"Wannan na maganar yadda Allah ya halici sama da duniya tun farko." Wannan maganar ya taƙaita sauran surar. Waɗansu harsuna sun juya wannan haka "Tun zamanin dã Allah ya halici sama da duniya." juya wannan ta hanyar da zai nuna cewa haƙiƙa wannan ya faru ba tatsuniyar waiwai ba.
Wannan na nufin a farkon duniya da komai da komai da ke cikin ta.
"sararin sama, ƙasa, da duk abin da ke cikin su"
Anan, wannan na nufin sararin sama.
Allah baya shirya duniyan ba tukunna.
"ruwan" ko "zurfin ruwa" (UDB) ko "babban ruwa"
"ruwan" ko "farfajiyan ruwa"
Wannan umurni ne. Ta wurin umurnin cewa haske ya kasance, Allah kuwa ya sa hasken ya kasance. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"Allah ya dubi hasken kuma ya faranta masa." "Kyau" anan na nufin "farantawa" ko "dacewa."
"raba haksen da duhu" ko "mayar da shi haske a wani loto, duhu kuma a wani lokaci." Wannan na nufin halitar Allah na yini da dare .
Allah ya yi waɗannan abubuwa a kwanan farko da duniya ya kasance.
Wannan na nufin rana ɗaya. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Waɗannan umurnai ne. Ta wurin umurtar cewa sarari ya kasance, ya kuma raba tsakanin ruwaye, Allah ya sa haka ya faru ya kuwa raba ruwayen. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"babban fili tsakanin." Yahudawa sun gane sarari a matsayin wani abu ne mai siffer zobe ko cikin kwano da aka juya kasa.
"cikin ruwan"
"Ta wannan hanyar ne Allah ya halici sararin da ya kuma raba ruwayen." Sa'ad da Allah yayi magana, abin da ya fada ya faru. Wannan jimlar na bayana abin da Allah ya yi a sa'ad da yayi magana.
"Ya faru kamar yadda ya ke" ko "haka abin ya faru." Abin da Allah ya umurta ya faru, haka kuwa ya faru.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.
Wannan na nufin rana ɗaya. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Wannan na nufin kwana na biyu kenan da kasancewar duniya. Duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.
Ana iya fassara wannan tare da aikatau. Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar ruwaye su tattaru, Allah ya sa sun tattaru. AT: "Bari ruwayen ... tattaru" ko "Bari ruwaye ... zo wuri ɗaya" (UDB) (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
Ruwan ya rufe ƙasa. Ruwan zai tattaru a gefe, sa'anan ƙasa ya kasance. Wannan umurni ne. Ta wurin umurta sandararriyar ƙasa ya kasance, Allah ya sa shi ya kasance. AT: "Bari a ga sandararriyar ƙasa" ko "bari sandararriyar ƙasa ya kasance a fili" ko "bari ƙasar ya zama a fili" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
Wannan na nufin ƙasa ne da ruwa baya rufe ba. Ba ana nufin cewa ƙasar ta bushe da ba za a iya noman ta ba.
"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.
"ƙasa" ko " filin ƙasa"
"Yana" anan na nufin ƙasar da teku. dubi yadda aka juya wannan cikin Farawa 1:3.
Wannan umurni ne. Ta wurin ba da umurnin cewa tsire-tsire so fito daga ƙasa, Allah ya sa hakan ya faru. AT: "Bari tsire-tsire su fito daga ƙasa" ko "Bari tsire-tsire su girma daga ƙasa" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"tsire-tsire, kowani shuka mai ba da tsaba da kowani itace mai ba da 'ya'ya" ko "tsire-tsire. Su zama shuka masu tsaba, da kuma itatuwa masu ba da 'ya'ya." An yi amfani da kalmar "tsire-tsire" a nufin kowani shuka da itatuwa.
Waɗannan 'yan tsire-tsire ne ba kamar manyan itatuwa ba.
"itatuwa masu ba da 'ya'ya da ke da ƙwaya a cikinsu"
Ƙwayar za su haifar da itatuwa irin wadda suka fito. ta wurin haka kuwa itatuwa za su "haifar da kansu" (UDB).
