Bisa ga Yakubu, Allah ne ya hana ta samun 'ya'ya.
Rahila ta ba wa Yakubu Bilha baiwanta domin ta samu 'ya'ya a madadin ta.
Rahila ta faɗa cewa ta ci nasara domin Bilha baiwar ta ta haifi 'ya'ya biyu wa Yakubu.
Liya ta ba wa Yakubu Zilfa baiwarta domin ta haifa 'ya'ya a madadin ta.
Liya ta faɗa cewa, "Wannan rabo ne." domin Zilfa baiwarta ta haifa wa Yakubu ɗa.
A maimakon 'ya'yan itacen manta'uwar Ruben, Rahila ta yarda wa Liya ta kwana da Yakubu a ɗaren.
Liya ta haifa wa Yakubu 'ya'ya maza shidda.
Sa'adda Rahila ta haifa wa Yakubu ɗa, ta faɗa cewa an ɗauke kunyarta.
Yakubu ya roka cewa Laban ya bar shi ya tafi da iyalinsa zuwa gidansa da kuma ƙasarsa.
Laban ya gane cewa Yahweh ya albarkace shi ta dalilin Yakubu ne.
Yakubu ya ɗauke tumaki dabbare-dabbare da masu ɗigo, da waɗanda ke baƙaƙe daga cikin tumakin, da masu ɗigo da kyalloli daga cikin awakin.
Da farko, Laban ya cire dabbobin da ya kamata Yakubu ya ɗauka kafin ya ba bashi tumakan ya yi kiwon.
Yakubu ya fera fararen zãne a da rassan itacen almon da rassan itacen durumi.
Yakubu ya sa fararen zãnen da yayi a gaban dabbobin, a gaban kwamamen ruwa in da suke zuwa su sha.
A lokacin da dabbobin suna barbara a gaban ƙiraren suna haihuwar 'ya'yai masu zãne, da kyalloli, da masu ɗigo.
Sakamakon shi ne tumakin Laban suna da rashin ƙarfi kuma ƙarfafan kuma na Yakubu ne.