "a yi maka baftisma da ruwa" za a iya fassarawa a matsayin , "tsoma ka cikin ruwa."
  • Kalmar "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "tsarkakewa," "zubawa," "lumawa," "tsabtacewa," ko "wankewar ruhaniya."
  • Sa'ad da ake nufin wahala, "baftisma" za a iya fassarawa a matsayin "zamanin matsananciyar wahala" ko "tsabtacewa ta wurin matsananciyar wahala."
  • A kuma yi la'akari da yadda ake fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki cikin yaren garin ko ƙasar.

(Hakanan duba: Yahaya (mai Baftisma), tuba, Ruhu Mai Tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:38
  • Ayyukan Manzanni 08:36
  • Ayyukan Manzanni 09:18
  • Ayyukan Manzanni 10:48
  • Luka 03:16
  • Matiyu 03:14
  • Matiyu 28:18-19

bagadi, bagadai

Ma'ana

Bagadi wani tudu ne da Isra'ilawa suke tayarwa suna ƙona dabbobi a kansa da tsaba domin baye-baye ga Allah.

  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, akan yi bagadi yawancin lokaci da tsibin ƙasa da aka mulmula ko a jera manyan duwatsu da za su iya tsayawa da kansu.
  • Wasu bagadai musamman an yi su kamar akwati da katako aka dalaye su da ƙarafa kamar su zinariya, jan ƙarfe, ko tagulla.
  • Wasu al'umman dake zaune kusa da Isra'ilawa suma sun gina bagadai domin allolinsu.

(Hakanan duba: bagadin turaren ƙonawa, allahn ƙarya, baikon hatsi, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 08:20
  • Farawa 22:09
  • Yakubu 02:21
  • Luka 11:49:51
  • Matiyu 05:23
  • Matiyu 23:19

baiwa, baye-baye

Ma'ana

"Baiwa" ita ce duk wani abu da aka ba wani. Baiwa akan yi ta ne ba tare da sauraron karɓar wani abu ba domin sakaiya.

  • Kuɗi, sutura, kosauran abububuwa da kae ba mabukata ana kiran su "kyautai,"
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, baiko ko hadayar da aka ba Allah ana kiran su kyauta.
  • Kyautar ceto wani abu ne da Allah ke bamu ta wurin bangaskiya a cikin Yesu.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kalmar nan "baye-baye" ana ma moron ta a ambaci baiwa ta musamman ta ruhaniya wani wanan ƙwarewa da Allah ya ba dukkan masu bi domin su hidimtawa sauran mutane.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "baiwa" kai tsaye za'a iya fassara ta da kalmar "kyautar da aka yi ta wani abu."
  • A wurin da wani yake da baiwa ko wani buɗi na musamman da ya zo daga wurin Allah, kalmar "baiwa ta Ruhu" ko kuma wata fasaha ta "musamman ta ruhu da Allah ya bayar."

(Hakanan duba: ruhu, Ruhu Mai Tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 12:1
  • 2 Sama'ila 11:8
  • Ayyukan Manzanni 08:20
  • Ayyukan Manzanni 10:4
  • Ayyukan Manzanni 11:17
  • Ayyukan Manzanni 24:17
  • Yakubu 01:17
  • Yahaya 04:9-10
  • Matiyu 05:23
  • Matiyu 08:4

ban girma, girmamawa

Ma'ana

Kalmar nan "girmamawa" da kuma "a girmama na" nufin aba wani girma, aga ƙimarsa ko a darajanta shi.

  • Girma akan fi bada shi ne ga wanda ya fi matsayi da mahimmanci, kamar sarki, ko Allah.
  • Allah ya gargaɗi Krista da su girmama juna.
  • An gargaɗi 'ya'ya da su girmama iyayensu a hanyar da zata nuna suna girmama su da kuma yi masu biyayya.
  • Kalmar nan "girma" da "ɗaukaka" akan fi moron su tare musamman in ana magana game da Yesu. Waɗanan zasu iya zama ta hanyoyi mabambanta da ake maganar abu ɗaya game da Yesu kan wani abu.
  • Hanyoyin girmama Allah sun haɗa da gode masa da kuma yabon sa da kuma bashi girma ta wurin yi masa biyayya da kuma yin rayuwar da ke nuna girmansa.

Shawarwrin Fassara:

  • Waɗansu sauran hanyoyi na yin fassarakan "ban girma" sun haɗa da "gimamawa" ko "ganin daraja" ko "matsanancin ganin ƙima."
  • Kalmar a "girmama" za'a iya yin fassarar ta a nuna "ban girma na musamman ga" ko "asa wani ya sami yabo" ko "matuƙar yin la'akari da wani" a "babban mataki mai daraja."

(Hakanan duba: rashin girmamawa, ɗaukaka, yabo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 02:8
  • Ayyukan Manzanni 19:17
  • Yahaya 04:44
  • Yahaya 12:26
  • Markus 06:o4
  • Matiyu 15:06

Banaziri, Nazirawa, wa'adin Nazirinci

Ma'ana

Wannan furci "Banaziri" na nufin wani mutum da ya ɗauki "wa'adin keɓewa." Yawancin lokaci maza ne ke ɗaukar wannan wa'adin, amma mata ma suna iya ɗauka.

  • Mutumin da ya ɗauki wa'adin Nazirinci ya yarda kenan ba zai ci abinci ko ya sha abin da aka yi daga 'ya'yan inabi ba har zuwa cikar tsawon lokaci da aka sa akan wa'adin. A wannan lokaci ba zai yi aski ba ko ya kusanci gawa.
  • Sa'ad da ƙayyadadden lokacin ya cika, kuma an cika wa'adin, Banazirin zai tafi wajen firist ya bada baiko. Wannan zai haɗa da yin aski sa'an nan a ƙona gashin. Duk wasu 'yanci da dã aka hana shi za a ɗauke.
  • Samson sanannen mutum ne a cikin Tsohon Alƙawari wanda ya kasance ƙarƙashin wa'adin Nazirinci.
  • Mala'ikan daya sanar da haihuwar Yahaya Mai Baftisma ya gaya wa Zakariya cewa ɗansa ba zai sha ruwan barasa ba, wannan zai nuna Yahaya ya kasance a ƙarƙashin "wa'adin Nazirinci."
  • Bisa ga wani nassi a littafin Ayyukan Manzanni manzo Bulus mai yiwuwa a wani lokaci ya ɗauki wannan wa'adi.

(Hakanan duba: Yahaya (mai Baftisma), hadaya, Samson, wa'adi, Zakariya (Tsohon Alƙawari))

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 18:18-19
  • Amos 02:11-12
  • Littafin Alƙalai 13:05
  • Littafin‌ Lissafi 06:1-4

bangaskiya

Ma'ana

A faiyace, kalmar nan "bangaskiya" tana magana ne akan imani, dogoro, ko amincewa da wani, ko wani abu.

  • A zama da "bangaskiya" ga wani shi ne ayi imani cewa abin da yake yi ko faɗi gaskiya ne, kuma abin amincewa ne.
  • A "bada gaskiya' a cikin Yesu shi ne a yi imani da koyarwar Allah game da Yesu. Musumman ta wurin dogara ga Yesu da kuma hadayarsa ta tsarkake mutane daga zunubansu, a kuma cece su dagahukuncin da ya wajabce su sabo da zunubansu.
  • Bangakiya ta ƙwarai ga Yssu za ta sa mutun ya bada 'ya'yan ruhaniya nagari ko yin halaiya mai kyau sabo da Ruhu mai Tsarki na rayuwa a cikinsa.
  • A wani lokacin "bangaskiya" tana magana ne akan dukkan koyarwa game da Yesu, kamar yadda yake a cikin "zantuttukan bangaskiya."
  • A wurwre kamar "riƙe bangaskiya" ko watsi da bangaskiya," lamar nan bangaskiya na nufin matsaya ce ta yin imani kan dukkan bangaskiya game da Yesu.

Shawarwarin Fassara:

  • Awaɗansu wuraren, "bangaskiya" za'a iya fassara ta a matsayin 'imani" ko "haƙaƙewa" ko "amincewa" ko "dogaro."
  • A waɗansu harsunan waɗanan kalmomin za'a iya fassara su da kalmar aikatau wato yin "imani." kamar sunayen abubuwan da ba'a iya gani
  • Ƙaulin nan "tsare imani" za'a iya fassara shi da "a ci gaba da yin imani a cikinYesu" ko kuma gaba da bada gaskiya a cikin Yesu."
  • Jimlar nan "tilas ne su riƙe zurfafan gaskiya" za'a iya fassara ta da cewa "dole ne su ci gaba da yin imani akan dukkan abubuwa na gaskiya wanda aka koya musu game da Yesu."
  • Ƙaulin nan " ɗana na hakika a cikin imani" za'a iya fassara shi da cewa wanda yake kamar ɗa ne a gare ni sabo da na koyar da shi ya yi imani cikin Yesu" ko kuma ɗana na hakika a cikin ruhaniya wanda ya yi imani a cikin Yesu."

(Hakanan duba: gaskata, amintacce)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:07
  • Ayyukan Manzanni 06:07
  • Galatiyawa 02:20-21
  • Yakubu 02:20

Bayahude, Yahudanci, Yahudawa

Ma'ana

Yahudawa mutane ne zuriyar Yakubu jikan Ibrahim. Kalmar "Bayahude" ta fito daga kalmar "Yahuda."

  • Mutane ne suka fara kiran Isra'ilawa "Yahudawa" bayan da suka dawo Yahuda daga hijira a Babila.
  • Yesu wanda yake shine Mesaya Bayahude ne. Duk da haka, shugabannin addinin Yahudanci suka ƙi Yesu suka kuma nemi cewa a kashe shi.
  • Yawancin lokaci furta kalmar "Yahudawa" ana nufin shugabannin Yahudawa, ba dukkan mutane Yahudawa ba. A cikin wannan rukunin, wurin fassarar kalmar wasu suna haɗawa da "shugabannin" domin a ƙara fahimta.

(Hakanan duba: Ibrahim, Yakubu, Isra'ila, Babila, shugabannin Yahudanci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan manzanni 02:05
  • Ayyukan manzanni 10:28
  • Ayyukan manzanni 14:5-7
  • Kolosiyawa 03:11
  • Yahaya 02:14
  • Matiyu 28:15

bayyanawa, ana bayyanawa, bayyananne, ruya ko wahayi

Ma'ana

kalmar "bayyanawa" na manufar a sa wani abu shi zama sananne. "Ruya" wani abin da aka sa aka san da shi ne.

  • Allah ya sa an san da shi ta wurin dukkan abubuwan da ya hallita da kuma ta wurin sadarwasa da mutanensa ta wurin magana da kuma saƙonnai a rubuce.
  • Allah yana bayyana kan sa kuma ta wurin mafalkai da wahayai.
  • Da Bulus ya ce ya karɓa Labarin nan Mai Daɗi ta "ruya daga Yesu Kristi," yana nufi da cewa Yesu ne da kansa ya yi masa bayanin Labarin Mai Daɗi.
  • A cikin littafin Sabuwar Alƙawari "Wahayi" Allah ke bayyana yanayin da zasu faru a kwanakin ƙarshe. Ya bayyana su ga ManzoYohanna ta wurin wahayi.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara "bayyanawa" zasu iya haɗawa da "asa ya zama sananne" ko "a buɗe" ko "a nuna a sarari."
  • Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara "ruya ko wahayi" zai iya zama magana daga Allah" ko "abubuwan da Allah ya bayyana

ko "koye-koye game da Allah." zaifi kyau a riƙe ma'anar "bayyanawa" a cikin fassarar.

  • Faɗar "inda babu ruya ko wahayi" za a iya fassarawa haka "sa'ad da Allah baya bayyana kansa ga mutane" ko "cikin mutane waɗanda Allah baiyi magana ba."

(Hakanan duba: labari mai daɗi, mafarki, wahayi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 11:1-2
  • Afisawa 03:05
  • Galatiyawa 01:12
  • Littafin Makoki 02:13-14
  • Matiyu 10:26
  • Filibiyawa 03:15
  • Wahayin Yahaya 01:01

bege, abin da aka yi bege, yin bege

Ma'ana

Bege wani babban jimiri wani abu ne da zai faru. Bege zai iya zama da tabbaci ko kuma rashin tabbaci kan abin da zai faru nan gaba.

  • A cikin Littafi mai Tsarki, kalmar "bege" tana da ma'anar "amincewa," misali "a cikin begena ga Ubangiji." Yana magana ne akan tabbaci sa zuciyar karɓar abin da Allah ya yi wa mutanennsa alƙawari.
  • Waɗansu lokutan wannan fassarar takan fassara ta a cikin harshen asali misali "tabbaci." Wannan na faruwa ne mafi yawa a cikin Sabon Alƙawari a cikin yanayin da mutanen da suka gaskata da Yesu a matsayin mai ceto da Ubangiji ke da tabbaci (ko yaƙiini ko bege)na karɓar abin da Allah ya alƙawarta.
  • "Zama da rashin bege" na nufin a zama da rashin sa zuciya ga komaI da ke da kyau da ke faruwa. Yana nufin cewa hakika ba zai faru ba.

Shawarwarin Fassara:

  • A waɗansu wuraren, kalmar yin "bege" za'a iya fassara ta da yin "fata" ko "marmarin" ko "tunanin."
  • Maganar nan "ba wani abin bege" ana iya fassara ta da "ba wani abin da za'a amince da shi" ko "ba wata sa zuciya kan duk wani abu nagari"
  • Zama da "rashin bege" na nufin "rashin sa zuciya ga ga duk wani abu nagari" ko "zama da rashin tsaro" ko yin imanin cewa ba wani abu nagari da zai faru."
  • Maganar nan "ku kafa begenku akan" za'a iya fassara ta da ku sa dogararku a" ko "ku amince cewa."
  • Batun nan cewa "na sami bege cikin maganarka" za'a iya fassara shi da "Ina da yaƙinin cewa maganarka gaskiya ce" ko "maganarka ta taimake ni in dogara gare ka" ko "in na yi biyayya da maganarka hakika zan yi albarka."
  • Ƙaulin nan kamar "kafa bege" ga Allah za'a iya fassara shi da "dogara ga Allah" ko "rantsewa cewa Allah zai yi abin da ya alƙawarta" ko "haƙƙaƙewa cewa Allah mai aminci ne."

(Hakanan duba:albarka, haƙƙaƙewa, nagarta, biyayya, dogara, maganar Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 29:14-15
  • Tassalonikawa 02:19
  • Ayyukan Manzanni 24:14-16
  • Ayyukan Manzanni 26:06
  • Ayyukan Manzanni 27:20
  • Kolosiyawa 01:25
  • Ayuba 11:20

ceto, ceton, cetacce, kãrewa,

Ma'ana

Kalmar "ceta" na nufin kãre wani daga abin da ke na rashin jin daɗi ko na cutarwa. A "kãre" na nufin a shinge daga abin dake cutarwa ko wahala.

  • A mutuntaka, ana kuɓutar da mutane ko a cecesu daga wani abin cuta ko cutarwa ko mutuwa.
  • A ruhaniya, idan aka "ceci" wani, to Allah, ta wurin mutuwar Yesu a kan gicciye, ya gafarta zunubansa ya kuma kuɓutar da shi daga hukuncin lahira domin zunubansa.
  • Mutane na iya ceto ko kuɓutar da mutane daga azaba, amma Allah kaɗai ke iya ceton mutane daga hukunci na har abada domin zunubansu.
  • Kalmar "ceto" na nufin kuɓutarwa daga mugunta da azaba.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, "ceto" na nufin kuɓutarwa ta ruhaniya da azaba ta har abada wadda ke zuwa daga Allah ga waɗanda suka tuba daga zunubansa suka kuma gaskanta da Yesu.
  • Littafi Mai Tsarki kuma ya sake magana game da ceton da Allah ke yiwa mutanensa daga maƙiyansu na zahiri.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "ceto" sun haɗa da "kuɓuta" ko "kiyayewa daga cutarwa" ko "ɗaukewa daga hanyar cuta" ko "kiyayewa daga mutuwa."
  • Faɗar "dukkan wanda zai ceci ransa," kalmar "ceto" za a kuma iya fassarawa haka "adanawa" ko "kiyayewa."
  • Kalmar "kãrewa" za a iya fassarawa haka "kiyayewa daga haɗari" ko "a wurin da babu abin cutarwa."
  • Kalmar "ceto" za a iya fassarawa da amfani da kalmomin dake dangantaka da "cetowa" ko "cafkowa," a matsayin "Allah ya ceto mutane (daga hukunta su domin zunubansu)" ko "Allah ya cafko mutane (daga maƙiyansu)."
  • "Allah ne cetona" za a iya fassarawa haka "Allah ne wanda ke cetona."
  • "Zaku jawo ruwa daga rijiyoyin ceto" za a iya fassarawa haka "za a wartsakar daku kamar da ruwa saboda Allah yana cafko ku."

(Hakanan duba: gicciye, mai kuɓutarwa, hukunta, zunubi, Mai ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 49:18
  • Farawa 47:25-26
  • Zabura 080:08
  • Irmiya 16:19-21
  • Mika 06:3-5
  • Luka 02:30
  • Luka 08:3637
  • Ayyukan Manzanni 04:12
  • Ayyukan Manzanni 28:28
  • Ayyukan Manzanni 02:21
  • Romawa 01:16
  • Romawa 10:10
  • Afisawa 06:17
  • Filibiyawa 01:28
  • 1 Timoti 01:15-17
  • Wahayin Yahaya 19:1-2

cika da Ruhu Mai Tsarki

Ma'ana

Kalmar nan "cika da Ruhu mai Tsarki" salon magana ne a lokacin da aka more ta ana nuna mutum ne wanda Ruhu Mai Tsarki domin yin nufin Allah.

  • Kalmar nan "cika da Ruhu Mai Tsarki" wani bayani ne da ke nuna bishewa ta "Ruhu Mai Tsarki"
  • Mutane na cika da Ruhu mai Tsarki a lokacin da suka bi shugabanci na Ruhu Mai Tsarki muka kuma dogara gare shi domin yin abin da Allah ke so.

Shawarwarin Fassara:

  • Wanan kalmar za'a iya fassara ta da "samun iko daga Ruhu Mai Tsarki" ko kuma Ruhu mai Tsarki ya bishe su." Amma ba zai zama kamar Ruhu Mai Tsarki na tilasta mutum ba ya yi wani abu ba ne.
  • Jimlar nan kamar "ya cika da Ruhu" tana nuna cewa Ruhu mai Tsarki na yi masa jagoranci kuma yana yin cikakkiyar rayuwa ta "Ruhu Mai Tsarki"
  • Kalmar ta yi dai-dai da kalmar "yin rayuwa ta Ruhu," amma kuma "cika da Ruhu mai Tsarki" an jaddada yin rayuwar da zata sa mutum ya bar Ruhu mai Tsarki ya jagoranci rayuwarsa. To waɗannan kalmomin guda biyu za'a iya fassara su ta mabambantan hanyoyi, idan mai yiwuwa ne.

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:31
  • Ayyukan Manzanni 05:17
  • Ayyukan Manzanni 06:8-9
  • Luka 01:15
  • Luka 01:39-41
  • Luka 04:1-2

cikasawa, cikakkake, yin wani abu

Ma'ana

Kalmar nan "cikasawa" tana nufin kammalawa ko cikasa wani abu da ake sauraro.

  • Lokacin da aka cika anabci, wanan ya nuna Allah ya sa abin da aka yi anabci ya cika.
  • Idan mutum ya cika abin da ya yi alƙawari ko wa'adi, wanan na nuna cewa ya cika abin da ya yi alƙawarin yi.
  • A cika wani aiki na nufin yin abin da ake bukaatar mutum ya yi.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "cikasawa" da "kammalawa" ko "gamawa" ko "iddawa" ko "sa abin ya faru" ko "biyayya" ko "cikasa."
  • Kalmar nan "an cikasa" za'a iya fassara ta da "abin ya tabbata" ko "ya zama gaskiya" ko "abin da ya faru" ko "abin da ya wakana."
  • Hanyoyin fassara "cikasawa," kamar a kalmar "cikasa hidamarku," zai haɗa da "kammala" ko "yin" ko "aiwatar" ko hidimta wa sauran mutane kamar yadda Allah ya kira ka ka yi."

(Hakanan duba: annabi, Kristi, mai hidima, kira)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 02:27
  • Ayyukan Manzanni 03:17-18
  • Lebitikus 22:17-19
  • Luka 04: 21
  • Matiyu 01:22-23
  • Matiyu 05:17
  • Zabura 116:12-15

Cin Jibin Ubangiji

Ma'ana

Wannan furci "jibin Ubangiji" manzo Bulus ya yi amfani da ita ya yi magana akan jibin da Yesu ya ci tare da al'majiransa a daren da shugabannin Yahudawa suka kama shi.

  • Lokacin wannan cin abinci, Yesu ya karya Idin gurasa gutsu-gutsu ya kira shi jikinsa, wanda bada jimawa ba za a buge a kashe.
  • Ya kira kokon inabin jininsa, wanda bada jimawa ba za a zubar sa'ad da zai mutu hadaya domin zunubi.
  • Yesu ya umarta cewa idan masu binsa suka riƙa raba abincin nan tare akai-akai, suke tunawa da mutuwarsa da tashinsa.
  • A cikin wasiƙarsa zuwa ga Korantiyawa, manzo Bulus ya ƙara jaddada Jibin Ubangiji ya zama abin yi akai-akai ga masu bada gaskiya ga Yesu.
  • Ikilisiyoyi a yau yawancin lokaci suna kiransa "zumunta da" manufarsu "Jibin Ubangiji. Wasu lokuttan ana amfani da "Jibin Ubangiji" kuma.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci kuma za a iya fassara shi haka "Cimar Ubangiji" ko "Cimar Ubangijinmu Yesu" ko "Cima domin tunawa da Ubangiji Yesu."

(Hakanan duba: Idin ‌Ƙetarewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 11:20
  • 1 Korintiywa 11:25-26

dikin, dikinoni

Ma'ana

Dikin mutun ne wanda ke yin hidima a cikin akkilisiya, yana temakon 'yan'uwa masubi ta fannin bukatu na na jiki kamar abinci da kuɗi.

  • Kalmar nan "dikin" an samo ta ne kai tsaye daga kalmar Girka wadda take nufin "bawa" ko kuma "mai hidima."
  • Daga lokacin masubi na farko dikin na da aikin yi sosai a cikin ikkilisiya.
  • Misali, a cikin Sabon Alƙawari, dikin zai tabbatar cewa duk kuɗi ko abinci da masubi ke rarrabawa za a raba shi ne gwargwadon hali ga gwaurayen da ke cikin su.
  • Kalmar nan "dikin" za a ƙara fassara ta a matsayin "mai hidimar ikkilisiyai" ko "ma'aikacin ikkilisiya" ko "bawan ikkilisiya" ko kuma ta wata hanyar zamu ce mutumin da aka sa ya yi wani aiki na musamman domin amfani ikkilisiya ko al'umar Krista.

(Hakanan duba: mai hidima, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 03:10
  • 1 Timoti 03:13
  • Filibiyawa 01:01

diyya, biyan diyya

Ma'ana

Kalmar "diyya" na ma'anar kuɗi ko wani farashin da aka nema ko aka biya domin sakin wani wanda aka kama.

  • Biyan diyya na nufin biyan farashin yin wata hidima ta miƙa kai domin a kubutar da wani wanda aka kama, aka bautar ko sakawa a kurkuku. A sake saye a maido na da ma'ana dai dai da a "fanso."
  • Yesu ya bada kansa domin a kashe shi ya zama diyya domin ya 'yantar da mutane masu zunubi daga bautarsu ga zunubi. Wannan sãke saye kuma na mutanensa ta wurin biyan farashin zunubansu shi ake kira "fansa" a Littafi Mai Tsarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "diyya" ana iya fassarawa kuma haka "biya domin saki" ko "a biya farashi domin a 'yantar" ko "a sake sawowa."
  • Faɗar "a biya diyya" ana iya fassarawa haka "a biya farashi (na 'yanci)" ko "a biya hukuncin laifi (domin a 'yantar da mutane)" ko "a biya cikakken farashi."
  • Jimlar suna na "diyya" za a iya fassarawa "a sake sawowa" ko "biyan farashin laifi" ko "farashin da aka biya" (domin a 'yantar ko a sake sawo mutane ko ƙasa).
  • Kalmomin "diyya" da "fansa" suna da ma'ana ɗaya a harshen turanci amma wasu lokutta ana ɗan banbantawa. Wasu yarurrukan suna iya kasancewa da ma'ana ɗaya.
  • A tabbatar cewa a fassara wannan daban da "kaffara."

(Hakanan duba: kaffara, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 02:06
  • Ishaya 43:03
  • Ayuba 6:23
  • Lebitikus 19:20
  • Matiyu 20:28
  • Zabura 049:07

duniya, na duniya

Ma'ana

Wannan kalma "duniya" na ma'anar sashen duniya da mutane ke zama ciki: ƙasa. Kalmar "na duniya" na bayyana mugayen ɗabi'u da al'amurran mutanen dake zama cikin duniyan nan.

  • Asalin ma'anarta, kalmar "duniya" na ma'anar sammai ne da ƙasa, duk da abin dake cikinsu.
  • A nassosi da dãma, "duniya" na manufar "mutanen dake cikinta."
  • Wani lokacin kuma ana nufin mugayen mutanen dake cikinta ko kuma mutanen da basu yiwa Allah biyayya ba.
  • Manzanni sun yi amfani da "duniya" su nuna bayyana halin sonkai da gurɓatacciyar ɗabi'un mazamnan wannan duniyar. Wannan zai ƙunshi bautar ganin ido cikin addinin dake na mutuntaka.
  • Mutane ko abubuwan da aka yi masu alaƙa da waɗannan ɗabi'u akan ce masu su "na duniya ne."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, "duniya" za a iya fassarawa a matsayin "duniyoyi" ko "mutanen duniya" ko "lalatattun abubuwan duniya" ko "miyagun ayyukan mutanen duniya."
  • Faɗar "dukkan duniya" yawanci na nufin "mutane da yawa" kuma ana nufin mutanen dake zama a wani lardi. A misali, "dukkan duniya suka zo Masar" za a iya fassarawa a matsayin "mutane da yawa daga ƙasashen kewaye suka zo Masar" ko "mutane daga dukkan ƙasashen dake kewaya da Masar suka zo nan."
  • Wata hanyar fassara "dukkan duniya suka tafi garuruwansu na asali domin ayi masu rigista a ƙidayar Romawa" zai zama "mutane da yawa da suke zaune a lardunan da daular Romawa ke mulki suka je..."
  • Ya danganta da nassin, kalmar "na duniya" za a iya fassarawa a matsayin, "mugunta" ko "cike da zunubu" ko "sonkai" ko "rashin ibada" ko "lalacewa" ko "dulmiya cikin lalatattun ɗabi'un mutanen duniya."
  • Faɗar "faɗin waɗannan abubuwa cikin duniya" za a iya fassarawa a matsayin "faɗin waɗannan abubuwa ga mutanen dake cikin duniya."
  • A wasu nassosin, "a cikin duniya" za a iya fassarawa a matsayin "zama a tsakanin mutanen duniya" ko "zama a tsakanin mutane marasa ibada."

(Hakanan duba: gurbacewa, sama, Roma, ibada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:15
  • 1 Yahaya 04:05
  • 1 Yahaya 05:05
  • Yahaya 01:29
  • Matiyu 13:36-39

dutse, duwatsu, jifa

Ma'ana

Dutse wani karamin abu ne "a Jifi wani" na nufi a jefa wa wani duwatsu da manyan duwatsu ga wani mutum da niyyar kashe shi. "jifa" yanayi ne na jifan wani.

  • A zamanin dã, jifa abu ne mai sauƙi a matsayin hanyar hukunta wanda ya yi laifi.
  • Allah ya umarci shugabannin Isra'ilawa su jefe mutanen da suka yi zunubi, kamar na zina.
  • A Sabon Alƙawari, Yesu ya gafarci matar da aka kama tana zina ya kuma hana mutane su jefe ta.
  • Istifanus wanda shi ne mutum na farko a cikin Littafi Mai Tsarki da aka fara kashewa saboda shaidar Yesu, an jefe shi ne har ya mutu.
  • A garin Listra, an jefi Manzo Bulus, amma bai mutu ta raunukansa ba.

(Hakanan duba: zina, aikata, laifi, mutuwa, Listra, shaida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:57-58
  • Ayyukan Manzanni 07:59-60
  • Ayyukan Manzanni 14:05
  • Ayyukan Manzanni 14: 19-20
  • Yahaya 08:4-6
  • Luka 13:34
  • Luka 20:06
  • Matiyu 23:37-39

dutsen kusurwa

Ma'ana

Wannan magana "dutsen kusurwa" wani babban dutse ne da aka sassaƙa musamman kuma aka aje shi a kusurwar harsashin gini.

  • Dukkan sauran duwatsun gini ana auna su ko a jiye su bisa ga duten kusurwa.
  • Wannan yana da muhimmanci domin ƙarfi da kuma tsayawar dukkan ginin.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Taron masu bada gaskiya an kwatanta su da gini wanda Yesu shi ne "dutsen kusurwa."
  • Haka kuma kamar yadda dutsen kusurwa yana riƙe da gini ya kuma tsara matsayin dukkan ginin, haka ma Yesu Kristi shi ne dutsen kusurwa wanda bisansa ne Taron dukkan masu gaskatawa suke kafe tare kuma suke samun tallafi.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "dutsen kusurwa" za a iya fassara shi haka, "mafificin dutsen gini" ko "dutsen harsashi."
  • A yi la'akari ko yaren da suke juyi suna da irin wannan kalma wadda take da harsashe mai rike dukkan gini.
  • Wata hanya ta fassara wannan kalmar shi ne, "dutsen harsashi da ake amfani da shi a kusurwar gini."
  • Yana da muhimmanci a sani wannan babban dutse ne, ana amfani da shi domin taurinsa da kuma lafiyarsa saboda gini. Idan ba a yin amfani da duwatsu wajen gine gine wataƙila akwai wata kalma da za a yi amfani da ita a fid da ma'anar "babban dutse."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:11
  • Afisawa 02:20
  • Matiyu 21:42
  • Zabura 118:22

ɗa, 'ya'ya maza

Ma'ana

'Ya'yan mutum maza da mata akan kira su "ɗa" a dukkan iyalansa. Ana kuma kransa ɗan wancan mutumin da ɗan waccan matar. Ɗan da aka "ɗauko" namiji wanda aka maida shi ɗaya daga cikin 'ya'ya ya zama ɗa.

  • "Ɗa" an yi amfani da kalmar a Littafi Mai Tsarki don a nuna ɗa namiji, kamar jika ko jikoro.
  • Kalmar "ɗa" akan yi amfani da ita don nuna yaro wanda bai kai tsarar mai maganar ba.
  • Waɗansu lokuta "'ya'ya Allah" da akayi amfani da shi a Sabon Alƙawari ana magana ne da masu gasgatawa da Almasihu.
  • Allah ya kira Isra'ila "ɗan farinsa." Wannan na nufin Allah ya zaɓi mutanensa Isra'ila su zama mutanensa na masamman. Ta gare su ne sakon fansa da ceto na Yahweh ya zo, da sakamakon haka da yawa suka zama 'ya'yansa na ruhaniya.
  • Faɗar " ɗan" na da ma'anoni da yawa, " mutumin da yake da ɗabi'a irin ta." Misalin wannan ya haɗa da "'ya'yan haske" "'ya'yan rashin biyyaya" " ɗan salama", da kuma "'ya'yan tsawa."
  • Kalmar "ɗan' akan yi amfani da kuma a faɗi mahaifin wani. wannan kalmar ana amfani da ita wajen faɗin asali da sauran wurare.
  • Amfani da "ɗan" domin bada sunan mahaifi yana matuƙar taimakawa a banbance mutanen dake da suna iri ɗaya. A misali, "Azariya ɗan Zadok" da "Azariya ɗan Natan" a cikin 1 Sarakuna 4, da "Azariya ɗan Amaziya" a cikin 2 Sarakuna 15 mutum uku ne kowanne daban.

Shawarwarin fassara:

  • A yawancin wuraren da a kayi amfan ida wannan kalma, mafi kyan fassara itace "ɗa" a sassauƙan harshe da ake nufin ɗa.
  • Yayin fassara kalmar "Ɗan Allah", yaren wannan aikin ya ce kalmar "ɗa" ita za a mora.
  • Idan akayi amfani da ita da nufin 'ya'ya ba ɗa ba, kalmar "'ya'ya" kan iya amfani, a wurin misali, Yesu "tsatson Dauda" ko a asali inda a wani lokaci "ɗa" ake nufin ɗa namiji wanda ba cikakken ɗa ba.
  • Waɗansu lokutan "'ya'ya" akan fassara shi da "yara," idan ana magana kan maza da mata baki ɗaya. Misali, "'ya'yan Allah" akan fassara shi da "yaran Allah" tunda wannan maganar ta kunshi dukkan maza da mata.
  • Yawan aukuwar wannan maganar "ɗan" akan iya fassara ta da "wani da yake da irin ɗabi'ar" ko " wani da yake kama da " ko " wani da yake da " ko kowani da yake yi kamar."

(Hakanan duba: Azariya, zuriya, kakanni, ɗan fãri, Ɗan Allah, 'ya'yan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 18:15
  • 1 Sarakuna 13:02
  • 1 Tasalonikawa 05:05
  • Galatiyawa 04:07
  • Hosiya 11:01
  • Ishaya 09:06
  • Matiyu 03:17
  • Matiyu 05:09
  • Matiyu 08: 12
  • Nehemiya 10:28

Ɗan Allah, Ɗa

Ma'ana

Kalmar "Ɗan Allah" na magana akan Yesu, Kalmar Allah, wanda ya zo duniya a matsayin, mutum. An kuma sha faɗinsa da "Ɗa."

  • Ɗan Allah na da siffa ɗaya da Allah Uba, kuma shi Allah ne cikkake.
  • Allah Uba, Allah Ɗa, da Allah Ruhu Mai Tsarki dukkan su ɗaya ne.
  • Ba kamar 'ya'yan mutane ba, Ɗan Allah a kodayaushe yana nan.
  • Tun daga farko, Ɗan Allah ya kasnce cikin hallitar duniya, tare da Uba da Ruhu Mai Tsarki.

Domin Yesu Ɗan Allah ne, ya ƙaunaci da kuma biyayya da Ubansa, kuma Ubansa yana ƙaunarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Don kalmar "Ɗan Allah", ita ce mafi dacewa da fassarar "Ɗa" dai-dai da kalmar da yare ke amfani da ita wajen yin nuni da ɗan mutum.
  • A tabbatar kalmar da aka mora warin fassara "‌ɗa" ta zo dai-dai da wadda aka mora wurin fassara "Uba" domin waɗannan kalmomin sune kalmomi na gaske da za su iya bada gaskiyar dangantakar dake tsakanin Uba da ɗa a wannan aikin.
  • Ta amfani da babban baƙi a "Ɗa" na iya taimakawa a gane cewa ana magana ne akan Allah.
  • Kalmar "Ɗa" ita ce a takaicen "Ɗan Allah," masamman inya fita a layi guda da "Uba."

(Hakanan duba: Almasihu, kaka, Allah, Allah Uba, Ruhu Mai Tsarki, Yesu, ɗa, 'ya'yan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:10
  • Ayyukan Manzanni 09:20
  • Kolosiyawa 01:17
  • Galatiyawa 02:20
  • Ibraniyawa 04:14
  • Yahaya 03:18
  • Luka 10:22
  • Matiyu 11:27
  • Wahayin Yahaya 02:18
  • Romawa 08:29

Ɗan Mutum, ɗan mutum

Ma'ana

Laƙabin "Ɗan Mutum" an sashi ga Yesu da nufin shi kansa. Yakan yi amfani da wannan a madadin ya ce "NI" ko "Ni."

  • A Littafi Mai Tsarki, "ɗan mutum" na nuna ana magana ne da mutum. yana kuma nufin "ɗan adam."
  • Baki ɗayan Tsohon alƙawari Littafin Ezekiyel, Yahweh ya yi ta kiran Ezekiyel da "ɗan mutum". A misali yakan ce, ya kai "ɗan mutum dole kayi anabci."
  • Annabi Daniyel yaga wahayi "ɗan mutum" yana zuwa a gajimare, wanda yake nuna zuwan mai ceto.
  • Yesu ma ya ce Ɗan Mutum zai zo wata rana a gajimare.
  • Wannan ya bayyana zuwan Ɗan Mutum a gajimare ya nuna cewa Yesu Mai Ceto Yahweh ne.

Shawarwarin fassara:

  • Da Yesu ya yi amfani da kalmar :"Ɗan Mutum" za a fassara ta da "wanda ya zama ɗan adam" ko "Mutum daga sama."
  • Waɗansu masu fassarar sukan haɗa da "Ni" ko "NI" da wannan laƙabin (kamar a "NI, Ɗan Mutum") don a bayyana cewa Yesu na magana da kansa ne.
  • Bincika a tabbatar da cewa fassarar wannan kalmar ba ta bada ma'ana marar kyau ba (kamar a nufi wani ɗa marar cancanta ko faɗar magana marar kyau a ce Yesu ɗan adam ne kawai ).
  • Idan akayi amfani da ita ana nufin mutum, "ɗan mutum" za a iya fassara shi da "kai, ɗan Adam" ko "kai, ɗan Adam" ko "mutum."

(Hakanan duba: samaniya, ɗa, Ɗan Allah, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan manzanni 07:56
  • Daniyel 07:14
  • Ezekiyel 43:6-8
  • Yahaya 03:12-13
  • Luka 06:05
  • Markus 02:10
  • Matiyu 13:37
  • Zabura 080: 17-18
  • Wahayin Yahaya 14:14

ɗan'uwa, 'yan'uwa maza

Ma'ana

Wannan kalma "ɗan'uwa" yawancin lokaci ana nufin namijin mutum wanda ya haɗa mahaifi ko mahaifiya ɗaya da wani mutum.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, wannan kalma "ɗan'uwa" ana amfani da ita wajen ambaton dangi, kamar kabila, iyali, ko jinsin mutane.
  • A cikin Sabon Alƙawari, manzanni yawancin lokaci sukan yi amfani da kalmar nan "ɗan'uwa" idan suna magana akan 'yan'uwansu Kirista, ko maza ko mata, tunda duk mai bada gaskiya cikin Almasihu ɗan ƙungiya ne na iyalin ruhaniya, Allah kuma shi ne Uban mu wanda ke cikin sama.
  • Ba safai ne a cikin Sabon Alƙawari, manzanni suka yi amfani da kalmar nan "'yar'uwa" ba sa'ad da suke magana masamman akan Kirista mata, ko su nanata cewa dukka maza da mata ake nufi. Ga misali, Yakubu ya nanata cewa yana magana akan dukkan masu bada gaskiya sa'ad da ya ambaci "ɗan'uwa ko 'yar'uwa wadda take buƙatar abinci ko sutura."

Shawarwarin Fassara:

  • Zai fi kyau a fassara wannan kalmar yadda da take a harshen masu karɓar juyi wato a yi amfani da ɗan'uwa na jiki, sai ko in zai bada ma'ana marar daɗi.
  • A cikin Tsohon Alƙawari musamman, lokacin da ake amfani da "ɗan'uwa" domin yin magana akan wani daga cikin iyali, dangi, yare, yakamata a yi amfani da waɗannan kalmomi cikin fassara, "'yan'uwa" ko "ɗaya daga iyali" ko "ɗan'uwa Ba'isra'ile."
  • Idan ana magana ne akan ɗan'uwa mai bada gaskiya cikin Almasihu, a iya fassara wannan magana zuwa, "ɗan'uwa Kirista" ko "ɗan'uwa cikin ruhaniya."
  • Idan ana magana ne akan dukka biyu maza da mata kuma kalmar ɗan'uwa zai bada ma'anar da bai dace ba, to sai a samo wata kalmar da ta nuna 'yan u'wancin jiki wanda zai haɗa maza da mata.
  • Wasu hanyoyi kuma na fassara wannan kalma domin haɗa maza da mata masu gaskatawa shi ne a ce haka, "'yan'uwa masu gaskatawa" ko "Kiristoci 'yan'uwa maza da 'yan'uwa mata."
  • A tabbata an duba yadda yake a cikin nassi domin aga ko maza kaɗai ake magana akai, ko kuma dukka biyu maza da mata aka haɗa.

(Hakanan duba: manzo, Allah Uba, 'yar'uwa, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:26
  • Farawa 29:10
  • Lebitikus 19:17
  • Nehemiya 03:01
  • Filibiyawa 04:21
  • Wahayin Yahaya 01:09

ɗanrago, ɗanragon Allah

Ma'ana

Kalmar "ɗanrago" na nufin ƙaramin tunkiya ko rago. Tumaki dai dabbobi ne masu ƙafafu huɗu da gashin jiki mai laushi, ana amfani dasu domin hadayu ga Allah. Ana kiran Yesu "Ɗanragon Allah" saboda ya zama hadaya domin biyan zunuban mutane.

  • Waɗannan dabbobi basu da wuyar a kawar da su daga hanya kuma suna buƙatar kariya. Allah na kwatanta 'yan adam a matsayin tumaki.
  • Allah ya umarci mutanensa a zahiri da su miƙa masa hadayar tumaki da 'yanraguna marasa aibi.
  • An kiran Yesu "Ɗanrago na Allah" wanda aka miƙa hadaya domin biyan zunuban mutane. Cikakke ne shi, hadaya marar aibi saboda gabaɗaya baya da zunubi.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan ansan tumaki a cikin harshen wani lardi, sai ayi amfani da sunan ƙananunsu a fassara kalmar "ɗanrago" da "Ɗanrago na Allah."
  • "‌Ɗanrago na Allah" za a iya fassarawa a matsayin "‌Ɗanragon (hadaya) na Allah," ko "‌Ɗanragon da aka yiwa Allah hadaya" ko "‌Ɗanragon (hadaya) daga Allah."
  • Idan ba a san tumaki ba, ana iya fassara kalmar a matsayin "ƙaramin tunkiya" tare da rubuta taƙaitaccen bayani game da kamannin tumaki. Bayanin kuma na iya kwatanta tumaki da 'yanraguna da dabbar dake a wannan wuri dake zaune cikin garke, wadda take da tsoro kuma bata iya kãre kanta, wadda kuma ke yawan sakin hanya ta kauce.
  • Sai kuma a duba yadda aka fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai tsarki a cikin wani harshe na kurkusa ko babban harshen ƙasar.

