Yahuda ya ɗauki mata daga mutum Kan'aniya.
Yahweh ya kashe Er domin mugu ne.
Onan ya zubar da maniyin a ƙasa a lokacin da ya kwana da Tama.
Yahweh ya kashe Onan domin abinda yayi mugunta ne.
Yahuda yayi wa Tama alkawarin ɗansa na uku a matsayin miji idan yaya girma.
Yahuda ya ta'azantu domin matarsa ta mutu.
Tama ta tuɓe tufafin gwaurancinta kuma ta rufe jikinta da abin lulluɓi ta kuma ɗaura wa jikinta. Ta zauna a ƙofar Enayim, wadda ke kan hanyar zuwa Timna.
Tama ta yi haka domin ta ga Shela ya girma amma ba a ba da ita a gare shi a matsayin mata ba.
Yahuda ya ba Tama zoben hatiminsa da ɗamararsa, da sandar dake a hannunsa.
Yahuda ya ji cewa babu wata karuwar asiri dake zaune a nan.
Yahuda ya so ya ƙona ta domin ta yi ciki a karuwanci.
Ta faɗa cewa ta yi ciki da mutum mai wannan zoben tambarin da ɗamarar da sandar da take da su.
Yahuda ya gane Tama ta fi shi adalci, tunda bai ba da ita a matsayin mata ga Shela, ɗansa ba.
Tama ta haifa tagwaye.
A lokacin da ɗaya daga cikin tagwayen ya fitar da hannunsa waje, matan nguwar zomar ta ɗauki jan zare ta ɗaura masa a hannu ta kuma ce, "Wannan ne ya fãra fitowa."
Sunayen 'ya'ya biyu da Tama ta haifa su ne Ferez da Zerah.