Mutanen daga Haran suke.
Rahila, ɗiyar Laban, ta kuma zo rijiyan da garken tumakai.
Yakubu ya gangarar da dutsen daga bakin rijiyar, ya kuma yi wa garken banruwa.
Yakubu ya gaya wa Rahila cewa shi dangin mahaifinta ne,sai Rahila ta ruga ta gaya wa mahaifinta.
Laban ya ruga domin ya same Yakubu, ya rungume shi, ya sumbace shi, ya kuma kawo shi cikin gidansa.
Liya ce babbar kuma idanunta tausasa ne amma Rahila na da kyakkyawar siffa kuma ita ne ƙaramar.
Sun amince cewa Yakubu zai bauta wa Laban na shekaru bakwai domin Rahila.
Shekaru bakwai na aiki sun zama masa kamar kwanaki kaɗan, domin ƙaunar da yake da ita wa Rahila.
Laban ya ba Yakubu Liya a maimakon Rahila, a daren bikin auren.
Laban ya ɗauki baiwarsa Zilfa ya ba ɗiyarsa Liya, ta zama baiwarta.
Laban ya ce ba al'adarsu ba ce su bayar da ƙaramar ɗiya kafin ta fãrin a aure ba.
Sun amince cewa Yakubu zai bauta wa Laban na wasu shekaru bakwai kuma a maimakon Rahila.
Laban ya bayar da Bilha ga ɗiyarsa Rahila, ta zama baiwarta.
Yahweh ya sa Liya ta yi juna biyu, amma Rahila ba ta da ɗa.
Liya ta yi begen cewa Yakubu zai ƙaunace ta idan ta haifa masa 'ya'ya.
Sunar ɗan farin Liya shine Ruben.
Bayan da ta haifi Yahuda ta ce, "Wannan lokacin zan yabi Yahweh."