(Hakanan duba: tumaki, makiyaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 12:03
  • Ezra 08:35-36
  • Ishaya 66:3
  • Irmiya 11:19
  • Yahaya 01:29
  • Yahaya 01:36
  • Lebitikus 14:21-23
  • Lebitikus 17:1-4
  • Luka 10:03
  • Wahayin Yahaya 15:3-4

ɗaukaka, ɗaukakakke, yin ɗaukaka, aikin ɗaukaka

Ma'ana

Kalmar nan "ɗaukaka babban yabo ne kogirmamawa ga wani. Za ta iya zama ɗora wani ne akan babban muƙami.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki kalmae nan "ɗaukaka" an fi moron ta ne a ɗaukaka Allah.
  • Sa'ad da mutum ya ɗaukaka kansa, wannan na nufin yana tunanin kansa ta hanyar fahariya, da rashintawali'u.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin da za'a fassara "ɗaukaka" sun haɗa da "babban yabo" ko "yabo mafi girma" ko "girmamawa sosai" ko "kwakwazantawa" ko faɗinmanyan abubuwa game da mutum."
  • A waɗansu wuraren za'a iya fassara ta ta amfani da kalmomin kirari, wato a yaba wa "mutuma kan babban matsayi"ko yin maganar ƙasaita game da mutum."
  • "Kada ka ɗaukaka kanka" za'a iya fassara shi da "kada ka ɗauki kanka fiye yadda ya kamata" ko "kada ka yi fahariya da kanka."
  • "Waɗanda suka ɗaukaka kansu" za'a iya fassara shi da "waɗanda ke tunanin kansu fiye da yadda ya kamata" ko "masu taƙama da kansu."

(Hakanan duba: yabo, sujada, ɗaukaka, fahariya, girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 05:5-7
  • 2 Sama'ila 22:47
  • Ayyukan Manzanni 05:31
  • Filibiyawa 02:9-11
  • Zabura 018:46

ɗaukaka, maɗaukaki, a ɗaukaka, ɗaukakakke, ɗaukakawa

Ma'ana

A batu na bai ɗaya kalmar nan "ɗaukaka" tana nufin girmamawa, darajantawa, da matuƙar ban girma. Duk wani abu da ke da ɗaukaka akan ce da shi "maɗaukaki."

  • A waɗansu lokutan "ɗaukaka" na nufin abin da ke da daraja sosai da kuma muhimmanci. A ɗaya hanun kuma yana nuna daraja ne, mai haske, ko hukunci.
  • Misali batu nan "ɗaukar makiyaya" wanan na nufin wuri mai dausayi inda dabbobinsu ke samu ciyawar ci.
  • Ana amfani da ɗaukaka a hanya ta musammam a ambaci Allah, wanda ya fi kowa da komai ɗaukaka a doron duniya. Kowane abu na baiyana ɗaukakarsa a cikin halaiyarsa da darajarsa.
  • Kalmar nan a "ɗaukaka a kai" tana nufin a yi fahariya da wani abu.

Kalmar nan "a ɗaukaka" tana nufin a nuna ko a faɗi yadda girma da muhimmanci na wani abu ko wani mutum. tana nufin a a "bada ɗaukaka."

  • Mutane kan iya ɗaukaka Allah ta wurin faɗar abubuwan al'ajabi da ya yi.
  • Haka nan za su iya ɗaukaka Allah ta wurin yin rayuwar da ke girmama shi da kuma nuna yadda yake da ɗaukaka.
  • Idan Littafi Mai Tsarki ya ce Allah na ɗaukaka kansa, yana nufin ya baiyana wa mutane girmansa na al'ajabi, mafi yawa ta wurin mu'ujjuza.
  • Allah Uba zai ɗaukaka Allah Ɗa ta wurin baiyana wa mutane cikarsa da darajarsa da girmansa.
  • Duk wanda ya gaskata da Kristi za'a ɗaukaka shi tare da shi. A lokacin dasuka tashia rai za,a canja su su nuna ɗaukakarsa da kuma nunaalherinsa ga dukkan halitta.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, a kwai mabambanta hanyoyi na fassara "ɗaukaka" da suka haɗa da "daraja" ko "mafi haske" ko 'mafi iko" ko "mafi kyau da girma" ko "mafi tsananin daraja."
  • Kalmar nan "maɗaukaki" za'a iya fassara ta da "cikarkiyar ɗaukaka" ko "mai matuƙar martaba" ko "mai tsananin haske" ko "mai matuƙar ban sha'awa da girma."
  • Kalmar nan "bada ɗaukaka ga Allah" za'a iya fassara ta da "girmama girman Allah" ko "yabon Allah sabo da martabarsa" ko "faɗa wa waɗansu yadda girman Allah yake."
  • Kalmar nan "yin ɗaukaka da" za'a iya fassara ta da "yabo" ko "yin fahariyaa cikin" ko "yin taƙama da" ko jin daɗi da."
  • "A ɗaukaka" zai iya zama bada "ɗaukaka ga" ko "a sa a baiyana girma."
  • Kalmar nan "a ɗaukaka Allah" za'a yi fassara ta da "yin magana game da girman Allah" ko "nuna yadda girman Allah yake" ko "girmama Allah ta wurin yi masa (biyayya)."
  • Kalmar nan "ya ɗaukaka" za'a iya fassara ta da nuna cewa "yana da girma sosai" ko a "yaba" ko "a girmama."

(Hakanan duba: ɗauka, biyayya, yabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 24:17
  • Littafin Lissafi 14:9-10
  • Ishaya 35:2
  • Luka 18:43
  • Luka 2:9
  • Yahaya 12:28
  • Ayyukan Manzanni 3:13-14
  • Ayyukan Manzanni 7:1-3
  • Romawa 8:17
  • 1 Korintiyawa 6: 19-20
  • Filibiyawa 2:14-16
  • Filibiyawa 4:19
  • Kolosiyawa 3:1-4
  • 1 Tassolonikawa 2:5
  • Yakubu 2:1-4
  • 1 Bitrus 4:15-16
  • Wahayin Yahaya 15:4

ɗaure, ɗauri, ɗaurarre

Ma'ana

Wannan kalma "ɗaure" ma'anarta shi ne kamar a sa igiya a zagaya abu a ɗaure kada ya kubce. Wani abin dake ɗaure ko aka haɗa su tare ana kiransa "karkiya."‌Ɗaurarre shi ne abin da aka rigaya aka ɗaure.

  • Idan ana "ɗaure" ma'ana shi ne a sa wani abu kamar igiya a zagaye shi a jikin wani abu.
  • A misalce mutum zai iya kasancewa "ɗaurarre" ga alƙawari, wato ana "buƙata ya cika" abin da ya alƙawarta zai yi.
  • Wannan kalma "ɗauri" ana nufin duk abin dake ɗaurewa, tsarewa, ko sa wani a kurkuku. Ana kuma nufin sa wani a sarƙa sosai, igiyar sarƙa ko igiyar kaba da zai hana mutum motsi.
  • A lokacin Littafi Mai Tsarki, maɗaurai kamar igiya ko sarka ana amfani da su a manne 'yan sarƙa da bango ko daɓen dutsen kurkuku.
  • Kalman nan "ɗaure" ana kuma amfani da ita sa'ad da aka sa tsumma kewaye da ƙurji domin a taimake shi ya warke.
  • Idan mutum ya mutu za a "ɗaure" shi da mayafi a shirya shi domin biznewa.
  • Kalmar nan "ɗaure" ana amfani da ita a yi kwatanci cikin magana akan wani abu, kamar zunubi, dake juya mutum yadda yaga dama ko ya bautar da mutum.
  • "‌Ɗauri" zai iya zama abuta na kurkusa tsakanin mutane har suke tallafar juna cikin ruhaniya da kuma jiki. Haka wannan yake game da ɗaurin aure.
  • Misali, miji da mata suna "ɗaure" ko kuma haɗe da juna. ‌Ɗauri ne da Allah baya so a kwance.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "ɗaure" za a iya fassara ta haka "ɗauri" ko "a ɗaɗɗaure" ko "ƙunshe."
  • A misalce, za a iya fassarawa a matsayin "tsarewa" ko "hanawa" ko a "ajiye daga (wani abu)."
  • Yin amfani na musamman da "ɗaure" a Matiyu 16 da 18 na ma'anar "hanawa" ko "bari."
  • Kalmar "ɗaure-ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "sarƙoƙi" ko "igiyoyi" ko "ƙangaye."
  • A misali kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ƙullewa" ko "mahaɗi" ko "zumunci na kurkusa."
  • Faɗar "ɗaurin salama" na ma'anar "zaman lafiya, wanda ke kawo mutane cikin zumuncin kurkusa da juna" ko "ɗaurewa tare da salama ke kawowa."
  • A "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "alƙawarin cika rantsuwa" ko "sadaukar da kai a cika wa'adi."
  • Ya danganta ga nassin, kalmar "ɗaure" za a iya fassarawa a matsayin "ɗauri" ko "ɗaurewa" ko "sarƙa" ko "an ƙayyada (a cika)" ko "a buƙaci ayi."

(Hakanan duba: cika, salama, kurkuku, bawa, wa'adi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Lebitikus 08:07

ɗiyar Sihiyona

Ma'ana

"Ɗiyar sihiyona wani salon magane da ke nufin mutanen Isra'ila. An fi amfani da wannan salon maganar a cikin anabce-anabce.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, ana fin yawn yin amfani da sunan "Sihiyona" a matsayin sunan birnin Yerusalem.
  • Ana amfani da "Sihiyona" da Yerusalem" da nufin ambaton Isra'ila.
  • Kalmar nan "Ɗiya" ƙauli ne na ƙauna ko tarairaya. Salon magna ne da ke nuna haƙuri da kulawar da Allah ke da su ga mutanensa.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyar yin fassara wananya haɗa da "ɗiyata Isra'ila, daga Sihiyona," ko "mutane daga Sihiyona, waɗanda ke kamar ɗiya a gare ni" ko "Sihiyona, ƙaunatattun mutanena Isra'ila."
  • Yafi kyau a riƙa moron kalmar "Sihiyona da yake an more ta sosai a cikin Littafi Mai Tsarki. Za a iya ɗan yin rubutu a cikin fassara don a nuna yadda aka mori misalin wata siffa domin a baiyana wata ma'ana ko wani anabci.
  • Hakanan ya fi kyau ayi ta moron "Ɗiya" a fassarar waɗanan kalmomin muddun dai an fahimce su da kyau.

(Hakanan duba: Yerusalem, annabi, Sihiyona)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Irmiya 06: 02
  • Yahaya 12:15
  • Matiyu 21:05

fahariya, yin fahariya

Ma'ana

Ma'anar "fahariya" shi ne yin magana da girman kai akan wani abu ko wani mutum. Yawancin lokaci yin maganganu ne na taƙama da kai.

  • Mutumin da yake "fahariya" yakan yi magana game da shi kansa da girman kai.
  • Allah ya kwaɓi Isra'ilawa akan yin "fahariya" da allolinsu. Suka yi taurinkai da yin sujada ga alloli maimakon Allah na gaskiya.
  • Littafi Mai Tsarki ya yi magana akan mutane masu fahariya cikin abubuwa kamar su dukiya, ƙarfinsu, gonakinsu masu amfani, da kuma umarnansu. Wato ya nuna suna da girman kai game da waɗannan abubuwa basu amince da Allah ba wanda shi ne ya tanada waɗannan abubuwa.
  • Allah ya iza Isra'ilawa suyi "fahariya" ko suyi taƙama game da cewa sun san shi.
  • Manzo Bulus, ya yi magana game da fahariya cikin Ubangiji, wato yin murna tare da godiya ga Allah domin dukkan abin da ya yi masu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara "fahariya sune "ɗaukaka kai" ko "yin magana da girman kai" ko "yin girman kai."
  • Wannan magana "girman kai" za a iya ba shi ma'ana haka, "cike da maganganun girman kai" ko "mai girman kai" ko "yin magana da girman kai game da kai."
  • Idan ana maganan fahariya cikin wani abu ko game da sannin Allah, za a iya fassara wannan haka, "yin taƙama cikin" ko "ɗaukaka" ko "yin murna akan wani abu" ko "bada godiya ga Allah saboda."
  • Waɗansu yarurruka suna da kalmomi biyu domin "girman kai": guda ɗaya marar kyau, da ma'anar izgilanci, na biyun mai kyau shi ne, da ma'anar jin daɗi da aikin daka yi, ga iyali, ko ƙasa.

(Hakanan duba: fahariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 20:11
  • 2 Timoti 03:1-4
  • Yakubu 03:14
  • Yakubu 04:15-17
  • Zabura 044:08

falmara

Ma'ana

Falmara ko riga mai baki biyu, wata irin riga ce firistocin Isra'ila ke sawa. Tana da haɓa biyu gaba da baya, da aka haɗa a kafaɗu sai haɗa a ɗaure tare da maɗaurin sutura.

  • Irin wanan falmarar akan yi ta da zane iri ɗaya kuma firistoci kan sa ta.
  • Falmarar da babban firist ke sawa an yi mata adon zinariya na musamman tana da kalar shunaiya, tsanwa, dakuma ja da ƙyal-ƙyal.
  • Wanan makarin ƙirji na babban frist an liƙe shi da falmarar, a bayansu kuma an sanya duwatsu masu sheƙi da ake amfani da su domin a tambayi Allah game da nufinsa akan waɗansu al'amura.
  • Alƙali Gidiyon cikinwawanci ya yi falmarar da ta zinariya sai ta zama abin da Isra'ilawa suka bautawa a matsayin gunki.

(Hakanan duba: firist)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 02:18-19
  • Fitowa 28:4-5
  • Hosiya 03:4
  • Littafin Alƙalai 08:27
  • Lebitikus 08:7

fansa, fansassu, mai fansa

Ma'ana

Kalmar "fansa" na manufar a saya domin maidowa da wani ko wani abu daga inda aka kai shi a dã ko aka 'yantar da shi daga bauta. "Mai fansa" wani ne wanda ke fansar wani abu ko wani.

  • Allah ya bada dokokinsa ga Isra'ilawa game da yadda zasu fanshi mutane da abubuwa.
  • Ga misali, wani na iya fansar wani daga bauta ta hanyar biyan farashi domin a fanshi ɗan kurkukun. Haka kuma kalmar "biyan diyya" ana amfani da ita ta wannan hanyar.
  • Idan an sayar da gonar wani, ɗan'uwa na kusa na iya "fansowa" ko "ya sake sayen" wannan gonar domin ta ci gaba da zama na wannan iyalin.
  • Wannan na bayyana yadda Allah ke fansar mutane daga bauta. Da ya mutu a bisa gicciye, Yesu ya biya farashi cikakke domin zunuban mutane ya kuma yi fansar dukkan waɗanda suka yarda da shi domin ceto. Mutanen da Allah ya fanshe su sun sami 'yanci daga zunubi da kuma hukuncinsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, kalmar "fansa" za a iya fassarawa haka "a sake sawowa" ko "a biya domin a 'yantar (da wani)" ko "biyan diyya.
  • Kalmar "fansowa" za a iya fassarawa haka "biyan diyya" ko "biyan 'yanci" ko "sake sawowa."
  • Maganganun "biyan diyya" da "fansa" a taƙaice suna da ma'ana iri ɗaya, domin haka wasu yarurrukan suna da kalma ɗaya ne dake fassara dukkan waɗannan kalmomi. Kalmar "biyan diyya," duk da haka, na iya zama biyan farashin da ya cancanta.

(Hakanan duba: 'yanci, biyan diyya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 01:13-14
  • Afisawa 01:7-8
  • Afisawa 05:16
  • Galatiyawa 03:13-14
  • Galatiyawa 04:05
  • Luka 02:38
  • Rut 02:20

Fentikos, Idin Makonni

Ma'ana

"Idin Makonni" bukin Yahudawa ne da ake yi bayan kwana hamsin da wucewar Idin ‌Ƙetarewa. Daga baya ne aka kira shi "Fentikos."

  • Bukin Makonni, yana ɗaukar makonni bakwai (kwana hamsin) bayan Bukin Nunar Fari. A lokatan Sabon Alƙawari, wannan buki ana kiransa "Fentikos" wanda yake lamba "hamsin" a cikin ma'anar sunansa."
  • Akan yi Bukin Makonni domin yin murnar girbin hatsi na fari. Lokaci ne kuma na tuna wa da sa'ad da Allah ya bada Shari'a ga Isr'ilawa akan allon dutse ta hannun Musa.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Ranar Fentikos yana da mahimmanci musamman domin lokacin ne masu bada gaskiya ga Yesu suka karɓi Ruhu Mai Tsarki a wani sabon yanayi.

(Hakanan duba: buki, nunar fãri, girbi, Ruhu Mai Tsarki, tashi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 08:12-13
  • Ayyukan Manzanni 02:01
  • Ayyukan Manzanni 20:15-16
  • Maimaitawar Shari'a 16:16 -17
  • Littafin ‌Lissafi 28:26

firist, firistoci, firistanci

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, firist mutum ne wanda aka zaɓa domin ya miƙa hadayu ga Allah a saboda mutanen Allah. ‌"Matsayin firistoci" sunan aiki ne ko zama firist.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya zaɓi Haruna da zuriyarsa su zama firistocinsa domin mutanen Isra'ila.
  • "Masayin firist" hakki ne kuma nawaya ce da aka miƙa daga mahaifi zuwa ga ɗa cikin iyalin Lebiyawa.
  • Firistocin Isra'ila suna da nawayar miƙa hadayun mutane ga Allah, kuma da waɗansu ayyuka a cikin haikali.
  • Firistoci kuma suna miƙa addu'o'i ga Allah akai akai domin mutane suna kuma yin wasu ayyukan addini da suka wajaba a cikin haikali.
  • Firistoci sukan furta albarku akan mutane su kuma koya masu dokokin Allah.
  • A lokacin Yesu, akwai matsayin firistoci hawa hawa, har ma da manyan firistoci da kuma babban firist.
  • Yesu shi ne namu "babban firist mai girma" wanda yake roƙo domin mu a gaban Allah. Ya miƙa kansa hadaya mafificiya domin zunubi. Wannan ya nuna cewa hadayu da firistoci 'yan adam suke miƙawa ba a buƙatar su kuma.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kowanne mai bada gaskiya ga Yesu ana kiransa "firist" zai iya zuwa kai tsaye gun Allah cikin addu'a ya yi roƙo domin kansa da kuma wasu mutane.
  • A zamanin dã, akwai firistoci matsafa dake miƙa baye-baye ga gumaku kamar su Ba'al.

Shawarwarin Fassara:

  • Zai danganta ga nassi, wannan magana "firist" za a iya fassarawa haka, "mutumin dake miƙa hadaya" ko "matsakanci na Allah" ko "matsakanci mai hadaya" ko " mutumin da Allah ya naɗa ya wakilce shi."
  • Fassara kalmar nan "firist" zai zama daban da "matsakanci."
  • Wasu juyin watakila sun fi son koyaushe su ce "firistocin Isra'ila" ko "firistocin Yahudawa" ko "firist ɗin Yahweh" ko "firist ɗin Ba'al" domin a fayyace da kyau ba wai ana nufin i firistoci irin na wannan zamani a yau ba.
  • Maganar da aka yi amfani da ita a fassara "firist" yakamata ta banbanta da wannan magana "shugaba firist" da "babban firist" da "Lebiyawa" da "annabi."

(Hakanan duba: Haruna, manyan firistoci, babban firist, matsakanci, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tarihi 06:41
  • Farawa 14:17-18
  • Farawa 47:22
  • Yahaya 01:19-21
  • Luka 10:31
  • Markus 01:44
  • Markus 02:25-26
  • Matiyu 08:4
  • Matiyu 12:04
  • Mika 03:9-11
  • Nehemiya 10:28-29
  • Nehemiya 10:34-36
  • Wahayin Yahaya 01:06

furta, furtawa

Ma'ana

Furtawa shi ne mutum ya yarda ko ya bayyana cewa wani abu gaskiya ne. "Furtawa" magana ce ko kuma amincewa ne cewa wani abu gaskiya ne.

  • Wannan kalma "furta" faɗin gaskiya ne gabagaɗi game da Allah. Zai kuma iya zama bayyana zunubin mu.
  • Littafi Mai Tsarki ya ce idan mutane suka furta zunubansu ga Allah, zai gafarta masu.
  • Manzo Yakubu ya rubuta a cikin wasiƙarsa cewa idan masu bada gaskiya suka furta zunbansu ga junansu, wannan yana kawo warkaswar ruhaniya.
  • Manzo Bulus ya rubuta wa Filibiyawa cewa wata rana kowa zai furta ko yayi shela cewa Yesu Ubangiji ne.
  • Bulus kuma ya ce idan mutane suka furta cewa Yesu Ubangiji ne kuma suka gaskata Allah ya tashe shi daga matattu, za su sami ceto.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga yadda ake so a yi amfani da shi cikin rubutu, ga wasu hanyoyin fassara "furtawa" za a iya cewa "yarda" ko "shaidawa" ko "shela" ko "amincewa" ko "tabbatarwa."
  • Ga wasu hanyoyi dabam dabam na juya wannan kalma "furtawa" zai iya zama, "furci" ko "shaidawa" ko "magana game da abin da muka gaskata" ko "bayyana zunubi."

(Hakanan duba: bangaskiya, shaida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:8-10
  • 2 Yahaya 01:7-8
  • Yakubu 05:5-6
  • Lebitikos 05:5-6
  • Matiyu 03:4-6
  • Nehemiya 01:6-7
  • Filibiyawa 02:9-11
  • Zabura 038:17-18

gãdo, abin gãdo, gãdajje, magaji

Ma'ana

Kalmar nan "gãda" na nufin karɓar wani abu mai daraja daga iyaye ko wani mutum sabo da wata dangantaka ta musamman da mutumin nan. "Abin gãdo" shi ne abin da aka gãda ko karɓa.

  • Gãdo na abubuwa shi ne abin da muka karɓa, kamar kuɗi, gona, da dai sauran abubuwa.
  • Gãdo na ruhaniya shi ne duk wani abu da Allah ya ba mutanen da suka yi imani cikin Kristi, waɗanda suka haɗa da albarku na wannan rai da kuma sauran albarku na wannan rai da kuma rai mai zuwa wato rai madawwmi tare da shi.
  • Hakanan Littafi Mai Tsarki ya kira mutanen Allah abin gadonsa, wannan na nufin cewa sun zama mallakarsa mai daraja.
  • Allah ya yiwa Ibrahim alƙawarin cewa zuriyarsa zasu gãji ƙasar Kan'ana da zata zama mallakarsu har abada.
  • Akwai salon magana da ake mora domin ambaton mutanen Allah, wato kamar "magãdan ƙasar" wannan na nuna cewa zasu wadata su zama da albarka ta ruhaniya da kuma ta kayan duniya.
  • A cikin Sabon Alƙawari, Allah ya yi alƙawari cewa waɗanda suka dogara ga Yesu "za su gãjiceto" shima ana kiransa zasu gãji mulkin Allah na har abada.
  • Akwai waɗansu salon magana da ake mora su bada ma'anar waɗannan kalmomin:
  • Littafi Mai Tsarki ya ce mutane masu hikima "za su gãji ɗaukaka" masu adalci kuma za "su gãji managartan abubuwa."
  • Domin "gãdar alƙawaran" wannan na nufin karɓar abubuwa managarta waɗanda Allah ya alƙawarta zai ba mutanensa.
  • Wannan kalma ga marasa azanci ko marasa biyayya za su "gãji wautarsu" wannan na nufin za su gãji ko kuma su karɓi sakamakon ayyukansu na zunubi, wanda ya haɗa da horo sabo da yin rayuwa mara kyau.

Shawarwarin Fassara:

  • Kamar dai yadda da yawa ke yin la'akari cewa ko dai akwai hakikannin wannan kalma a cikin harshen da ake fassara akan wanann kalma magaji, ko gãdo kan iya moron wannan kalmomi.
  • Ya danganta ga wurin, kuma waɗansu hanyoyi da ake fassara wannan kalma "gãdo" za'a iya fassara ta da "karɓa" ko "mallaka" ko "zuwa a mallaka."
  • Da ake yin maganar mutanen Allah akan mãgadansa za'a iya fassara ta da mutanensa masu daraja."
  • Kalmar "magaji" za'a iya fassara ta da dãma ce da ake "mallakar mallakar uba" ko "a sami damar samun gãdar abubuwa na ruhaniya ko albarku."
  • Kalmar nan "abin gãdo" za'a iya fassara ta da "albarku daga wurin Allah" ko kuma "gãdoon albarku."

(Hakanan duba: mãgaji, Kan'ana, Ƙasar Alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 06:9
  • 1 Bitrus 01:04
  • 2 Sama'ila 21:03
  • Ayyukan Manzanni 07:4-5
  • Maimaitawar Shari'a 20:16
  • Galatiyawa 05:21
  • Farawa 15:07
  • Ibraniyawa 09:15
  • Irmiya 02:07
  • Luka 15:11
  • Matiyu 19:29
  • Zabura 079:01

gafara, yin gafara, gafartacce, halin gafara, jinƙai, wanda aka nuna wa jinƙai

Ma'ana

Yin gafara shi ne kada a riƙe wani da zafi a zuciya duk da yake sun yi abu na cutarwa. "Yin gafara" shi ne gafartawa wani.

  • Gafartawa wani a mafi yawan lokuta shi ne rashin horon mutum a sakamakon kuskuren da ya aikata.
  • Kalmar nan akan yi amfani da ita cikin salon magana ta bada ma'anar "sokewa" kamar "soke bashi."
  • Lokacin da mutane suka furta zunubansu, Allah yakan gafarta musu bisa ga hadayar mutuwar Yesu a kan gicciye.
  • Yesu ya koya wa almajiransa su gafartawa sauran kamar yadda ya gafarta musu.

Kalmar "jinƙai" tana nufin a gafartawa ba tare da bada horo akan zunubin wani ba.

  • Wanan kalma tana da ma'ana ɗaya da "yin gafara" amma tana ɗauke da ra'ayi na ɗaukan ƙudiri na kai na ƙin horon wani sabo da laifinsa.
  • A sahi'ance, Alƙali kan iya yin gafara ga mutumin da aka samu da laifi.
  • Ko da yake munyi laifin zunubi, Yesu ya yi mana jinƙai don kada a hukunta mu da wutar jahannama, bisa mutuwarsa ta hadaya akan gicciye.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, za'a iya fassara "gafara" da "jinƙai" ko "sokewa" ko "saki" ko "rashin jin zafin" (wani)
  • Kalmar "gafartawa" za'a iya fassara ta da rashin aiyana hukunci akan (wani) akan "ba shi da laifin" wato "nuna halin jinƙai."
  • Idan harshen na da wata tsararriyar matsaya ta gafara, za'a iya amfani da kalmar a fassara "jinƙai."

(Hakanan duba: laifi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 50:17
  • Littafin Lissafi 14:17-19
  • Maimaitawar Shari'a 29:20-21
  • Yoshuwa 24:19-20
  • 2 Sarakauna 05:17-19
  • Zabura 025:11
  • Zabura 025:17-19
  • Ishaya 55:6-7
  • Ishaya 40:2
  • Luka 05:21
  • Ayyukan Manzanni 08:22
  • Afisawa 04:31-32
  • Kolosiyawa 03:12-14
  • 1 Yahaya 02:12

gargaɗi, yin gargaɗi

Ma'ana

Kalmar nan "gargaɗi" tana nufin a ƙarfafa da ƙarfi da kuma roƙon wani ya yi abib da ke daidai. irin wanan gargaɗin ne ake kira "yingargaɗi."

  • Dalilin yin gargaɗi shi ne a sa mutune su dena yin zunuba su kuma bi nufin Allah.
  • Sabon Alƙawari yana koyar da cewa mu gargaɗi juna cikin ƙauna, ba da kaushin murya ko da ƙuntatawa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, "gargaɗi" za'a fassara da "kira ne da babbar murya" ko ku "sa" ko a "shawarta."
  • Ku tabbatar cewa fassarar wanan kalma ba ta nuna cewa mai yin gargaɗin bai yi fushi ba. Kalmar za ta haɗa da ƙarfafawa da kuma gaske, amma ba tare da nuna wani fushi ba cikin magana.
  • A wurare da yawa kalmar nan "gargaɗi" za'a iya fassara ta ta hanyoyi da bam da ban fiye da "ƙarfafawa" wadda ke bada ƙwaein gwiwa, ko bada tabbas, ta'azantarwa ga wani.
  • Har kullum wanan kalmar za'a iya fassara ta mabambantan hanyoyi daga "kashedi" wanda ke nufin a tsautar ko ayi guara ga wani, sabo da halinsa da bai dace ba.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasolonikawa 02:3-4
  • 1 Tasolonikawa 02:12
  • 1 Timoti 05:2
  • Luka 03:18

gaskata, gaskatawa, mai gaskatawa, marar gaskatawa, marasa gaskatawa, rashin bangaskiya

Ma'ana

Wannan kalma "gaskata" da "gaskata da" suna 'yan'uwa da juna, amma akwai bambancin ma'ana kaɗan:

  1. gaskatawa
  • A gaskata da abu shi ne a karɓe shi kuma a dogara da shi a matsayin gaskiya.
  • A gaskata da wani shi ne a jaddada cewa abin da wannan taliki ya ce gaskiya ne.
  1. gaskatawa da
  • A "gaskata da" wani na ma'anar a "dogara da" wannan taliki. Yana ma'ana a dogara da cewa wannan taliki shi abin da ya ce shi ne, cewa a koyaushe yana faɗin gaskiya, kuma zai yi abin da ya yi alƙawarin zai yi.
  • Sa'ad da wani da gaske ya gaskata da wani abu, zai yi aiki ta hanyar da zata nuna lallai ya gaskata.
  • A faɗar "yi bangaskiya da" yawanci yana da ma'ana dai-dai da "gaskatawa da."
  • A "gaskata da Yesu" na ma'anar a gaskata da cewa shi ɗan Allah ne, cewa shi Allah ne da kansa wanda kuma ya zama mutum wanda kuma ya mutu a matsayin hadaya domin ya biya zunubanmu. Ana nufin a dogara da shi a matsayin Mai Ceto a kuma yi rayuwa dake darjanta shi.

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "mai gaskatawa" na nufin wani wanda ya gaskata da kuma ya dogara ga Yesu Almasihu a matsayin Mai Ceto.

  • Kalmar "mai gaskatawa" a kaitsaye na nufin "wani wanda ya gaskata."
  • Kalmar "Kirista" daga bisani ta zama ainihin laƙabi domin masu bada gaskiya saboda yana nuna cewa sun gaskata da Almasihu kuma suna biyayya da koyarwarsa.

Kalmar "rashin bangaskiya" na nufin a ƙi gaskatawa da wani abu ko wani taliki.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, "rashin bangaskiya" na nufin a ƙi gaskatawa da ko a ƙi dogara ga Yesu a Matsayin Mai Ceton wani.
  • Wanda bai gaskata da Yesu ba ana kiransa "marar gaskatawa."

Shawarwarin Fassara

  • Za a iya fassara "gaskata" haka, "sanin cewa wannan gaskiya ne" ko "sanin cewa wannan dai-dai ne."
  • Za iya fassara "gaskatawa da" haka "a dogara ɗungum" ko "a dogara kuma ayi biyayya" ko "a jingina ɗungum akan abu kuma a bi.'
  • Wasu fassararorin zasu fi so su ce "gaskatawa da Yesu" ko "gaskatawa da Almasihu."
  • Wannan kalma kuma ana iya fassarata da wata magana ko faɗar dake nufin "wanda ya dogara ga Yesu" ko "wanda ya san Yesu kuma yake rayuwa dominsa."
  • Wasu hanyoyin fassara "mai gaskatawa" zasu iya zama "mai bin Yesu" ko "wanda ya san kuma yake biyayya da Yesu."
  • Kalmar "mai gaskatawa" kalma ce domin kowanne mai gaskatawa da Almasihu, yayin da "almajiri" da "manzo" ake amfani da su musamman domin mutanen da suka san Yesu yayin da yake da rai. Zai fi kyau a fassara waɗannan kalmomi ta hanyoyi daban-daban, saboda a banbanta su.
  • Wasu hanyoyin fassara "rashin bangaskiya" zasu haɗa da "rashin gaskatawa" ko "ƙin gaskatawa."
  • Kalmar "marar gaskatawa" za a iya fassarawa a matsayin "wanda bai gaskaya da Yesu ba" ko "wani wanda bai dogara ga Yesu ba a matsayin Mai Ceto."

(Hakanan duba: gaskatawa, manzo, Kirista, almajiri, bangaskiya, dogara)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 15:06
  • Farawa 45:26
  • Ayuba 09:16-18
  • Habakuk 01:5-7
  • Markus 06:4-6
  • Markus 01:14-15
  • Luka 09:41
  • Yahaya 01:12
  • Ayyukan Manzanni 06:05
  • Ayyukan Manzanni 09:42
  • Ayyukan Manzanni 28:23-24
  • Romawa 03:03
  • 1 Korintiyawa 06:01
  • 1 Korintiyawa 09:05
  • 2 Korintiyawa 06:15
  • Ibraniyawa 03:12
  • 1 Yahaya 03:23

gaskiya, gaskiyar, gaskiyoyi

Ma'ana

Kalmar "gaskiyar" na ma'anar abu ɗaya ko fiye da haka da yake tabbatacce, al'amuran da suka ainihin faru, kuma maganganun da ainihin an faɗe su. Waɗannan abubuwa ana ce masu "gaskiya."

  • Abubuwan dake gaskiya zahiri ne, na asali, tabbatacce, dai-dai, bisa ga doka, tabbas.
  • Gaskiyar fahimta ce, da gaskatawa, da tabbaci, ko maganganun dake gaskiya.
  • A cewa anabci "ya zama gaskiya" ko "zai zama gaskiya" na ma'anar ainihin ya faru kamar yadda aka furta ko zai faru ta hanyar haka.
  • Gaskiyar ta haɗa da tafiyar da al'amari ta hanyar abin dogara da aminci.
  • Yesu ya bayyana gaskiyar Allah ta wurin maganganun da ya furta.
  • Maganar Allah gaskiyar ce. Tana zancen al'amuran da ainihi sun faru tana kuma koyar da abin da ke gaskiya game da Allah kuma game da abubuwan da ya halitta.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin da kuma abin da ake bayyanawa, kalmar "gaskiya" za a iya fassarawata haka "zahiri" ko "tabbatacce" ko "da kyau" ko "dai-dai" ko "babu shakka" ko "na asali."
  • Hanyoyin fassara kalmar "gaskiyar" zasu haɗa da "abin da ke gaskiya" ko "tabbas" ko "babu shakka" ko "ka'ida."
  • Faɗar "ya zama gaskiya" za a iya fassarawa haka "ainihin ya faru" ko "ya cika" ko "ya faru kamar yadda aka furta."
  • Faɗar "faɗi gaskiyar" ko "furta gaskiyar" za a iya fassarawa haka "faɗi abin da ke gaskiya" ko "faɗi ainihin abin da ya faru" ko "faɗi abubuwan abin dogara."
  • A "karɓi gaskiyar" za a iya fassarawa haka "a gaskata abin da ke gaskiya game da Allah."
  • A faɗar kamar haka "ayi sujada ga Allah cikin ruhu da cikin gaskiyar," faɗar "cikin gaskiyar" za a iya fassarawa ta "yin biyayya da aminci ga abin da Allah ya koyar da mu."

(Hakanan duba: gaskatawa, aminci, cikawa, biyayya, anabci, fahimta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:6-8
  • 1 Yahaya 01:5-7
  • 1 Yahaya 02:08
  • 3 Yahaya 01:08
  • Ayyukan Manzanni 26:24-26
  • Kolosiyawa 01:06
  • Farawa 47:29-31
  • Yakubu 01:18
  • Yakubu 03:14
  • Yakubu 05:19
  • Irmiya 04:02
  • Yahaya 01:9
  • Yahaya 01: 16-18
  • Yahaya 01:51
  • Yahaya 03:31-33
  • Yoshuwa 07:19-21
  • Littafin Makoki 05:19-22
  • Matiyu 08:10
  • Matiyu 12:17
  • Zabura 026:1-3
  • Wahayin Yahaya 01:19-20
  • Wahayin Yahaya 15:3-4

giciye

Ma'ana

A lokacin Littafi Mai Tsarki, giciye wani itace ne da ake soka shi ƙasa, sa'annan a ratsa wani gungume a kusan karshen samansa.

  • Lokacin mulkin Romawa, gwamnatin Roma takan kashe masu laifi tawurin tsire su akan giciye a barsu su mutu a nan.
  • An zargi Yesu akan laifin da bai yi ba Romawa kuwa suka kashe shi akan giciye.
  • A yi lura cewa wannan kalmar dabam take da "tsallakewa" wanda ma'anar ta ƙetarewa ne zuwa wancan hayin, misali, rafi ko tafki.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma za a iya fassarata tawurin amfani da wasu magana a harshen masu juyi da ya fassara yadda siffar giciye take.
  • Ayi kokarin bayyana yadda giciye yake wato abu ne da ake kashe mutane a kansa, yi amfani da furci haka, "gungumen kisa" ko "itacen mutuwa."
  • Yi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin wani Littafi Mai Tsarki na yaren kasar.

(Hakanan duba: gicciyewa, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 01:17
  • Kolosiyawa 02:15
  • Galatiyawa 06:12
  • Yahaya 19:18
  • Luka 09:23
  • Luka 23:26
  • Matiyu 10:38
  • Filibiyawa 02:08

giciye

Ma'ana

Wannan kalma "giciye" ma'anarta a kashe wani mutum tawurin ɗibiya shi akan giciye a bar shi nan domin ya sha wahala ya kuma mutu cikin azaba.

  • Wannan mai mutuwa akan ɗaure shi a jikin giciyen ko a kafe shi da ƙusa. Giciyeyyun muane sukan mutu saboda tsiyayewar jini ko maƙurewa don rashin lumfashi.
  • Mulkin Roma ta dã sukan yi amfani da wannan hanyar kisa akai akai su hukunta ko su kashe mutane waɗanda suka aikata mugayen laifofi ko waɗanda suka yi wa gwamnatinsu tawaye.
  • Shugabannin Yahudawa suka roƙi gwamnan Romawa ya dokaci sojojinsa su giciye Yesu. Sojojin suka rataye Yesu da ƙusoshi a kowanne tafin hannunsa da kafafunsa akan giciye. Ya sha azaba a nan har tsawon sa'a shida, sa'annan ya mutu.

Shawarwarin Fassara

Wannan kalma "giciye" za a iya fassara ta haka, "kashewa akan giciye" ko "kisa tawurin ratayewa da bugun ƙusoshi akan giciye."

(Hakanan duba: giciye, Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:23
  • Galatiyawa 02:20-21
  • Luka 23:20-22
  • Luka 23:34
  • Matiyu 20:17-19
  • Matiyu 27:23-24

gidan Allah, gidan Yahweh,

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "gidan Allah" da "gidan Yahweh" na nufin wuri inda ake yiwa Allah sujada.

  • Wannan na nufinmusamman haikali da bukka.
  • A waɗansu lokutan "gidan Allah" na nufin mutanen Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Lokacin da ake magana kan wurin sujada, wannan na nufin, a fassara shi akan "gida domin bautar Allah."
  • Idan yana magana ne akan haikali da bukka yin sujada, za'a iya fassara ta da "haikali" (bukkar yin sujada) inda ake bautawa Allah (ko inda Allah yake" ko "inda Allah ke saduwa da mutanensa.")
  • Kalmar "gida" zata iya zama da muhimmanci a more ta a cikin fassara domin a bayyana cewa allah na "zama" a can, wato ruhunsa yana a wannan wurin domin ya sadu da mutanensa domin su bauta masa.

(Hakanan duba: mutanen Allah, bukkar sujada, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 03:14-15
  • 2 Tarihi 23:8-9
  • Ezra 05:13
  • Farawa 28:17
  • Littafin Alƙalai 18:30-31
  • Markus 02:26
  • Matiyu 12:04

gidan wuta, tabki na wuta

Ma'ana

Gidan wuta shi ne wuri na ƙarshe wuri mai wahala mara iyaka inda Allah zai hori duk waɗanda sukaa yi masa tayarwa suka kuma ƙi shirinsa na ceton su ta wurin hadayar Yesu. haka kuma ana kirangidan wuta "tabki na wuta"

  • An baiyana gidan wuta a matsayin wuri maiwuta da matuƙar wahala.
  • Shaiɗan da miyagun ruhohi za'a tura su gidan wuta domin hukunci na har abada.
  • Mutanen da basu yi imani da hadayar Yesu sabo da zunubansu ba basu kuma dogara gare shi domin ya cece su ba za'a yi musu hukunci na har abada a gidan wuta.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗannan kalmomin mai yiwuwa a iya fassara su ta hanyoyi mabambanta tun da yake sun kasance a wurare da bam da ban.
  • Waɗansu harsuna basu amfani da "tabki" a cikin kalmar "tabkin wuta" sabo da tana magana ne akan ruwa.
  • Kalmar "gidan wuta" za'a iya fassara ta da wurin "shan azaba" kowuri na ƙarshena duhu da azaba.
  • Kalmar nan "tabki na wuta" za'a iya fassara ta da "teku na wuta" ko "gagarumar wuta (ta azaba)" ko "filin wuta."