"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.
Anan "na" na nufin tsire-tsiren, shuka, da itatuwa. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:9.
Wannan na nufin rana ɗaya ne. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:3. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Wannan na nufin kwana na uku kenan da kasancewar duniya. duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.
Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar haskoki su kasance, Allah kuwa ya sa sun kasance. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"abubuwan da suke haskakawa a cikin sarari" ko "abubuwan da suke kawo haske a cikin sarari." Wannan na nufin rana, wata, da ta taurari.
"cikin sararin sama" ko "a babban sararin sama"
"su raba yini da dare." Wannan na nufin "su taimake mu bambanta tsakanin yini da dare." Rana na nuna yini, wata da taurari kuwa na nuna dare.
Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar cewa su zama alamu, Allah kuwa ya sa sun zama alamu. AT: "Bari su kasance alamu" ko "su kuma nuna" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
Wannan na nufin wani abu ne da ke bayyanar da wani abu.
"yanayin shekara" na nufin lokaci da aka keɓe domin bukukuwa da wasu abubuwan da mutane ke yi.
Rana, wata, da taurari na nuna yadda lokaci ke wucewa. Wannan na bamu damar sani aukuwar kowani mako, watani, ko shekara.
Wannan umurni ne. Ta wurin umurta cewa su haskaka duniya, Allah kuwa sa sun haskaka duniya. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"su kawo haske a duniya" ko "su sa haske a duniya." Duniya ba ta hasken kanta amma ana haskakata ne, sai ta kuma maimaita hasken.
"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance. Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:6.
"Ta haka kuwa Allah ya yi manyan haskoki biyun." The jimlar na bayana abin da Allah ya yi a sa'ad da ya yi magana.
"haskoki biyu mas girma" ko "hasken biyu masu haskakawa." Manyan haske biyun sune rana da wata.
"ya shugabanci yini kamar yadda shugaba ke tafiyad da mutane" ko "ya ba da alamar lokaci na yini" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-personification)
Wannan na nufin iyakar sa'a da rana ke haskakawa.
"haske mara girma" ko "ƙaranci haske"
"cikin samai" ko "a sarari sama"
"ya raba haksen da duhu" ko "mayar da shi haske a wani loto, duhu kuma a wani lokaci." Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:3.
"yana" na nufi rana, wata, da taurari. Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:3.
Wannan na nufin rana ɗaya ne. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:3. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Wannan na nufin kwana na huɗu kenan da kasancewar duniya. duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.
Wannan umurni ne. Ta umurtar cewa halitu masu rai su cika ruwaye, Allah ya sa haka ya kasance. wasu harsuna na iya samun kalma ɗaya wa kowani irin kifi da dabbobin ruwa. AT: "Bari ruwayen su cika da abubuwa da yawa masu rai" ko "Bari dabbobi da suke ninƙaya su rayu a cikin teku" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
Wannan umurni ne. Ta umurtar cewa tsuntsaye su riƙa tashi, Allah ya sa haka ya kasance. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"dabbobin da suke tashi" ko "abubuwan da suke tashiwa"
"a sarari" ko "a sama"
"Ta haka ne Allah ya halicci"
"manya manyan dabbobi da suke zama a cikin teku"
Abubuwa masu rai iri ɗaya na kamar waɗanda suka fito a gare su.
"kowani abu mai fifike da ke tashi." zai fi saukin ganewa a wasu harsuna idan an yi amfani da kalmar "kowani tsuntsu", tun da yake dukka tsuntsaye na da fifike.
"yana" anan na nufi tsuntsaye da kifi. Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:3.
"albarkace dabbobin da ya halitta"
Wannan albarkan Allah ne. Ya ce da dabbobin tekun su haifar da wasu dabbobin teku irin su domin su zama dayawa a cikin tekuna. Kalmar "riɓaɓɓanya" na bayana yadda ya kamata su "hayayyafa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
"ƙaru sosai" ko "su zama da yawa"
Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar cewa tsuntsaye su riɓaɓɓanya, Allah ya sa tsunstaye sun riɓaɓɓanya. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"dabbobin da suke tashi" ko "abubuwan da suke tashiwa."