(Hakanan duba: sama, mutuwa, hades, ƙibiritu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yakubu 03:6
  • Luka 12:5
  • Markus 09:42-44
  • Matiyu 05:21-22
  • Matiyu 05:29
  • Matiyu 10:28-31
  • Matiyu 23:33
  • Matiyu 25:41-43
  • Wahayin Yahaya 20:15

gurasa marar gami

Ma'ana

Kalmar "gurasa marar gami" na manufar gurasar da ba a sanya gami ciki ba ko wani abin sa gurasar ta yi kumburi. Irin wannan gurasa falle-falle ne domin babu gami da zai sa ta yi kumburi.

  • Sa'ad da Allah ya kuɓutar da Isra'ilawa daga bauta a Masar, ya gaya masu da su tsere Masar cikin sauri ba tare da gurasarsu ta tashi ba. Don haka suka ci abincin su da gurasa marar gami. Tun daga wannan lokaci ana amfani da gurasa marar gami kowacce shekara a Bikin ƙetarewarsu domin tunashshe su game da wannan lokaci.
  • Tunda gami wani lokacin ana amfani da shi a bayyana zunubi, "gurasa marar gami" na matsayin cire zunubi daga rayuwar mutum domin ya yi rayuwa ta hanyar dake kawo girmamawa ga Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara kalma sun haɗa da "gurasa wadda babu gami" ko "gurasa falle-falle wanda bata kumbura ba."
  • A tabbata cewa an fassara wannan kalma dai-dai yadda aka fassara kalmar "gami, abin sa tsami da kumbura."
  • A wasu nassosin, kalmar "gurasa marar gami" na nufin "Bukin gurasa marar gami" za a kuma iya fassarawa ta wannan hanya.

(Hakanan duba: gurasa, Masar, biki, Bukin Ƙetarewa, zunubi, gami)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:6-8
  • 2 Tarihi 30:13-15
  • Ayyukan Manzanni 12:03
  • Fitowa 23:14-15
  • Ezra 06:21-22
  • Farawa 19:1-3
  • Littafin Alƙalai 06:21
  • Lebitikus 08:1-3
  • Luka 22:01

gwaji ko jarabta, gwadawa ko jarabawa

Ma'ana

A yiwa wani gwaji shi ne a nemi a sa wannan taliki ya yi abin da ba dai-dai ba.

  • Gwadawa shi ne wani abu dake sa wani taliki ya yi marmarin yin abin da ba dai-dai ba.
  • Mutane na samun gwaji ta wurin ɗabi'arsu ta zunubi da kuma wasu mutane.
  • Shaiɗan shima yana jarabtar mutane suyi rashin biyayya da Allah su kuma yi zunubi gãba da Allah ta wurin yin abubuwan da ba dai-dai ba.
  • Shaiɗan ya gwada Yesu ya kuma yi ƙoƙarin sanya shi ya yi abin da ba dai-dai ba, amma Yesu ya yi tsayayya da dukkan jarabobin Shaiɗan kuma bai taɓa yin zunubi ba.
  • Wanda ke "gwada Allah" ba yana neman yasa shi ya yi abin da ba dai-dai ba ne, amma dai, yana ci gaba cikin taurin kan rashi biyayya da shi har ya kai ga inda dole ne Allah ya maida martani ta wurin horonsa. Wannan shima ana kira "jaraba Allah."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "gwaji" za a iya fassarawa haka, "yin ƙoƙarin sa ayi zunubi" ko "jarabce" ko "yin ƙoƙarin sa ayi marmarin yin zunuba."
  • Hanyoyin da za a fassara "jarabawa" zasu haɗa da, "abubuwan dake sa gwaji" ko "abubuwan dake jarabtar wani ya yi zunubi" ko "abubuwan dake sa marmarin ayi wani abin da ba dai-dai ba."
  • A "gwada Allah" za a iya fassarawa haka "a sa Allah a gwaji" ko "jaraba Allah" ko ayi "ƙoƙarin gwada haƙurin Allah" ko "asa Allah ya hori wani" ko "taurin kan ci gaba da rashin biyayya da Allah."

(Hakanan duba: rashin biyayya, Shaiɗan, zunubi, jarabawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 03:4-5
  • Ibraniyawa 04:15
  • Yakubu 01:13
  • Luka 04:02
  • Luka 11:04
  • Matiyu 26:41

hadayar sulhu

Ma'ana

Wannan magana "hadayar sulhu" yana magana akan hadaya da ake yi domin gamsarwa ko cika adalcin Allah a kuma gamshi fushinsa.

  • Baikon hadayar jinin Yesu Almasihu hadayar sulhu ne ga Allah domin zunuban 'yan adam.
  • Mutuwar Yesu akan gicciye ya gamshi fushin Allah gãba da zunubi. Wannan ya samar da hanyar da Allah zai dubi mutane da tagomashi ya kuma basu rai madawwami.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana za a iya fassarawa haka, "gamsarwa" ko "sa Allah ya gafarta zunubai ya kuma yi wa mutane alheri."
  • Wannan kalma "kaffara" kusan ma'anarsa ɗaya da "hadayar sulhu." Zai yi kyau idan an auna waɗannan maganganu biyu a ga yadda ake amfani da su.

(Hakanan duba: kaffara, har abada, gafartawa, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:02
  • 1 Yahaya 04:10
  • Romawa 03:25-26

haikali

Ma'ana

Haikali gini ne dake kewaye da katangaggun harabai inda Isra'ilawa suke zuwa suyi addu'a su kuma miƙa hadayu ga Allah. Yana bisa Tsaunin Moriya a cikin birnin Yerusalem.

  • Yawanci kalmar "haikali" yana nufin harabar haikalin gabaɗaya, duk da harabun dake kewaye da ainihin ginin. Wasu lokutan yana nufin ginin kaɗai.
  • Ginin haikalin nada ɗakuna biyu, Wuri Mai Tsarki da Wuri Mafi Tsarki.
  • Allah na nuna haikalin a matsayin wurin zamansa.
  • Sarki Suleman ya gina Haikalin a zamanin mulkinsa. Ya kamata ya zama wurin sujada na din-dindin a Yerusalem.
  • A Sabon Alƙawari, kalmar "haikalin Ruhu Mai Tsarki" ana amfani da ita da nufin masu bin Yesu a matsayin ƙungiya, saboda Ruhu Mai Tsarki na zama cikin su.

Shawarwarin Fassara:

  • Yawanci idan nassi ya ce mutane na "cikin haikali," yana nufin harabun dake waje da ginin. Za'a iya fassara wannan haka "cikin harabun haikali" ko "cikin harabar haikalin."
  • Inda yake nufin ainihin ginin kai, wasu juyin sun fassara "haikali" a matsayin "ginin hajkali," domin a bayyana nassin sosai.
  • Hanyoyin da za a fassara "haikali" zasu haɗa da, "gidan Allah mai tsarki" ko "wurin sujada mai tsarki."
  • Yawanci a cikin Littafi Mai Tsarki, haikali na nufin "gidan Yahweh" ko "gidan Allah."

(Hakanan duba: hadaya, Suleman, Babila, Ruhu Mai Tsarki, haraba, Sihiyona, gida)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 03:02
  • Ayyukan Manzanni 03:08
  • Ezekiyel 45:18-20
  • Luka 19:46
  • Nehemiya 10:28
  • Zabura 079:1-3

hallaka, hallakarwa, lalacewa

Ma'ana

Wannan kalma "hallaka" ma'anarta shi ne mutuwa ko lalatarwa, yawancin lokaci haka takan faru ne da ƙarfi da yaji ko kuma wani bala'i. A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma nada ma'ana musamman ta hukunci na har abada a wutar lahira.

  • Mutanen dake "hallaka" sune waɗanda an ƙaddara su ga wutar lahira domin sun ƙi su bada gaskiya ga Yesu domin cetonsu.
  • Yahaya 3:16 ya koyar da cewa "hallaka" shi ne rashin kasancewa har abada a sama.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, hanyoyin fassara wannan magana za a haɗa da waɗannan, "mutuwa ta har abada" ko "a hukunta a lahira ta wuta" ko "a lalatar."
  • A tabbata fassarar "hallaka" ta bada ma'anar kasancewa a wutar lahira har abada ba wai kuma mutumin nan "bashi da rai ne ba."

(Hakanan duba: mutuwa, har abada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:23
  • 2 Korintiyawa 02:16-17
  • 2 Tasalonikawa 02:10
  • Irmiya 18:18
  • Zabura 049:18-20
  • Zakariya 09:5-7
  • Zakariya 13:08

hannun dama

Ma'ana

"Hannun dama" kalma ce dake nuna wuri mai daraja ko ƙarfi a hannun dama na mai mulki ko wani mai muhimmanci.

  • Hannun dama ana iya kwatanta shia da alamar iko, izini, ko ƙarfi.
  • Littafi Mai Tsarki ya faɗi cewa Yesu na zama "a hannun dama na" Allah Uba a matsayinsa na kan jiki na masu bi (Ikilisiya) kuma yana tafiyar da dukkan abu mai mulkin dukkan hallita.
  • Hannaun daman wani ana kwatanta shi da wani girmamawa na musamman ga wanda aka ɗora a bisa kan wanda aka yi wa albarka (kamar yadda ya faru da Yakubu da ya albarkaci Ifraim ɗan Yosef).
  • Yin hidima a "hannun dama" na wani na nufin hidimarka na da muhimmanci da amfani ga ayyukan wannan mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu lokuta wannan kalma "hannun dama" kai tsaye na ma'anar hannun daman wani taliki, kamar sa'ad da sojojin Romawa suka sa sandar ba'a a hannun daman Yesu. A fassara wannan ana yin amfani da kalmar da yaren ke amfani da ita wurin kiran wannan hannu.
  • Game da yin misali, idan faɗar ta haɗa da wannan kalma "hannun dama" baya kuma da ma'ana iri ɗaya da yaren aikin, daga nan ayi la'akari da ko yaren na da wata faɗar daban mai ma'ana iri ɗaya.
  • Faɗar "a hannun daman" za a iya fassarawa "a gefen damansa" ko "a gefen wurinsa na daraja" ko "a matsayin iko" ko "a shirya domin taimako."
  • Hanyoyin fassara "da hannun damansa" zai iya haɗawa da "da izininsa" ko "amfani da iko" ko "da ƙarfinsa na ban mamaki."
  • Faɗar misali "hannun damansa da ikon damtsensa" ana amfani da hanyoyi biyu a jaddada ikon Allah da ƙarfinsa mai girma. Wata hanya ɗaya ta fassara wannan faɗar zata kasance haka "ƙarfinsa mai ban mamaki da babban ikonsa."
  • Faɗar "hannunsu na dama munafunci ne" za a iya fassarawa haka, "koma abinsu mai daraja ya gurɓata da ƙarya" ko "wurin darajarsu ya gurɓata da ruɗi" ko "suna amfani da ƙarya su ikonta kansu."

(Hakanan duba: zargi, mugunta, daraja, ƙarfi, horo, tawaye)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:33
  • Kolosiyawa 03:01
  • Galatiyawa 02:09
  • Farawa 48:14
  • Ibraniyawa 10:12
  • Littafin Makoki 02:03
  • Matiyu 25:33
  • Matiyu 26:64
  • Zabura 044:03
  • Wahayin Yahaya 02:1-2

hasala, zafin fushi

Ma'ana

Hasala haushi ne mai ƙuna da wani lokaci ke daɗewa. Wannan na bayyana hukuncin Allah na adalci da kuma hukuncinsa ga mutane waɗanda ke tayar masa.

  • A Littafi Mai Tsarki, "hasala" yawancin lokaci na bayyana fushin Allah zuwa ga waɗanda suka yi masa zunubi.
  • "Hasalar Allah" na nufin shari'arsa da kuma hukuncinsa bisa zunubi.
  • Hasalar Allah hukuncinsa ne na adalci ga waɗanda suka ƙi su tuba daga zunubi.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin a za a iya fassara wannan kalma su haɗa da "fushi mai zafi" ko "hukuncin adalci" ko "fushi."
  • Sa'ad da ake magana game da hasalar Allah, a tabbata da cewa kalmar ko faɗar da aka yi amfani da ita aka fassara wannan kalmar bai bada ma'anar cike da fushi zunubi ba. Hasalar Allah mai adalci ne da tsarki.

(Hakanan duba: mahukunci, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 01:8-10
  • 1 Timoti 02:8-10
  • Luka 03:7
  • Luka 21:23
  • Matiyu 03:07
  • Wahayin Yahaya 14:10
  • Romawa 01:18
  • Romawa 05:09

himma, ƙwazo

Ma'ana

Kalmomin "himma" da kuma "ƙwazo" suna nuna manne wa wani ko wani abu da dukkan zuciya.

  • Himma ta haɗa da so da ayyuka da suka yarda da wata hidimar. Kalmar na bayyana mutum wanda ke da aminci ga Allah yana kuma koyar da wasu su yi hakan.
  • Yin ƙwazo ya kunshi yin niyya cikin abin da kake yi kana kuma ci gaba da yin juriya ga wannan abu.
  • "Himma Ubangiji" ko "himma Yahweh" na manufar ƙarfin Allah, naciyarsa wurin albarkatar mutanensa ko ya ga anyi adalci.

Shawarwarin Fassara:

  • A "zama da ƙwazo" za a iya fassarawa haka, "ayi niyya tuƙuru" ko "a maida hankali sosai."
  • Kalmar "himma" za a iya fassarawa haka "ibada mai ƙarfi" ko "garajen niyya" ko "gabagaɗin adalci."
  • Faɗar, "himma domin gidanka" za a iya fassarawa haka, "ƙaƙƙarfan girmama haikalinka" ko "naciyar marmarin girmama gidanka."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 12:31
  • 1 Sarakuna 19:9-10
  • Ayyukan Manzanni 22:03
  • Galatiyawa 04:17
  • Ishaya 63:15
  • Yahaya 02:17-19
  • Filibiyawa 03:06
  • Romawa 10:1-3
  • Filibiyawa 03:06

horarwa, iya horarwa, horarre, horar da kai

Ma'ana

Kalmar nan "horarwa" tana nufin horar da mutane su yi biyayya da waɗansu aiyanannun ka'idoji domin yin rayuwa mai kyau.

  • Iyaye kan horar da 'ya'yansu ta wurin gindaya musu sharuɗan rayuwa ta gari da kuma nuna musu yadda za su yi biyayya da wanan koyarwa.
  • Hakama Allah kan horar da 'ya'yansa domin taimakon su wajen samun rayuwa ta ruhaniya ingantacciya da za ta bada 'ya'ya a rayuwarsu, kamar farin ciki ƙauna da haƙuri.
  • Horarwa ta haɗa da ummarni kan yadda za'a yi rayuwar da zata gamshi Allah, haka nan da hukunci na halaiyar da ta saɓawa nufin Allah.
  • Haron kai mataki ne na samar da kuma moron ka'idoji na ruhaniya a cikin rayuwar mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da abin da ke wurin horarwa za'a iya fassara ta da "koyo da ba da ummarni" ko "wani nuni na yin rayuwa tagari"ko "ladabtarwa sabo da yin abin da ba dai-da- ba"
  • Kalmar "horarwa" za'aiya fassara ta da "horarwa ta halaiya" ko ladabtarwa ko "gyaran hali" ko "nuni kan yin rayuwa tagari."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 06:4
  • Ibraniyawa 12:05
  • Littafin Misalai 19:18
  • Littafin Misalai 23:13-14

hukuntawa, alƙalai, hukunci, hukunce-hukunce

Ma'ana

Kalmomin "hukuntawa" da "hukunci" yawanci suna ma'anar ɗaukar mataki game da ko ɗabi'ar wani al'amari mai kyau ne ko marar kyau.

  • "Hukuncin Allah" yawanci yana ma'ana matakin da ya ɗauka ya kayar da wani abu ko wani a matsayin mai zunubi.
  • Hukuncin Allah yawancin yana haɗa wa da horon mutane domin zunubinsu.
  • Kalmar "hukuntawa" kuma na iya ma'anar "kayarwa." Allah ya ba mutanensa umarni da cewa kada suyi hukunci ta wannan hanyar.
  • Wata ma'anar kuma ita ce "shar'antawa tsakani" ko "hukuntawa tsakani," kamar ɗaukar matakin wanene ke da gaskiya a tsakanin masu saɓani.
  • A cikin wasu nassin, hukunce-hukuncen Allah sune abin da ya ɗauki matakin cewa dai-dai ne ko mai adalci ne. Suna kama da dokokinsa, shari'unsa, ko ka'idajinsa.
  • "Hukunci" na iya nufin iya ɗaukar mataki mai hikima. Talikin da ya rasa "hukunci" baya da hikimar ɗaukar matakai masu hikima.

Shawarwarin Fassarawa:

  • Dogara akan sashen nassin, hanyoyin fassarawa "hukuntawa" na iya haɗa wa da "ɗaukar mataki" ko "kayarwa" ko "horarwa" ko "doka."
  • Kalmar "hukunci" ana iya fassarata a matsayin "horo" ko "ɗaukar mataki" ko "shari'a" ko "doka" ko "kayarwa."
  • A cikin wasu sashen nassosi, faɗin "a cikin hukunci" ana iya fassarawa da "a ranar hukunci" ko "a lokacin da Allah zai hukunta mutanensa."

(Hakanan duba: doka, hukuntawa, ranar hukunci, mai adalci, shari'a, shari'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:17
  • 1 Sarakuna 03:09
  • Ayyukan Manzanni 10:42-43
  • Ishaya 03:14
  • Yakubu 02:04
  • Luka 06:37
  • Mika 03:9-11
  • Zabura 054:01

Ibraniyanci, Ibraniyawa

Ma'ana

"Ibraniyawa" mutane ne da suka zama zuriyarsu daga Ibrahim ta layin Ishaku da Yakubu. A cikin Littafi Mai Tsarki Ibrahim ne aka fara kira "Ba'Ibrane."

  • Kalmar nan "Ibraniyanci" zata iya zamaharshen da mutanen Ibraniyawa ke magana da shi. Mafi yawa daga cikin sashe na Littafi Mai Tsarki an rubuta shi ne da harshen Ibraniyanci.
  • A wurare da bam da ban a cikin Littafi Mai Tsarki, ana kiran Ibraniyawa "Yahudawa" ko "Isra'ilawa." Ya fi kyau a mori waɗannan sunaye guda uku a cikin ayoyin, muddin dai an gane cewa wurin na magana ne akan waɗannan mutanen.

(Hakanan duba: Isra'ila, Yahudu, shugabannin Yahudawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 26:12-14
  • Farawa 39:13-15
  • Farawa 40:15
  • Farawa 41:12-13
  • Yahaya 05:1-4
  • Yahaya 19:13
  • Yahaya 01:8-10
  • Filibiyawa 03:5

Idin ‌Ƙ‌etarewa

Ma'ana

"Idin ‌Ƙ‌etarewa" sunan wani idi ne na addini wanda Yahudawa suke bikinsa kowacce shekara, domin su tuna da yadda Allah ya kuɓutar da kakanninsu, Isra'ilawa, daga bauta a ƙasar Masar.

  • Sunan wannan buki ya zo daga lokacin da Allah ya "‌Ƙetare" gidajen Isra'ilawa bai kashe 'ya'yansu maza ba sa'ad da ya kashe 'ya'yan fari maza na Masarwa.
  • Wannan bukin ‌Ƙetarewar ya haɗa da cin musamman abinci na naman ɗan rago da aka kashe aka gasa da kuma gurasa marar gami. Waɗannan cimar suna tunashe su kan abincin da Isra'ilawa suka ci a daren da zasu kubce daga Masar.
  • Allah ya gaya wa Isra'ilawa su ci wannan abinci kowace shekara domin su tuna da yadda Allah ya "‌Ƙetare" gidajensu da yadda ya baratar dasu daga bautar Masar.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci "‌Ƙetarewa" za a iya fassara shi ta wurin haɗa waɗannan kalmomin "Idi" da "Ƙetarewa." ko kuma haɗin wasu kalmomi da suke da wannan ma'ana.
  • Zai taimaka idan sunan wannan buki yana da kalmomin da suka faɗi yadda mala'ikan Ubangiji ya tsallake gidajen Isra'ilawa ya bar 'ya'yansu maza da rai.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:07
  • 2 Tarihi 30:13-15
  • 2 Sarakuna 23:23
  • Maimaitawar Shari'a 16:02
  • Fitowa 12:26-28
  • Ezra 06:21-22
  • Yahaya 13:01
  • Yoshuwa 05:10-11
  • Lebitikus 23:4-6
  • Littafin ‌Lissafi 09:03

ikilisiya, Ikilisiya

Ma'ana

A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma "ikilisiya" na nufin karamar ƙungiyar masu bada gaskiya ga Yesu waɗanda suke tattaruwa kullum su yi addu'a su kuma ji wa'azin maganar Allah. Wannnan kalma "Ikilisiya" kuma ana nufin dukkan Kristoci.

  • Wannan kalam ma'anarta majalisar "kirayayyu da aka fitar" ko kuma taron mutane da suke haɗuwa saboda wani dalili musamman.
  • Sa'ad da aka yi amfani da wannan kalmar domin dukkan masu bada gaskiya ko'ina a jikin Kristi, wasu fasarar Littafi Mai Tsarki sukan fara rubuta shi da babban harufa kamar haka (Ikilisiya) domin a bambanta shi da ƙaramar ikilisiya.
  • Yawancin lokaci masu bada gaskiya a wani birni za su taru a gidan wani mutum. Irin waɗannan ƙananan ikilisiyoyi ana basu sunan birnin misali "ikilisiyar dake Afisa."
  • A cikin Lttafi Mai Tsarki, "ikilisiya" ba gini ba ce.

Shawarwarin Fassara

  • Wannan kalma "ikilisiya" za a iya fassarata haka "taruwa tare" ko "majalisa" ko "taro" ko "waɗanda da suke saduwa tare."
  • Kalma ko furcin da ake amfani da su a fassara wannan magana yakamata su zama ga dukkan masu gaskatawa, ba domin wata ƙungiya kawai ba.
  • A tabbatar cewa fassarar "ikilisiya" ba ta gini kaɗai ba ce.
  • Maganar da aka yi amfani da ita a fasara "majalisa" a Tsohon Alƙawari za a iya amfani da ita a fassara wannan.
  • Kuma yakamata ayi la'akari da yadda aka fassarata a cikin juyi na Littafi Mai Tsarki na ƙasar.

(Hakanan duba: taruwa, gaskatawa, kirista)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:12
  • 1 Tasalonikawa 02:14
  • 1 Timoti 03:05
  • Ayyukan Manzanni 09:31
  • Ayyukan Manzanni 14:23
  • Ayyukan Manzanni 15:31
  • Kolosiyawa 04:15
  • Afisawa 05:23
  • Matiyu 16:18
  • Filibiyawa 04:15

iko, hukuma, ikoki

Ma'ana

Wannan kalma "iko" fassararta shi ne karfin bishewa da mallaka da wani mutum yake da shi akan wani mutum daban.

  • Sarakai da masu sarauta suna da iko akan mutanen da suke mulki.
  • Kalman nan "mulkoki" yana nufin mutane, gwamnatai, ko ƙungiyoyi da suke da iko kan wasu.
  • Maigida yana da iko akan barorinsa ko bayi. Iyaye suna da iko akan 'ya'yansu.
  • Gwamnati tana da iko ko 'yanci ta kafa dokoki da zasu kare 'yan ƙasarta.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "iko" za a iya fassarata haka, "sarrafa" ko "'yanci" ko "fannin ƙwarewa."
  • Wani lokaci "iko" zai iya zama da ma'ana haka "ƙarfi."
  • Sa'ad da aka yi amfani da "masu iko" game da mutane ko ƙungiyoyi dake mulkin mutane, za a iya fasara shi a ce "shugabanni" ko "masu mulki" ko "ikoki."
  • Wannan faɗar "da ikon kansa" za a iya juya shi a ce "da 'yancin kansa na shugabanci" ko "bisa ga fannin kwarewarsa."
  • Wannan furci "ƙarƙashin iko" za a iya fassara shi haka, "yana da kamun kai yayi biyayya." ko "yana biyayya da umarnan waɗansu."

(Hakanan duba: ɗan ƙasa, umarni, biyayya, iko mai mulki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 02:10
  • Esta 09:29
  • Farawa 41:35
  • Yona 03:6-7
  • Luka 12:05
  • Luka 20:1-2
  • Markus 01:22
  • Matiyu 08:09
  • Matiyu 28:19
  • Titus 03:01

iko, ikoki, cike da iko

Ma'ana

Wannan magana "iko" shi ne iya yin abubuwa ko ka sa abubuwa su faru, yawancin lokaci ana amfani da ƙarfi sosai "Ikoki" na nufin mutane ko ruhohi waɗanda suke da iko su sa abubuwa su faru.

  • "Ikon Allah" na nufin Allah ya iya komai, musamman abubuwan da mutane basu iya yi ba.
  • Allah yana da cikakken iko bisa dukkan abubuwan da ya hallita.
  • Allah yana ba mutane iko suyi abin da yake so, sa'ad da suka warkar da mutane ko suka yi wani aikin al'ajibi, sukan yi shi ne da ikon Allah.
  • Saboda Yesu da Ruhu Mai Tsarki Allah ne, suna da wannan ikon.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, za a iya fassara "iko" haka "iyawa" ko "ƙarfi" ko "iya aikin al'ajibi" ko "kamawa"
  • Wasu hanyoyin fassara "iko" za a haɗa da waɗannan "hallitu masu iko" ko "ruhohi masu bishewa" ko "masu bida wasu."
  • Furci kamar haka "ka cece mu daga ikon magabtanmu" za a iya fassarawa haka "ka cece mu daga magabtanmu waɗanda suke wahalshe mu" ko "ka kwace mu daga masu danniyar magabtanmu." A wannan, ma'anar "iko" shi ne yin amfani da ƙarfin kanka ka danne waɗansu.

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, Yesu, al'ajibi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 01:05
  • Kolosiyawa 01:11-12
  • Farawa 31:29
  • Irmiya 18:21
  • Yahuza 01:25
  • Littafin Alƙalai 02:18
  • Luka 01:17
  • Luka 04:14
  • Matiyu 26:64
  • Filibiyawa 03:21
  • Zabura 080:02

isã, darajar abu ko wani, rashin isã, marar daraja

Ma'ana

Kalmar "isã" na bayyana wani ko wani abu da ya cancanci bangirma da daraja. A zama da daraja na nuna yadda mutum ke da muhimmanci. A zama da "rashin daraja" na nufin rashin muhimmanci da daraja.

  • A zama da isã na da alaƙa da zama da daraja ko da muhimmanci.
  • A zama da "rashin isã" na nufin rashin cancantar bangirma da kula.
  • Jin yanayin rashin isã na nufin jin yanayi kamar baka da muhimmanci kamar wani ko ganin kamar ba a cancanci a sami bangirma ko alheri ba.
  • Kalmomin "rashin isã" da "marar daraja" na da alaƙa, amma ma'anarsu ta banbanta. A zama da "rashin isã" na nufin zama da rashin cancantar bangirma ko kula. Zaman "rashin amfani" na nufin rashin daraja da manufa.

Shawarwarin Fassara:

  • "Isã" za a iya fassa rawa a matsayin "cancanta" ko "muhimmanci" ko "mai daraja."
  • "Darajar abu ko wani" za a iya fassa rawa a matsayin "daraja" ko "mai muhimmanci."
  • Faɗar "kasancewa da daraja" za a iya fassa rawa a matsayin "zama mai daraja."
  • Ya danganta da nassin, kalmar "rashin isã" da kalmar "marar daraja" za a iya fassa rawa a matsayin "marar muhimmanci" ko "marar daraja" ko "marar cancanta."
  • Kalmar "marar daraja" za a iya fassa rawa a matsayin "babu isã" ko "babu dalili" ko "bai isã komai ba."

(Hakanan duba: daraja)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 22:04
  • 2 Tasalonikawa 01:11-12
  • Ayyukan Manzanni 13:25
  • Ayyukan Manzanni 25:25-31
  • Ayyukan Manzanni 26:31
  • Kolosiyawa 01:9-10
  • Irmiya 08:19
  • Markus 01:07
  • Matiyu 03:10-12
  • Filibiyawa 01:25-27

Isra'ila, Isra'ilawa

Ma'ana

Kalmar nan "Isra'ila" ita ce kalmar da Allah ya ba Yakubu. Ma'anarta ita ce "Ya sha gwagwarmaya da da Allah."

  • Zuriyar Yakubu an san su da "mutanen Isra'ila" ko "banin Isra'ila" ko Isra'ilawa."
  • Allah ya yi yarjejeniya da mutanen Isra'ila. Su ne zaɓaɓɓun mutanensa.
  • Banin Isra'ila kabila goma sha biyu.
  • Tun bayan mutuwar Sarki Suleman, Isra'ila ta kasu gida biyu a sarauce: mulkin kudu, da ake kira "Yahuda," da mulkin arewa, da ake kira "Isra'ila."
  • Sau da yawa kalmar nan "Isra'ila" za'a iya fassara ta da "mutanen Isra'ila" ko "banin Isra'ila" ya danganta ga wurin.

(Hakanan duba: Yakubu, mulkin Isra'ila, Yahuda, banin, kabila goma sha biyu ta Isra'ila)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 10:01
  • 1 Sarakuna 08:02
  • Ayyukan Manzanni 02:36
  • Ayyukan Manzanni 07:24
  • Ayyukan Manzanni 13:23
  • Yahaya 01:49-51
  • Luka 24:21
  • Markus 12:29
  • Matiyu 02:06
  • Matiyu 27:09
  • Filibiyawa 03:4-5

jarabawa, jarabobi, anyi jarabawa, jarabawa cikin wuta

Ma'ana

Kalmar "jarabawa" na nufin wani mawuyacin yanayi mai zafi wanda ke bayyana ƙarfin wani taliki da kasawarsa.

  • Allah yana jaraba mutane, amma baya gwada su zuwa zunubi. Shaiɗan, kuwa, yana yiwa mutane gwaji zuwa zunubi.
  • Wasu lokuta Allah na jaraba mutane domin ya bayyana zunubinsu. Jarabawa na taimakawa wani ya guje wa zunubi ya kuma yi kusa da Allah.
  • Ana gwada zinariya da sauran ƙarafuna da wuta domin a tantance tsantsarsu da ƙarfinsu. Wannan ne hoton yadda Allah ke amfani da yanayai masu zafi ya gwada mutanensa.
  • A "sanya cikin jarabawa" zai iya nufin, "ƙalubalantar wani abu ko wani taliki ya tabbatar da darajarsa."
  • A nassin sanya Allah ga jarabawa, yana nufin ayi ƙoƙarin sanya shi ya yi al'ajibai domin mu, ana ɗaukar zarafin jinƙansa.
  • Yesu ya gayawa Shaiɗan ba dai-dai ba ne asa Allah ga jarabawa. Shi mai iko dukka ne, Allah mai tsarki wanda yake bisa komai da kowa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "jarabawa" za a iya fassarawa haka, a "ƙalubalanci" ko a "sanya a fuskanci yanayi mai wuya" ko a "tabbatar."
  • Hanyoyin fassara "jarabawa" zasu zama, "ƙalubalanci" ko "mawuyacin yanayi." "tilasta tabbatar da kai."
  • A "sanya cikin jarabawa" za a iya fassarawa haka, "jarabawa" ko "a shirya ƙalubalanci" ko "tilasta tabbatar da kai."
  • A cikin nassin jaraba Allah, wannan za a iya fassarawa haka, "ƙoƙarin tilasta Allah ya tabbatar da ƙaunarsa."
  • A cikin nassosin, inda ba Allah ba ne kan maganar, kalmar "jarabawa" zai iya zama "gwaji."

(Hakanan duba: gwaji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:01
  • 1 Tasalonikawa 05:21
  • Ayyukan Manzanni 15:10
  • Farawa 22:01
  • Ishaya 07:13
  • Yakubu 01:12
  • Littafin Makoki 03:40-43
  • Malakai 03:10
  • Filibiyawa 01:10
  • Zabura 026:02

jarumi

Ma'ana

Jarumi hafsan soja ne na Roma wanda yake da sojoji 100 a ƙarƙashin jagorancinsa.

  • Za a iya fassara wannan kalma da ma'ana haka, "shugaban mutane ɗari" ko "shugaban mayaƙa" ko "hafsa mai duban ɗari."
  • Wani jarumin Roma ya zo gun Yesu neman warkarwar bawansa.
  • Jarumin da ya shugabanci giciye Yesu yayi mamaki da ya ga yadda Yesu ya mutu.
  • Allah ya aiki wani jarumi wurin Bitrus domin Bitrus ya bayyana masa labari mai daɗi game da Yesu.

(Hakanan duba: Roma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 10:01
  • Ayyukan Manzanni 27:01
  • Ayyukan Manzanni 27:42-44
  • Luka 07:04
  • Luka 23:47
  • Markus 15:39
  • Matiyu 08:07
  • Matiyu 27:54

jiki

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "jiki" tana nufin jiki na mutum ko na dabbobi da ake iya gani.

  • Hakanan Littafi Mai Tsarki ya mori kalmar "jiki" a cikin salon magana domin yin magana akan dukkan abu mai rai da kuma mutum.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kalmar nan "jiki" ya more ta domin a baiyana halin wani mutum kamar halin zunubi. A kan fi yawan amfani da wannan kalma sansance rayuwa ta jiki da rayuwa ta ruhatiya.
  • Batun nan "jiki na kai da na jini" na nufin wani da ke da dangantaka ta jini da wani mutum, kamar iyaye dangi ɗa ko jika.
  • Batun nan "jiki da jini" za su iya zama ubannin mutum ko zuriya..
  • Kalmar nan "jiki ɗaya" tana magana ne akan haɗin kai na zahiri na namiji da kuma mace a cikin aure.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin wurin da ake batun jikin dabba, za'a iya fassara "jiki" "fata" ko "nama"
  • A lokacin da aka more ta wajen ambaton dukkan halittu, wanan kalmar za'a fassara ta da "rayayyun halitta" ko kuma "duk wani abu da ke da rai."
  • Idan ana maganar dukkan mutane, wanan kalmar za'a fassara ta "dukkan mutane" ko "duk mai rai" ko "duk wani abu mai rai."
  • Wanan batu na "jiki da jini" shima za'a fassara shi da "dangi"ko "iyali" ko "makusanci" ko "kabilar iyali" kuma za'a iya samun wurin da za'a fassara ta da "ubanni" ko "zuriya."
  • Waɗansu harsunan za su iya zama da wata kalmar da ke da kamancin ma'ana da jiki da jini."
  • Kalmar nan "zama jiki ɗaya" ko "a zama kamar jiki ɗaya" ko "ku manne wa juna" ko "ku zama kamar jiki ɗaya a cikin jiki da ruhu." Za a duba wanan fassarar domin a tabbatar ta sami karɓuwa bisa al'adar harshen da ake fassarar hakana nan kuma ya kamata a san cewa salon magana ne aka mora, kuma baya nufin cewa daga miji da mace zan zama jiki ɗaya ko jiki ɗaya ba ne.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:16
  • 2 Yahaya 01:07
  • Afisawa 06:12
  • Galatiyawa 01:16
  • Farawa 02:24
  • Yahaya 01:24
  • Yahaya 01:14
  • Matiyu 16:17
  • Romawa 08:8

jiki, jikuna

Ma'ana

Wannan kalma "jiki" ana nufin jikin mutum ko na dabba. Wannan kalmar ana amfani da ita a kwatanta wani abu ko ƙungiya da take da gaɓoɓi ɗai ɗaya.

  • Yawanci lokaci kalmar nan "jiki" na nufin mataccen mutum ko dabba. Wani lokaci ana ambato haka "mataccen jiki" ko "gawa."
  • Lokacin da Yesu ya cewa almajiransa a Idin ‌Ƙetarewarsa na ƙarshe, "Wannan (gurasa) jikina ne," yana magana ne akan jikinsa da za a karya (kashe) domin biyan zunubanmu.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ƙungiyar Kiristoci ana ce da ita "jikin Almasihu'
  • Kamar yadda jiki yake da gaɓoɓi da yawa, haka ma "jikin Almasihu" yake da kowanne ɗan ƙungiya.
  • Kowanne mai bada gaskiya yana da nasa aiki musamman a cikin jikin Almasihu domin ya taimaki ƙungiyar gabaɗaya a bauta wa Allah tare a kuma kawo masa ɗaukaka.
  • Yesu shi ne "kai" (shugaba) na "jiki" na masu gaskatawa da shi. Kamar yadda kan mutum ke gayawa jikinsa abin da zai yi, haka ma Yesu shi ne wanda yake jagoranci yana bida Kiristoci 'yan ƙungiyarsa "jikinsa."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanya mafi kyau da za a fassara wannan furci shi ne a yi amfani da kalmar da kowa ya saba da ita wato na jikin mutum a yaren masu juyi. A tabbabta kalmar da ake amfani da ita ba ƙazamtacciya ba ce.
  • Idan ana magana akan masu gaskatawa gabaɗaya, ga waɗansu yarurruka zai fi dacewa su ce, "jikin Almasihu na ruhaniya."
  • Lokacin da Yesu ya ce, "Wannan jikina ne" ya fi kyau a fassara shi yadda yake, amma tare da bayani idan ana buƙata.
  • Wasu yarurruka watakila suna da wata kalma daban idan ana magana akan mataccen jiki, misali "gawa" game da mutum ko "mushe" game da dabba. A tabbatar kalmar da ake amfani da ita a fassara "jiki" yana da ma'ana a cikin nassi kuma karɓaɓɓe ne.

(Hakanan duba: kai, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 10:12
  • 1 Korintiyawa 05:05
  • Afisawa 04:04
  • Littafin Alƙalai 14:08
  • Littafin Lissafi 06:6-8
  • Zabura 031:09
  • Romawa 12:05

jini

Ma'ana

Kalmar nan "jini" ma'anarta shi ne jan ruwannan dake fitowa daga fatar mutum sa'ad da ya ji rauni ko ciwo. Jini yana kawo abinci mai amfani ga dukkan jikin mutum.

  • Jini kwatancin rai ne kuma sa'ad da aka zubda shi ko kwararar da shi, yana kwatanta rasa rai, ko mutuwa.
  • Lokacin da mutane suka yi hadaya ga Allah, sukan yanka dabba su zuba jininsa akan bagadi. Wannan yana kwatanta hadayar ran dabbar domin biyan zunuban mutane.
  • Ta wurin mutuwarsa akan gicciye, jinin Yesu ya wanke mutane daga zunubansu ya kuma biya hukuncin daya cancanci zunubansu.
  • Wannan furci "nama da jini" ana nufin 'yan adam ne.
  • Wannan furci "namana da jinina" na nufin mutane da suka haɗa dangi cikin jiki.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma ya kamata a fassarata da furcin da ake ambatan jini a yaren da ake masu juyi.
  • Wannan furci "nama da jini" za a iya fassara shi "mutane" ko "'yan adam."
  • Zai danganta ga nassin, wannan furci "namana da jinina" za a iya juya shi zuwa "iyalina na kaina" ko "'ya'uwana na kaina" ko mutanena."
  • Ko akwai furci a cikin harshen da ake masu juyi da ake amfani da wannan ma'ana, sai a yi amfani da wannan a fassara "nama da jini."

(Hakanan duba: jiki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:07
  • 1 Sama'ila 14:32
  • Ayyukan Manzanni 02:20
  • Ayyukan Manzanni 05:28
  • Kolosiyawa 01:20
  • Galatiyawa 01:16
  • Farawa 04:11
  • Zabura 016:4
  • Zabura 105:28-30

jinƙai, mai jinƙai

Ma'ana

Waɗannan maganganu "jinƙai" da "mai jinƙai" ana nufin taimaka wa mutane ne waɗanda ke da buƙata, musamman sa'ad da suke cikin yanayin kasawa da ƙasƙanci.

  • Wannan kalmar "jinƙai" ma'anarta fasa hukunta mutane saboda laifinsu ya ƙunshi ma'anar ƙin hukunta mutane don wani abin da basu yi dai-dai ba.
  • Mutum mai iko kamar sarki za a ce yana da "jinƙai" sa'ad da ya yi wa mutane alheri maimakon mugunta.
  • Nuna jinƙai shi ne lokacin da muka taimaki wani mutum da ya yi mana laifi.
  • Mukan nuna jinƙai sa'ad da muka taimaki mutanen da suke cikin buƙata mai

tsanani.

  • Allah yana mana jinƙai, yana so mu kuma mu yiwa wasu jinƙai.

Shawarwarin Fassara

  • Yadangana ga nassi, za a iya fassara "jinƙai" a ce "alheri" ko "juyayi" ko "tausai."
  • Wannan magana "jinƙai" za a iya fassara ta haka "nuna tausai" ko "yin alheri ga" ko "gafartawa."
  • "Nuna jinƙai ga" ko "yin jinƙai ga" za a iya fassarawa haka "yin kirki" ko "yin jinƙai ga."

(Hakanan duba: juyayi, gafartawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 01:3-5
  • 1 Timoti 01:13
  • Daniyel 0:17
  • Fitowa 34:06
  • Farawa 19:16
  • Ibraniyawa 10:28-29
  • Yakubu 02:13
  • Luka 06:35-37
  • Matiyu 09:27
  • Filibiyawa 02:25-27
  • Zabura 041:4-6
  • Romawa 12:01

jinƙai, yawan jinƙai, wanda aka nuna wa jinkai, halin nuna jinƙai

Ma'ana

A nuna "jinƙai" shi ne fifita. Lokacin da wani ya nuna jinƙai ga wani mutum, to ya ga cewa wanan mutumin ya yi wani abu mai kyau domin haka sai a ƙara nuna jin daɗi domin ya ƙara yin haka domin amfanin saura mutane.

  • Kalmar nan "halin nuna fifiko" tana nufin ɗabi'ar fifita wani amma ba wasu ba. Tana nufin tunanin fifita wani mutum akan waɗansu, ko wani abu bisa wani abu, saboda fin so ga wanan mutum ko abin. hakika nuna fifiko an ɗauke shi a matsayin abin da bai kamata ba.
  • Yesu ya yi girma "cikin jinƙai" tare da Allah da kuma mutane. Wanan na nuna sun yarda da rayuwarsa da kuma halinsa.
  • Ƙaulin nan "samun jinƙai" ga wani yana nufin cewa mutumin ya sami amincewa a wurin wani mutum.
  • "Jinƙai" har ila yau zai iya zama wani tagomashi ne ga wani mutum domin amfani wanan mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi da za'a fassara kalmar "jinƙai" sun haɗa da "albarka" ko "amfani."
  • "Shekarar jinƙai ta Yahweh" za'a iya fassara ta da "shekarar da Yahweh zai kawo albarka mai yawa."
  • Kalmar nan "nuna fifiko" za'a fassara ta da "nuna bambanci" ko "nuna tara" ko nuana rashin adalci ga wani." Wanan kalmar tana da nasaba da kalmar nuna an fi ƙaunar wani."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 02:25-26
  • 2 Tarihi 19:07
  • Korintiyawa 01:11
  • Ayyukan Manzanni 24:27
  • Farawa 41:16
  • Farawa 47:25
  • Farawa 50:05

juyayi, tausayi

Ma'ana

Wannan kalma 'juyayi" ana nufin jin tausayi game da mutane, musamman ga waɗanda suke cikin wahala. Mutum "mai juyayi" yana kula da wasu mutane yana kuma taimakon su.

  • Wannan kalma "juyayi" yawancin lokaci ya ƙunshi lura da mutane, da ɗaukar mataki wajen taimakon su.
  • Littafi Mai Tsarki ya ce Allah mai juyayi ne, wato, yana cike da ƙauna da jinƙai.
  • A cikin wasiƙar Bulus zuwa ga Kolosiyawa ya ce masu su "tufatar da kansu da juyayi." Yana koya masu su lura da mutane kuma su aikata ainihin taimako ga waɗanda suke cikin buƙata.

Shawarwarin Fassara

  • Ma'anar "juyayi" shi ne "jinkai." Wannan furci ma'anarsa "jinƙai" ko "tausayi." Wasu yaruruka wataƙila suna da tasu fassarar da kuma ma'anar.
  • Ga wasu hanyoyin fasara "juyayi" kamar haka, "lura da abu sosai" ko "taimako da tausayi."
  • Wannan kalma "juyayi" za a iya fassara ta haka, "lura tare da taimakawa" ko "sahihiyar ƙauna da tausai."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 01:8-10
  • Hosiya 13:14
  • Yakubu 05:9-11
  • Yonah 04:1-3
  • Markus 01:41
  • Romawa 09:14-16

kãda mai laifi, kayarwa

Ma'ana

Wannan magana "kãda mai laifi " da "kayarwa" ana nufin sharianta mutum ne domin abin da bai yi dai dai ba.

  • Yawancin lokaci "kãda mai laifi" ya haɗa da hukunta wannan mutumin domin abin da yayi da ba dai dai ba.
  • Wani lokaci "kãda wa" yana da ma'ana haka zargin marar laifi ko a sharianta wani da haushi kwarai.
  • Wannan kalma "kayarwa" ana nufin kãda wa ko zargin wani.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da yadda za a yi amfani da shi cikin nassi, za a iya fassara wannan kalma haka "shria'antawa tsawa maitsanani" ko "kushe mutum cikin rashin gaskiya."
  • Wannan furci "kãda shi" za a iya juya shi zuwa "zartar da shari'a cewa wani yana da laifi" ko "a ce dole a hore shi domin zunubinsa."
  • Wannan kalma "kayarwa" za a iya fassara shi haka "shari'antawa da haushi" ko "a furta wani da laifi" ko "hukunci domin laifi."

(Hakanan duba: alƙalai, horo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:20
  • Ayuba 09:29
  • Yahaya 05:24
  • Luka 06:37
  • Matiyu 12:07
  • Littafin Lissafi 17:15-16
  • Zabura 034:22
  • Romawa 05:16

kaffara, yin kaffara

Ma'ana

Kalmar nan "yin kaffara" da "kaffara" ana nuna yadda Allah ya bada hadaya domin biyan hakin zunuban mutane a kuma huce hushin Allah akan zunubi.

  • A lokacin Tsohon Alƙawari, Allah ya bari a yi kaffara na ɗan gajeren lokaci a yi shi domin zunubin Isra'ilawa ta wurin miƙa jinin hadaya, wanda ya ƙunshi yanka dabba.
  • Kamar yadda yake a rubuce cikin Sabon Alƙawari, mutuwar Amasihu akan gicciye ita ce kaɗai gaskiya da kuma kaffara ta din din-dindin domin zunubi.
  • Lokacin da Yesu ya mutu, ya ɗauki hukunci da ya cancanci mutane saboda zunubansu. Ya biya hakin kaffara ta wurin hadayar mutuwarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "kaffara" za a iya fassarata da kalma ko furci mai ma'ana haka, "biya domin" ko "tanada abin biya domin" ko "ayi dalilin da za a gafarta zunuban wani" ko "gyara domin laifi da aka aikata."
  • hanyoyin fassara "kaffara" za su haɗa da waɗannan, "biya" ko "hadaya domin a biya sabili da zunubi" ko "tanada abu domin gaffara."
  • A tabbatar fassarar wannan kalma bai nuna biyan kuɗi ba.

(Hakanan duba: marfi kaffara, yafewa, sasantawa, sulhu, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 43:25-27
  • Ezekiyel 45:18-20
  • Lebitikus 04:20
  • Littafin Lissafi 05:08
  • Littafin Lissafi 28:22

kaito

Ma'ana

Kalma na "kaito" na bayyana mawuyacin halin da ake ciki. Tana kuma bada kashedi da cewar wani zai shiga wata matsala mai zafi ƙwarai.

  • Kalmar "kaito" na zuwa da kashedi zuwa ga mutane da cewa zasu fuskanci mawuyaciyar wahala a matsayin hukunci bisa zunubansu.
  • A wurare da yawa cikin Littafi Mai Tsarki, "kaito" ana maimaita shi, domin musamman a nuna hukunci mai tsanani.
  • Mutumin da yake cewa "kaito na" ko "kaito gare ni" yana kuka ne ya bayyana zafin azabarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, kalmar "kaito" za a iya fassarawa haka "babban baƙinciki" ko "ɓacin rai" ko "masifa" ko "bala'i."
  • Wasu hanyoyin fassara faɗar "kaito ga (sunan birnin)" zasu haɗa da, "Iya irin azabar da zata kasance domin (sunan birni)" ko "Mutanen cikin (sunan birnin) zasu sha tsananin horo" ko "Mutanen nan zasu sha babbar wahala."
  • Faɗar, "kaito na!" ko "kaito a gare ni!" za a iya fassarawa haka "yaya ɓacin raina!" ko "raina ya ɓaci sosai!" ko "yaya tsananin wannan a gare ni!"
  • Faɗar "kaito gare ka" za a iya fassarawa haka "zaka sha wahala sosai" ko "zaka fuskanci azabai masu wahala."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 13:17-18
  • Habakuk 02:12
  • Ishaya 31:1-2
  • Irmiya 45:1-3
  • Yahuda 01:9-11
  • Luka 06:24
  • Luka 17:1-2
  • Matiyu 23:23

karya doka, ana karya doka, an karya doka

Ma'ana

"Karya doka" na ma'anar a karya shari'a ko a keta hakkin wani taliki. "Karya doka" na nufin aikata aikin "karya doka."

  • Karya doka na iya nufin keta ɗabi'a ko shari'ar hukuma ko zunubin da aka yi gãba da wani.
  • Wannan kalma na da dangantaka da kalmomin "zunubi," da "laifi," musamman idan suna dangantaka da rashin biyayya da Allah.
  • Dukkan zunubai karya doka ne gãba da Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, a "karya doka gãba da" za a iya fassarawa haka "yin zunubi gãba da" ko a "karya sharaɗi."
  • Zai iya kasancewa wasu yarurrukan suna da faɗar haka "a gitta layi" da za a iya amfani da shi a fassara "karya doka."
  • Ayi la'akari da yadda ma'anar wannan kalma ta yi dai-dai da nassin dake kewaye da Littafi Mai Tsarki sai kuma a kwatanta ta da kalmomin dake da ma'ana shigen iri ɗaya kamar su "laifi" da "zunubi."

(Hakanan duba: rashin biyayya, lalata, zunubi, laifi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 25:28
  • 2 Tarihi 26:16-18
  • Kolosiyawa 02:13
  • Afisawa 02:01
  • Ezekiyel 15:7-8
  • Romawa 05:17
  • Romawa 05:20-21

kira, ana kira, kirayowa, kirayayye

Ma'ana

Waɗannan maganganu "kira" da "ƙwala kira" hanya ce ta faɗin wani abu da ƙãra ga wani mutum wanda baya kusa. Akwai wasu ma'anan da yawa.

  • A "ƙwala wa wani mutum kira shi ne yin magana da ƙarfi wa wani mutum dake nesa. Za a iya fassara shi neman taimako daga wani, musamman daga Allah.
  • Yawancin lokaci a Littafi Mai Tsarki, "kira" na da ma'anar "umarni" ko "umarnin a zo" ko roƙon a zo."
  • Allah yakan kira mutane su zo gare shi su zama mutanensa. Wannan shi ne "kiransu."
  • Wannan kalma "kirayayye" ana amfani da ita a Littafi Mai Tsarki da ma'anar Allah ya aza ko ya zaɓi mutane su zama 'ya'yansa, su zama bayinsa da masu shelar maganarsa ta ceto ta wurin Yesu.
  • Wannan kalma kuma ana amfani da ita in za a kira mutum da suna. Misali, "Ana ce da shi Yahaya," ma'ana "Ana ce da shi Yahaya" ko "Sunansa Yahaya."
  • Idan an ce "ana kiransa da sunan wani" ma'anar shi ne an ba wani mutum sunan wani mutum. Allah ya ce ya kira mutanensa da sunansa.
  • Ga wani furci daban, "na kira ka da suna" ma'ana Allah ya san sunan mutumin kansa ya kuma zaɓe shi musamman.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalman nan "kira" za a iya fassarata haka ' kiran umarni," wato kiran hakika ne kuma da dalili.
  • Wannan furci "an ƙwala maka kira" za a iya fassarta shi "na roƙe ka taimako" ko "na yi maka addu'a nan da nan."
  • Sa'ad da LIttafi Mai Tsarki ya ce Allah ya "kiraye" mu mu zama bayinsa, za a iya fassara wannan haka, "an zaɓe mu musamman" ko "ya sa mu" mu zama bayinsa.
  • "Dole ka kira sunansa" za a iya juya shi zuwa "dole ka raɗa masa suna."
  • "Ana kiran sunansa" za a iya fassara shi haka, "sunansa" ko "ana kiran sa."
  • "‌Ƙwala kira" za a iya fassara shi haka "faɗi da ƙarfi" ko "yi ihu" ko " faɗa da murya mai ƙarfi." A tabbata fassarar bata nuna kamar mutumin yana fushi ba.
  • Wannan furci "kiran ka" za a iya fassara shi zuwa "dalilin ka" ko "nufin Allah domin ka" ko "aikin Allah musamman domin ka."
  • A "kira bisa sunan Ubangiji" za a iya cewa "nemi Ubangiji ka kuma dogara a gare shi" ko "ka dogara ga Ubangiji ka yi masa biyayya."
  • Ma'anar "kira domin" shi ne "tilasta" ko "roƙo domin" ko "umarta."
  • Wannan furci "ana kiran ku da sunana" za a iya fassara shi haka, "na baku sunana, yana nunawa ku nawa ne."
  • Sa'ad da Allah ya ce, "na kirayeka da suna," za a iya fassara shi haka, "na san sunanka na kuma zaɓe ka."

(Hakanan duba: addu'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 18:24
  • 1 Tasalonikawa 04:07
  • 2 Timoti 01:09
  • Afisawa 04:01
  • Galatiyawa 01:15
  • Matiyu 02:15
  • Filibiyawa 03:14

Kishi

Ma'ana

Kalmar "kishi" na ma'anar wani babban marmarin kiyaye tsarkin zumunci. Yana kuma iya zama wani babban marmarin riƙe mallakar wani abu ko wani taliki.

  • Ana kuma amfani da wannan kalma a bayyana haushin da wani taliki keji game da abokin aurensa wanda ke aikata rashin aminci cikin aurensu.
  • Sa'ad da akayi amfani da kalmar cikin Littafi Mai tsarki, yawanci wannan kalma na nuna babban marmari Allah game da mutanensa su kasance da tsarki basu kuma sami ɗigo ba ta wurin zunubi.
  • Allah kuma yana "kishi" domin sunansa, yana marmarin a ɗauke shi tare da daraja da bangirma.
  • Wata ma'anar kishi kuma ya haɗa da jin haushin cewa wani taliki na ci gaba ko yafi fice. Wannan na kusa da ma'anar "ƙyashi."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "kishi" zai haɗa da "babban jin marmarin kiyaye abu" ko "marmarin mallakewa."
  • Kalmar "kishi" za'a iya fassara ta a matsayin "babban jin marmarin kiyaye abu" ko "marmarin mallakewa."

Sa'ad da ake magana game da Allah, a tabbatar cewa fassara wannan kalma bata bada wata ma'anar ƙi ko gujewa wani ba.

  • A cikin al'amarin cewa mutane na jin haushin ci gaba ko ficen wasu, ana iya amfani da kalmar "ƙyashi." Amma ba za'a yi amfani da Kalmar ba game da Allah.

(Hakanan duba: kishi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 12:20
  • Maimaitawar Shari'a 05:09
  • Fitowa 20:05
  • Yoshuwa 24:19
  • Nahum 01:2-3
  • Romawa 13:13

Krista

Ma'ana

Bayan wasu lokuta da Yesu ya koma sama, mutane suka ƙirƙiro wannan suna "Krista" ma'ana, "mai bin Kristi."

  • A cikin birnin Antakiya ne inda aka fara kiran mabiyan Yesu "Kristoci."
  • Krista mutum ne wanda ya bada gaskiya cewa Yesu ‌Ɗan Allah ne, wanda kuma ya dogara ga Yesu ya cece shi daga zunubansa.
  • A zamanin mu na yau, yawancin lokaci wannan kalma "Krista" ana amfani da ita ga wanda ya yarda da addin Krista, amma fa lallai baya bin Yesu. Wannan ba shi ne ma'anar "Krista" a Littafi Mai Tsarki ba.
  • Saboda kalmar nan "Krista" a cikin Littafi Mai Tsarki kullum ana nufin mutum ne da hakika ya bada gaskiya ga Yesu, sai Krista ana kiransa kuma "mai bada gaskiya."

Shawarwarin Fassara

  • Wannan kalma za a iya fassarata haka "Kristi- da mai binsa" ko "mai bin Kristi."
  • A tabbatar an fassara wannan kalma dabam da kalmomin da ake amfani da su domin almajiri ko manzo.
  • A yi lura a fassara wannan kalma da kalmar da zata nuna kowanne mutum wanda ya bada gaskiya ga Yesu, ba wasu ƙungiya kawai ba,
  • Kuma ayi la'akari da yadda aka fasara wannan kalma a cikin Littafi Mai Tsarki na wani yare a ƙasar.

(Hakanan duba: Antiyok, Almasihu, ikilisiya, almajiri, gaskatawa, Yesu, Ɗan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 06:7-8
  • 1 Bitrus 04:16
  • Ayyukan Manzanni 11:26
  • Ayyukan Manzanni 26:28

Kristi, Almasihu

Ma'ana

Waɗannan kalmomi "Almasihu" da "Kristi" ma'anarsu shi ne "Keɓaɓɓe ‌Ɗaya" kuma ana nufin Yesu,‌ Ɗan Allah.

  • Dukka biyu "Almasihu" da "Kristi" anyi amfani da su game da ‌Ɗan Allah ne, wanda Allah Uba ya zaɓa yayi mulki akan mutanensa, ya cece su daga zunubansu daga kuma mutuwa.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, annabawa sun rubuta anabtai akan Almasihu shekaru ɗari bisa ɗari kafin ya zo duniya.
  • Yawancin lokaci wannan kalma "‌keɓaɓɓe ‌(ɗaya)" ana amfani da shi a Tsohon Alƙawari game da Almasihu wanda zai zo.
  • Yesu ya cika waɗannan anabtai da yawa ya kuma yi ayyukan al'ajibai da yawa da suka tabbatar shi ne Almasihu; sauran anabtai za su cika sa'ad da zai sake dawowa.
  • Wannan kalma "Kristi" yawancin lokaci ana amfani da shi domin a nuna matsayinsa, kamar a haka "shi ne Kristi" da kuma "Kristi Yesu."
  • Wannan sunan girma "Kristi" aka zo ana ta amfani da shi har aka haɗa da sunansa "Yesu Kristi."

Shawarwarin Fassara

  • Wannan suna za a iya fassara shi da wannan ma'ana, "‌Keɓaɓɓe ‌Ɗaya" ko "Keɓaɓɓe Mai Ceto Na Allah."
  • Yaruruka da yawa sun sifanta kuma suna amfani da tasu kalmar da ta yi kama da "Kristi" ko "Almasihu."

(Hakanan duba: ɗan Allah, Dauda, Yesu, shafaffe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 05:1-3
  • Ayyukan Manzanni 02:35
  • Ayyukan Manzanni 05:40-42
  • Yahaya 01:40-42
  • Yahaya 03:27-28
  • Yahaya 04:25
  • Luka 02:10-12
  • Matiyu 01:16

‌ƙaddara, an ƙaddara

Ma'ana

Wannan kalma "ƙaddara" manufarta shi ne yanke shari'a ko shiryawa cewa wani abu zai faru.

  • Wannan magana masamman akan Allah ne mai ƙaddara wa mutane su karɓi rai madawwami."
  • Wani lokaci kalmar nan "rigasaninsa" ana amfani da ita wanda ma'anarta ita ma yanke shari'a kafin abu ya faru ne.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma "ƙaddara" za a iya fassarawa haka, "yanke shari'a kafin" ko "yanke shari'a tun gabannin lokaci."
  • Wannan kalma "ƙaddara" za a iya fassarawa haka, "yanke shari'a tun dã dã" ko "shirin da aka yi tun gabannin lokaci." ko "yanke shari'a tun kafin."
  • Furci kamar haka "an ƙaddara mu" za a iya fassarawa haka, "ya yanke shari'a tun dã dã cewa mu" ko "ya rigaya ya yanke shari'a tun gabannin lokaci cewa mu."
  • A yi lura domin fassarar wannan kalmar ta bambanta da fassarar wannan kalmar "rigasani."

(Hakanan duba: rigasani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 02:6-7

ƙaron mur

Ma'ana

Ƙaron Mur wani irin mai ne ko kayan ƙanshi da ake yinsa daga ƙaron itacen mur dake yaɗuwa a sa a Afrika da Asiya. Yana kama da turaren ƙaron frank.

  • Ana amfani da mur domin ayi kayan ƙamshi, turare, da magani da kuma shirya gawawwaki domin biznewa.
  • Mur yana ɗaya daga cikin kyautai da masana suka ba Yesu da aka haife shi.
  • An miƙa wa Yesu ruwan inabi gauraye da mur don a sauƙaƙe wa Yesu zafin azaba da aka giciye shi.

(Hakanan duba: turaren ƙaron frank, masana)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 30:22-25
  • Farawa 37:25-26
  • Yahaya 11:1-2
  • Markus 15:23
  • Matiyu 02:11-12

‌Ƙasar Alƙawari

Ma'ana

Wannan furci ‌Ƙasar Alƙawari yana cikin labarun Littafi Mai Tsarki amma ba cikin nassin Littafi Mai Tsarki yake ba. Wata hanya ce ta bayyana ƙasar Kan'ana da Allah ya rigaya ya alƙawarta wa Ibrahim da zuriyarsa.

  • lokacin da Ibrahim yake zaune a cikin birnin Ur, Allah ya umarce shi ya tafi ya zauna cikin ƙasar Kan'ana. Shi da zuriyarsa, Isra'ilawa sun zauna a can shekaru da yawa.
  • Lokacin da aka yi fari, wannan babbar yunwa ta sa babu abinci a Kan'ana, Isra'ilawa suka tafi zuwa Masar.
  • Bayan shekaru ɗari huɗu, Allah ya kuɓutar da Isra'ilawa daga bauta a Masar ya kuma sake dawo da su Kan'ana, ƙasar da Allah ya yi alƙawari zai basu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "‌Ƙ‌asar Alƙawari" za a iya fassarawa haka, "ƙasar da Allah yace zai bayar ga Ibrahim" ko "ƙasar da Allah ya alƙawarta wa Ibrahim" ko "ƙasar da Allah ya alƙawarta wa mutanensa" ko "ƙasar Kan'anan."
  • A cikin nassin Littafi Mai Tsarki, wannan sunan wuri an faɗe shi haka, "ƙasar da Allah ya alƙawarta."

(Hakanan duba: Kan'ana, alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 08:1-2
  • Ezekiyel 07:26-27

ƙauna, mai ƙauna, ƙaunatacce

Ma'ana

Idan kana ƙaunar wani za ka lura da mutumin nan za ka yi abin da zai amfane shi. ‌"Ƙauna" tana da ma'ana da yawa wasu yarurruka mai yiwuwa su yi amfani da kalmomi da bam domin fassara ta:

  1. Irin ƙauna da ta zo daga Allah na kulawa da lafiyar wasu ko dama mai kulawar bai amfana ba. Irin wannan ƙauna tana lura da wasu, ko dama me suka yi. Allah kansa ƙauna ne shi ne tushen ƙauna mai gaskiya.
  • Yesu ya nuna irin wannan ƙaunar ta wurin bada ransa domin ya yi ceto daga zunubi da mutuwa. Ya kuma koya wa masu binsa su ƙaunaci mutane irin yadda ya yi.
  • Sa'ad da mutane suka aunaci wasu da irin wannan ƙauna, suna nuna son ci gaban wasu. Irin wannan ƙauna takan haɗa duk da gafarta wa mutane.
  • A cikin ULT, kalmar nan "ƙauna" na nufin sadakakkiyar ƙauna, sai ko idan Fannin Taimako don Fassara ya bada wata ma'ana dabam.
  • Wasu wurare a cikin Sabon Alƙawari an yi magana a kan ƙaunar 'yan'uwa, ko ƙaunar aboki ko ɗan'uwa cikin iyali.
  1. Wannan kalma tana magana ne a kan irin ƙaunar da mutane suka saba yi tsakanin abokai ko 'yan'uwa na jiki.
  • Za a iya amfani kuma da kalmar a haka, "Suna ƙaunar su zauna a mafifitan kujeru a wajen biki." Ma'anar wannan shi ne "sun fi so sosai" ko "suna da marmari" su yi haka.
  1. Wannan kalma "ƙauna" tana magana kuma a kan irin soyayyar dake tsakanin namiji da mace.
  2. A wannan misali da aka ce "Na ƙaunaci Yakubu, amma na tsani Isuwa," wannan kalmar "ƙauna" na nufin Allah ya zaɓi Yakubu ya kasance cikin dangantakar alƙawarinsa. Za a iya fassara wannan ya zama "zaɓe." Koda yake Allah ya albarkaci Isuwa shi ma, amma ba a bashi zarafin kasancewa cikin alƙawarin ba. Wannan kalma "na tsani" an yi amfani ne da ita ne matsayin "ƙi" ko "ba a zaɓa ba."

Shawarwarin Fassara:

  • Sai ko in an faɗi wani abu daban a FanninTaimako don Fassara, kalmar nan "ƙauna" a cikin ULT na nufin irin ƙauna ta sadakarwa dake zuwa daga Allah.
  • Wasu yarurruka watakila suna da wata kalma ta musamman domin irin wannan ƙauna marar son kai da sadakarwa da Allah ke da ita. Wasu hanyoyi na fassara wannan sune, "himma, aminci, kulawa" ko "kulawa babu son kai" ko ƙauna daga Allah." A tabbata kalmar da aka yi amfani da ita a fassara ƙaunar Allah ta haɗa da sadaukar da abin da wani ke so don wasu su ribatu da ƙaunar wasu koda mene ne suka yi.
  • Wasu lokutan wannan kalmar "ƙauna " da Turanci takan nuna kulawa mai ƙarfi da mutane suke da shi domin abokai da 'ya'uwa na jiki. Wasu yarurruka mai yiwuwa za su fassara wannan kalma guda ko maganganu masu ma'ana haka "so da yawa ko "kulawa domin" ko "soyayya mai ƙarfi domin."
  • A cikin rubutu inda aka yi amfani da wannan kalma "ƙauna" don a nuna zafin son wani, za a iya fassara shi haka "an fi so fiye da" ko "ana so ƙwarai" ko "ana da marmari sosai."
  • Wasu yarurrukan watakila suna da wasu kalmomi daban domin ƙauna irin ta jiki dake tsakanin miji da mata.
  • Yarurruka da yawa suna faɗin "ƙauna' aba ce da ake nuna ta. Misali, zasu fassara waɗannan "ƙauna tana da haƙuri", ƙauna tana da kirki" zuwa "idan wani mutum ya ƙaunaci wani, yana haƙurcewa da shi ya yi masa alheri kuma."

Wuraren da ake samunsa a LIttafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 13:07
  • 1 Yahaya 03:02
  • 1 Tasalonikawa 04:10
  • Galatiyawa 05:23
  • Farawa 29:18
  • Ishaya 56:06
  • Irmiya 02:02
  • Yahaya 03:16
  • Matiyu10:37
  • Nehemiya 09:32-34
  • Filibiyawa 01:09
  • Waƙar Suleman 01:02

ƙaunatacce, ƙaunatattu

Ma'ana

Wannan kalma "ƙaunatacce" magana ce ta soyayya da yake nuna wanda ake ƙauna da kuma kwarjini ga wani daban.

  • Kalman nan "ƙaunatacce" ma'anarta shi ne "wani wanda yake ƙaunatacce" ko "(wanda ake) ƙauna."
  • Allah ya ambaci Yesu "ƙaunataccen ‌Ɗansa ne."
  • A cikin wasiƙunsu zuwa ga ikilisiyoyin Kirista, yawancin lokaci manzanni sukan ce da 'yan'uwansu masu bada gaskiya "ƙaunatattu."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalmar za a iya fassarata a ce "ƙauna" ko "ƙaunataccen nan" ko "wanda an ƙaunace shi" ko "mai daraja."
  • Idan ana magana akan aboki na kurkusa, za a iya fassara wannan haka "abokina mai daraja" ko "abokina amini." A Turance za a ce, "mai daraja abokina, Bulus" ko "Bulus wanda abokina ne mai daraja." Wasu yare zai fi masu sauƙi su sa shi a wani jerin.
  • Ayi lura kalmar nan "ƙaunatacce" ta zo ne daga magana game da ƙaunar Allah, wanda ba sai da dalili ba, babu son kai, kuma hadaya ce.

(Hakanan duba: ƙauna)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:14
  • 1 Yahaya 03:02
  • 1 Yahaya 04:07
  • Markus 01:11
  • Markus 12:06
  • Wahayin Yahaya 20:09
  • Romawa 16:08
  • Waƙar Suleman 01:14

la'ana, la'ananne

Ma'ana

Wannan kalma "la'ana" fasarar ta shi ne a sa wani abu marar daɗi ya faru da wani mutum ko abin da ake la'antarwa."

  • La'ana zai iya zama maganar da zai kawo abin cutarwa ya faru da wani mutum ko wani abu.
  • Idan an la'anci wani mutum za a faɗi mugayen abubuwa da ake so su faru da shi.
  • Zai iya zama horo ko abubuwa marasa kyau da wani ya sa suka abko kan wani mutum.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana za a iya fassara ta zuwa "sa wani rashin jin daɗi ya faru" ko "a furta cewa wani abu marar daɗi zai faru da" ko "a yi rantsuwar wani mugun abu zai faru da."
  • A game da Allah ya kan aiko la'anu akan mutanensa marasa biyayya, za a iya fassara shi haka, "hukuntawa tawurin barin abubuwa marasa daɗi su faru.
  • Wannan kalma "la'ananne" idan aka yi amfani da shi game da mutane za a iya fassara shi haka,

(Hakanan duba: mai albarka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 14:24-26
  • 2 Bitrus 02:12-14
  • Galatiyawa 03:10
  • Galatiyawa 03:14
  • Farawa 03:14
  • Farawa 03:17
  • Yakubu 03:10
  • Littafin Lissafi 22:06
  • Zabura 109:28

labari mai kyau, bishara

Ma'ana

Kalmar nan "bishara" ma'anarta ita ce "labari mai kyau" tana kuma nufin saƙo ne ko wani aike da ke faɗawa mutane abin da zai amfane su ya kuma sa su murna.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, wanan kalmar har kullum tana magana ne akan aikin ceto na Allah domin mutane ta wurin hadayar Yesu a kan gicciye.
  • A cikin mafi yawa daga fassarorin Littafi Mai Tsarki na turanci akan fi fassara ta da "bishara" hakan nan akan mori kalmar "bisharar Yesu Kristi," "bisharar Allah" da kuma "bisharar mulkin."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyi mabambanta na fassarar wanan kalmar sun haɗa da, "saƙo mai kyau" ko "sanarwa mai kyau" ko "saƙon Allah domin ceto" ko "abu mai kyau da Allah ke koyarwa game da Yesu."
  • Ya danganta ga wurin, hanyoyin fassara wanan kalma, "labari mai daɗi na" sun haɗa da, "saƙo mai kyau game da" ko "labari mai daɗi game da" ko "saƙo mai kyau daga" ko "abu mai kyau da Allah ke faɗa mana game da" ko "abin da Allah ke faɗi game da yadda ya ceci mutane."

(Hakanan duba: mulki, hadaya, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tassalonikawa 01:5
  • Ayyukan Manzanni 08:25
  • Kolosiyawa 01:23
  • Galatiyawa 01:6
  • Luka 08:1-3
  • Markus 01:14
  • Filibiyawa 02:22
  • Romawa 01:3

Lahira

Ma'ana

Kalmar nan "Lahira" an more su a cikin Littafi Mai Tsarki domin ayi batun mutuwa da kuma wurin da rayukan mutane zasu bayan sun mutu. Ma'anarsu ɗaya ce.

  • Kalmar "Lahira" a Ibraniyanci an fi amfani da ita a cikin Tsohon Alƙawari domin a baiyana inda matattu suke.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kalmar Girkanci "Hades" tana magana ne akan wurin da rayukan mutanen da suka tayar wa Allah za su kasance. A kan ce waɗanan rayukan za'a tura su can "ƙarƙas" zuwa Hades. A waɗansu lokuta wanan ya saɓawa tafiya zuwa "sama" inda rayukan mutanen da suka yi biyayya ga Allah za su kasance.
  • Kalmar nan "Hades" tattare take dakalmar "mutuwa" a cikin littafin Wahayin Yahaya. A lokuta na ƙarshe, da Hades da mutuwa duk za'a zuba su cikin tafki nija wuta, wadda ita ce jahannama.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "Lahira" a cikin Tsohon Alƙawari za'a iya fassara ta da "wuri na mutuwa" ko "wuri na rayukan matattu." Waɗansu Fasssarori na fassara shi da "rami" ko "mutuwa" ya danganta dai ga wurin.
  • Kalmar "Hades" a Sabon Alƙawari za'a iya fassara ta da wurin da rayukan marasa bada gaskiya za su zauna" ko wuri na azaba ga matattu" ko wuri na mutanen da basu bada gaskiya ba."
  • Waɗansu fassarori suna moron kalmomin "Lahira" da "Hades" suna rubuta su a matsayin rami bisa ga furcin harshensu.
  • Za'a iya ƙarawaɗansu 'yan harufa ga kowanen su domin yin bayani a kan su, misali na yin haka su ne "Lahira, wurin da matattu suke" da "Hades kuma wuri ne na mutuwa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 02:31
  • Farawa 44:29
  • Yona 02:2
  • Luka 10:15
  • Luka 16:23
  • Matiyu 11:23
  • Matiyu 16:18
  • Wahayin Yahaya 01:18

laifi, laifofi

Ma'ana

Kalmar nan "laifi" kalma ce da ta yi kama da kalmar "zunubi" amma zata iya bambanta da sanin yin zunubi da gangan ko wani babban aikin mugunta.

  • Kalmar nan "laifi" ma'anarta mai sauƙi ita ce murɗe ko kuma (gulɓata shari'a) Tana nufin yin wani abu na rashin adalci.
  • Za'a iya baiyana laifi da cewa yin wani abu ne na cutarwa da gangan, ko yin wani abu da ya saɓawa sauran mutane.
  • Waɗansu ma'anonin laifi sun haɗa da "fanɗarewa"ko "zamba" waɗanda duk suke nufin zunubi ne mai muni.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "laifi" za'a iya fassara ta da aikin "mugunta" ko "aikin kangara" ko "aikin cutarwa."
  • A sau da yawa laifi kan baiyana a wuri ɗaya da kalmar "zunubi" da "laifofi" domin haka yana da muhimmanci a sami mabambantan hanyoyi na fassara waɗannan kalmomi.

(Hakanan duba: zunubi, saɓawa, aikata zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Daniyel 09:13
  • Fitowa 34:5-7
  • Farawa 15:14-16
  • Farawa 44:16
  • Habakuk 02:12
  • Matiyu 13:41
  • Matiyu 23:27-28
  • Mika 03:10

laifi, yin laifi

Ma'ana

Kalmar nan "laifi" tana nufin yin wani abu dake na zunubi ko kuma taka doka.

  • A zama "mai laifi" na nufin ayi wani abu ba bisa tsarin rayuwa ba, wato keta dokar Allah.
  • Kishiyar kalmar "laifi" ita ce "mara laifi."

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu harsuna na iya fassara "laifi" da "ladan zunubi" ko kuma "ƙirga zunubai."
  • Hanyoyin fassara ga "zama mai laifi" sun haɗa da faɗar "kalmar da ta zama laifi" ko kuma "yin wani abu wanda bai dace ba" ko kuma "aikata zunubi."

(Hakanan duba: mara laifi, laifi na zuci, hukunci, zunubi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 28: 36-38
  • Ishaya 06:7
  • Yakubu 02:10-11
  • Yahaya 19: 4
  • Yona 01:14

lamiri

Ma'ana

Lamiri shi ne sashen nan na tunani cikin mutum wanda ta gareshi ne Allah ke sanar wa mutu cewa yana yin abin da yake zunubi.

  • Allah ya ba mutane lamiri domin ya taimake su sanin abin dake daidai da abin daba daidai ba.
  • Mutumin da yake biyayya da Allah akan ce yana da "tsarki" ko "marar aibu" ko "tsabtar lamiri."
  • Idan mutum yana da "tsabtar lamiri" wato ba shi da ɓoyayyen zunubi.
  • Idan wani mutum ya ƙyale lamirinsa kuma baya jin kashewa in yayi zunubi, wato lamirinsa ya mutu baya jin zafin laifi kuma. Littafi Mai Tsarki ya kira wannan lamirin da aka yi wa "lalas," wanda aka "zana" kamar da wutar ƙarfe. Irin wannan lamiri ana kiransa "marar jin motsawa" kuma "ƙazamtacce" ne.
  • Ga wasu hanyoyin fassara wannan kalma kuma, "mai bida rai na ciki" ko "tunanin rayyuwa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 01:19
  • 1 Timoti 03:09
  • 2 Korintiyawa 05:11
  • 2 Timoti 01:03
  • Romawa 09:01
  • Titus 01:15-16

Maɗaukaki

Ma'ana

Wannan furci "Maɗaukaki" sunan naɗi ne na Allah. Ana nufin girmansa da ikonsa.

  • Ma'anar wannan furci ya yi kama da "Marar Takwara" ko Mafifici Dukka."
  • Wannan kalma "sama" a cikin sunan nan ba ana nufin tsayin jiki ne ba ko nisa. Ana nufin girmansa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan furci za a iya fassara shi haka "Allah na Sama" ko "Mai Dukka" ko "Allah Maɗaukaki" ko "Babban nan" ko "Mafificin nan" ko "Allah" wanda Ya Fi Kowa."
  • Idan an yi amfani da "na sama" ba wai ana nufin tsayin jiki ko dogo ba.

(Hakanan duba: Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 07:47-50
  • Ayyukan Manzanni 16:16-18
  • Daniyel 04:17-18
  • Maimaitawar Shari'a 32:7-8
  • Farawa 14:17-18
  • Ibraniyawa 07:1-3
  • Hosiya 07:16
  • Littafin Makoki 03:35
  • Luka 01:32

maganar Allah, maganganun Allah, maganar Yahweh, maganar Ubangiji, maganar gaskiya, nassi, nassosi

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "maganar Allah" na manufar kowanne abin da Allah ya faɗa wa mutane. Wannan ya haɗa da abin da ya faɗi da rubutattun saƙonni. Ana ce da Yesu "Maganar Allah."

  • Kalmar "nassosi" na nufin "rubuce-rubuce." An yi amfani da su ne a Sabon Alƙawari tana nufin nassosin Ibraniyawa, wato Tsohon Alƙawari . ̀Waɗannan rubuce-rubucen saƙonnin Allah ne da ya faɗi wa mutane su rubuta domin mutanen dake zuwa daga baya su iya karantawa.
  • Wani kalma makamancin haka "maganar Yahweh" da "maganar Ubangiji" na nuna saƙo na musamman daga Allah da aka bayar ga wani annabi ko wani mutum a cikin Littafi Mai Tsarki.
  • Wasu lokutai wannan kalmar na bayyana haka "magana" ko "magana ta" ko "maganarka" (sa'ad da kake magana game da maganar Allah).
  • A cikin Sabon Alƙawari, ana ce da Yesu "Kalmar" da kuma "Kalmar Allah." Waɗannan laƙaban na manufar cewa Yesu ya bayyana wane ne Allah, domin shi da kansa Allah ne.

Haka kuma kalmar "maganar gaskiya" wata hanya ce ta nuna "maganar Allah," wadda ita ce saƙonsa ko koyarwarsa. Ba wai kawai magana ɗaya take nufi ba.

  • Maganar gaskiya ta Allah ta ƙunshi dukkan abubuwan da Allah ya koya wa mutane game da kansa, hallitarsa, da kuma shirinsa na ceto ta wurin Yesu.
  • Wannan ya tabbatar da cewar abin da Allah ya faɗi mana gaskiya ne, amintacce, tabbas kuma.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara wannan kalma sun haɗa da "saƙon Yahweh" ko "saƙon Allah" ko "koyarwa daga Allah."
  • A wasu yarurrukan zaifi kyau a rubuta wannan kalma a matsayin jimla kuma ace "maganganun Allah" ko "maganganun Yahweh."
  • Faɗar "maganar Yahweh ta zo" yawanci ana amfani da shi a gabatar da wani abin da Allah ya cewa annanbawansa ko mutaƒnensa. Za a iya fassara wannan a matsayin "Yahweh ne ya faɗi wannan saƙon" ko "Yahweh ne ya faɗi waɗannan maganganu."
  • Kalmar "nassi" ko "nassosi" za a iya fassarawa haka "rubuce-rubuce" ko "rubutaccen saƙo daga Allah." A fassara wannan kalma daban da fassarar "magana."
  • Sa'ad da "magana" ta afku ita kaɗai kuma ana nufin maganar Allah, za a iya fassarawa a matsƒayin "saƙon" ko "maganar Allah" ko "koyarwar." Sai kuma a duba kwatancin fassara da aka shawarta a sama.
  • Sa'ad da Littafi Mai Tsarki ya yi nufin Yesu a matsayin "maganar," za a iya fassara wannan a matsayin "saƙon" ko "gaskiyar."
  • "Maganar gaskiya" za a iya fassarawa haka "saƙon Allah na gaskiya" ko "maganar Allah wadda ke gaskiya."
  • Yana da muhimmanci a fassarar wannan kalma a haɗa da ma'anar kasancewa gaskiya.

(Hakanan duba: annabi, gaskiya, magana, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 15:01
  • 1 Sarakuna 13:01
  • Irmiya 36:1-3
  • Luka 08:11
  • Yahaya 05:39
  • Ayyukan Manzanni 06:02
  • Ayyukan Manzanni 12:24
  • Romawa 01:02
  • 2 Korintiyawa 06:07
  • Afisawa 01:13
  • 2 Timoti 03:16
  • Yakubu 01:18
  • Yakubu 02:8-9

mai adalci, adalci, marar adalci, rashin adalci, sahihi, sahihanci

Ma'ana

kalmar "adalci" na nuna yadda cikakkiyen alherin Allah, amincinsa, gaskiyarsa, da ƙauna. Yadda waɗannan ɗabi'un sun sa Allah ya zama "mai adalci." Domin Allah mai adalci ne, dole ya kayar da zunubi.

  • Kalmomin nan na bayyana mutum wanda ke biyayya da Allah kuma yana aikata abu mai dai-dai. Amma saboda dukkan mutane sun yi zunubi, babu wani sai Allah kaɗai cikakken mai adalci.
  • Ga misalai cikin Littafi Mai Tsarki na mutanen da aka ce da su masu "adalci" Nuhu, Ayuba, Ibrahim, Zakariya, da kuma Elizabet.
  • Yayin da mutane suka dogara ga Yesu don ya cece su, Allah na tsarkake su daga zunubansu sai ya kuma furta su masu adalci saboda adalcin Yesu.

Kalmar "marar adalci" na manufar rayuwar zunubi da gurɓatacciyar rayuwa. "Rashin adalci" zunubi ne ko yanayin zaman rayuwa ta zunubi.

  • Waɗannan kalmomi na nuna rayuwa dake ta rashin biyayya ga koyarwar Allah da dokokinsa.
  • Mutane marasa adalci tunaninsu da ayyukansu gurɓatattu ne.
  • Wani lokacin "marasa adalci" na nuna mutane ne waɗanda basu gaskanta da Yesu ba.

Kalmar "mai gaskiya" da "aikin gaskiya" na bayyana ayyuka ne da ya yi dai-dai da dokokin Allah.