Wannan na nufin rana ɗaya ne. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:3. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Wannan na nufin kwana na biyar kenan da kasancewar duniya. duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.
"Bari ƙasa ta fid da abubuwa masu rai" ko "Bari dabbobi dayawa masu rai su rayu a duniya." Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar duiya ta fid da masu rai, Allah ya sa duniya ta fid da masu rai. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-imperative)
"domin kowani dabba ta haifar da irin ta"
Wannan na nuna cewa Allah ya halicci dukka irin dabbobi. Idan harshe ku na da yadda kuke kiran tarin dabbobi, kuna iya amfani da shi, ko kuma kuna iya amfani da wannan.
"dabbobin da mutane ke kiwo"
"ƙananan dabbobi"
"dabbobin jeji" ko "dabbobi masu haɗari"
"Ya faru kamar yadda ya ke" ko "haka abin ya faru."Abin da Allah ya umurta ya faru, haka kuwa ya faru.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.
"Ta haka ne Allah ya halicci dabbobin"
"yana" anan na nufi abubuwa masu rai a duniya.
Kalmar "mu" anan na nufin Allah ne. Allah na faɗin abin da ya ke niyar yi. Yana iya yiwuwa cewa dalilin da sa an yi amfani da kalmar "mu" shi ne 1) jam'in na iya ba da ra'ayin cewa Allah na magana ne da mala'iku da suke a tare a cikin sama ko 2) jam'in na nuna cewa Allah ɗaya ne a cikin uku, yadda aka gane a sabon alkawari. Wasu sun juya wannan cewa "Bari in yi" ko "zan yi." idan ku juya haka, to a tabbatar an sharihinta cewa wannan kalmar na jam'i ce. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-pronouns)
"'yan adam" ko "mutane." Ba maza ne kadai wannan kalman ke nufi ba.
Waɗannan kalmomi biyu na da nufi ɗaya ne, kuma yana jadada cewa Allah ya halicci mutum ya zama kamar shi. Wannan ayar bai bayana hanyar da mutane ke kama da Allah ba, kuma Allah ba shi da jiki. haka ya nuna cewa ba kamani jiki ne mutane suke da shi da Allah ba. AT: "kasance cikin gaskiyar kamani Allah" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-pronouns)
"mulki bisa" ko "samu iko akan"
Waɗannan jimla biyun na nufin abu ɗaya ne, kuma yana jadada cewa Allah ya halicce mutum a cikin siffan shi. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-parallelism)
Ba yadda Allah ya halacci sauran abubuwa bana ya halicci mutum. Ka da a ambaci cewa ya halicci mutum ta wurin maganar baki kamar yadda ya ke a ayoyin baya.
Kalmar "su" na nufin na mijin da macen da Allah ya halitta.
Allah ya ce da na mijin da macen su haifar da wasu mutane kamar su, domin a samu irin su dayawa. Kalmar "riɓaɓɓanya" na bayana yadda ya kamata su "hayayyafa." (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-doublet da /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)
cika duniya da mutane.
Allah ya ci gaba da magana.
"dukka tsuntsaye da tashi a sararin sama"
"da ke numfashi" (UDB). Wannan na jadada cewa rayuwan dabbobin dabam ne da na tsire-tsire. tsire tsire ba su numfashi, kuma za su amfana wajen zama abinci wa dabbobin. "Rayuwa" na nufin samun rai na zama.
"Ya faru kamar yadda ya ke" ko "haka abin ya faru."Abin da Allah ya umurta ya faru, haka kuwa ya faru.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.
"Haƙĩƙa." Kalmar "gã shi" anan na jadada maganar da ke zuwa.
Allah ya ga dukka abubuwa da ya yi na da kyau ƙwarai.
Wannan na nufin rana ɗaya ne. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:3. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)
Wannan na nufin kwana na shida kenan da kasancewar duniya. duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.