  • Wasu ma'anar kalmar kuwa kamar a ce mutum ya tashi ya miƙe tsaye yana fuskantar gaba.
  • Mutumin dake "mai gaskiya" wannan baya aikata wani abin da ya saɓa wa dokoki da ka'idojin Allah ko ya yi abin dake gãba da nufinsa.
  • Kalmomi kamar "mutunci" da "adalci" na da ma'ana kusan ɗaya kuma wani lokacin ana amfani da su a faɗi abu ɗaya.

Shawarwarin Fassara:

  • Sa'ad da ake kwatanta Allah, kalmar "adali" za a iya fassarawa haka "cikakken nagarta da barata" ko "aikata abin da ke dai-dai koyaushe."
  • "Adalcin" Allah za a iya fassarawa haka "cikakken aminci da nagarta."
  • Sa'ad da ake kwatanta mutanen dake biyayya da Allah, kalmar "adali" za a iya fassarawa "nagarrtaccen hali" ko "kamili" ko "zaman rayuwar gamsar Allah."
  • Faɗar "adali" za a iya fassarawa haka "adalan mutane" ko "mutane masu tsoron Allah."
  • Ya danganta da nassin, "adalci" za a iya fassarawa da kalma ko faɗar da ke ma'anar "nagarta" ko "zama cikacce a gaban Allah" ko "aiki cikin hanya mai kyau ta wurin biyayya da Allah" ko "yin abu dai-dai sosai."
  • Wasu lokuta "adalai" ana amfani da shi a misali kuma da nufin "mutanen da suke tsammani su nagari ne" ko "mutanen da suke ganin su masu adalci ne."
  • " Kalmar "marar adalci" za a fassara a taƙaice "wanda bai da adalci."
  • Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara wannan zasu haɗa da "miyagu" ko "ƙazantattu" ko "mutanen da suka yiwa Allah tawaye" ko "masu zunubi."
  • Faɗar "marasa adalci" za a iya fassarawa haka "mutane marasa adalci."
  • Kalmar "rashin adalci" za a iya fassarawa haka "zunubi" ko "miyagun tinane-tinane da ayyuka" ko "mugunta."
  • Idan mai yiwuwa ne, zai fi kyau a fassara wannan a hanyar da zata nuna dangantakar ta da "adalai, adalci."
  • Hanyoyin da za a fassara "sahihi" zai haɗa da "aikata dai-dai" ko "wanda ke aikata dai-dai" ko "bin shari'un Allah" ko "biyayya da Allah" ko "tafiyar da kai ta hanyar dake dai-dai."
  • Kalmar "sahihanci" za a iya fassarawa haka "halin tsarki" ko "halin tsabtar rai" ko "sahihin hali."
  • Faɗar "sahihai" za a iya fassarawa haka "mutanen da suke sahihai" ko "sahihan mutane."

(Hakanan duba: mugunta, aminci, mai kyau, mai tsarki, mutunci, dai-dai, doka, biyayya, mai tsabta, mai adalci, zunubi, abin da ya saɓawa doka)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 19:16
  • Ayuba 01:08
  • Zabura 037:30
  • Zabura 049:14
  • Zabura 107:42
  • Wakar Suleman 12:10-11
  • Ishaya 48:1-2
  • Ezekiyel 33:13
  • Malakai 02:06
  • Matiyu 06:01
  • Ayyukan Manzanni 03:13-14
  • Romawa 01:29-31
  • 1 Korintiyawa 06:09
  • Galatiyawa 03:07
  • Kolosiyawa 03:25
  • 2 Tasalonikawa 02:10
  • 2 Timoti 03:16
  • 1 Bitrus 03:18-20
  • 1 Yahaya 01:09
  • 1 Yahaya 05:16-17

mai bishara, masu bishara

Ma'ana

"Mai bishara" mutum ne da ke faɗawa waɗansu labari mai daɗi game da Yesu Kristi.

  • Ma;anar kalmar nan "mai bishara" a cikin sauƙi ita ce "wani da ke wa'azin bishara"
  • Yesu ya aiki manzanninsawaje su yaɗa bishara game da yadda za'a zama 'ya'yan mulkin Allah ta wurin dogara ga Yesu da kuma hadayarsa sabo da zunubi.
  • Dukkan Krista an gargaɗe su da su yaɗa bishara.
  • Waɗansu Krista a basu wata baiwa ta musamman domin isar da bishara ga waɗansu yadda ya kamata. Waɗannan mutanen an ce suna da baiwar wa'azantarwa kuma ana kiransu "masu bishara."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "mai bishara" Za'a iya fassara ta da Mutum mai wa'azin bishara" ko "mai koyar da bishara" ko "mutum mai shelar bishara (game da Yesu)" ko "ɗan shelar bishara."

(Hakanan duba: bishara, ruhu, baiwa)

Wuraren da ake samusa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Timoti 04:5
  • Afisawa 04:11-13

Mai ceto, mai ceto

Ma'ana

Kalmar "mai ceto" na nufin mutum wanda ke cetowa ko mai kuɓutar da wasu daga azaba. Yana iya kuma zama wani wanda ke bada karfi ga wasu ko ya yi masu tanadi.

  • A Tsohon Alƙawari, ana ce da Allah Mai ceton Isra'ila domin yana kuɓutar da su daga maƙiyansu, ya basu karfi, ya kuma tanada masu da duk abin da suke bukata na zaman gari.
  • A Sabon Alƙawari, "Mai ceto" ana amfani da shi domin bayyana Yesu Almasihu a matsayin Mai ceton mutane daga hukunci na har abada daga zunubansu. Yana kuma kuɓutar da su daga ikon zunubi dake tafiyar da rayuwarsu.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan mai yiwuwa ne "Mai ceto"za a fassara da kalmar dake dangantaka da kalmomin "samun ceto" ko "ceto."
  • Hanyoyin fassara wannan kalma zasu haɗa da "Wanda ke ceto" ko "Allah, wanda kee ceto" ko "wanda ke kuɓutarwa daga haɗari" ko "wanda ke cafkowa daga maƙiya" ko "Yesu, wanda ya cafko (mutane) daga zunubi."

(Hakanan duba: kuɓuta, Yesu, ceto, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 04:10
  • 2 Bitrus 02:20
  • Ayyukan Manzanni 05:29-32
  • Ishaya 60:15-16
  • Luka 01:47
  • Zabura 106:19-21

mai gãba da Almasihu, masu gãba da Almasihu

Ma'ana

Wannan kalma "mai gãba da Almasihu" fassararta mutum ko koyarwa dake gãba da Yesu Almasihu da aikinsa. Akwai masu gãba da Almasihu da yawa a cikin duniya.

  • Manzo Yahaya ya rubuta cewa mutum zai zama mai gãba da Almasihu idan ya ruɗi mutane yana cewa Yesu ba shi ne Almasihu ba, ko kuma ya yi musu cewa Yesu ba Allah ba ko ya ce Yesu mutum ne kawai.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar cewa akwai ruhohi da yawa a duniya dake mai gãba da Almasihu suna kuma tsayayya da aikin Yesu.
  • Littafin Wahayin Yahaya a cikin Sabon Alƙawari ya ce za ayi wani mutum da ake kira "mai gãba da Almasihu" wanda za a bayyana shi a ƙarshen zamani. Wannan mutum zai yi ƙoƙarin hallaka mutanen Allah, amma Yesu zai ci nasara a kansa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara wannan kalma shi ne, "mai tsayayya da Almasihu" ko "maƙiyin Almasihu" ko "mutumin dake gãba da Almasihu."
  • Wannan magana, "ruhun mai gãba da Almasihu" za a iya fassara shi haka, "ruhun dake gãba da Almasihu." ko "wani" dake koyar da ƙarya game da Almasihu."
  • Sai kuma ayi la'akari da yadda aka fassara wannan kalma a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki a yaren garin ko ƙasar.

(Hakanan duba: Almasihu, bayyana, tsanani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:18
  • 1 Yahaya 04:03
  • 2 Yahaya 01:07

mai hikima, hikima

Ma'ana

Kalmar "hikima" na bayyana wani ne da ya fahimci abin dake dai-dai na gari abin yi ya kuma aikata. "Hikima" fahimta da kuma aikata abin da ke gaskiya ne da kuma abin da ke dai-dai.

  • Zama mai hikima ya ƙunshi ɗaukar matakai, musamman zaɓen a aikata abin da zai farantawa Allah rai.
  • A Littafi Mai Tsarki, kalmar "hikimar duniya" ana amfani da ita a bayyana abin da mutanen duniya ke tunanin shi ne hikima, amma alhali kuwa wawanci ne.
  • Mutane na zama masu hikima ta wurin sauraron Allah su kuma aikata nufinsa cikin biyayya.
  • Mutum mai hikima zai nuna 'ya'yan Ruhaniya a cikin rayuwarsa, kamar farinciki, nagarta, ƙauna da hakuri.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, wasu hanyoyin fassara "mai hikima" zasu haɗa da "biyayya ga Allah" ko "hankali da biyayya" ko "tsoron Allah."
  • "Hikima" za a iya fassarata da kalma ko faɗar dake da ma'anar "rayuwar hikima" ko "rayuwar hankali da biyayya" ko "nagartaccen hukunci."
  • Zaifi kyau a fassara "mai hikima" da "hikima" ta yadda zasu kasance kalmomi daban da wasu kalmomi masu muhimmanci kamar su adali ko mai biyayya.

(Hakanan duba: yi biyayya, 'ya'yan itace)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:03
  • Kolosiyawa 03:15-17
  • Fitowa 31:06
  • Farawa 03:06
  • Ishaya 19:12
  • Irmiya 18:18
  • Matiyu 07:24

Mai Iko Dukka

Ma'ana

Wannan kalma "Mai Iko Dukka" yana nufin "mai dukkan ƙarfi;" a cikin Littafi Mai Tsarki, a kowanne lokaci ana nufin Allah ne.

  • Wannan laƙabi "Mai Iko Dukka" ko "Wannan Mai Iko Dukka" ana nufin Allah ne kuma ya bayyana cewa yana da dukkan ƙarfi da iko bisa komai.
  • Wannan kalmar kuma akan yi amfani da ita a kwatanta Allah a cikin laƙabai masu nuna zatinsa , "Mai Iko Dukka Allah" ko "Allah Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Allah Mai Iko."

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalmar za a iya fassarata haka "Mai Dukkan Iko" ko "Mai Iko Gabaɗaya" ko "Allah, wanda shi ne mai ƙarfi gabaɗaya."
  • Hanyoyin fassara wannan faɗar "Ubangiji Allah Mai Iko Dukka" sune, "Allah, Mai Iko a Mulki" ko "Mai Iko Allah Makaɗaici" ko "Mai Girma Allah Ubangiji Mamallakin Komai."

(Hakanan duba: Allah, ubangiji, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 06:2-5
  • Farawa 17:01
  • Farawa 35:11-13
  • Ayuba 08:03
  • Littafin Lissafi 24:15-16
  • Wahayin Yahaya 01:7-8
  • Rut 01:19-21

mai kyau, hali mai kyau

Ma'ana

Kalmar nan "kyau" tana da ma'ana iri-iri bisa ga wurin. harsuna da yawa za su mori mabambantan kalmomi domin fassara waɗanan mabambantan ma'anoni.

  • A batu na kai tsaye, abin da ke da kyau shi ne abin da ya yi dai-dai da halaiyar Allah, da shurin Allah da abin da Allah ke so.
  • Abin da ke da "kyau" zai zama da ƙayatarwa, martaba, temako, gamsarwa, kawo riba, kuma dai-dai.
  • Ƙasar dake da "kyau" ana kiranta ƙasa ta gari ko kuma ƙasa mai bayar da "yalwa."
  • Hatsi mai "kyau" zai iya zama gwarzon hatsi.
  • Mutum kan iya zama mai "kyau" ta wurin abin da suke yi, idan suna da fasaha a cikin aikinsu ko sana'arsu, kamar a cikin batun "manomi mai kyau."
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, ma'anar mai "kyau" ta bai ɗaya ita ce duk abin da ba "mugunta ba" ko ya sha bamban da "mugunta."
  • Kalmar nan "managarcin halin" har kullum ana nufin kasancewa nagari ko adali a cikin tunani da kuma ayuka.

Shawarwarin Fassara:

  • Batu na bai ɗaya game da wanan kalma "kyau" a harshen da za'ayi fassara a duk sa'ad da ta bada ma'ana ta bai ɗaya ta bada ma'ana a wurin a duk wurin ta saɓawa mugunta.
  • Ya danganta ga wurin, waɗansu hanyoyi da za'a fassara wanan kalma zai haɗa da "irin" ko "martaba" "mai gamsar da Allah" ko "adalci" ko "na dai-dai" ko "na riba."
  • "Ƙasa mai kyau" za'a iya fassara ta da "ƙasa mai bada yalwar hatsi" "hatsi mai ƙwari" za'a fassara ta da "kaka mai albarka" ko "an sami hatsi mai yawa"
  • Kalmar nan "yin abu mai kyau ga" tana nufin ka yi wani abu da zai amfani waɗansu, kuma za'a iya fassara ta da "yin abin kirki" ko "temako" ko "amfanar" da wani
  • "Yin abu mai kyau a ranar Asabaci" yana nufin yin abin da zai temaki waɗansu a ranar Asabaci"
  • Ya danganta ga abin da ke, hanyoyin fassara kalmar "halin nagarta" sun haɗa da "albarka" ko "halin kirki" ko "ɗabi'a ta gari" ko "aikin adalci" ko "tsaftataccen hali."

(Hakanan duba: mugunta, tsarki, riba, adalci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 05:22-24
  • Farawa 01:12
  • Farawa 02:9
  • Farawa 02:17
  • Yakubu 03:13
  • Romawa 02:4

Mai Tsarki

Ma'ana

Kalmar nan "Mai Tsarki" muƙami ne a cikin Littafi Mai Tsarki har kullum kalmar na nufin Allah.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, wannan muƙamin yakan baiyana a "Mai Tsarki na Isra'ila."
  • A cikin Sabon Alƙawari, shima Yesu ana kiran sa da "Mai Tsarki."
  • Kalmar nan "mai tsarki" a wani lokaci ana amfani da ita a ambaci mala'ika.

Shawarwarin Fassara:

  • Ma'anar kalmar nan "Mai Tsarki" a sauƙaƙe ita ce a cikin harsunan kamar hausa kan ce "Ɗaya" ko "Allah."
  • Wannan kalmar za a fassara ta da "Allah, wanda yake mai tsarki" ko "Keɓaɓɓe."
  • Kalmar nan za'a iya fassara da "Allah, Mai Tsarki na Isra'ila" za'a fassara ta "Allah Mai Tsarki wanda Isra'ila ke bautawa" ko "Mai Tsarki da ke mulkin Isra'ila."
  • Ya fi kyau a fassara wannan kalmar ta wurin amfani da kalmar "tsarki."

(Hakakan duba: tsarki, Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:20
  • 2 Sarakuna 19:22
  • Ayyukan Manzanni 02:27
  • Ayyukan Manzanni 03:13-14
  • Ishaya 05:15-17
  • Ishaya 41:14
  • Luka 04:33-34

maidowa, ana maidowa, an maido, maidowa

Ma'ana

Kalmar "maidowa" na manufar a sa wani abu ya dawo zuwa wurinsa na asali da kuma cikin cikakkiyar lafiya.

  • Yayin da wani sashe na jiki mai ciwo aka maido da shi, wannan ya nuna an "warkar" da shi.
  • Lallataccen zumuncin da aka maido an "sasanta." Allah na maido da mutane masu zunubi ya kuma dawo da su gare shi.
  • Idan aka dawo da mutane ga ƙasarsu ta asali, an "maido da su kuma" ko "sun dawo" ga wannan ƙasa.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassi, hanyoyin fassara "maidowa" za su iya haɗawa da "sabuntawa" ko "sake biya" ko "warkarwa" ko "kawowa baya."
  • Wasu faɗar wannan kalma zasu iya haɗawa da "asa ya sabunta" ko "asa ya sake zama sabo."
  • Ya danganta da nassi, "maidowa," za a iya fassarawa haka "sabuntawa" ko "warkarwa" ko "sulhuntawa."

Wuraren ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sarakuna 05:10
  • Ayyukan Manzanni 03:21
  • Ayyukan Manzanni 15:15-18
  • Ishaya 49:5-6
  • Irmiya 15:19-21
  • Littafin Makoki 05:22
  • Lebitikus 06:5-7
  • Luka 19:08
  • Matiyu 12:13
  • Zabura 080:1-3

majami'a

Ma'ana

Majami'a gini ne inda mutanen Yahuda ke taruwa tare su yi sujada ga Allah.

  • Tun zamanin dă, hidimomi a majami'a sun haɗa da lokacin addu'a, karatun maganar Allah, da koyarwa daga maganar Allah.
  • Da fari yahudawa sun fara gina majami'a ne a matsayin wurin addu'a da bautar Allah a garuruwansu, domin da yawansu na zama a wurare masu nisa da haikali a Yerusalem.
  • Yesu ya yi ta koyarwa a majami'u da kuma warkar da mutane a can.
  • Kalmar "majami'a" anyi amfani da ita da yawa da nufin nuna tattaruwar mutane wuri ɗaya.

(Hakanan duba: warkaswa, Yerusalem, Bayahude, addu'a, haikali, maganar Allah, sujada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 06:09
  • Ayyukan Manzanni 14:1-2
  • Ayyukan Manzanni 15:21
  • Ayyukan Manzanni 24:10-13
  • Yahaya 06:59
  • Luka 04:14
  • Matiyu 06:1-2
  • Matiyu 09:35-36
  • Matiyu 13:54

makoki

Ma'ana

Kalmar "makoki" na nufin nuna babban baƙinciki, damuwa ko ɓacin rai.

  • Wasu lokutta wannan na haɗawa da yin ladama mai girma game da zunubi, ko tausayi domin mutane da suka fuskanci babban bala'i.
  • Makoki na iya haɗawa da zaman makoki, kuka da koke-koke.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "makoki" ana iya fassarawa a matsayin "baƙinciki mai zurfi" ko "koke-koke cikin ɓacin rai" ko "ayi baƙinciki."
  • "Makoki" na iya fassaruwa a matsayin "koke-koke da murya mai ƙarfi da kuka" ko "baƙinciki mai zurfi" ko "hawayen baƙinciki" ko "makoki mai zafi."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 08:9-10
  • Ezekiyel 32:1-2
  • Irmiya 22:18
  • Ayuba 27:15-17
  • Littafin Makoki 02:05
  • Littafin Makoki 02:08
  • Mika 02:04
  • Zabura 102:1-2
  • Zakariya 11:02

makoma, dawwamamme, mara iyaka, har abada

Ma'ana

Kalmar nan "mara iyaka" da kuma "har abada" suna da kamanci da wani abu da zai dawwama har abada.

  • Kalmar nan "mara iyaka" tana nufin baiyana wanda ba shi da farko ne ko ƙarshe ne ko farko.
  • Bayan wanan rayuwar ta duniya, mutane za su je su zauna a sama har abada abadin tare da Allah, ko kuma a cikin jahannama ware daga Allah.
  • Kalmar nan "rai na har abada ko "rai madawwami" an more su a cikin Sabon Alƙawari domin a nuna rayuwa ta har abada tare da Allah a samaniya.
  • Kalmar nan "har abada abadin" tana da bayani ne kan rayuwa marar matuƙa, da kuma nuna yadda rai na har abada yake.
  • Kalmar nan "har abada" tana magana ne akan lokaci marar ƙarewa, wato "na tsawon lokaci."

Kalmar "har abadin abadin" tana jaddadaabin da zai faru ne ko kuma ya kasance.

  • Kalmar nan "har abada abadin" wata hanya ce ta baiyana abin da samaniya ke magana ne kan fasalin samaniya da take, tana nuna rayuwa ne maraiyaku.
  • Allah ya ce kursiyin Dauda zai dawwama "har abada." Wanan na magana ne kan yadda zuriyar Dauda za ta yi sarauta har abada a matsayin sarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi na fassara "har abada" ko "Madawwami" sun haɗa da "rashin iyaka" ko "marar tsayawa" ko mai ci gaba a kullum.'
  • Kalmar nan rai "madawwami" da "rai madauwami" za'a iya fassara su kalmar "rai marar taɓa ƙarewa" ko "rai da ke ci gaba ba tare da tsayawa ba, ko "Tayar da jikkunanmu mu rayu har abada."
  • Ya danganta ga wurin akwai hanyoyi da yawa na fassara "har abada" kamar "yin rayuwa na tsawon lokaci" ko "rai madawwami"
  • Haka nan a duba yadda ake fassara kalmar harsunan ƙasa.
  • "Har abada" zai iya nufin "yau da kullum ba tare ƙarewa ba."
  • Kalmar nan "zai tabbata har abada' za'a iya fassara ta da kasancewa har kullum."
  • Wanan nanaci na kalmar nan har abada abadin za'a iya fassara ta da "rashin ƙarshe" ko marar ƙarshe kwata-kwata."
  • Gadon sarautar Dauda zai dawwama har abada, za' iya fassara ta da cewa zuriyar Dauda za ta yi sarauta har abada."

(Hakanan duba: Dauda, sarauta, rai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 17:8
  • Farawa 48:4
  • Fitowa 15 17
  • 2 Sama'ila 03:28-30
  • 1 Sarakuna 02 :32-33.
  • Ayuba 04:20 -21
  • Zabura 021:4
  • Ishaya 40:27-28
  • Daniyel 07:18
  • Luka 18:18.
  • Ayyukan Manzani 13:46
  • Romawa 05:21
  • Ibraniyawa 06:19-20
  • Ibraniyawa 10:11-14
  • 1 Yahaya 01:2
  • 1 Yahaya 05:12
  • Wahayin Yahaya 01:4-6
  • Wahayin Yahaya 22:3-5

mala'ika, mala'iku, babban mala'ika

Ma'ana

Mala'ika ruhu ne mai iko wanda Allah ya hallita. Mala'iku sun kasance domin su bauta wa Allah ta wurin yin abin da ya umarce su su yi. Wannan kalma "babban mala'ika" ana nufin mala'ikan dake mulki ko bida dukkan sauran mala'iku.

  • Wannan kalma "mala'ika" fassarar shi ne "manzo."
  • Wannan furci "babban mala'ika" a iya fassara shi a ce "babban manzo." mala'ika ɗaya ne tak a Littafi Mai Tsarki aka ce da shi "babban mala'ika" shi ne Maikel.
  • A Littafi Mai Tsarki, mala'iku suna bada saƙonni ga mutane daga Allah. Waɗannan saƙonnin sun haɗa har da abubuwan da Allah yake so mutanen suyi.
  • Mala'iku sukan faɗa wa mutane abubuwan da za su faru nan gaba ko abubuwan da suka rigaya suka faru.
  • Mala'iku suna da iko na Allah domin su wakilansa ne kuma wani lokaci a Littafi Mai Tsarki sukan yi magana kamar Allah ne da kansa yake magana.
  • Wasu hanyoyi da mala'iku suke bauta wa Allah shi ne ta wurin tsaro da ƙarfafa mutane.
  • Wannan magana musamman, "mala'ikan Yahweh" yana da ma'ana fiye da ɗaya: 1) Zai iya zama "mala'ikan da ya wakilci Yahweh" ko "manzo dake bauta wa Yahweh.' 2) Zai iya zama Yahweh da kansa, wanda ya yi kama da mala'ika idan yana yiwa mutum magana.‌ Ɗaya dai daga cikin waɗanan maganganu zai bayyana dalilin da mala'ika yake magana da "Ni" kamar Yahweh da kansa ne ke magana.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "mala'ika" zai haɗa da "manzo daga Allah" ko "Bawan Allah daga sama" ko "ruhun Allah manzo."
  • Wannan furci "babban mala'ika" za a iya fasara shi zuwa "mala'ika sarki" ko "mala'ikan dake bisa mala'iku" ko "shugaban mala'iku."
  • Sai a lura da yadda aka fassara wannan kalma a harshen ƙasar ko kuma wasu harsunan wurin.
  • Wanna furci "Mala'ikan Yahweh" za a fassara shi ta wurin amfani da waɗannan kalmomi "mala'ika" da "Yahweh." Wannan zai bada 'yancin yin fassara daban-daban na wannan furcin. Ga wasu ƙarin fassara masu yiwuwa, "mala'ika daga Yahweh" ko "mala'ikan da Yahweh ya aika" ko "Yahweh da ya yi kama da mala'ika."

(Hakanan duba: shugaba, kai, manzo, Makel, mai mulki, bawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 24:16
  • Ayyukan Manzanni 10:3-6
  • Ayyukan Manzanni 12:23
  • Kolosiyawa 02:18-19
  • Farawa 48:16
  • Luka 02:13
  • Markus 08:38
  • Matiyu 13:50
  • Wahayin Yahaya 01:20
  • Zakariya 01:09

manna

Ma'ana

Manna wata farar, ƙwayar abinci ce da Allah ya tanada wa Isra'ilawa su ci lokacin kasancewarsu shekara 40 a jeji bayan sun baro Masar.

  • Manna tayi kama da farar waina mai faɗowa kowacce safiya a ƙasa ƙarƙashin raɓa. Tana da zaƙi, kamar zuma.
  • Isra'ilawa sukan tara wainar manna kowacce rana amma banda ranar Asabaci.
  • A ranar kafin Asabaci, Allah ya gayawa Isra'ilawa su tattara riɓi biyu na manna domin kada su fita tara ta a ranar hutawarsu.
  • Wannan kalma "manna" ma'anarta "Mene ne wannan?"
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, a kan ce da ita "waina daga sama" da "kwaya daga sama."

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyin fassara wannan magana za a iya cewa "wani siririn abinci fari" ko "abinci daga sama."
  • Kuma a duba yadda aka fassara wannan kalmar a cikin Littafi Mai tsarki a cikin wani harshen ƙasar.

(Hakanan duba: waina, jeji, ƙwayar, sama, Asabaci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 08:3
  • Fitowa 16:27
  • Ibraniyawa 09:3-5
  • Yahaya 06:30-31
  • Yoshuwa 05:12

manzo, manzanni, manzanci

Ma'ana

Yesu ne ya aiki "manzanni" su yi wa'azi akan Allah da mulkinsa. Idan an ce "manzanci" fassarar shi ne matsayi da ikon da su waɗanda aka zaɓa su zama manzanni suke da shi.

  • Wannan kalma "manzo" ma'anarta "wani mutum ne da aka aika saboda wani dalili." Manzo yana da iko iri ɗaya da wanda ya aike shi.
  • Almajiran Yesu guda goma sha biyu na kurkusa da shi suka zama manzanni na fari. Sauran mutane kamar su Bulus da Yakubu su ma suka zama manzanni.
  • Ta wurin ikon Allah manzanni suka iya yin wa'azin bishara da gabagaɗi suka warkar da mutane, har kuma da tilasta wa aljannu su fita daga cikin mutane.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalman nan "manzo" za a iya fassara ta da kalma ko faɗa mai ma'ana haka "wani da aka aike shi" ko "aikakke" ko "mutumin da aka kira ya je ya yi wa'azin saƙon Allah ga mutane."
  • Yana da mahimmanci a fassara waɗannan kalmomi "manzo" da "almajiri" a hanyoyi da zai bambanta su daga junansu.

(Hakanan duba: hukuma, almajiri, Yakubu (ɗan Zebedi), Bulus, sha biyun)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahuda 01:17-19
  • Luka 09:12-14

mara bada gaskiya, halin rashin bada gaskiya

Ma'ana

Kalmar nan "mara bada gaskiya" tana nufin a zama da rashin bangaskiya ko a ƙi gaskatawa.

  • Wanan kalmar an more ta domin a nuna mutane waɗanda ba su yi imani da Allah ba. Ƙarancin imanin ana ganinsa ta wurin mummunar rayuwarsu da suke yi.
  • Annabi irmiya ya zargi Isra'ila da zama da rashin bada gaskiya ga Allah.
  • Sun bautawa gumaka suka kuma bi waɗansu al'adu na waɗansu mutane da ba su bautar Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga wurin, kalmar nan "marar bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin aminci" ko "marar yin imani" ko "marar biyayya ga Allah" ko marar imani."
  • Kalmar nan "halin rashin bada gaskiya" za'a iya fassara ta da "rashin imani" ko "rashin aminci" ko "tayarwa ga Allah."

(Hakanan duba: gaskatawa, aminci, rashin biyayya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ezekiyel 43:6-8
  • Ezra 09:1-2
  • Irmiya 02:19
  • Littafin Misalai 02:22
  • Wahayin Yahaya 21:7-8

mara laifi

Ma'ana

Kalmar nan "mara laifi" na nufin zama da rashin laifi na karya doka ko yin wani abu da ba dai-dai ba. Hakanan zata iya zama da nufin mutanen da ke aikata miyagun abubuwa.

  • Mutumin da ake zargi da aikata wani abu da ba daidai ba bashi da laifi in har bai aikata wani abu da ba dai-dai ba.
  • Waɗansu lokutan kalmar "mara laifi" ana moron ta ga mutanen da ba su aikata wani abu da ba dai'dai ba kuma basu cancanci musgunawar da ake yi masu ba, misali kamar yadda maƙiyi ke harar "mutane marasa laifi."

Shawarwarin Fassara:

  • A mafi yawan wurare, kalmar nan "mara laifi" za'a iya fassara ta da "rashin laifi"ko "rashin zama da wani abin zargi kan aikata abin da ba dai-dai ba.
  • In ana magana bai ɗaya kan mutane marasa laifi, za'a iya fassara ta da "wanda bai yi wani abu da ba dai-dai ba" ko "wanda ba'a same shi a cikin wani mugun aiki ba."
  • Wannan kalmar da ake yawan ambato "jinin marasa laifi" za'a iya fassara ta da "mutane marasa aikata kowaccace irin muguntar da za ta sa a kashe su."
  • Batun nan "zubar da jinin marasa laifi" za'a iya fassara ta da "kisan mutane marasa laifi" ko "kisan mutane waɗanda ba su yi wani aikin mugunta da ya cancanci mutuwa ba."
  • A wurin da aka ambaci an kashe wani, zama da rashin laifin jinin wani" za'a iya fassara ta da "rashin laifi kan mutuwar wani."
  • Sa'ad da ake magana game da mutanen da ba su ji labari mai daɗi game da Yesu ba kuma ba su karɓe shi ba, "rashin zama da laifin jinin wani" za'a iya fassara ta da "rashin zama sanadin na" ko "sun ƙi karɓar wannan saƙo."
  • Da Yahuda ya ce "Na bayar da marar laifi," cewa ya yi "Na bada mutum wanda bai yi wani laifi ba" ko "Na zama sanadin mutuwar mutum mara zunubi."
  • Da Filate ya yi magana game da Yesu cewa "Ba ni da laifin jinin wannan mutum mara laifi" za'a iya fassara ta da "Ba ni na zama sanadin mutuwar mutumin nan mara laifi da bai yi wani abu na laifi da ya cancanci haka ba."

(Hakanan buba: laifi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:04
  • 1 Sama'ila 19:05
  • Ayyukan Manzanni 20:26
  • Fitowa 23:07
  • Irmiya 22:17
  • Ayuba 09:23
  • Romawa 16:18

marar zargi

Ma'ana

Kan maganan nan "marar zargi" ma'anar shi ne "babu abin zargi." Ana amfani da shi ga mutumin dake biyayya da Allah da dukkan zuciyarsa, amma ba ana nufin mutumin bashi da zunubi ba.

  • Da Ibrahim da Nuhu an ɗauke su marasa abin zargi a gaban Allah.
  • Mutumin da ya yi suna domin bashi da "abin zargi" yakan nuna halaiyar girmama Allah.
  • Bisa ga wata aya, mutumin da bashi da abin zargi shi ne "wanda yake jin tsoron Allah yana kuma ƙin mugunta."

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara wannan haka "babu wani abin zargi a halinsa" ko "mai cikakken biyayya ga Allah" ko "mai kauce wa zunubi" ko "yana guje wa mugunta."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 02:10
  • 1 Tasalonikawa 03:11-13
  • 2 Bitrus 03:14
  • Kolosiyawa 01:22
  • Farawa 17:1-2
  • Filibiyawa 02:15
  • Filibiyawa 03:06

martaba

Ma'ana

Wannan kalma "martaba" na nufin girma da daraja, yawancin lokaci sarakai ake gaya wa wannan.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki yawancin lokaci "martaba" game da girman Allah take, wanda shi ne mafificin Sarki bisa sammai.
  • "Mai martaba" hanya ce ta gabatar da sarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalmar za a iya fassara ta haka "girman sarauta" ko "darajar sarauta."
  • " Mai martaba" za a iya fssara shi haka "Mai Girma" ko "Mai Gaskiya" ko ayi amfani da maganganu da aka saba amfani da su a wannan yaren.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 01:16-18
  • Daniyel 04:36
  • Ishaya 02:10
  • Yahuda 01:25
  • Mika 05:04

marubuci, marubuta

Ma'ana

Marubuta shugabanni ne waɗanda ke da aikin rubutu ko su ajiye ta wurin rubutun abin dake na gwamnati ko na addini da hannu. Wani suna na marubutan Yahudawa shi ne "ƙwararru a shari'ar Yahudanci."

  • Aikin Marubuta ne su yi rubutu domin su adana takardun Tsohon Alƙawari.
  • Haka kuma, suna rubuta, su adana, su kuma fassara ra'ayoyi da kalmomi na shari'ar Allah.
  • Wasu lokutan, marubut ma'aikata ne masu muhimmanci na gwamnati.
  • Wasu daga cikin manyan marubuta sun haɗa da Baruk da kuma Ezra.
  • A cikin Sabon Alƙawari, kalmar "marubuta" ana fassara shi "malaman Shari'a."
  • A cikin Sabon Alƙawari, marubuta tare suke da ƙungiyar addini da ake ce da su "Farisiyawa," kuma waɗannan ƙungiyoyin biyu ana ambatarsu yawancin lokuta tare.

(Hakanan duba: shari'a, Farisi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 04:05
  • Luka 07:29-30
  • Luka 20:47
  • Markus 01:22
  • Markus 02:16
  • Matiyu 05:19-20
  • Matiyu 07:28
  • Matiyu 12:38
  • Matiyu 13:52

marufin kaffara

Ma'ana

Wannan "marufin kaffara" marufin katako ne da aka dalaye shi da zinariya akan yi amfani da shi a rufe kan akwatin alƙawari. A cikin fassara na Turanci da yawa akan ce dashi "marufin kaffara."

  • Tsawon marufin kaffara wajen sentimitar kamu 115 ne faɗinsa kuma sentimitar kamu 70 ne.
  • Akan marufin kaffara akwai kerubobi na zinariya guda biyu da fukafukansu masu taɓa juna.
  • Yahweh ya ce zai gamu da Isra'ilawa akan marufin kaffara ƙarƙashin miƙaƙƙun fukafukan kerubobi. Babban firist ne kaɗai aka yardar masa ya yi haka, domin shi ne wakilin mutane.
  • Wani lokaci wannan marufin kaffara ana ce da shi "kursiyin jinƙai" domin yana nuna jinƙan Allah daya sauko domin ya fanshi talikan mutane masu zunubi.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyin fassara wannan suna za a haɗa da waɗannan, "marufin akwati inda Allah ya yi alƙawari zai yi fansa" ko "wurin da Allah ke kaffara" ko "marufin akwati inda Allah ke yin gafara da maido da mai tuba."
  • Zai iya zama da wannan ma'ana "wajen sulhu."
  • Auna wannan da yadda aka fassara "kaffara," "sulhu," da "fansa."

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, kaffara, kerubim, sasantawa, fansa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 25:17
  • Fitowa 30:06
  • Fitowa 40:17-20
  • Lebitikus 16:1-2
  • Littafin Lissafi 07:89

masarautar Allah ko mulkin Allah, masarautar sama ko mulkin sama

Ma'ana

Kalmomin "masarautar Allah" da "masarautar sama" dukka na nufin mulkin Allah da hukuncinsa bisa mutanensa da bisa dukkan halitta.

  • Yawanci Yahudawa na amfani da kalmar "sama" da manufar Allah, domin su kaucewa faɗin sunansa kai tsaye.
  • A cikin Littafin Sabon Alƙawari da Matiyu ya rubuta, yana faɗin masarautar Allah da ma'anar "masarautar sama," watakila saboda yana rubutawa ne musamman ga al'ummar Yahudawa.
  • Masarautar Allah na nufin Allah yana mulkin mutane a ruhaniya yayin da yake kuma mulkin duniyar zahiri.
  • Annabawan Tsohon Alƙawari sunce Allah zai aiko da Almasihu domin ya yi mulki tare da adalci. Yesu, Ɗan Allah, shi ne Almasihun wanda zai yi mulki bisa masarautar Allah har abada.

Shawarwarin Fassara:

  • Dogara bisa ga nassin, "za a iya fassara "masarautar Allah" a matsayin "Allah na mulki (a matsayin sarki)" ko "sa'ad da Allah ke mulki a matsayin sarki" ko "Allah na mulki bisa komai."
  • Kalmar "masarautar sama" ita ma ana iya fassarawa "Allah na mulki daga sama a matsayin sarki" ko "Allah na sama yana mulki" ko "mulkin sama" ko "sama na mulki bisa komai." Idan baya yiwuwa a fassara wannan cikin sauƙi a sarari, furcin "masarautar Allah" shi za a fassara a maimako.
  • Wasu masu fassara zasu so su rubuta "Sama" da babban baƙi domin su nuna cewa ana ma'anar Allah. Wasu zasu haɗa da ɗan rubutu a nassin, kamar haka "masarautar sama (wato, 'masarautar Allah')."
  • Rubutun dake ƙasan shafin Littafi Mai Tsarki shima za a iya amfani dashi ayi bayani game da ma'anar "sama" a wannan wurin.

(Hakanan duba: Allah, sama, sarki, masarauta, Sarkin Yahudawa, mulki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Tasalonikawa 01:05
  • Ayyukan Manzanni 08:12-13
  • Ayyukan Manzanni 28:23
  • Kolosiyawa 04:11
  • Yahaya 03:03
  • Luka 07:28
  • Luka 10:09
  • Luka 12:31-32
  • Matiyu 03:02
  • Matiyu 04:17
  • Matiyu 05:10
  • Romawa 14:17

masujada

Ma'ana

kalmar "masujada " na nufin "wuri mai tsarki" yana kuma nuna wurin da Allah ya maida da tsarki da mai tsarki. Haka kuma wurin na nufin wajen bada kariya da mafaka.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, kalmar "masujada " ana yawan amfani da ita domin a ambaci rumfar sujada ko ginin haikali inda "wuri mai tsarki" da "wuri mafi tsarki" yake.
  • Allah ya ambaci masujada a matsayin inda yake zama a tsakanin mutanensa, Isra'ilawa.
  • Ya kuma ce da kansa "masujada " ko wuri na tsaro inda mutanensa zasu iya zama ciki.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma na da ainihin ma'ana "wuri mai tsaki" ko "wurin da aka keɓe."
  • Ya danganta da nassin, kalmar "masujada" za a iya fassarawa haka "wuri mai tsarki" ko "keɓaɓɓen gini" ko " keɓaɓɓen wurin mafaka."
  • Faɗar "ma'aunin masujada" za a iya fassarawa haka "wani irin ma'auni da ake bayar wa domin rumfar sujada" ko "ma'aunin da ake amfani da shi wajen biyan haraji domin lura da haikali."
  • Lura: Ayi hankali da cewa fassara wannan kalma ba ta da ma'anar ɗakin sujada irin na ikilisiyoyin zamanin yau.

(Hakanan duba: mai tsarki, Ruhu Mai Tsarki, keɓewa, rumfar sujada, haraji, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Amos 07:13
  • Fitowa 25:3-7
  • Ezekiyel 25:03
  • Ibraniyawa 08:1-2
  • Luka 11:49-51
  • Littafin Lissafi 18:01
  • Zabura 078:69

maya haihuwa, haihuwar Allah, sabuwar haihuwa

Ma'ana

Kan maganan nan "maya haihuwa" Yesu ya fara faɗin ta domin ya fassara ma'anar abin da Allah ya yi ya canza mutum daga zaman matacce a ruhaniya zuwa rayayye a ruhu. Wannan furci "haifaffe daga Allah" da "haifaffe daga Ruhu" ana nufin mutumin da aka bashi sabon rai na ruhaniya.

  • Dukkan mu 'yan adam an haife mu matattu a ruhaniya kuma ana ba mu "sabuwar haihuwa" sa'ad da muka karɓi Yesu Almasihu ya zama mai cetonmu.
  • A lokacin sabuwar haihuwa ta ruhaniya, Ruhu Mai Tsarki na Allah yakan fara zama a cikin sabon mutum mai bada gaskiya ya bashi ikon bada kyawawan 'ya'ya na ruhaniya a rayuwarsa.
  • Aikin Allah ne ya sa a sake haihuwar mutum ya zama ɗansa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wasu hanyoyi na fassara "maya haihuwa" zai haɗa da waɗannan, "sabon haihuwa ful" ko "haihuwa ta ruhaniya."
  • Ya fi kyau a fassara wannan a sauƙaƙe ayi amfani da kalmomin da aka saba da su a cikin yaren da za a yi amfani da sake haihuwa.
  • Wannan kalma "sabuwar haifuwa" za a iya juya ta zuwa "haihuwar ruhaniya."
  • Wannan faɗar "haifaffen Allah" za a iya fassara shi haka "Allah ne yakan sa a sami sabon rai kamar jariri sabon haihuwa" ko "Allah ya bada sabon rai."
  • Haka kuma, "haihuwa ta Ruhu" za a iya fassara ta "an bada sabon rai ta wurin Ruhu Mai Tsarki" ko " Samun iko ta wurin Ruhu Mai Tsarki a zama ɗan Allah" ko "Ruhu ya sa in sami sabon rai kamar jariri sabon haihuwa."

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, ceto)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:09
  • 1 Bitrus 01:03
  • 1 Bitrus 01:23
  • Yahaya 03:04
  • Yahaya 03:07
  • Titus 03:05

miƙawa

Ma'ana

Keɓewa shi ne a miƙa wani abu ko wani mutum domin yi wa Allah hidima. Mutumin ko abin da aka keɓe akan ɗauke shi mai tsarki ne kuma akan ajiye shi da bam domin Allah.

  • Ma'anar wannan kalma kusan ɗaya take da "tsarkakewa" ko "a sa ya zama mai tsarki," amma tare da ƙarin bayyanin keɓe wannan mutum domin hidimar Allah.
  • Abubuwan da ake miƙa wa Allah sun haɗa har da dabbobi da za a yi hadaya, bagadin baikon ƙonawa, da rumfar taruwa.
  • Mutanen da akan keɓe ga Allah sune firistoci, mutanen Isra'ila, da babban ɗan fari namiji.
  • Wani lokaci wannan kalma "miƙawa" tana da ma'ana kusan ɗaya da "tsarkakewa," musamman idan game da shirya mutane ko abubuwa domin hidimar Allah saboda a wanke su su zama karɓaɓɓu gareshi.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "miƙawa" za a iya haɗawa da waɗannan, "a keɓe waje guda domin hidimar Allah" ko "tsarkakewa domin hidima ga Allah."
  • Kuma a yi la'akari da yadda aka fassara waɗannan kalmomi "tsarki" da "tsarkakewa."

(Hakanan duba: tsarki, tsantsa, tsarkakewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 04:3-5
  • 2 Tarihi 13:8-9
  • Ezekiyel 44:19

misali, misalai

Ma'ana

Wannan kalma "misali" ɗan gajeren labari ne da ake amfani da shi a koyar da wata gaskiya.

  • Yesu ya yi amfani da misalai domin ya koyar da almajiransa. Koda shike yakan faɗa wa taron mutane misalai, ba kullum ne yake bayyana masu ma'anar ba.
  • Yakan yi amfani da misalai ya bayyana wa almajiransa gaskiya amma ta zama ɓoyayya ga mutane kamar Farisawa waɗanda basu bada gaskiya gare shi ba.
  • Annabi Nathan ya faɗa wa Dauda wani misali domin ya nuna wa sarki mugun zunubinsa.
  • Labarin Basamariye Mai Nagarta misali da aka faɗe shi kamar labari. Labarin tsofaffi da sabobbin salkuna da Yesu ya faɗi misali ne domin ya taimaki almajiransa su fahimci koyarwarsa.

(Hakanan duba: Samariya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 05:36
  • Luka 06:39
  • Luka 08:04
  • Luka 08:9-10
  • Markus 04:01
  • Matiyu 13:03
  • Matiyu 13:10
  • Matiyu 13:13

mugunta, mugu, aikin mugunta, abu na mugunta

Ma'ana

Kalmomin nan "mugu" da "mugunta duk suns magana ne akan duk wani abu da ya yi saɓani da nufin Allah mai tsarki.

  • Amma "mugunta" tana baiyana halin mutum ne,"mugu" kuma ana nuna irin ɗabi'ar mutum ne. Duk da haka dukkan kalmomin na da kamancin ma'ana.
  • Kalmar nan "aikin mugunta" tana magana ne akan yanayi na kasancewar mutanen da ke yin mugayen ayuka.
  • Sakamakon mugunta an nuna shi a fili ta yadda ake zaluntar mutane ta wurin kisa, sata, gulma, da zama algungumai da rashin kirki.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da wurin, kalmar nan "mugunta" da "mugu" za'a iya fassara su akan "abu marar kyau" ko "zunubi" ko "mummunar rayuwa"
  • Waɗansu Hanyoyi kuma na fassara waɗannan sun haɗa da" marar kyau"ko marar "adalci" ko "rayuwa marar dacewa"
  • A tabbata kalmomin ko ƙaulolin da aka mora domin yin fassarar waɗannan kalmoin sun dace da wurin bisa ga wanan harshen ake ƙoƙarin yin fassarar.

(Hakanan duba: rashin biyyaya, zunubi, nagarta, adalci, aljani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 24:11
  • 1Timoti 06:10
  • 3 Yahaya 01:10
  • Farawa 02:17
  • Farawa 06:5-6
  • Ayuba 01:1
  • Ayuba 08:20
  • Littafin Alƙalai 09:57
  • Luka 06:22-23
  • Matiyu 07:11-12
  • Littafin Misalai 03:7
  • Zabura 022:16-17

mulki

Ma'ana

Kalmar nan " mulki" tana nufin iko,sarrafawa, kohukumanci akan mutane, dabbobi ko ƙasa.

  • An ce Yesu yana da mulki akan dukkan duniya, a matsayin annabi, firist da sarki.
  • Sheɗan an yi nasara da mulkinsa har abada ta wurin mutuwar Yesu akan giciye.
  • A akin hallitta, Allah ya ce mutum ya sami mulki akan kifaye, tsuntsaye da dukkan hallitu da ke duniya.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta akan wurin, waɗansu hanyoyi da za'a iya fassara ta sun haɗa da "mulki" "iko" "mallaka."
  • Kalmar nan ku yi mulki akan za'a iya fassara ta da cewa ku "mallaka" ko "sarrafa."

(Hakanan: duba mulki, iko)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Bitrus 05:10-11
  • Kolosiyawa 01:13
  • Yahuda 01:25

munafuki, munafunci, halin munafunci

Ma'ana

Kalmar nan "munafiki" tana nufin mutum wanda ke yin abubuwan da ke kamar na adalci a ganin ido, amma a asirce yana yin miyagun ayuka. Kalmar halin "munafunci" na nufin halin da ke yaudarar mutane inda suke tunanin mutumin adali ne.

  • Munafuki na son yin abubuwa da mutane zasu yi tunanin nagari ne.
  • Sau da yawa munafukai kan dinga ganin kuskuren sauran mutane sabo da suna yin wannan abin da su da kansu suke aikatawa.
  • Yesu ya kira Farisiyawa munafukai sabo da duk da yake suna yin ayukan addini, kamar sa waɗansu suturu da cin wani irin abinci, amma basu da kirka ga sauran mutane.
  • Munafuki kan ga laifin sauran mutane, amma shi bai karɓar nasa kurakuran.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu harsuna na da kalma kamar "fuska biyu" wannan na nufin aiki munafuki.
  • Waɗansu hanyoyi na yin fassara "munafuki" sun haɗa da "fankama" ko "aikin ganin ido" ko "ɗaga kai, mayaudarin mutum."
  • Kalmar "halin munafunci" za'a iya fassara ta da "yaudara" ko "yin ayuka na jabu" ko "na ganin ido."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Galatiyawa 02:13
  • Luka 06:41-42
  • Luka 12:54-56
  • Luka 13:15
  • Markus 07:6-7
  • Matiyu 06:1-2
  • Romawa 12:9

mutanen Allah, mutanena

Ma'ana

Wannan magana "mutanen Allah" ana nufin mutanen da Allah ya kirawo su daga duniya domin ya kafa wata dangantaka ta masamman da shi kansa.

  • Idan Allah ya ce "mutanena" yana magana ne akan mutanen daya rigaya ya zaɓa kuma suna da dangantaka da shi.
  • Allah ne mai zaɓen mutanensa kuma ya keɓe su daga duniya domin suyi rayuwar da ta gamshe shi. Shi kuma ya kira su 'ya'yansa.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, "mutanen Allah" na nufin al'ummar Isra'ila wadda Allah ya zaɓa ya kuma keɓe ta daga sauran wasu al'umman duniya domin su bauta masa su kuma yi masa biyayya.
  • A cikin Sabon Alƙawari "mutanen Allah" masamman ana nufin dukkan waɗanda suka bada gaskiya ga Yesu ana kuma kiran su ikilisiya. Wannan ya haɗa dukka biyu, da Yahudawa da kuma Al'ummai.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "mutanen Allah" za a iya fassara ta a ce "mutane dake na Allah" ko "mutanen dake wa Allah sujada" ko "mutanen dake bauta wa Allah" ko "mutane waɗanda su na Allah ne."
  • Sa'ad da Allah ya ce "mutanena" wasu hanyoyin fassarawa sune "mutanen dana zaɓa" ko "mutanen dake yi mani sujada" ko "mutane waɗanda su nawa ne."
  • Haka kuma "mutanenka" za a iya fassara shi haka, mutanen dake naka" ko mutanen daka zaɓa su zama naka."
  • Kuma "mutanensa" za a iya fasara shi haka "mutanen da su nasa ne" ko "mutanen da Allah ya zaɓa domin su zama nasa."

(Hakanan duba: Isra'ila, ƙungiyar mutane)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Tarihi 11:02
  • Ayyukan Manzanni 07:34
  • Ayyukan Manzanni 07:51-53
  • Ayyukan Manzanni 10:36-38
  • Daniyel 09:24-25
  • Ishaya 02:5-6
  • Irmiya 06:20-22
  • Yowel 03:16-17
  • Mika 06:3-5
  • Wahayin Yahaya 13:7-8

nagari, hali nagari, miskili, mara Allah, mara halaiya ta gari, halin rashin tsoron Allah

Ma'ana

Kalmar "nagari" ana moron ta a baiyana mutum wanda ke yin abin da ke girmama Allah, da kuma nuna yadda kamannin Allah yake. "Hali nagari" halaiya ce da ke gimama Allah ta wurin yin nufinsa.

  • Mutumin da ke da hali nagari zai nuna 'ya'ya na Ruhu Mai Tsarki, kamar ƙauna, farinciki, salama, haƙuri, kirki, da kamun kai.
  • Yadda ake gane nagarin mutum shine ta wurin zama da Ruhu Mai Tsarki da kuma yi masa biyayya.

Kalmar nan "miskili" da "marar sanin Allah" tana nuna mutane waɗanda ke tayarwa Allah. Suna rayuwa cikin muguwar hanya, ba tare da tunani game da Allah ba, irinsu ake kira "miskilai" ko "marasa sanin Allah."

  • Ma'anar waɗanan kalmomin suna kama da da. Duk da yake, mara "sanin Allah" da "halinrashin sanin Allah" yana cikakken nuni ne akan yadda mutane ko al'umma ba su yin la'akari da Allah ko yarda ya yi mulki a kansu.
  • Allah ya hurta hukunci da fushi ga maras tsoronsa da kuma akan duk wanda ya ƙi shi da kuma hanyoyinsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "nagari" za'a iya fassara ta da "mutanen kirki" ko "mutanen da ke yiwa Allah biyyaya."
  • Kalmar baihyanau ta "nagari" za'a iya fassara ta da "mai biyayya ga Allah" ko "adali" ko "mai farantawa Allah rai."
  • Kalmar "cikin hali nagari" za'a iya fassara ta da "a cikin hanyar yin biyayya ga Allah" ko "cikin aiki ko maganar da ke girmama farantawa Allah rai."
  • Hanyoyi na fassara hali na gari sun haɗa da "yin abin da ke faranta wa Allah rai ko kuma yi wa Allah biyayya, ko "yin rayuwar adalci."
  • Ya danganta ga wurin, kalmar nan "miskili" za'a iya fassara ta da "halin da ba ya faranta wa Allah rai" ko "halin ƙazanta" ko "rashin biyayya ga Allah."
  • Kalmar nan "rashin sanin Allah" ko "halin rashin tsoron Allah" za'a iya fassara ta da mutanen da "basu tare da Allah" ko "basu yin tunani game da Allah" wato "basu yin la'akari game da Allah."
  • Waɗansu hanyoyi kuma na yin fassara "halin rashi tsoron Allah" ko "halin rashin sanin Allah" su haɗa da "aikin mugungta" ko "mugunta" ko "tayar wa Allah."

(Hakanan duba: mugunta, girmamawa, biyayya, adalci, adali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayuba 27:10
  • Misalai 11:9
  • Ayyukan Manzanni 03:12
  • 1 Timoti 01:9-11
  • 1 Timoti 04:7
  • 2 Timoti 03:12
  • Ibraniyawa 12:14-17
  • Ibraniyawa 11:7
  • 1 Bitrus 04:18
  • Yahuza 01:16

nufin Allah

Ma'ana

"Nufin Allah" na ma'anar marmarin Allah da shirinsa .

  • Nufin Allah musamman yana bayyana yadda Allah ke yin hurɗa da mutane da kuma yadda yake so mutanen su amsa masa.
  • Kalmar na bayyana shiri ko marmarinsa ga sauran hallitunsa.
  • Kalmar "nufi" na ma'anar ayi "ƙuduri" ko ayi "marmari."

Shawarwarin Fassara:

  • "Nufin Allah" za a iya fassarawa haka "abin da Allah yake marmari" ko "abin da Allah ya shirya" ko "dalilin Allah" ko "abin dake gamsar Allah."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:15-17
  • 1 Tasalonikawa 04:3-6
  • Kolosiyawa 04:12-14
  • Afisawa 01:1-2
  • Yahaya 05:30-32
  • Markus 03:33-35
  • Matiyu 06:8-10
  • Zabura 103:21

pasto, pastoci

Ma'ana

Wannan kalma "pasto" ɗaya take da "makiyayi". Sunan matsayi ne da ake naɗa wa mutumin da shi ne shugaban addini na ƙungiyar masu bada gaskiya.

  • A cikin dukkan juyin Turanci na Littafi Mai Tsarki, an ambaci "pasto" sau ɗaya tak ne, a cikin Littafin Afisawa. Kalma guda ce an kuma fassarata "makiyayi" a wurin.
  • A wasu yaren, kalmar nan "pasto" ɗaya take da kalmar nan "makiyayi."

Shawarwarin Fassara:

  • Zai fi kyau a fassara wannan kalma haka "makiyayi" a harshen masu juyi.
  • Wasu hanyoyin fassara wannan magana zai haɗa da waɗannan maganganu "shugaban ruhaniya" ko "makiyayin Kiristoci shugaba."

(Hakanan duba: makiyayi, tumaki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 04:11-13

Rabbi

Ma'ana

A kalmar "Rabbi" a zahiri tana nufin "shugabana" ko "malamina."

  • Laƙabi ne na bangirma da ake amfani da shi domin mutum malami na Addini a Yahudanci, musamman malami mai koyar da shari'ar Allah.
  • Almajiran Yahaya mai Baftisma da na Yesu na kiransu da suna "Rabbi."

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara wannan kalma zasu haɗa da "Shugabana" ko "Malamina" ko "Malami mai Girma" ko "Malamin Addini." Wasu yarurrukan zasu yi gaisuwa da manyan haruffa kamar haka, yayin da wasu kuma ba za suyi ba.
  • Yaren da ake yin fassara a ciki zai yiwu yana da hanya musamman da ake kiran malamai da ita.
  • A tabbatar da cewa fassara wannan kalma a yaren bai nuna cewa Yesu malamin makaranta ba ne.
  • A kuma duba yadda aka fassara "Rabbi" a cikin fassarar Littafi Mai Tsarki cikin wani yaren mai dangantaka da shi ko yaren ƙasar bakiɗaya.

(Hakanan duba: malami)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yahaya 01:49-51
  • Yahaya 06:24-25
  • Markus 14:43-46
  • Matiyu 23:8-10

rai, rayuka

Ma'ana

Rai shine abin da ba a gani, na cikin mutum, yana nufin ɓangaren da ba jiki ba na cikin mutum.

  • Wannan kalma "rai" da "ruhu" na iya zama abubuwa biyu daban, ko sukan iya zama abu biyu dake nufin abu guda.
  • Idan mutum ya mutu, ransa yakan bar jikinsa.
  • Kalmar "rai" wani lokacin akan yi amfani da ita akai akai ana nufin dukkan mutum. A misali, "ran da ya yi zunubi" na nufin "mutumin da ya yi zunubi" da "rai na ya gaji" na nufin, "na gaji."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "rai" akan iya fassara ta da "can ciki wani" ko "mutumin dake ciki."
  • A waɗansu nassosin, "rai na" ana fassara wa da "NI" ko "Ni".
  • Sau da yawa kalmar "rai" akan fassara ta da "talikin" ko "shi" ya danganta da wurin da kalmar take.
  • Waɗansu yarurrukan kan iya samun kalma ɗaya domin "rai" da "ruhu".
  • A cikin Ibraniyawa 4:12, an raba wannan kalmar "rai da ruhu" suna nufin "zuzzurfan nutsewa ko fayyace mutumin ciki."

(Hakanan duba: ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 02:08
  • Ayyukan Manzanni 02:27-28
  • Ayyukan Manzanni 02: 41
  • Farawa 49:06
  • Ishaya 53:10-11
  • Yakubu 01:21
  • Irmiya 06:16-19
  • Yona 02:7-8
  • Luka 01:47
  • Matiyu 22:37
  • Zabura 019: 07
  • Wahayin Yahaya 20:4

ranar hukunci

Ma'ana

Kalmar "ranar hukunci" na nufin wani lokaci a nan gaba sa'ad da Allah zai shar'anta kowanne taliki.

  • Allah ya sanya ɗansa, Yesu Almasihu, alƙalin dukkan mutane.
  • A ranar hukunci, Almasihu zai hukunta mutane bisa ga ɗabi'arsa ta adalci.

Shawarwarin Fassara:

  • Ana iya fassara wannan kalma "lokacin hukunci" tunda yana nufin fiye da rana ɗaya.
  • Sauran hanyoyin fassara wannan kalma na iya haɗawa da "ƙarshen zamani sa'ad da Allah zai hukunta dukkan mutane."
  • Wasu fassarorin na dasa wa akan wannan kalma suna nuna cewa sunan wata rana ce ko lokaci na musamman:" "Ranar hukunci" ko "Lokacin Hukunci."

(Hakanan duba: alƙali, Yesu, sama, lahira)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 10:12
  • Luka 11:31
  • Luka 11:32
  • Matiyu 10:14-15
  • Matiyu 12:36-37
  • Matiyu 12:36-37

ranar ƙarshe, kwanakin ƙarshe, kwanaki na gaba

Ma'ana

Kalmar "kwanakin ƙarshe" ko "kwanaki na gaba" yana nufin lokaci ko zamanin ƙarshen wannan duniya.

  • Tsawon wannan lokaci ba a san ƙurewarsa ba.
  • "Kwanakin ƙarshe" lokaci ne na hukunci bisa waɗanda suka kauce daga Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "kwanakin ƙarshe" za a iya fassarawa a matsayin "ƙarshen zamani" ko "ƙarshen lokutta."
  • A wasu nassosin, ana iya fassara wannan a matsayin "ƙarshen duniya" ko "sa'ad da wannan duniya ta kai ƙarshe."

(Hakanan duba: ranar Ubangiji, hukunci, juyawa, duniya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 03:3-4
  • Daniyel 10:14-15
  • Ibraniyawa 01:02
  • Ishaya 02:02
  • Yakubu 05:03
  • Irmiya 23:19-20
  • Yahaya 11:24-26
  • Mika 04:1

ranar Ubangiji, ranar Yahweh

Ma'ana

A cikin Tsohon Alƙawari "ranar Yahweh" ana ambatonta ne domin a nuna wani lokaci na musamman da Allah zai hukunta mutane sabo da zunubinsu.

  • Sabon Alƙawari a yau yana baiyana "ranar Ubangiji" a kan ranar da Yesu zai dawo ya sharianta mutane a ƙarshen lokaci.
  • Wannan hukunci na ƙarshe da kuma tashi daga matattu ke tafe shima ana ganinsa a kan "ranar Ubangiji." Wannan lokacin zai fara a lokacin da Yesu zai dawo domin ya shari'anta masu zunubi ya kuma kafa mulkinsa na har abada.
  • Kalmar nan "rana" a wasu lokutan ana moron ta domin a nuna wata rana ko kuma wani "lokaci" ko "taro" wanda ya wuce rana ɗaya.
  • A wani lokaci kuma ana ganin hukunci akan cewa shi ne "saukar da fushin Allah" a kan waɗanda ba su bada gaskiya ba.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga abin da ke rubuce a wurin, waɗansu hanyoyi da za a fassara "ranar Yahweh" za su iya haɗawa da "lokacin da Yahweh zai hukunta masu ƙin sa" ko kuma "lokacin fushin Yahweh."
  • Waɗansu hanyoyi kuma da za a fassara "ranar Ubangiji" sun haɗa da Ubangiji Yesu zai zo ya yi wa duniya shari'a."

(Hakanan duba: rana, ranar hukunci, Ubangiji, tashi daga matattu, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:05
  • 1Tassolonikawa 05:02
  • 2 Bitirus 03:10
  • 2 Tassalonikawa 02:02
  • Ayyukan Manzanni 02:20-21
  • Filibiyawa 01:9 -11.

rayuwa, rai, zauna, mai rai, da rai

Ma'ana

Dukkan waɗannan kalmomi na nufin kasancewa da rai a zahiri, ba mutuwa ba. Ana kuma amfani dasu a misali da nufin kasancewa da rai a ruhaniya. Na biye ma'ana "rayuwa a zahiri" da "rayuwar ruhaniya."

  1. Rayuwa a zahiri
  • Rayuwa a zahiri na nufin kasancewar ruhu cikin jiki. Allah ya hura rai a cikin jikin Adamu sai ya zama rayayyen taliki.
  • "Rayuwa" kuma na nufin wani taliki a matsayin "an ceto rai."
  • Wasu lokutta kalmar "rayuwa" na nufin abin da ake fuskanta a zaman rayuwa, "yana jin daɗin rayuwa."
  • Zai iya zama kuma tsawon ran mutum, kamar a bayanin, "ƙarshen rayuwarsa."
  • Kalmar nan "mai rai" zai iya kasancewa mai rai a zahiri, a matsayin "mahaifiyata na nan da rai." Zai kuma iya nufin zaunawa a wani wuri kamar, "suna zama a cikin birni."
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, fannin "rayuwa" yawancin lokaci ana gwada akasinsa da fannin "mutuwa."
  1. Rai ta Ruhaniya
  • Mutum yana da rai ta ruhaniya sa'ad da ya gaskanta da Yesu. Allah yakan ba mutumin nan sabon rai tare da Ruhu Mai Tsarki dake zaune cikinsa.
  • Wannan rai kuma ana ce da shi "rai madawwami" domin a nuna baya ƙarewa.
  • Akasin rai na ruhaniya shi ne mutuwar ruhaniya, ma'ana rabuwa da Allah da kuma shan hukunci na har'abada.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta bisa ga nassi, "rai" za a iya fasara shi a ce "zama a raye" ko "mutum" ko "lamiri" ko "wani" ko "ɗanɗanawa."
  • Kalmar nan "rayuwa" za a iya fasara ta haka "zama" ko "kasancewa" ko "ana nan."
  • Wannan furci "ƙarshen rayuwarsa" za a iya fasara shi zuwa "sa'ad da ya dena rayuwa."
  • Wannan furci "an tsare rayukansu" za a iya fasara shi haka "ya bar su su rayu" ko "bai kashe su ba."
  • Wannan furci "sun sadakar da ransu" za a iya fasara shi haka "sun sa kansu cikin hatsari" ko "sun yi wani abin da zai iya kashe su.
  • Sa'ad da nassin Littafi Mai tsarki yayi magana akan zaman rayayyu a ruhu, za a iya fassara "rayuwa" haka "rayuwar ruhaniya" ko "rai madauwwami" ya danganta ga nassi.
  • Wannan furci "rayuwar ruhaniya" za a iya fassarata haka "Allah yakan sa mu zama a raye a ruhohinmu" ko "sabon rai tawurin ruhun Allah" ko "an maida mu rayayyu a cikinmu."
  • Ya danganta ga yadda yake a nassi, wannan furci "bada rai" za a iya fassarawa "sa shi ya rayu" ko "bada rai madawwami" ko "sa shi rayu har abada."

(Hakanan duba: mutuwa, har abada)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Bitrus 01:03
  • Ayyukan Manzanni 10:42
  • Farawa 02:07
  • Farawa 07:22
  • Ibraniyawa 10:20
  • Irmiya 44:02
  • Yahaya 01:04
  • Littafin Al‌ƙalai 02:18
  • Luka 12:23
  • Matiyu 07:14

ringi

Ma'ana

Kalmar "ringi" fassara kai tsaye na manufar "sauran da suka rage" ko na mutane ko na wani abu daga masu yawa.

  • Yawancin lokatai "ringi" na nuna ragowar mutane ne waɗanda suka rayu daga cikin matsalar rayuwa ko suka yi tsayaya cikin aminci ga Allah yayin da suke fuskantar tsanani.
  • Ishaya ya yi magana game da ragowar Yahudawan da zasu rage sun tsira daga hare-haren bãƙi su kuma dawo ga ‌‌Ƙasar Alƙawari a Kana"an.
  • Manzo Bulus ya yi magana game da "ringi" mutanen da Allah ya zaɓa da zasu karɓi alherinsa.
  • Kalmar nuna "ringi" mutanen da basu yi aminci ba ko basu rayu ba ko ba a zaɓe su ba.

Shawarwarin Fassara:

  • Faɗa kamar haka "ringin mutanen nan" za a iya fassarawa haka "sauran mutanen nan" ko "mutanen da suka rage amintattu" ko "mutanen da aka bari."
  • "Dukkan ringin mutanen" za a iya fassarawa ta haka " dukkan sauran mutanen" ko "mutanen da suka rage."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:17
  • Amos 09:12
  • Ezekiyel 06:8-10
  • Farawa 45:07
  • Ishaya 11:11
  • Mika 04:6-8

roƙo a madadi, yin roƙo a madadi, aikin yin roƙo a madadi

Ma'ana

Kalmomin nan "roƙo" da "yin roƙo" na nufin yin roƙo domin wani ko a madadin wani mutum. A cikin Littafi Mai Tsarki harkullum wannan na nufin yin addu'a domin waɗansu mutane.

  • Maganan nan "yin roƙo domin" da kuma "tsaya wa a tsakani domin" yana nufin yin roƙo ga Allah domin amfanin sauran mutane.
  • Littafi Mai Tsarki na koyar da mu Ruhu Mai Tsarki na yin addu'a domin mu, Yana addu'a zuwa ga Allah domin mu.
  • Mutumin da ke roƙo domin sauran mutane ta wurin kai roƙonsu ga wata hukuma kowani mai mulki.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi na fassara "roƙo a madadi" zai haɗa da "yin roƙo domin" ko "roƙon wani domin ya yi wani abu domin (wani)."
  • Kalmar nan ana fassara ta da yin "koke" ko "roƙo" ko "addu'a ta matsananciyar bukata."
  • Kalmar nan "yin addu'a domin" za'a iya fassara ta "yin roƙo domin amfanin waɗansu" ko "yin koke a madadin" ko "roƙon Allah domin ya taimaki wani" ko "roƙon Allah ya albarkaci (wani)."

(Hakanan duba: addu'a)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ibraniyawa 07:25-26
  • Ishaya 53:12
  • Irmiya 29:6-7
  • Romawa 08:26-27
  • Romawa 08:33-34

Ruhu Mai Tsarki, Ruhun Allah, Ruhun Ubangiji, Ruhu

Ma'ana

Waɗannan kalmomi na nufin Ruhu Mai Tsarki, wanda shi Allah ne. Allah ɗaya na gaskiya wanda yake har bada a matsayin Uba, Ɗa, da Ruhu Mai Tsarki.

  • Ruhu Mai Tsarki shima "Ruhu ne" da kuma "Ruhun Yahweh" da "Ruhu na gaskiya."
  • Saboda Ruhu Mai Tsarki Allah ne, shi yana da cikakken tsarki kuma mara aibi ne kuma cikakke ta kowacce fuska a cikin kuma dukkan abin da yake yi.
  • Tare da Uba da Ɗa, Ruhu Mai Tsarki duk su suka hallici duniya.
  • Lokacin da Ɗan Allah, Yesu, ya koma sama, Allah ya aiko da Ruhu Mai Tsarki ga mutanensa domin ya shugabance su, ya koyar da su, ya ƙarfafa su, ya basu ikon yin nufin Allah.
  • Ruhu Mai Tsarki ne ya bi da Yesu yake kuma bi da waɗanda suka bada gaskiya cikin Yesu.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma cikin sauƙi za'a iya fassara ta da kalmomin da aka mora wajen fassara "tsarki" da "ruhu"
  • Hanyoyin fassara wannan kalma sun haɗa da "Tsaftataccen Ruhu" ko "Ruhu wanda yake mai Tsarki" ko "Allah Ruhu."

(Hakanan duba: tsarki, ruhu, Allah, Ubangiji, Allah Uba, Ɗan Allah, kyauta)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 10:10
  • 1 Tasalonikawa 04:7-8
  • Ayyukan Manzanni 08:17
  • Galatiyawa 05: 25
  • Farawa 01:1-2
  • Ishaya 63:10
  • Ayuba 33:04
  • Matiyu 12:31
  • Matiyu 28:18-19
  • Zabura 051:10-11

ruhu, ruhohi, ruhaniya

Ma'ana

Kalmar "ruhu" na nufin ɓangaren da ba na jiki ba a cikin mutum wanda ba a iya gani. Idan mutum ya mutu, ruhunsa na barin jikinsa. "Ruhu" akan iya danganta shi da halaiya ko lamiri.

  • Kalmar "ruhu" kan iya zama halittar da ba ta da gangar jiki a zahiri, masamman mugun ruhu.
  • Ruhun mutum ɓangarensa ne da kan san Yahweh ya kuma gaskata da shi.
  • Ga bakiɗaya, kalmar "ruhaniya" na nuna kowanne abu da ba a gani a duniya.
  • A cikin Littafi Mai Tsarki, masamman ya danganta shi da kowanne abu da yake da nasaba da Allah, masammanma ga Ruhu Mai Tsarki.
  • A misali, "abincin ruhaniya" na nufin Koyarwar Allah, wadda take kawo ingantuwa ga ruhun mutum, da kuma "hikima ta ruhu" na nufin sani da hali mai kyau da yake zuwa ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
  • Allah ruhu ne ya kuma halicci sauran ruhohin waɗanda basu da gangar jiki a zahiri.
  • Mala'iku suma ruhohi ne, harda waɗanda suka yiwa Allah tawaye suka zamanto mugayen ruhohi.
  • Kalmar "ruhun" tana nufin, "samin halaiya" kamar "ruhun hikima" ko "a cikin ruhun Iliya."
  • Misalan "ruhu" a kamar halaiya ko lamiri zai haɗa da "ruhun tsoro" da "ruhun baƙinciki."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, waɗansu hanyoyin fassara "ruhu" na iya haɗawa da "wanda ba a gani" ko "bangaren dake ciki."
  • A waɗansu nassosin, kalmar "ruhu" akan fassara ta da "mugun ruhu."
  • Waɗansu lokutan kalmar "ruhu" tana amfani wajen bayyana yadda mutum ya ke ji, kamar a "ruhuna yana ƙũna a cikin cikina." za a iya fassara wannan da " ina jin haushi a cikin ruhuna" ko " ina matuƙar damuwa."
  • Faɗar "ruhun" na iya fasartuwa da "halin" ko "rinjayar" ko "ɗabi'ar" ko "tunanin dake da halaiya da."
  • Ya danganta da nassin, "ruhaniya" na iya fasartuwa da kamar"abin da ba'a gani" ko "daga Ruhu Mai Tsarki" ko "na Allah" ko "ɓangaren abin da ba na duniya ba."
  • An sha amfani da "madara ta ruhaniya" akan fasarta ta da "tsagwaron koyarwa daga wurin Allah" ko " koyarwar Allah da take inganta ruhu (kamar yadda madara keyi)."
  • Faɗar "ballagar ruhaniya" akan iya fasarata da "halaiya ta gari da take nuna biyayya da Ruhu Mai Tsarki."
  • Kalmar "bayarwa ta ruhaniya" ta kan fasartu kamar "wata mahimmiyar dama da Ruhu Mai Tsarki kan bayar."

(Hakanan duba: mala'ika, aljani, Ruhu Mai Tsarki, rai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 05:05
  • 1 Yahaya 04:03
  • 1 Tasalonikawa 05:23
  • Ayyukan Manzanni 05:09
  • Kolosiyawa 01:09
  • Afisawa 04:23
  • Farawa 07:21-22
  • Ishaya 04:04
  • Markus 01:23-26
  • Matiyu 26:41
  • Filibiyawa 01:27

rumfar sujada

Ma'ana

Rumfar sujada rumfa ce ta musamman da Isra'ilawa ke yiwa Allah sujada cikin shekaru 40 da suka yi tafiya a jeji.

  • Allah ya ba Isra'ilawa umurnai domin ginin wannan babbar rumfar, wadda ke da ɗakuna biyu kuma tana zagaye da labule.
  • Duk sa'ad da Isra'ilwa suka matsa zuwa wani wuri a cikin dajin domin su zauna, sai firistoci su ɗauki rumfar sujadar zuwa sansanin suna gaba. Sai su sake shirya ta a tsakiyar sabon sansaninsu.
  • An yi rumfar sujadar da Itace aka zagaye ta da labulai da akayi da sutura, gashin akuya, da fatun dabbobi. tsakiyarta sun kewaye ta an kuma rufeta da labule.
  • Sassan rumfar sujadar guda biyu sune wuri mai tsarki (inda bagadin ƙona turare yake) da kuma wuri mafi tsarki (inda Akwatin Alƙawari yake).
  • Tsakiyar rumfar sujadar na da bagadi na ƙona hadayar dabbobi da kuma wasu tasoshi na musamman don tsarkakewa.
  • Isra'ilawa suka daina amfani da rumfar sujada lokacin da aka gina haikali a Yerusalem ta hannun Suleman.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "rumfar sujada" na nufin "wurin zama". Wasu hanyoyin fassara shi kuma zai iya zama "wuri mai tsarki" ko "rumfa inda Allah yake" ko "rumfar Allah."
  • A tabbatar cewa fassarar wannan kalmar ta banbanta da fassarar "haikali."

(Hakanan duba: bagadi, bagadin ƙona turare, akwatin alƙawari, haikali, rumfar taruwa)

Wuraren da ake samusa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 21:30
  • 2 Tarihi 01:2-5
  • Ayyukan Manzanni 07:43
  • Ayyukan manzanni 07:45
  • Fitowa 38:21
  • Yoshuwa 22:19-20
  • Lebitikus 10:16-18

saɓo, saɓa, saɓawa

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, wannan kalma "saɓo" shi ne faɗar maganar dake nuna mummunan rashin bangirma ga Allah ko mutane. "Saɓawa" mutum shi ne yin magana gãba da shi domin waɗansu su ɗauke shi marar gaskiya ko domin wasu su yi tunanin abu marar kyau game da shi.

  • Yawancin lokaci, saɓawa Allah shi ne faɗar ƙarairayi da maganganun reni, da faɗar rashin gaskiya game da shi ko kuma ta wurin nuna halin shashanci da zai ƙasƙantar da shi.
  • Saɓo ne taliki ɗan adam ya ce shi Allah ne ko kuma ya ce akwai wani allah banda Allah na gaskiya.
  • Wasu juyi na Turanci sun fassara wannan kalma da "kushewa" sa'ad da ake saɓon mutane.

Shawarwarin Fassara:

  • Za a iya fassara yin "saɓo" da "faɗar mugayen abu game da" ko "rashin ba Allah girmansa" ko "faɗar mugayen maganganun kushe shi."
  • Hanyoyin fassara "saɓo" za su haɗa har da "faɗin abubuwan daba dai-dai ba game da wasu" ko "kushe wani" baza jita-jitar ƙarya."

(Hakanan duba: rashin girmamawa, yanke)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Timoti 01:12-14
  • Ayyukan Manzanni 06:11
  • Ayyukan Manzanni 26:9-11
  • Yakubu 02:5-7
  • Yahaya 10:32-33
  • Luka 12:10
  • Markus 14:64
  • Matiyu 12:31
  • Matiyu 26:65
  • Zabura 074:10

sama, sararin sama, sararin sammai, sammai, na sama

Ma'ana

Kalmar nan da aka fassara ta da "sama" har kullum abin da take magana shi ne wurin da Allah yake rayuwa. Haka ma kalmar "sararin sama," ita ma ma'anarsu ɗaya ce ya danganta ga wurin.

  • Kalmar nan "sammai" tana nufin duk wani abu da muke gani a saman duniya, haɗe da rana, da wata, da taurari. Hakanan ya ƙunshi duk abin da ke a sararin sama, kamar su manisantan sammai, duniyoyi, da bamu iya gani kai tsaye daga duniya.
  • Kalmar nan "sararin sama" tana magana ne akan wanan shunaiyar da ke sararin sama wadda ke tattare da giza-gizai da kuma iskar da muke shaƙa. Sauu da yawa akan ce rana da wata suna "sararin sama ne."
  • A waɗansu wurare a cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "sama" zata iya nufin sararin sama ko kuma wurin da Allah yake rayuwa.
  • A lokacin da aka mori sama cikin salon magana, wata hanya ce ta ambaton Allah. Misali, lokacin da Matiyu ya yi rubutu game da "mulkin sama" yana magana ne akan mulkin Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan an mori sama cikin salon magana, za'a iya fassara ta da "Allah."
  • Domin "mulkin sama" a cikin littafin Matiyu, ya fi kyau a mari kalmar "sama" da yake ita aka sharara da ita a cikin bishara ta hanun matiyu.
  • Kalmar nan "sammai" ko "rundunar sama" ita ma za'a iya fassara ta da "rana, wata, da taurarin sama" ko "taurarin da ke cikin sammai."

(Hakanan duba: mulkin Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 08:22-24
  • 1 Tassalonokawa 01:8-10
  • 1 Tassalonikawa 04:17
  • Maimaitawar Shari'a 09:1
  • Afisawa 06:9
  • Farawa 01:1
  • Farawa 07:11
  • Yahaya 03:12
  • Yahaya 03:27
  • Matiyu 05:18
  • Matiyu 05:46-48

Sarkin Yahudawa, sarkin Yahudawa

Ma'ana

Kalmar "Sarkin Yahudawa" tãke ne dake nufin Yesu, Almasihun.

  • Karo na farko da Littafi Mai tsarki ya rubuta wannan tãken shi ne sa'ad da masu hikima suka mori kalmar da suka zo Baitalami suna neman jaririn wanda shi ne "Sarkin Yahudawa."
  • Mala'ika ya bayyanawa maryamu cewa ɗanta, zuriyar Sarki Dauda, zai zama sarki wanda mulkinsa zai dawwama har abada.
  • Kafin a gicciye Yesu, sojojin Roma cikin ba'a sun kira Yesu "Sarkin Yahudawa." wannan tãken kuma an rubuta shi a jikin katako aka buga da ƙusa a bisa gicciyen Yesu.
  • Yesu tabbas shi ne Sarkin Yahudawa kuma sarki bisa dukkan halitta.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "Sarkin Yahudawa" ana iya kuma fassara ta da "sarki bisa Yahudawa" ko "sarki mai mulki bisa Yahudawa" ko "babban mai mulkin Yahudawa."
  • A bincika a ga yadda aka fassara furcin "sarkin" a wasu wuraren cikin fassarar.

(Hakanan duba: zuriya, Yahudawa, Yesu, sarki, masarauta, masarautar Allah, masu hikima)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 23:03
  • Luka 23:28
  • Matiyu 02:02
  • Matiyu 27:11
  • Matiyu 27:35-37

sasantawa, an sasanta, sasantuwa, sulhu, sulhunta

Ma'ana

A "sasanta" da kuma "sasantawa" na nufin "yin sulhu" tsakanin mutanen da can baya maƙiyan juna ne. "Sasantawa" ayyuka ne na yin sulhu.

  • A Littafi Mai Tsarki, wannan kalmar na nuna yadda Allah ke sulhunta mutane zuwa gare shi ta wurin Ɗansa, Yesu Almasihu.
  • Saboda zunubi, dukkan mutane sun zama maƙiyan Allah. Amma saboda ƙaunarsa mai girma, Allah ya yi tanadin hanya domin mutane a sasanta su ta wurin Yesu.
  • Ta wurin yarda da hadayar da Yesu ya yi domin biyan fansar zunubansu, mutane zasu iya gafartawa su kuma sami salama da Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "sulhu" za a iya fassarawa haka "a kawo salama" ko "a maido da kyakkyawan zumunci" ko "a sa a zama abokai."
  • Kalmar "sulhuntawa" za a iya fassarawa haka "maido da kyakkyawan zumunci" ko "sanya salama" ko "a haddasa zumunci mai salama."

(Hakanan duba: salama, hadaya)

Wuraren ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 05:19
  • Kolosiyawa 01:18-20
  • Littafin Misalai 13:17-18
  • Romawa 05:10

sha biyun, sha ɗayan

Ma'ana

Kalmar "sha biyun" na ma'anar mazajen nan sha biyu da Yesu ya zaɓa su zama almajiransa na kurkusa, ko manzanni. Bayan da Yahuda ya kashe kansa, sai aka riƙa kiransu "sha ɗayan."

  • Yesu na da wasu almajiran da yawa, amma laƙabin "sha biyun" ya banbanta tsakanin waɗanda a fili suke kurkusa da Yesu.
  • Sunayen waɗannan almajirai sha biyun an lissafa su a Litattafan Matiyu 10, da Markus 3, da Luka 6.
  • Wani lokaci bayan da Yesu ya koma sama, "sha ɗayan" suka zaɓi wani almajiri mai suna Matiyas ya maye gurbin Yahuda. Daga nan aka sake komawa da kiransu "sha biyun."

Shawarwarin Fassara:

  • Ga wasu yarurrukan zai fi sauƙi kuma ga al'ada a kara da nahawun suna ace, "manzanni sha biyun" ko "almajiran Yesu na kurkusa sha biyu."
  • "Sha ɗayan" za a iya fassarawa haka, "almajiran Yesu da suka rage sha ɗayan."
  • Wasu juyin zasu so suyi amfani da manyan haruffa su nuna cewa anyi amfani da kalmar a matsayin laƙabi, kamar haka, "Sha Biyun" da "Sha Ɗayan."

(Hakanan duba: manzo, almajiri)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:5-7
  • Ayyukan Manzanni 06:02
  • Luka 09:01
  • Luka 18:31
  • Markus 10:32-34
  • Matiyu 10:07

shafewa, shafaffe

Ma'ana

Wannan kalma "shafewa" na nufin zuba wa wani mutum ko wani abu mai. Wani lokaci akan kwaɓa man da kayan ƙamshi, da zai bashi daɗin ƙamshin turare. Ana amfani da wannan kalmar game da Ruhu Mai Tsarki yadda yake zaɓa ya kuma bada iko ga wani mutum.

  • A Tsohon Alƙawari, firistoci, sarakai, da annabawa akan shafe su da mai don a keɓe su musamman domin hidima ga Allah.
  • Abubuwa kamar su bagadai ko rumfar sujada, akan shafe su da mai domin a nuna za a yi amfani da su don sujada da ɗaukaka Allah.
  • A Sabon Alƙawari, mutane masu ciwo akan shafe su da mai domin su warke.
  • A Sabon Alƙawari sau biyu aka rubuta cewa an shafe Yesu da man turare wato mace tayi wannan ta nuna sujadarta. A wani lokaci Yesu ya yaba mata ya ce tayi wannan domin shirya shi don jana'izarsa.
  • Bayan da Yesu ya mutu, abokansa suka shirya jikinsa domin jana'iza ta wurin shafe shi da mai da kayan ƙamshi.
  • Wannan laƙabi "Almasihu" (Ibraniyanci) da "Kristi"(Girik) ma'anar su "Shafaffen (Nan)."
  • Yesu Almasihu shi ne aka zaɓa aka ƙeɓe shi Annabi, Babban Firist, da Sarki.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, wannan kalma "shafewa" za a iya fassara ta zuwa "zuba mai a kai" ko "sa mai a kan" ko "keɓewa ta wurin zuba man ƙamshi a kai."
  • A "zama shafaffe" a iya fassara shi haka, "a keɓe da mai." ko "a zaɓa" ko "a keɓe."
  • A wasu nassosin kalmar "shafewa" za a fassara ta a ce "zaɓi."
  • Faɗa kamar "shafaffen firist," za a iya fasara shi ya zama "firist wanda aka ƙeɓe da mai" ko "firist da aka keɓe ta wurin zuba masa mai."

(Hakanan duba: Almasihu, keɓewa, babban firist, Sarkin Yahudawa, firist, annabi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:20
  • 1 Yahaya 02:27
  • 1 Sama'ila 16:2-3
  • Ayyukan Manzanni 04:27-28
  • Amos 06:5-6
  • Fitowa 29:5-7
  • Yakubu 05:13-15

shaida, bada shaida, mashaidi, masu shaida, mashaidi da ido, shaidu da ido

Ma'ana

Sa'ad da wani ya bada "shaida" yana bada bayani game da wani abu wanda ya sani, da jaddada cewa bayanin gaskiya ne. A "bada shaida" shi ne ayi "shaida."

  • Yawanci wani "yana shaida" game da abin da ya fuskanta kai tsaye.
  • Mashaidi wanda ya bada "shaidar ƙarya" baya faɗar gaskiyar abin da ya faru.
  • Wasu lokutan kalmar "shaida" na ma'anar anabci da annabi ya furta.
  • A cikin Sabon Alƙawari, wannan kalma ana yawan ambaton ta da nuna yadda mabiyan Yesu suka yi shaida game da al'amuran rayuwar Yesu, mutuwa, da tashinsa.

Kalmar "mashaidi" na nufin wani wanda ya fuskanci wani abu da ya faru kai tsaye. Yawanci mashaidi kuma wani ne ko wasu dake shaida kan abin da sukka sani cewa gaskiya ne. Kalmar "mashaidi da ido" na jaddada cewa wannan taliki na wurin kuma yaga abin da ya faru.

  • Ayi "shaidar" wani abu ana nufin aka sa'ad da ya faru.
  • A zaman shari'a, mashaidi na "bayar da shaida" ko "yana shaida." Wannan na da ma'ana dai-dai da "shaidawa."
  • Ana buƙatar shaidu su bada shaidar abin da suka gani ko suka ji.
  • Mashaidin da bai faɗi gaskiya ba game da abin da ya faru ana kiransa "mashaidin ƙarya." Za a ce ya bada "shaidar ƙarya" ko ya "faɗi shaidar ƙarya."
  • A faɗar "zama shaida tsakanin" yana ma'ana da cewa wani abu ko wani taliki zai zama shaidar cewa anyi yarjejeniya. Mashaidin zai tabbatar da cewa kowanne taliki ya yi abin da ya alƙawarta zai yi.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "yin shaida" ko "bada shaida" za a iya fassarawa haka, "faɗin gaskiyar" ko " "faɗin abin da aka gani" ko "aka ji" ko "faɗi daga abin da aka fuskanta kai tsaye" ko "bada tabbaci" ko "faɗin abin da ya faru."
  • Hanyoyin fassara "shaida" zai haɗa da, "bada rahoton abin da ya faru" ko "bayani akan abin da ke gaskiya" ko "tabbaci" ko "abin da aka riga aka faɗa" ko "anabci."
  • A faɗar, "a matsayin shaida a gare su" za a iya fassarawa haka, a "nuna masu abin da gaskiya" ko a "tabbatar masu da abin da ke gaskiya."
  • A faɗar, "a matsayin shaida gãba dasu" za a iya fassarawa haka, "wanda zai nunu masu zunubinsu" ko "bayyana riyarsu" ko "wanda zai tabbatar da cewa ba suyi dai-dai ba."
  • A "bada shaidar ƙarya" za a iya fassarawa haka, "a faɗi ƙarya game da" ko "tsara abubuwan daba gaskiya ba."
  • Kalmar "mashaidi" ko "mashaidi da ido" za a iya fassarawa tare da kalmar ko faɗar dake ma'anar "wanda ya gani" ko "wanda ya gan shi ya faru" ko "waɗanda suka gani kuma suka ji (waɗannan abubuwa)."
  • Wani abu da yake "mashaidi" za a iya fassarawa haka, "tabbaci" ko "shaidar alƙawarinmu" ko "wani abin dake shaida cewa wannan gaskiya ne."
  • A faɗar "zaku zama shaiduna" za a iya fassarawa haka, "zaku gayawa sauran mutane game dani" ko "zaku koyar da mutane gaskiyar dana koyar da ku" ko "zaku gayawa mutane abin da kuka ga na yi da abin da kuka ji na koyar."
  • A "shaida ga" za a iya fassarawa haka, a "faɗi abin da aka gani" ko a "yi shaida" ko a "zayyana abin da ya faru."
  • A "shaidi" wani abu za a iya fassarawa haka, a "dubi wani abu" ko a "fuskanci wani abin da ya faru."

(Hakanan duba: akwatin alƙawari, laifi, hukunci, annabi, shaida, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Maimaitawar Shari'a 31:28
  • Mika 06:03
  • Matiyu 26:60
  • Markus 01:44
  • Yahaya 01:07
  • Yahaya 03:33
  • Ayyukan Manzanni 04:32-33
  • Ayyukan Manzanni 07:44
  • Ayyukan Manzanni 13:31
  • Romawa 01:09
  • 1 Tasalonikawa 02:10-12
  • 1 Timoti 05:19-20
  • 2 Timoti 01:08
  • 2 Bitrus 01:16-18
  • 1 Yahaya 05:6-8
  • 3 Yahaya 01:12
  • Wahayin Yahaya 12:11

Shaiɗan, Iblis, mugun

Ma'ana

Koda yake iblis ruhu ne wanda Allah ya hallita, ya yi wa Allah tawaye ya kuma zama maƙiyin Allah. Iblis ana ce da shi kuma "Shaiɗan" da "mugun."

  • Iblis ya tsani Allah da dukkan abin da Allah ya hallita domin yana son ya ɗauki mazaunin Allah domin a kuma yi masa sujada kamar Allah.
  • Shaiɗan na jarabtar mutane domin su yi tawaye gãba da Allah.
  • Allah ya aiko ɗansa, Yesu, ya ceci mutane daga shugabancin shaiɗan.
  • Sunan "Shaiɗan" na nufin "magabci" ko "maƙiyi."
  • Kalmar "Iblis" na nufin "mai zargi."

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "iblis" za a iya fassarawa haka "mai zargi" ko "mugun" ko "sarkin miyagun ruhohi" ko "shugaban mugunruhu."
  • "Shaiɗan" za a iya fassarawa haka "abokin gãba" ko "magabci" ko wasu sunayen da zasu nuna cewa shi ne iblis.
  • Waɗannan kalmomi a fassara su daban da aljanu da miyagun ruhohi.
  • Ayi la'akari da yadda ake fassara waɗannan kalmomi a cikin yaren lardin ko na ƙasar.

(Hakanan duba: shaiɗan, mugu, mulkin Allah, gwaji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:08
  • 1 Tasalonikawa 02:17-20
  • 1 Timoti 05:15
  • Ayyukan Manzanni 13:10
  • Ayuba 01:08
  • Markus 08:33
  • Zakariya 03:01

shari'ar Musa, shari'ar Allah, shari'ar Yahweh, shari'a

Ma'ana

Dukkan waɗannan kalmomi na nufin dokoki da umarnai da Allah ya ba Musa domin Isra'ilawa suyi biyayya. Kalmomin "shari'a" ko "shari'ar Allah" ana amfani dasu da nufin dukkan abubuwan da Allah ke son mutanensa su yi biyayya dasu.

  • Ya danganta da nassin, "shari'a" na iya nufin:
  • Dokoki goma da Allah ya rubuta a bisa allon dutse domin Isra'ilawa
  • Dukkan dokokin da aka ba Musa
  • Litattafai biyar na farkon Tsohon alƙawari
  • Tsohon alƙawari bakiɗaya (yana kuma nufin "nassosi" a cikin Sabon alƙawari).
  • Dukkan umarnin Allah da nufinsa
  • Furcin "shari'a da annabawa" ana amfani da shi a Sabon Alƙawari ana nufin littafin Ibraniyawa (ko "Tsohon Alƙawari")

Shawarwarin Fassara:

  • Ana iya fassara wannan kalma a matsayin jam'i, "shari'u," tunda tana nufin umarnai masu yawa.
  • "Shari'ar Musa" ana iya fassarawa a matsayin "shari'un da Allah ya faɗi wa Musa ya bayar ga Isra'ilawa."
  • Ya danganta ga nassin, "shari'ar Musa" ana iya fassarawa a matsayin "shari'ar da Allah ya faɗi wa Musa" ko "shari'un Allah da Musa ya rubuta" ko "shari'un da Allah ya gaya wa Musa cewa ya bayar ga Isra'ilawa."
  • Hanyoyin fassara "shari'a" ko "shari'ar Allah" ko "shari'un Allah" zasu haɗa da "shari'u daga Allah" ko "dokokin Allah" ko "shari'un da Allah ya bayar" ko "dukkan abubuwan da Allah ya dokatar" ko "dukkan umarnan Allah."
  • Furcin "shari'ar Yahweh" ana iya fassarawa a matsayin "shari'un Yahweh" ko "shari'un da Yahweh ya ce ayi biyayya da su" ko "shari'u daga Yahweh" ko "abubuwan da Yahweh ya dokatar."

(Hakanan duba: umarnai, Musa, dokoki goma, bisa ga shari'a, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 15:06
  • Daniyel 09:13
  • Fitowa 28:42-43
  • Ezra 07:25-26
  • Galatiyawa 02:15
  • Luka 24:44
  • Matiyu 05:18
  • Nehemiya 10:29
  • Romawa 03:20

siffar Allah, siffa

Ma'ana

Kalmar nan "siffa" na nufin wani abu da ya yi kama da wani abu ko kama da halaiyar wani abu da bam. Kalmar nan " "siffar Allah" an yi amfani da ita a hanyoyi da bam da bam, bisa dai ga wurin.

  • A farkon lokaci, Allah ya halicci mutum "cikin siffarsa", wato, "cikin kamanninsa." Wannan na nufin cewa mutane na da wata ɗabi'a da ke nuana siffar Allah, kamar ji, yin tunani, magana, da kuma ruhun da ke cikin mu.
  • Littafi Mai Tsarki ya koya mana cewa Yesu ɗan Allah, "kammanin Allah ne," ma'ana shi da kansa Allah ne. Ba kamar mutane ne ba, ba a hallici Yesu ba. Tun farko can Yesu na da ɗabi'un Allah domin daidaitakarsu ɗaya da Allah Uba.

Shawarwarin Fassara:

  • In ana magana game da Yesu, kan "kamannin Allah" za'a fassara shi dada "cikkarkiyar kama da Allah"ko "matsayi ɗaya da Allah" ko "dai-dai da Allah."
  • In ana magana game da mutane "Allah ya hallice su cikin kamannisa" za'a iya fassar ta da cewa "Allah ya hallice su su zama kamar sa", ko "Allah ya hallice su da ɗabi'a irin tasa."

(Hakanan duba: siffa, Ɗan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Korintiyawa 04:3-4
  • Kolosiyawa 03:9-11
  • Farawa 01:26-27
  • Farawa 09:06
  • Yakubu 03:9-10
  • Romawa 08:28-30

Sihiyona, Tsaunin Sihiyona

Ma'ana

Asali waɗannan kalmomi "Sihiyona" ko "Tsaunin Sihiyona" na nuna wurin tsaro da mafaka da Sarki Dauda ya karɓe daga wurin Yebusawa. Kalmomin guda biyu ana amfani da su ana kiran Yerusalem.

  • Tsaunin Sihiyona da Tsaunin Moriya a bisa waɗannan tuddai birnin Yerusalem ke zaune. Daga baya, "Sihiyona" da "Tsaunin Sihiyona" sun zama kalmomin da ake amfani da su a ambaci birnin Yerusalem. Wani lokaci su na ma'anar haikalin dake a Yerusalem.
  • Dauda ya kira Sihiyona, ko Yerusalem, "Birnin Dauda." Wannan daban yake da ƙauyen da Dauda ya fito, Betlehem, wanda shima ana ce da shi Birnin Dauda.
  • Kalmar "Sihiyona" ana amfani da ita ta hanyoyi daban-daban, ana nuna bayyana Isra'ila ko masarautar Allah ta ruhaniya ko ga sabuwar Yerusalem basamaniya wadda Allah ke shiryawa.

(Hakanan duba: Ibrahim, Dauda, Yerusalem, Betlehem, Yebusawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 11:05
  • Amos 01:02
  • Irmiya 51:35
  • Zabura 076:1-3
  • Romawa 11:26

sujada

Ma'ana

Yin "sujada" na nufin a girmama, yabo da kuma yin biyayya ga wani, musamman Allah.

  • Wannan kalmar a zahiri na nufin "durkusawa ƙasa" ko " mutum ya rusuna da fuskansa ƙasa" domin girmama wani.
  • Muna yin sujada ga Allah sa'ad da muke bauta masa da kuma girmama shi, ta wurin yi masa yabo da yi masa biyayya.
  • Sa'ad da Isra'ilawa ke yiwa Allah sujada, sukan yi hadayar dabbobi a bisa bagadi.
  • Wasu na yiwa allolin ƙarya sujada.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "sujada" za a iya fassarawa a matsayin "rusunawa ƙasa ga" ko "girmamawa da hidima" ko "girmamawa da biyayya."
  • Wasu nassosin, za a iya fassarawa a matsayin "yabo mai tawali'u" ko "bayar da girmamawa da yabo."

(Hakanan duba: hadaya, yabo, girmamawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Kolosiyawa 02:18-19
  • Maimaitawar Shari'a 29:18
  • Fitowa 03:11-12
  • Luka 04:07
  • Matiyu 02:02
  • Matiyu 02:08

suna, sunaye, sa suna

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "suna" an yi amfani da ita domin misali.

  • A wasu nassin, "suna" zai iya zama ɗaukaka kai, misali "bari mu yiwa kanmu suna."
  • Wannan magana "suna" na da manufar tunawa da wani abu. Ga misali, "a datse sunayen gumaku" na nufin a rushe waɗannan gumaku domin kada a ƙara tunawa da su ko ayi masu sujada.
  • A yi magana "cikin sunan Allah" na nufin yin magana cikin ƙarfinsa da ikonsa, ko kuma a matsayin wakilinsa.
  • idan an ce "sunan" wani mutum ana nufin dukkan abin da mutumin nan ya ƙunsa sukutum, misali "ba wani suna duk duniyan nan inda ya isa mu sami ceto."

Shawarwarin Fassara:

  • Magana kamar wannan "sunansa mai kyau" za a iya fassarawa zuwa "an san shi da hali mai kyau"
  • Yin wani abu "a sunan wane" za a iya fassarawa haka "tare da ikon wane" ko "da yardar wane" ko "a matsayin wakilin" wane.
  • Wannan magana "muyi wa kanmu suna" za a iya fassara wa haka "mu sa mutane da yawa su sanmu" ko "mu sa mutane su yi tsammanin muna da mahimmanci."
  • Wannan furci "kiran sunansa" za a iya fassarawa haka "raɗa masa suna" ko "a bashi suna."
  • Wannan furci "waɗanda suke ƙaunar sunanka" za a iya fassara shi haka "masu ƙaunarka."
  • Wannan furci "datse sunan gumaku" za a iya fassara shi haka "zubar da gumakun matsafa don kada a ƙara tunawa da su" ko "a sa mutane su dena bautar gumaku" ko "a lalatar da dukkan gumaku domin kada mutane su ƙara ko tunawa da su.

(Hakanan duba: kira)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 02:12
  • 2 Timoti 02:19
  • Ayyukan Manzanni 04:07
  • Ayyukan Manzanni 04:12
  • Ayyukan Manzanni 09:29
  • Farawa 12:02
  • Farawa 35:10
  • Matiyu 18:05

tashi daga matattu

Ma'ana

Kalmar "tashi daga matattu" na manufar ayyukan sake dawowa da rai kuma bayan an mutu.

  • A tada wani daga matattu na nufin a sake maido da wannan mutum zuwa ga rayuwa kuma. Allah kaɗai ke da iko ya yi wannan.
  • Kalmar "tashi daga matattu" na bayyana musamman dawowar Yesu da rai bayan da ya riga ya mutu.
  • Da Yesu ya ce, "Ni ne Tashin matattu da kuma Rai" yana nufin shi ne tushen tashi daga matattu, da kuma wanda yake sa mutane su dawo da rai.

Shawarwarin Fassara:

  • "Tashi daga matattun" na wani za a iya fassarawa haka "dawowa da rai" ko yana "sake dawowa da rai bayan ya mutu."
  • Taƙaitaccen ma'anar wannan kalma "tashi tsaye" ko "aikin tadawa(daga matattu)." Waɗannan suma wasu hanyoyi ne na fassara wannan kalma.

(Hakanan duba: rai, mutuwa, tashi)

Wuraren ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 15:13
  • 1 Bitrus 03:21
  • Ibraniyawa 11:35
  • Yahaya 05:28-29
  • Luka 20:27
  • Luka 20:36
  • Matiyu 22:23
  • Matiyu 22:30
  • Filibiyawa 03:11

tawali'u, yin tawali'u, ƙasƙantarwa, halin tawali'u

Ma'ana

Kalmar nan "tawali'u" na bayyana mutum wanda baya ɗaukan kansa cewa ya fi wani. Bai da da girman kai ko fahariya. Tawali'u shi ne a zama da hali na rashin ɗaga kai.

  • Zama da tawali'u a gaban Allah na nufin mutun ya gane kasawarsa da rashin cikarsa in an kwatanta da girmansa, hikimarsa, cikarsa.
  • Lokacin da mutum ya zama da tawali'u ya sa kansa a ƙaramin matsayi.
  • Halin tawali'u shi ne kula da bukatun sauran mutane fiye da bukatun mutum.
  • Hakanan halin tawali'u na nufin yin hidima da nuna gurbin da ya kamata a lokacin da mutum ke moron baiwarsa.
  • Batun nan "zama mai mai tawali'u" za'a iya fassara shi da "kada ka nuna girman kai."
  • "Ku zama da tawali'u a gaban Allah" za'a iya fassara ta da "Ku miƙa nufinku ga Allah, ku yi la'akari da girmansa."

(Hakanan duba: girman kai)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Yakubu 01:21
  • Yakubu 03:13
  • Yakubu 04:10
  • Luka 14:11
  • Luka 18:14
  • Matiyu 18:04
  • Matiyu 23:12

tetrak

Ma'ana

Kalmar "tetrak" na nufin wani muƙaddashin gwamnati dake mulkin sashen Daular Roma. Kowanne tetrak na ƙarƙashin ikon sarkin Roma wato emfero.

  • Laƙabin "tetrak" na ma'anar "ɗaya daga cikin masu mulki huɗu."
  • Farawa daga ƙarƙashin Emfero Diyokiletiyan, an raba daular Roma cikin manyan sassa huɗu kuma kowanne tetrak na mulkin sashe ɗaya.
  • Masarautar Herod "Babban," wanda ya zamanto shi ne sarki sa'ad da aka haifi Yesu, an raba ta kashi huɗu bayan mutuwarsa, kuma 'ya'yansa maza suka yi mulki a matsayin "tetrakai," ko "masu mulkin huɗu."
  • Kowanne sashe na da ƙaramin sashe ko ƙananan sassa da ake kira "larduna," kamar su Galili ko Samariya.
  • "Tetrak Herod" ya sami ambato sau da yawa a cikin Sabon Alƙawari. An sanshi kuma da suna "Herod Antifas."
  • Kalmar "tetrak" za a iya fassarawa haka, "gwamnan gunduma" ko " mai mulkin lardi" ko "mai mulki" ko "gwamna."

(Hakanan duba: gwamna, Herod Antifas, lardi, Roma, mai mulki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 03:1-2
  • Luka 09:07
  • Matiyu 14:1-2

tsabta, tsabtacewa

Ma'ana

Wannan kalma tsabta ma'anarta shi ne rashin dauɗa ko ɗigon datti. A cikin Littafi mai Tsarki yawancin lokaci akan yi misali da shi a ce "mai kyau," "mai tsarki," ko "marar zunubi."

  • "Tsabtacewa" hanyoyin gyara wani abu ne domin ya zama da "tsabta." Za a iya fasara shi haka "wanki" ko "tsarkakewa."
  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya gaya wa Isra'ilawa dabbobi masu "tsabta" da mararsa "tsabta." Dabbobi masu tsabta ne kawai aka basu izini su ci ko suyi hadaya da su. Idan bisa ga wannan ne kalmar nan "tsabta" ma'anarta ya zama dabbar da Allah ya karɓa domin yin hadaya.
  • Mutumin dake da wata cutar fata zai ƙazamtu har sai fatar ta warke yadda ba zata iya bazuwa ba kuma. Dole ayi biyayya da ka'idodin tsarkake fata domin a iya furta wannan mutumin "tsarkakakke."
  • Wasu lokatai wannan kalma "tsabta" ana misalta ta da tsabtar rai.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma za a iya fassara ta da kalman nan "tsabta" ko "marar aibu."

(Hakanan duba: ɓatawa, aljani, tsarki, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 07:02
  • Farawa 07:08
  • Maimaitawar Shari'a 12:15
  • Zabura 051:07
  • Littafin Misalai 20:30
  • Ezekiyel 24:13
  • Matiyu 23:27
  • Luka 05:13
  • Ayyukan Manzanni 08:07
  • Ayyukan Manzanni 10:27-29
  • Kolosiyawa 03:05
  • 1 Tasalonikawa 04:07
  • Yakubu 04:08

tsarkake, a tsarkake, tsarkakewa

Ma'ana

A tsarkake na nufin a keɓe ko a maishe da tsarki. Tsarkakewa shi ne yadda ake maishe wa da tsarki.

  • A Tsohon Alƙawari, wasu mutane da abubuwa an tsarkake su, ko a keɓe, domin hidima ga Allah.
  • Sabon Alƙawari na koyarwa cewa Allah ya tsarkake mutane waɗanda suka bada gaskiya ga Yesu. Wato, ya maishesu masu tsarki ya kuma keɓe su domin su yi masa sujada.
  • Masu bada gaskiya ga Yesu an dokace su da su tsarkake kansu ga Allah, su zama da tsarki cikin dukkan abin da suke yi.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, kalmar "tsarkake" za a iya fassarawa haka "a keɓe" ko "a maida da tsarki" ko "a tsarkake."
  • Sa'ad da mutane suka tsarkake kansu, sun tsarkake kansu kuma sun bada kansu ga hidimar Allah. Yawanci kalmar "keɓewa" a cikin Littafi Mai Tsarki ana amfani da ita da wannan manufar.
  • Sa'ad da ma'anar ta zama "keɓewa," wannan kalma za a iya fassarawa haka "a keɓe wani (ko wani abu) ga hidimar Allah."
  • Ya danganta da nassin, faɗar "tsarkakewarka" za a iya fassarawa "sanya ka tsarkaka" ko "keɓe ka (domin Allah)" ko "abin da zai sa ka yi tsarki."

(Hakanan duba: tsarkakke, mai tsarki, keɓaɓɓe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 04:3-6
  • 2 Tasalonikawa 02:13
  • Farawa 02:1-3
  • Luka 11:2
  • Matiyu 06:8-10

tsarki, tsarkakakke, marar tsarki, keɓaɓɓe

Ma'ana

Kalmar nan "tsarki" da "tsarkakakke" na nufin halaiyar Allah wadda aka ware ta aka kuma keɓe ta daga duk wani abu na zunubi da kuma kasawa.

  • Allah ne kaɗai yake da cikakken tsarki. Ya kan mayar da mutane da abubuwa su zama da tsarki.
  • Mutumin da ke da tsarki mallakar Allah ne kuma an keɓe shi sabo da yiwa Allah hidima da kuma kawo masa ɗaukaka.
  • Wani abu da Allah ya aiyana shi mai tsarki si ne wanda ya keɓe shi domin ɗaukakarsa da kuma amfaninsa, kamar su bagadi wanda yake domin miƙa hadaya gare shi.
  • Mutane baza su iya kusantarsa ba har sai ya yardar masu su kusance shi, domin shi mai tsarki ne su kuma mutane ne masu zunubi kasassu kuma.
  • A cikin Tsohon Alƙawari, Allah ya keɓe firistoci su zama tsarkaka domin hidima ta musamman a gare shi. Suna bukatar wata sujada ta keɓewa domin tsarkake su daga zunubi domin su iya samun damar kusantar Allah.
  • Allah ya keɓe waɗansu wurare na musamman da kuma abubuwa da ke nasa ko a cikin abin da ya baiyana kansa, kamar haikalinsa.

Bisa ga ma'anar wannan kalma "marar tsarki" ko "ƙazantacce" tana baiyana abu wanda ba ya girmama Allah.

  • Ana amfani da wanan domin a nuna wani wanda ba ya girmama Allah ta wurin tayar masa.
  • Abin da aka kira "marar tsarki" akan dube shi a matsayin abu da ya ƙazantu. Kuma ba na Allah ba ne.

Kalmar nan wuri mai tsarki tana baiyana wani abu ne da ke da nasaba da bautar Allah ko ga bautar arna ta allohlin ƙarya.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, kalmar nan "keɓewa" akan fi moron ta ne wajen baiyana dutse da kuma waɗansu abubuwa da ake mora cikin sujada ga allohlin ƙarya. Za a kuma iya fassara wannan a matsayin "abu na addini."
  • "Waƙoƙi masu tsarki" da "kaɗe-kaɗe masu tsarki" suna nufin waƙoƙi da kaɗe da muke yi domin ɗaukakar Yahweh" ko "waƙoƙi na yabon Allah."
  • Batun nan "aiki mai tsarki" na nufin "aikin addini" ko "hidimar sujada" da firist ke yi a jagorantar mutane cikin yin sujada ga Allah. haka nan zata iya nufin aikin sujada da firistocin arna ke yi domin bautar allohlin ƙarya.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "tsarki" sun haɗa da "keɓewa domin Allah" ko "mallakar Allah" ko "mai cikin tsarki" ko "cikakke marar zunubi" ko "rababbe daga zunubi."
  • A "tsarkake" har kullum ana fassara shi da "tsarkakewa" a hausa zamu ƙara da cewa "keɓe (wani) domin ɗaukakar Allah."
  • Hanyoyin da za a fassara "marar tsarki" sun haɗa "rashin tsarki" ko "zama ba na Allah ba" ko "rashin girmama Allah" ko "rashin jin tsoron Allah."
  • A waɗansu wuraren, "rashin tsarki" za a fassara shi a "matsayin ƙazantacce."

(Hakanan duba: Ruhu Mai Tsarki, keɓewa, tsarkakewa, warewa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 28:22
  • Sarakuna 03:2
  • Littafin Makoki 04:1
  • Ezekiyel 20:18-20
  • Matiyu 07:6
  • Markus 08:38
  • Ayyukan Manzanni 07:33
  • Ayyukan Manzanni 11:8
  • Romawa 01:22
  • 2 Korintiyawa 12:3-5
  • Kolosiyawa 01:22
  • 1 Tasalonikawa 03:13
  • 1 Tasalonikawa 04:7
  • 2 Timoti 03:15

tsarki, tsarkakakke, tsarkakewa

Ma'ana

Ma'anar zama "tsarkakakke" shi ne kasancewa ba aibi ko abu ya zama babu gauraye a cikinsa da bai kamata ya kasance ba. Tsarkake wani abu shi ne a wanke shi a fitar da duk wani abin daya ƙazantar ko ya ɓata shi.

  • Game da dokokin Tsohon Alƙawari, "tsarkaka" da "tsarkakewa" na magana ne musamman akan wankewa daga abubuwa dake sa kaya ko mutum ya ƙazantu a addini, kamar su cuta, miƙin jiki, ko haifar jariri.
  • Tsohon Alƙawari kuma na da dokoki masu gaya wa mutane yadda za su tsarkaka daga zunubi, yawancin lokaci ta wurin yin hadaya da dabba. Wannan domin ɗan lokaci ne kuma hadayar dole a yita maimaita ta akai akai.
  • A cikin Sabon Alƙawari, yawancin lokaci tsarkakewa na nufin wankewa daga zunubi.
  • Hanya guda ɗaya ce tak da mutane za su iya tsarkaka gabaɗaya kuma har abada daga zunbansu shi ne ta wurin tuba da karɓar gafarar Allah, ta wurin dogara ga Yesu da hadayarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana "tsarkakewa" za a iya fassarawa haka "a sa ya tsarkaka" ko "wankewa" ko "wankewa daga dukkan ƙazantarwa" ko "a yar da dukkan zunubi."
  • Furci makamancin haka "da lokacin tsarkakewarsu ya cika" za a iya fassarawa haka "sa'ad da suka tsarkake kansu ta wurin jira kwanakin da aka ƙayyada su cika."
  • Wannan magana "tanada tsarkakewa domin zunubai" za a iya fassara shi haka "tanada hanya da mutane za su tsarkaka gabaɗaya daga zunubansu."
  • Wasu hanyoyin fassara "tsarkakewa" zai haɗa da waɗannan "wankewa" ko "wankewa ta ruhaniya" ko "zama da tsabta ta wurin aikace aikacen addini."

(Hakanan duba: kaffara, tsabta, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1Timoti 01:05
  • Fitowa 31:6-9
  • Ibraniyawa 09:13-15
  • Yakubu 04:08
  • Luka 02:22
  • Wahayin Yahaya 14:04

tsoro, halin jin tsoro, jin tsoro

Ma'ana

Kalmar nan "tsoro" da jin t"soro" tana nufin wani ji ne a cikin jiki wanda bashi da daɗi ko kuma mai gigitarwa a cikin yanayin da mutum ya gane akwai cutarwa da zata same shi ko kuma waɗansu.

  • Kalmar nan "tsoro" za'a iya fassara ta da matƙar girmamawa ga mutumin da ke kan mulki.
  • Kalmar nan "tsoron Yahweh," duk ɗaya ce da kalmar "tsoron Allah" da kuma "tsoron Ubangiji," duk suna magana ne akan matuƙar girmamawa ga Allah kuma ana nuna wanan girmamawar ta wurin yi masa biyayya. Wanan tsoron yakan samu ne ta sanin cewa Allah mai tsarki ne kuma baya son zunubi.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar da mu cewa mutumin da ke tsoron Yahweh zai zama mai fahimi.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da wurin, aji "tsoro" za'a iya fassara shi a yi matuƙar bada "girma" ko girmamawa sosai, ko "tsananin girmamawa."
  • Kalmar nan "tsoro" za'a iya fassara ta da kalmar "gigicewa" ko "ɗimauta" ko furgita."
  • Kalmar nan "Tsoron Allah ya sauko a kan dukkansu" za'a iya fassara ta da cewa, "duk sun yi farin ciki, suka kuma girmama Allah sosai" ko "can baya suna jin tsoron Allah sosai (sabo da ikonsa mai girma)."
  • Kalmar nan "kada ku ji tsoro" itama za'a iya fassara ta da "ku dena jin tsoro."
  • Lura da kalmar "tsoron Yahweh" bata faɗo ba a cikin Sabon Alƙawari. Amma sai aka mori kalmar "yi tsoron Ubangiji" ko "tsoron Ubangiji Allah" shi aka mora a maimako haka.

(Hakanan duba: mamaki, tsananin girmamawa, Ubangiji, iko, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 04:18
  • Ayyukan Manzanni 02:43
  • Ayyukan Manzanni 19:15-17
  • Farawa 50:21
  • Ishaya 11:3-5
  • Ayuba 06:14
  • Yona 01:09
  • Luka 12:05
  • Matiyu 10:28
  • Littafin Misalai 10:24-25

Ubangiji Yahweh, Yahweh Allah

Ma'ana

A cikin Tsohon Alƙawari, yawancin lokaci ana amfani da "Ubangiji Yahweh" idan ana magana akan Allah na gaskiya.

  • Wannan magana "Ubangiji" sunan allantaka ne kuma "Yahweh" sunan Allah ne kansa.
  • Yawancin lokaci ana haɗa Yahweh da Allah ya zama "Yahweh Allah."

Shawarwarin Fassara:

  • Idan wannan suna "Yahweh" an yi amfani da shi domin fassara sunan Allah kansa, To, waɗannan sunaye "Ubangiji Yahweh" da "Yahweh Allah" za a iya fassara su suma dai-dai. Kuma a lura da yadda wannan suna "Ubangiji" aka fassara shi a wasu nassin sa'ad da ana magana akan Allah.
  • Wasu yarurruka suna sa sunan girmamawa bayan sunan sai su fassara shi haka "Yahweh Ubangiji." A yi lura da abin da ya amince a yaren da ake yin juyi: idan sunan girmamawa ko "Ubangiji" ya zo kafin ko bayan "Yahweh"?
  • "Yahweh Allah" za a iya fassarawa haka "Allah da ake kira Yahweh" ko "Alllah wanda shi ne Rayayyen Nan" ko "Ni ne wanda nake Allah."
  • Idan fassarar ta bi yadda aka saba faɗin "Yahweh" shi ne "Ubangiji" ko UBANGIJI," wannan magana "Ubangiji Yahweh" za a iya fssara ta haka "Ubangiji Allah" ko "Allah wanda shi ne Ubangiji". "Wasu fassarorin masu yiwuwa sune, "Ubangidana Ubangiji" ko "Allah shi Ubangiji ne."
  • Wannan furcin "Ubangiji Yahweh" kada a sa shi a haka "Ubangiji UBANGIJI" saboda mai yiwuwa masu karatu ba zasu fahimci bambancin ba a girman rubutu da aka saba amfani da shi a rarrabe waɗannan maganganu biyu kuma za a dube shi da shakka.

(Hakanan duba: Allah, ubangiji, Ubangiji, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 04:3-4
  • 2 Sama'ila 07:21-23
  • Maimaitawar Shari'a 03:23-25
  • Ezekiyel 39:25-27
  • Ezekiyel 45:18
  • Irmiya 44:26
  • Littafin Al‌ƙalai 06:22
  • Mika 01:2-4

ubangiji, Ubangiji, maigida

Ma'ana

Wannan kalma "ubangiji" na nufin wani mutum da ya mallaki ko yana da iko bisa wasu mutane.

  • Wannan kalma wani lokaci ana fassarawa haka "maigida" sa'ad da ana magana da Yesu ko idan ana magana da wani mutum wanda ya mallaki bayi.
  • Wasu juyin Turanci sun fassara wannan zuwa "sa" a sa'ad da wani mutum yana magana da na sama da shi a muƙami.

Sa'ad da aka rubuta "Ubangiji" da babban harufi ana nufin Allah, (A lura fa, sa'ad da aka yi amfani da ita domin magana da wani ko kuma an fara rubutu da wannan kalmar za a fara da babban harufi da ma'anar "sa" ko "ubangidana.")

  • A cikin Tsohon Alƙawari, an yi amfani da waɗannan furci "Ubangiji Allah Mai Iko Dukka" ko "Ubangiji Yahweh" ko "Yahweh Ubangijinmu."
  • Cikin Sabon Alƙawari, manzanni sun yi amfani da wannan magana haka "Ubangiji Yesu" da "Ubangiji Yesu Almasihu," wanda ya fayyace cewa Yesu Allah ne.
  • Wannan magana "Ubangiji" a cikin Sabon Alƙawari an yi amfani da ita kaɗai wajen ambaton Allah, musamman a cikin nassi da aka ɗauko daga Tsohon Alƙawari. Misali, Tsohon Alƙawari yace "Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunan Yahweh" sai Sabon Alƙawari ya ce "Mai albarka ne wanda yake zuwa a cikin sunnan Ubangiji."
  • A cikin ULB wannan sunan naɗi "Ubangiji" an yi amfani da shi ne kawai domin a fassara zahiri yadda kalmomin Ibraniyanci da Helinanci suka bada ma'anar "Ubangiji. Ba a taɓa amfani da shi a fassara sunan Allah (Yahweh) kamar yadda ake yi a wasu juyi da yawa.
  • Wasu yaruruka sukan fassara "Ubangiji" su ce "Maigidana" ko "Mai Mulki" ko wasu furci da suka nuna mallaƙa ko mai mulki dukka.
  • A madaidaicin nassi, wasu juyi da yawa sukan yi amfani da babban harufa a rubuta wannan kalmar domin mai karatu ya fahimci cewa wannan sunan naɗi ana nufin Allah ne.
  • A wasu wurare a Sabon Alƙawari inda aka ɗebo magana a Tsohon Alƙawari, za a iya amfani da wannan furci "Ubangiji Allah" domin a bayyana sosai wannan ana nufin Allah ne.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan magana za a iya fassarata ƙawanyarta "maigida"sa 'ad da ana nufin mutum da ya mallaƙi bayi. Bawa zai iya amfani da ita yayi magana da wanda yake wa aiki.
  • Sa'ad da ana nufin Yesu, idan mai maganan ya na ganin Yesu malamin addini ne, sai a fassara shi da bangirma domin malamin addini misali "mallam."
  • Idan wanda yake magana akan Yesu amma bai san shi ba, za a iya fassara "ubangiji" da girmamawa ace "mallam". Wannan fassarar za a iya amfani da ita a inda akwai buƙatar nuna bangirma a cikin nassi ga wani mutum.
  • Sa'adda ana magana akan Allah Uba ko Yesu, wannan magana sunan naɗi ne za a fara rubuta shi da babban harufa haka "Ubangiji" a Hausance.

(Hakanan duba: Allah, Yesu, mai mulki, Yahweh)

Wuraren da za a samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 39:02
  • Yoshuwa 03:9-11
  • Zabura 086:15-17
  • Irmiya 27:04
  • Littafin Makoki 02:02
  • Ezekiyel 18:29
  • Daniyel 09:09
  • Daniyel 09:17-19
  • Malakai 03:01
  • Matiyu 07:21-23
  • Luka 01:30-33
  • Luka 16:13
  • Romawa 06:23
  • Afisawa 06:9
  • Filibiyawa 02:9-11
  • Kolosiyawa 03:23
  • Ibraniyawa 12:14
  • Yakubu 02:01
  • 1Bitrus 01:03
  • Yahuza 01:05
  • Wahayin Yahaya 15:04

umarta, umarci, umarni

Ma'ana

Wannan kalma "umarci" shi ne a dokaci wani mutum ya yi wani abu. "Umarta" ko "umarni" abin da aka dokaci wani mutum yayi ne.

  • Koda shike waɗannan kalmomi suna da ma'ana ɗaya, "umarni" yawancin lokaci ana nufin wasu dokokin Allah waɗanda tsararru ne kuma basa sakewa, kamar "Dokoki Goma."
  • Umarni zai iya zama haka ("Ka girmama iyayenka") ko doka ("Ba zaka yi sata ba").
  • Idan aka "karɓi umarni" ma'ana "an bada doka" ko "a bishe da" wani abu ko wani mutum.

Shawarwarin Fassara

  • Zai fi kyau a fassara wannan maganar dabam da, "shari'a." Kuma zai yi kyau a kwatanta fassararsa da "dokoki" da "ka'idodi."
  • Wasu masu fassara za su fi so su fasara "umarta" da "umarni" da kalma iri guda a yarensu.
  • Waɗansu za su fi so su yi amfani da wata kalma musamman domin umarni da zai nuna daɗewar, tsararrun umarnai da Allah yayi.

(Hakanan duba: umarni, farilla, shari'a, dokoki goma)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Luka 01:06
  • Matiyu 01:24
  • Matiyu 22:38
  • Matiyu 28:20
  • Littafin Lissafi 01:17-19
  • Romawa 07:7-8

wa'adi, wa'adodi, anyi wa'adi

Ma'ana

Wa'adi alƙawari ne da mutum yake yi ga Allah. Mutumin ya yi alƙawari ne zai yi wani abu na musamman domin ya girmama Allah ko ya yi ibadarsa ga Allah.

  • Bayan da wani ya yi wa'adi, yana da nauyi a kansa na cika wannan wa'adi.
  • Littafi Mai Tsarki ya koyar da cewa duk wanda ya yi wa'adi amma bai cika wa'adinsa ba za a hukunta shi.
  • Wasu lokuta mutumin na iya roƙon kariyar Allah ko ya yi masa tanadi ta sanadiyyar yin wa'adinsa.
  • Amma ba lalle bane Allah ya cika buƙatar da mutum ya nema daga gare shi domin ya yi wa'adi.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta da nassin, "wa'adi" za a iya fassarawa haka "alƙawari na ladama" ko "alƙawarin da aka yiwa Allah."
  • Wa'adi wata rantsuwa ce ta musamman da ake yi ga Allah.

(Hakanan duba: alƙawari, rantsuwa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korintiyawa 07:27-28
  • Ayyukan Manzanni 21:23
  • Farawa 28:21
  • Farawa 31:12-13
  • Yona 01:14-16
  • Yona 02:9-10
  • Littafin Misalai 07:14

wanda aljani ya kama

Ma'ana

Mutumin da aljani ya kama yana da aljani ko kuma mugun ruhun da ke sarrafa shi akan abin da yake tunani ko yi.

  • A lokuta da yawa mutumin da mugun ruhu ya buge yakan ciwatar da kansa ko kuma sauran mutane domin aljanin yakan sa shi ya yi haka.
  • Yesu ya warkar da mutane waɗanda aljanu suka kama ta wurin umartar aljanun su fita daga cikinsu. Wannan akan fi yawan kira da "fitar" da aljanu.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi da za'a yi fassara wanda aljani ya kama sune sune "mai aljanu" ko "mai bugun aljanu" ko wanda ke da mugun ruhu a cikinsa."

(Hakanan duba: aljani)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Markus 01:32
  • Matiyu 04:24
  • Matiyu 08:16
  • Matiyu 08:33

warewa daban

Ma'ana

Kalmar "warewa da ban" na nufin warewa daga wani abu domin wani dalili. Kuma "warewa daban" waɗansu mutane ko wani abu na nufin a ware su " da ban".

  • Isra'ilawa an ware su domin bautar Yahweh.
  • Ruhu Mai Tsarki ya umarci kiristoci a Antiyok su ware Bulus da Barnabas domin aikin da Yahweh yake so suyi.
  • Mai bi wanda ya "ware" don hidima ga Yahweh an ware shi ne domin cika nufin Yahweh.
  • Ɗaya daga cikin ma'anar "tsarki" shi ne a keɓe a matsayin kayan Yahweh a kuma ware daga hanyar zunubi ta duniya.
  • A "tsarkake" wani na nufin a ware mutum domin aikin Yahweh.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "a ware daban" kan haɗa da " zaɓe na musamman" ko "warewa daga gare ka" ko a "ɗauki wani ɓangaren domin wani aiki na musamman".
  • A "ware daban" za a iya fassara shi a kamar " iya warewa (daga)" ko " a iya zaɓenka na musamman."

(Hakanan duba: tsarki, tsarkakewa, zaɓe)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 03: 17-19
  • Fitowa 31:12-15
  • Littafin Alƙalai 17:12
  • Littafin Lissafi 03: 11-13
  • Filibiyawa 01:1-2
  • Romawa 01:01

wawa, wawaye, marar kangado, mai halin wawanci

Ma'ana

Kalmar nan "wawa" tana nufin mutum ne wanda hafr kullum kan yi zaɓin da ba dai-dai ba, musamman zaɓi na rashin biyayya. Kalmar "wawanci" na nuna mutum wanda halinsa bai da hikima.

  • A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar "wawa" tana magana ne akan mutum wanda bai yi imani da Allah ba ko kuma marar biyayya da Allah. Wanan ya sha bamban da mutum mai hikima wanda ya dogara ga Allah yake kuma biyayya da Allah.
  • A cikin Zabura, Dauda ya baiyana wawa a matsayin mutum wanda bai yi imani da Allah ba, mutumin da ya jahilci dukan shedun Allah a cikin hallitarsa.
  • Littafin Misalai a cikin Tsohon Alƙawari na shima ya nuna yadda wawa ko wawanci yake.
  • Kalmar nan "wawanci" tana nufin duk wani aiki na rashin hikima domin ya saɓawa nufin Allah. A mafi yawan lokuta kalmar wawanci na nufin yin wani abu na ganganci ko na wauta.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "wawa" za'a iya fassara ta da "wawan mutum" ko "mutum marar hikima" ko "mutum marar hankali" ko "mutum marar tsoron Allah."
  • Hanyoyin fassara "wawanci" sun haɗa da "ƙarancin ganewa" ko "rashin azanci" ko "rashin hankali."

(Hakanan duba: azanci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Littafin Mai Wa'azi 01:17
  • Afisawa 05:15
  • Galatiyawa 03:3
  • Farawa 31:28
  • Matiyu 07:26
  • Matiyu 25:8
  • Littafin Misalai 13:16
  • Zabura 049:13

wuri mai tsarki

Ma'ana

A cikin Littafi mai Tsarki, kalmar nan "wuri mai tsarki" da "wuri mafi tsarki" tana nufin waɗansu ɓangarori biyu ne na ginin haikali ko alfarwa.

  • "Wuri mai tsarki" shi ne ɗaki na farko, kuma ya haɗa da bagadi na ƙona turare da kuma teburi da gurasa ta musamman "gurasa keɓaɓɓiya" a kansa.
  • "Wuri mafi tsarki" shi ne, sashe na biyu na ƙuryar ɗaki kuma yana da akwatin alƙawari a ciki.
  • Kakkauran labule mai nauyi shi ne ya raba tsakar ɗakin da ɗaki na ciki.
  • Babban firist shi ne kaɗai aka ba damar shiga cikin wuri mafi tsarki.
  • A waɗansu lokutan "wuri mafi tsarki" na nufin ginin da kuma harabar ginin haikali ko majami'a. Kuma za'a iya duben sa a wuri da aka keɓe domin Allah.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar nan "wuri mai tsarki" za'a iya fassara ta da "ɗakin da aka keɓe domin Allah" ko "ɗaki na musamman domin saduwa da Allah" ko "wurin da aka keɓe domin Allah".
  • Kalmar nan "wuri mafi tsaki" za'a iya fassara ta a matsayin ɗaki da aka fi keɓewa domin Allah."
  • Ya danganta ga wurin, hanyoyin fassara bayani na bai ɗaya game da "wuri mai tsarki sun haɗa da "wurin da aka keɓe" ko "wurin da Allah ya keɓe" ko "wani wuri a cikin haikali, wanda yake da tsarki" ko "farfajiyar haikalin Allah mai tsarki."

(Hakanan duba: bagadin turare, akwatin alƙawari, gurasa, keɓaɓɓe, farfajiya, labule, tsarki, wararre, alfarwa, haikali)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:16-18
  • Ayyukan Manzanni 06:12-15
  • Fitowa 26:33
  • Fitowa 31:10-11
  • Ezekiyel 41:01
  • Ezra 09:8-9
  • Ibraniyawa 09:1-2
  • Lebitikus 16:18
  • Matiyu 24:15-18
  • Wahayin Yahaya 15:05

yadda, an yadda, abin yadda, isar yadda

Ma'ana

A "yadda" da wani abu ko wani mutum shi ne a gsakata cewa abin ko mutumin gaskiya ne ko abin dogaro ne. Wannan gaskatawar ita ma ana kiranta "yadda." Mutum "abin yadda" shi ne talikin da zaka yadda da shi cewa zai yi kuma zai faɗi abin da ke dai-dai da gaskiya kuma, saboda haka wannan shi ne keda halin "isar yadda."

  • Yadda na dangantaka kurkusa da bangaskiya. Idan muka yadda da wani, muna bada gaskiya da wannan su yi abin da suka ce za su yi.
  • Kasancewa da yadda da wani yana ma'ana kuma dogara ne da wannan taliki.
  • A "yadda da" Yesu na ma'anar a gaskata da cewa shi Allah ne, a gaskata da cewa ya mutu bisa gicciye domin ya biya zunubanmu, kuma mu dogara da shi domin ya cece mu.
  • "Zance abin yadda" na nufin wani abu da aka ce wanda za a iya lissafa shi a matsayin gaskiya.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "gaskiyar" zasu haɗa da "bangaskiya" ko "kasancewa da bangaskiya" ko "kasancewa da ƙarfafawa" ko "dogara da."
  • Faɗar "ku sanya bangaskiyar ku cikin" ya yi dai-dai sosai da "bangaskiya cikin."
  • Kalmar "abin yadda" za a iya fassarawa haka "abin dogara" ko "abin amincewa" ko "abin yadda koyaushe."

(Hakanan duba: bangaskiya, gabagaɗi, gaskatawa, amincewa, gaskiya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:22-24
  • 1 Timoti 04:09
  • Hosiya 10:12-13
  • Ishaya 31:1-2
  • Nehemiya 13:13
  • Zabura 031:05
  • Titus 03:8

Yahweh

Ma'ana

Kalmar "Yahweh" sunan Allah ne na musamman da ya bayyana sa'ad da ya yi magana da Musa a kurmi mai ci da wuta.

  • Sunan "Yahweh" ya samu ne daga kalmar dake nufin "kasancewa" ko "wanzuwa."
  • Wasu ma'anonin "Yahweh" sun haɗa da, "shi ne" ko "Ni ne" ko "wanda ke sanyawa a kasance."
  • Wannan suna na bayyana cewa Allah ya kasance tun fil'azar kuma zai ci gaba da kasancewa har abada. Tana kuma nuna cewa yana nan koyaushe.
  • Bisa ga al'ada, juyin Littafi Mai Tsarki masu yawa sun yi amfani da kalmar "UBANGIJI" ko "UBANGIJIN" a madadin "Yahweh." Wannan al'adar ta zo ta dalilin yadda a tarihi, Yahudawa suka ji tsoron yin kuskure wajen furta sunan Yahweh sai suka fara kira "Ubangiji" a duk sa'ad da kalmar "Yahweh" ya bayyana a karatu. Litattafai na zamani sun rubuta "UBANGIJI" dukkan kalmomi manyan domin su nuna bangirmansu ga sunan Allah da kuma domin su banbanta shi daga "Ubangiji" wanda ita ma wata kalma ce daban a Ibraniyanci.
  • Juyin ULB ta yi amfani da sunan "Yahweh" kamar yadda aka rubuta shi cikin Tsohon Alƙawari.
  • Kalmar "Yahweh" babu ita sam a Sabon Alƙawari na asali; sai dai kalmar a yadda take a Girik "Ubangiji" aka yi amfani da ita, har ma wasu kalmomi daga Tsohon Alƙawari haka suke.
  • A Tsohon Alƙawari, idan Allah ya yi magana game da kansa, yakan kira sunansa ne.
  • Idan ya yi amfani da "Na" ko "Ni," ULB na nuna wa mai karatu da cewa Allah ke magana.

Shawarwarin Fassara:

  • "Yahweh" za a iya fassarawa da kalma ko faɗar dake da ma'ana "Ni ne" ko "mai ran nan" ko "wanda yake" ko "wanda ke da rai."
  • Wannan kalmar kuma za a iya rubutawa ta hanya da ta yi kama da yadda ake rubuta "Yahweh."
  • Wasu ɗarikun ikilisiyoyi basu so suyi amfani da kalmar "Yahweh" a maimako suna amfani da sunan al'ada, "UBANGIJI." Wani abin la'akari mai muhimmanci shi ne wannan zai zama da ruɗami sa'ad da ake karatu da ƙarfi domin sautin furci zai yi dai-dai da yadda ake kiran "ubangiji." Wasu yarurrukan suna iya kasancewa da harufi ko wani alamar jimal da za a haɗa domin su banbanta "UBANGIJI" a matsayin sunan "Yahweh" daban da "ubangiji" a matsayin laƙabi.
  • Zai fi kyau idan mai yiwuwa ne abar sunan Yahweh yadda yake a duk inda ya wanzu a cikin nassi, amma wasu fassarorin zasu gwammace suyi amfani da laƙabin suna a wasu wurare, domin a sa nassin ya zama da saukin fahimta.
  • A gabatar da faɗar da qani abu kamar haka, "Wannan ne abin da Yahweh ta faɗa."

(Hakanan duba: Allah, ubangiji, Ubangiji, Musa, bayyanawa)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 21:20
  • 1 Sama'ila 16:07
  • Daniyel 09:03
  • Ezekiyel 17:24
  • Farawa 02:04
  • Farawa 04:3-5
  • Farawa 28:13
  • Hosiya 11:12
  • Ishaya 10:04
  • Ishaya 38:08
  • Ayuba 12:10
  • Yoshuwa 01:09
  • Littafin Makoki 01:05
  • Lebitikus 25:35
  • Malakai 03:04
  • Mika 02:05
  • Mika 06:05
  • Littafin Lissafi 08:11
  • Zabura 124:03
  • Rut 01:21
  • Zakariya 14:5

Yahweh mai rundunai, Allah mai rundunai, rundunar sama, rundunar sammai, Ubangiji mai rundunai

Ma'ana

Kalmomin "Yahweh mai runduna" da "Allah mai runduna" laƙabai ne dake bayyana ikon Allah bisa dubban mala'ikun dake masa biyayya.

  • Kalmar "runduna" ko "rundunai" kalma ce dake bayyana abu mai yawa, kamar rundunar mutane ko taruwar taurari masu yawan gaske. Yana iya zama kuma dukkan hallitun ruhohi, har ma da mugayen ruhohi. Nassin na iya bayyana wane irin ruhu ake nufi.
  • Kalmomi dai-dai da "rundunar sammai" na bayyana dukkan taurari, duniyoyi da wasu hallitun samaniya.
  • A Sabon Alƙawari, kalmar, "Ubangiji mai rundunai" duk ma'anarsu ɗaya ne da "Yahweh mai rundunai" amma ba za a iya fassara su haka ba domin kalmar Ibraniyanci ta "Yahweh" ba a yi amfani da ita ba a Sabon Alƙawari.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin fassara "Yahweh mai rundunai" zasu haɗa da, Yahweh, wanda ke mulkin dukkan mala'iku" ko "Yahweh, mai mulki bisa mayaƙan mala'iku" ko "Yahweh, mai mulki bisa dukkan halitta."
  • Faɗar "rundunai" a cikin kalmomin "Allah mai rundunai" da "Ubangiji mai rundunai" za a fassara su dai-dai yadda aka fassara faɗar "Yahweh mai rundunai" a sama.
  • Wasu ikilisiyoyi basu karɓi ainihin kalmar "Yahweh" ba kai tsaye amma sun fi so suyi amfani manyan haruffan kalmar, "UBANGIJI" a maimako, bin al'adar juyin Litattafai Masu Tsarki da yawa. Game da waɗannan ikilisiyoyi, fassarar kalmar "UBANGIJI mai rundunai" za a yi amfani da ita a Tsohon Alƙawari domin "Yahweh mai rundunai."

(Hakanan duba: mala'ika, iko, Allah, ubangiji, Ubangiji, Ubangiji Yahweh, Yahweh)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Zakariya 13:02

yashewa, halin yashewa, yasasshe, watsattse

Ma'ana

Kalmar nan "yashewa" tana nufin yin watsi da wani ko kuma a watsar da wani abu. Mutumin da aka yashe shi wani ya yi banza da shi kenan, ko kuma ya yi watsi da shi kenan.

  • Lokacin da mutanen Allah suka "yashe" da Allah sun kasance da rashin aminci kenan ta wurin yi masa rashi biyayya.
  • Sa'ad da Allah ya yi watsi da mutanensa, ya dena temakon su, ya kuma bar su su fuskanci tsanani domin hakan ya sa su juyo gare shi.
  • Kalmar nan zata iya nufin yin watsi da waɗansu abubuwa, kamar dai yin watsi da koyarwar Allah.
  • Kalmar nan "yasasshe" za'a iya moron ta a matsayin shuɗaɗɗen lokaci kamar ya "yashe ku" ko kuma yin magana akan wani da aka yashe shi."

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu hanyoyi da za'a fassara wanan kalmar sun haɗa da yin "watsi" ko yin "banza" ko "bari" ko "kora" ko barin mutum can baya," ya danganta da wurin.
  • "Yashe" da dokokin Allah za'a fassara shi da yin rashin biyayya da dokokin Allah." Wanan za'a iya fassara shi "yin watsi" "bari" ko "dena biyayya" ga koyarwarsa ko shari'unsa.
  • Kalmar nan "a yashe" za'a iya fassara ta "za'a yi watsi" ko za'a "guje"
  • Yafi ganewa in an mori waɗansu kalmomi mabambanta domin fassara wanankalma, ya danganta da wurin ko dai wurin na magana ne akan yashe da mutum ko wani abu.

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sarakuna 06:11-13
  • Daniyel 11:29-30
  • Farawa 24:27
  • Yoshuwa 14:16-18
  • Matiyu 27:45-47
  • Littafin Misalai 27:9-10
  • Zabura 071:18

Yesu, Yesu Kristi, Kristi Yesu

Ma'ana

Yesu ɗan Allah ne. Sunan "Yesu" na ma'anar "Yahweh na ceto." Kalmar "Almasihu" take ne dake ma'anar "Shafaffe" ana kuma kiran kalmar Kristi ko Mesaya.

  • Yawanci sunayen biyu ana haɗa su a matsayin "Yesu Almasihu, Yesu Kristi" ko "Almasihu Yesu" ko "Kristi Yesu." Wannan na jaddada cewa ɗan Allah shine Mesaya ko Almasihu, wanda ya zo ya ceci mutane daga madawwamin hukuncin azaba domin zunubansu.
  • Ta hanyar al'ajibi, Ruhu Mai tsarki yasa aka haifi madawwamin ɗan Allah aka haife shi a matsayin mutum. Mahaifiyarsa ta wurin mala'ika aka gaya mata cewa ta kira shi "Yesu" domin an ƙaddara shi ya ceci mutane daga zunubansu.
  • Yesu ya aiwatar da al'ajibai da yawa waɗanda suka bayyana cewa shi Allah ne cewa kuma shine Almasihun, ko Mesaya, ko Kristi.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin harsuna da yawa "Yesu" da "Kristi" ana rubuta shi ta hanyar da idan an furta sautin sa zai zama kusan yadda ake furtawa a asalinsa. A misali, "Yesukristo," "Yezus Kristus" "Yesus Kristos," da "Hesukristo" wasu daga cikin hanyoyi ne da ake fassara shi cikin harsuna daban-dabam.
  • Game da taken "Kristi, Almasihu," wasu masu fassarar sunfi so su bar sunan a matsayin "Mesaya" yadda ake rubutawa a harshensu.
  • A kuma yi la'akari da yadda ake rubuta wannan suna a wasu ƙananan harsuna na kusa da manyan harsuna na ƙasa.

(Hakanan duba: Almasihu, Kristi, Allah, Allah Uba, babban firist, masarautar Allah, Maryamu, Mai ceto, Ɗan Allah)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Korantiyawa 06:11
  • 1 Yahaya 02:02
  • 1 Yahaya 04:15
  • 1 Timoti 01:02
  • 2 Bitrus 01:02
  • 2 Tassalonikawa 02:15
  • 2 Timoti 01:02
  • Ayyukan Manzanni 02:23
  • Ayyukan Manzanni 05:30
  • Ayyukan Manzanni 10:36
  • Ibraniyawa 09:14
  • Ibraniyawa 10:22
  • Luka 24:20
  • Matiyu 01:21
  • Matiyu 04:03
  • Filibiyawa 02:05
  • Filibiyawa 02:10
  • Filibiyawa 04:21-23
  • Wahayin Yahaya 01:06

yi addu'a, addu'a, addu'oi, addu'ewa

Ma'ana

Wannan kalma "addu'a" magana ce da Allah. Waɗannan maganganu ana amfani da su kuma ga mutanen da suke ƙoƙarin yin magana da gumaku.

  • Mutane zasu iya yin addu'a shuru, suyi magana da Allah da tunaninsu, ko su yi addu'a da ƙara, suna magana da Allah da muryarsu. Wasu lokatan ana rubuta addu'a, kamar yadda Dauda ya rubuta addu'arsa a Littafin Zabura.
  • Addu'a za ta iya ƙunsar roƙon Allah jinƙai, domin taimako a wata matsala da kuma domin hikima a ɗaukar wasu matakai.
  • Yawancin lokaci mutane sukan roƙi Allah ya warkar da mutane marasa lafiya ko waɗanda suke buƙatar taimakonsa a wasu fannoni.
  • Mutane kuma sukan yi godiya da yabon Allah sa'ad da suke addu'a a gare shi.
  • Addu'a ta haɗa da furta zunubanmu ga Allah da roƙonsa ya gafarta mana.
  • Ana kiran magana da Allah "zumunci" da Allah sa'ad da ruhunmu yana magana da ruhunsa, muna gaya masa yadda muke ji kuma muna jin daɗin kasancewarsa da mu.
  • Za a fassara wannan haka "magana da Allah" ko "zumunta da Allah." Fassara wannan magana yakamata a haɗa har da addu'a shuru.

(Hakanan duba: gunki, gafartawa, yabo)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tasalonikawa 03:09
  • Ayyukan Manzanni 08:24
  • Ayyukan Manzanni 14:26
  • Kolosiyawa 04:04
  • Yahaya 17:09
  • Luka 11:1
  • Matiyu 05:43-45
  • Matiyu 14:22-24

yin hidima, hidima

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki, kalmar nan "hidima" manufarta bauta wa wasu ne ta wurin koya masu maganar Allah da kuma kulawa da buƙatunsu na ruhaniya.

  • A cikin Tsohon Alƙawari, firist zai yiwa Allah "hidima" a cikin haikali ta wurin miƙa masa hadayu.
  • Cikin "hidimarsu" har da lura da haikali da miƙa addu'o'i ga Allah domin mutane.
  • Aikin yiwa mutane "hidima" zai haɗa tare da ciyar da su a ruhaniya ta wurin koya masu game da Allah.
  • Wannan kuma ya ƙunshi bauta wa mutane a cikin jiki kamar lura da marasa lafiya, da ciyar da matalauta.

Shawarwarin Fassara:

  • A cikin yiwa mutane hidima, za a iya fassara "hidima" haka "bauta" ko "ayi lura da" ko "biyan buƙatar wani."
  • Idan ana magana akan hidima a haikali, wannan kalma "hidima" za a iya fassarawa haka " bauta wa Allah a cikin haikali ko "miƙa haɗayu ga Allah domin mutane."
  • Idan ana yiwa Allah hidima, za a iya cewa "bauta wa" ko "ana yiwa Allah aiki."
  • Wannan furci "yin hidima ga" za a iya fassara shi haka, "lura da" ko "biyan buƙatu" ko "taimako."

(Hakanan duba: bauta, hadaya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Sama'ila 20:23-26
  • Ayyukan Manzanni 06:04
  • Ayyukan Manzanni 21:17-19

yin kaciya, kaciya

Ma'ana

Wannan kalma "yin kaciya" yanke loɓar abin fitsarin ɗa namiji ne. Za a iya bikin yin kaciya game da wannan.

  • Allah ya umarci Ibrahim yayi wa kowanne ɗa na miji a cikin iyalinsa da barorinsa kaciya alamar alƙawarin Allah da shi kenan.
  • Allah ya umarci zuriyarsa su cigaba da yin haka don kowanne yaron da aka haifa a gida.
  • Wannan furci "kaciyar zuciya" fasarar shi ne "yankewa" ko "fitar da zunubi daga mutum.
  • A cikin ruhaniya, "masu kaciya" sune mutane waɗanda Allah ya tsarkake daga zunubi tawurin jinin Yesu kuma sune mutanensa.
  • Wannan furci "marar kaciya" na nufin waɗanda ba a yi masu kaciyar jiki ba. Zai iya zama kamar misalin waɗanda ba a yi masu kaciyar ruhaniya ba, waɗanda ba su da zumunci da Allah.

Shawarwarin Fassara

  • idan a yaren masu yin fassara akwai al'adar kaciyar maza, kalmar da suke amfani da ita sai ayi amfani da ita a wannan.
  • Wasu hanyoyin fassara wannan kalma sune, "yanka kewaye" ko "yanka a zagaye" ko "yanke loɓar abin fitsarin maza."
  • A al'adar da ba a san kaciya ba, zai zama dole a fassara shi a ƙarshen shafin littafi.
  • A tabbata kalmar da aka yi amfani da ita wajen fassara bai haɗa da mãta ba. Mai yiwuwa ya zama dole a fassara da kalma ko furci da zai haɗa da ma'anar "namiji."

(Hakanan duba: Ibrahim, alƙawari)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Farawa 17:11
  • Farawa 17:14
  • Fitowa 12:48
  • Lebitikos 26:41
  • Yoshuwa 05:03
  • Littafin Alƙalai 15:18
  • 2 Sama'ila 01:20
  • Irmiya 09:26
  • Ezekiyel 32:25
  • Ayyukan Manzanni 10:44-45
  • Ayyukan Manzanni 11:03
  • Ayyukan Manzanni 15:01
  • Ayyukan Manzanni 11:03
  • Romawa 02:27
  • Galatiyawa 05:03
  • Afisawa 02:11
  • Filibiyawa 03:03
  • Kolosiyawa 02:11
  • Kolosiyawa 02:13

zabura, zaburai

Ma'ana

Wannan magana "zabura" na nufin keɓaɓɓun waƙoƙi, yawancin lokaci an rubuta su kamar haddace da za a raira.

  • Littafin Tsohon Alƙawari na Zabura nada tarin waɗannan waƙoƙi waɗanda Sarki Dauda ya rubuta da wasu Isra'ilawa kamar su Musa, Suleman, da Asaf, da dai sauransu.
  • Al'ummar Isra'ila sun yi amfani da waɗannan zaburan a cikin sujadarsu ga Allah.
  • Za a iya amfani da zabura a bayyana murna, bangaskiya, da girmamawa, da kuma ciwo da baƙinciki.
  • A cikin Sabon Alƙawari, an gargaɗemu muyi waƙoƙin zabura ga Allah a matsayin yi masa sujada.

(Hakanan: Dauda, bangaskiya, murna, Musa, tsarki)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Ayyukan Manzanni 13:33
  • Ayyukan Manzanni 13:35
  • Kolosiyawa 03:16
  • Luka 20:42

zaɓaɓɓe, wanda aka zaɓa, zaɓaɓɓu, zaɓi, Zaɓaɓɓun Mutane, kirayayyu, zaɓaɓɓu

Ma'ana

Kalmar nan "zaɓaɓɓe tana nufin wanda aka zaɓo" ko "mutanen da aka zaɓo" kuma tana nufin waɗanda Allah ya naɗa ko ya zaɓo su zama mutanensa. "Zaɓaɓɓe"ko zaɓaɓɓu na Allah" muƙami ne dake magana game da Yesu, wanda shi ne Zaɓaɓɓen masihi.

  • Kalmar nan "zaɓi" tana nufin zaɓenwani abu ko wani mutum ko kuma zaɓi na yin wani abu. An fi amfani da ita wajen nuna yadda Allah ya naɗa mutane su zama mutanensa, su kuma bauta masa.
  • Zama zaɓaɓɓe na nufin a zaɓi mutum domin yin wani aiki.
  • Allah ya zaɓi mutane su zama da tsarki, su zama keɓaɓɓu ta wurinsa sabo da su bada 'ya'ya masu kyau na ruhaniya. Shi ya sa ake kiran su "zaɓaɓɓu."
  • Kalmar nan "wanda aka zaɓa" wani abu ne da aka mora a cikin Littafi Mai tsarki domin a yi magana kan waɗansu mutane, kamar Musa da sarki Dauda waɗanda Allah ya naɗa su zama shugabannin mutanensa. Hakanan ana moron ta domin ayi magana akan banin Isra'ila a matsayin zaɓaɓɓun mutanen Allah
  • Kalmar nan" kirayayyu" tsohuwar kalma ce ta "zaɓɓaɓu." wadda ke nufin waɗanfa aka kira ana nufin masu bin Yesu kristi.
  • A cikin tsohuwar hausa an ta morar zaɓaɓɓu da kirayayyu a cikin Tsohon Alƙawari da Sabon Alƙawari sababbin fassarori suna magana akan "kirayayyu" a cikin Sabon Alƙawari ana amfani da wanan kalma ne akan waɗanda aka ceta ta wurin bada gaskiya a cikin Yesu, kusan a cikin dukkan Littaf Mai Tsarki an fassara wanan kalma akan "zaɓaɓɓu."

Shawarwarin Fassara:

  • Ya fi kyau a fasarta "zaɓaɓu" da kalmar kirayayyu ko "mutanen da aka zaɓo" a a iya fassara wanan da kalmar mutanen da Allah ya kirawo su zama nasa."
  • Kalmar nan "waɗanda aka zaɓo" za a iya fassara ta da "waɗanda aka ƙaddara" ko "waɗanda aka keɓe" ko "waɗanda Allah ya zaɓo."
  • "Na zaɓe ku" za 'a iya fassara ta da "na naɗa ku."
  • A wurin Yesu, za'a iya fassara "zaɓaɓɓu" a matsayin zaɓaɓbun mutanen Allah, ko "zaɓaɓɓen Masaya" (ko "wanda Allah ya zaɓa ya ceci mutanen duniya)."

(Hakanan duba: zaɓe, Kristi)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 2 Yahaya 01:1
  • Kolosiyawa 03:12
  • Afisawa 01:3-4
  • Ishaya 65:22-23
  • Luka 18:7
  • Matiyu 24:19-22
  • Romawa 08:33

zaɓe, zaɓi, zaɓaɓɓe

Ma'ana

Wannan kalma "zaɓe" da "zaɓaɓɓe" ana magana ne game da idan an zaɓi wani mutum ya yi wani aiki na musamman ko domin ya cike wani gurbi.

  • Idan "an zaɓa" za a iya cewa "zaɓaɓɓe" domin ya karɓi wani abu, kamar a ce, "zaɓaɓɓe don rai na har abada" Wannan na nufin an zaɓe su domin su karɓi rai madawwami.
  • Wannan furcfaɗar "zaɓaɓɓen lokaci" ana nufin "lokacin da Allah ya ƙaiyada" ko "lokcin da aka shirya" domin wani abu ya faru.
  • Wannan kalma "zaɓe" za a iya fassarata da ma'ana haka "in an umarta" ko "asa" wani mutum ya yi wani aiki.

Shawarwarin Fassara:

  • Ya danganta ga nassin, hanyoyin fassara "zaɓe" zai iya zama "zaɓi" ko "asa" ko "ƙuri'ar zaɓe" ko "wakilci."
  • Wannan kalma "zaɓaɓɓe" za a iya fassarawa ta zama "an sanya" ko "shirya" ko "zaɓaɓɓe musamman."
  • Wannan faɗar "an naɗa" za a iya fasara ta a ce "an zaɓa."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Sama'ila 08:11
  • Ayyukan Manzanni 03:20
  • Ayyukan Manzanni 06:02
  • Ayyukan Manzanni 13:48
  • Farawa 41:33-34
  • Littafin Lissafi 03:9-10

zama 'ya'ya, maidawa 'ya'ya

Ma'ana

Wannan furci "zama 'ya'ya" yana nuna hanyar da wani bisa tsarin shari'a zai iya zama ɗan wasu mutane waɗanda ba su suka haife shi cikin jiki ba.

  • Littafi mai Tsarki ya yi amfani da "zama 'ya'ya" domin a misalta yadda Allah yake sa mutane su shigo cikin iyalinsa, ya sa cikin ruhaniya su zama 'ya'yansa maza da mata.
  • Waɗanda suka zama 'ya'ya, masu gaskatawa sun zama magãda tare da Yesu Almasihu, suna da dukkan 'yancin da 'ya'ya maza da mata na Allah suke da shi.

Shawarwarin Fassara:

  • Wannan kalma za a iya fassara ta da irin furci da masu juyi zuwa yarensu suke amfani da ita su faɗi irin dangantakar dake musamman tsakanin iyaye da yaro. A tabbatar an gane cewa ana bada misali ne ko kuma ma'ana ne cikin ruhaniya.
  • Wannan furci "ɗanɗana zama 'ya'ya" za a iya juya shi ya zama, "Allah ya ɗauki wasu a matsayin 'ya'yansa" ko "'zama 'ya'yan (ruhaniya) na Allah."
  • A "jira zama 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a sa begen zama 'ya'ya" ko "a jiea da bege ga Allah ya karɓa a matsayin 'ya'ya."
  • Faɗar "maida su 'ya'ya" za a iya fassarawa haka "a karɓe su a matsayin 'ya'yansa" ko "a maida su 'ya'yansa na (ruhaniya)."

(Hakanan duba: magãji, gãdo, ruhu)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Afisawa 01:5
  • Galatiyawa 04:3-5
  • Romawa 08:14-15
  • Romawa 08:23
  • Romawa 09:04

zina, zinace-zinace, mazinaci, mazinaciya, mazinata

Ma'ana

Wannan kalma "zina" ma'anarta zunubi ne wanda mutum mai aure yake yi sa'ad da yana sha'anin kwana da wadda ba matarsa ko wanda ba mijinta ba. Zinace-zinace na nufin maimaita halin zina ko mutum mai yin wannan zunubi.

  • Ma'anar "mazinaci" shi ne namijin dake aikata zina.
  • Ma'anar "mazinaciya" shi ne matar aure musamman da take aikata zina.
  • Zina yana karya alƙawarin da miji da mata suka yiwa juna a aurensu.
  • Allah ya dokaci Isra'ilawa kada su yi zina.
  • Yawancin lokaci akan yi amfani da kalmar "zina" domin a nuna yadda mutanen Isra'ila suke yin rashin aminci wa Allah musamman sa'ad da suke wa gumaku sujada.

Shawarwarin Fassara:

  • Idan yaren da suke fassara basu da kalma guda mai ma'anar "zina," za a iya fassara wa da faɗar haka, "yin jima'i da matar wani" ko "shafar abokin auren wani ko wata.
  • Wasu harsuna watakila suna da yadda suke fassara zina, misali "kwana da wanda ba matarka ko mijinki ba" ko kuma "yin rashin aminci ga matar mutum."
  • Sa'ad da aka yi amfani da "zina"a misali, zai fi kyau a fassara kai tsaye domin a nuna yadda Allah ke kallon mutanensa marasa biyayya idan aka kwatanta da abokin aure marar aminci. Idan wannan baiyi bayani ba sosai a yaren fassarar, amfani da misalin "zina" za a iya fassarawa a matsayin "rashin aminci" ko "lalata" ko "kamar abokin aure marar aminci."

(Hakanan duba: aikata, alƙawari, lalatar zina, kwanciya da, aminci)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • Fitowa 20:14
  • Hosiya 04:1-2
  • Luka 16:18
  • Matiyu 05:28
  • Matiyu 12:39
  • Wahayin Yahaya 02:22

zuciya, zukata

Ma'ana

A cikin Littafi Mai Tsarki kalmar nan "zuciya" akan fi yawan moron salon magana a ambaci tunani, lamiri, marmarin, ko abin da mutum ke so.

  • A zama da "taurin zuciya" kalma ce da aka sani wadda ke nuna mutum ya tayar ya kuma ƙi yin biyayya ga Allah.
  • Maganar nan "da dukkan zuciyata" na nufin ayi wani abu ba tare da ƙunƙune ba, amma da matuƙar sadaukarwa da yardar rai.
  • Maganar nan "ku sashi a zuciya" na nufin a ɗauki abu da matuƙar mahimmanci ya kuma zauna a rayuwar mutum.
  • Kalmar nan "karyayyiyar zuciya" na baiyana mutum wanda ke cikin baƙin ciki sosai wanda abin ya nuna a fuskarsa.

Shawarwarin Fassara:

  • Waɗansu harsunan na morar mabambantan wasu sassan jiki kamar "ciki", ko "hanta" baiyana wanan magana.
  • Sauran harsuna na iya moron kalma ɗaya su baiyana waɗanan batutuwa da kuma wata kalmar su baiyana sauran.
  • Idan jiki ko "zuciya" ko waɗansu sassan jiki basu da wanan ma'anar, waɗansu harsunan za su iya fassara waɗanan kalmomin da "zace zace" ko "lamirai", ko "marmari."
  • Ya danganta ga wurin, da "dukkan zuciyata" za'a iya fassara shi da "dukkan ƙarfina" ko da "dukkan sadaukarwa" ko da "dukkan komai" ko da "matuƙar sadaukarwa."
  • Maganar nan "a sa shi a zuciya" za'a iya fassara shi da ɗaukarsa da "matuƙar muhimmanci" ko kuma "matuƙar yin hankali da shi."
  • Maganar nan "taurin zuciya" za'a iya fassara ta da "halin tayarwa" ko "ƙin yin biyayya" ko "ci gaba da rashin biyayya ga Allah."
  • Hanyoyin da za'a fassara "karyayyiyar zuciya" sun haɗa da "nadama" ko "jin matuƙar zafi a rai."

̇(Hakanan duba: wuya)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 03:17
  • 1Tasalonikawa 02:4
  • 2 Tasalonikawa 03:13-15
  • Ayyukan Manzanni 08:22
  • Ayyukan Manzanni 15:9
  • Luka 08:15
  • Markus 02:6
  • Matiyu 05:8
  • Matiyu 22:37

zumunci

Ma'ana

A batu na bai ɗaya, kalmar nan "zumunci" tana nufin tattaunawa ce ta abokantaka a tsakanin ƙungiyoyin mutane da ke da ra'ayi iri ɗaya da kuma fuskantar abu iri ɗaya.

  • A cikn Littafi Mai Tsarki "zumunci" harkullun na nufin haɗin kan masu bi a cikin Kristi.
  • Zumuncin masu bi tattaunawa ce da masubi kan yin tare da juna ta wurin dangantakar su da Kristi da kuma Ruhu Mai Tsarki.
  • Masu bi na farko sun yi nasu zumuncin ta wurin sauraron koyarwar maganar Allah da kuma yin addu'a tare, ta wurin rarraba abin da suka mallaka, da kuma ta wurin cin abinci tare.
  • Haka nan Krista na da zumunci da Allah ta wurin bangaskiyarsu a cikin Yesu da kuma hadayar mutuwarsa akan gicciye wadda ta kawar da shinge tsakanin Allah da mutane.

Shawarwarin Fassara:

  • Hanyoyin da za'a fassara "zumunci" za su haɗa da "yin tattaunawa tare ko "samun dangantaka" ko "taraiya" ko "al'umar Krista."

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Yahaya 01:03
  • Ayyukan Manzanni 02:40-42
  • Filibiyawa 01:3-6
  • Filibiyawa 02:01
  • Filibiyawa 03:10
  • Zabura 055:12-14

zunubi, zunubai, anyi zunubi, cike da zunubi, mai zunubi, yin zunubi

Ma'ana

Kalmar "zunubi" na nufin ayyuka, tunani, da maganganu da suke saɓawa nufin Yahweh da shari'u. Zunubi na kuma iya zama aikata wani abu da Yahweh baya so mu aikata.

  • Zunubi ya haɗa da aikata kowanne abu da ya nuna rashin biyyaya ko rashin gamsar Yahweh, har da abubuwan da waɗansu ba su ma sansu ba.
  • Tunani da ayyuka da suka yi tsayyaya da nufin Yahweh, ana kiransu "zunubi".
  • Saboda zunubin Adamu, dukkan 'yan adam aka haife su "cikin zunubi", siffar da take jagorantarsu su aikata zunubi.
  • Mai "zunubi" shi wani mutum ne wanda ya yi zunubi, don haka kowanne mutum mai zunubi ne.
  • Wani lokacin kalmar "masu zunubi" mutane masu addini kamar farisiyawa suna amfani da kalmar da nufin waɗanda suka kasa kiyaye dokoki kamar yadda farisiyawa ke tunanin za su kasance.
  • Kalmar"mai zunubi" an kuma amfani da ita ga mutanen da ake kallonsu masu mummunan zunubi fiye da sauran mutane. A misali, an sa wannan ga masu ƙarɓar haraji da karuwai.

Shawarwarin Fassara:

  • Kalmar "zunubi" akan fassara ta da kalma ko faɗar da yake nufin " rashin biyyaya ga Yahweh" ko "tafiya ba bisa nufin Yahweh ba" ko " mugun hali da tunani" ko "aikata rashin dai-da.i"
  • "Zunubi" za a iya fassara shi kuma da "bijire wa Yahweh" ko "yin rashin dai-dai."
  • Ya danganta da nassin, kalmar "zunubi" za a iya fassara shi da "cikakken yin rashin dai-dai" ko "mugunta" ko "rashin ɗa'a" ko "mugun abu" ko "tayarwa gãbã da Yahweh."
  • Ya danganta da nassin kalmar "mai zunubi" za a iya fassara ta da kalma ko faɗar da take nufin,"mutumin da ya yi zunubi" ko "mutumin da ya aikata abubuwa marasa kyau" ko " mutumin da ya yiwa Yahweh rashin biyayya" ko "mutumin da ya yi rashin biyayya ga doka."
  • Kalmar "masu zunubi" za a iya fassara ta da kalma ko faɗar dake nufin " mutane masu zunubi sosai" ko" mutanen da ake kallon su masu zunubi sosai" ko "mutane marasa ɗa'a."
  • Hanyoyin fassara "masu karɓar haraji da masu zunubi" na iya haɗawa da mutane masu karɓar kuɗi don gwamnati, da sauran mutane masu zunubi" ko "matane masu zunubi sosai, sun haɗa da masu karɓar haraji."
  • Magana kamar "bayin zunubi" ko "wanda zunubi ke mulka" kalmar "zunubi" akan fassarata da "rashin biyayya" ko "kwaɗayin mugunta da aikatawa."
  • A tabbatar fassarar wannan kalmar ta haɗa da halin zunubi da tunane-tunane, harda waɗanda waɗansu mutane basa gani ko sanin su.
  • Kalmar "zunubi" ta haɗa komai kuma ta banbanta da "mugunta" da "mugu."

(Hakanan duba: rashin biyayya, mugu, jiki, mai karɓar haraji)

Wuraren da ake samunsa a Littafi Mai Tsarki:

  • 1 Tarihi 09:1-3
  • 1 Yahaya 01:10
  • 1 Yahaya 02:02
  • 2 Sama'ila 07:12-14
  • Ayyukan Manzanni 03: 19
  • Daniyel 09:24
  • Farawa 04:07
  • Ibraniyawa 12: 02
  • Ishaya 53:11
  • Irmiya 18:23
  • Lebitikus 04:14
  • Luka 15:18
  • Matiyu 12:31
  • Romawa 08:04