Genesis 2

Genesis 2:1

sammai

"sararin"

da duk abubuwa masu rai da suke cike a ciki

"da dukkan abubuwa da yawa masu rai da ke cikin su" ko "da duk taron rayayyu da ke cikin su"

aka gama

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Allah ya gama halittar su" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

a kwana na bakwai Allah ya gama aikinsa

Allah ba ya yi kowani aiki ba a kwana na bakwai

kawo zuwa ga karshe

Wannan karin magana ne. AT: "ya gama" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

ya kuma huta a kwana na bakwai daga dukka aikinsa

"ba ya yi aiki ba a wannan ranar"

Allah ya sa wa kwana na bakwain albarka

Mai yiwuwa ana nufi 1) Allah ya sarrafe kwana na bakwai da sakamako mai kyau, ko 2) Allah ya ce kwana na bakwan na da kyau.

ya kuma tsarkake shi

"ya kuma keɓe shi" ko "ya kuma kira ranar na shi"

a cikinsa ya huta daga dukkan aikinsa

"a cikinsa bai yi aiki ba"

Genesis 2:4

Muhimmin Bayani:

Sauran Farawa sura biyun na magana game da yadda Allah ya halicci mutane a cikin kwana na shida.

Waɗannan sune aukuwan sama da duniya

"Wannan shi ne tarihin sama da duniya" ko "Wannan shi ne labari game da sama da duniya." Mai yiwuwa ana nufi 1) wannan taƙaitaciyar labari ne da aka bayar a Farawa 1:1-2:3 ko 2) Na gabatar da abin da ke faruwa a Farawa 2. in mai yiwuwa ne, juya a hanyar da mutane za su fahimce dukka.

ya halicce su

"Allah Yahweh ya halicce su." A sura 1 marubucin na ambatar Allah da sunar sa "Allah", amma a sura 2 yana kiran shi "Allah Yahweh."

a ranar da Allah Yahweh ya yi

"a sa'ad da Allah Yahweh ya halicci." Kalmar "rana" na nufin iyakar lokacin halitta, ba wani kwana ɗaya ba.

Yahweh

Wannan shi ne sunar da Allah ya bayyanar wa mutanen sa a cikin Tsohon Alkawari. Duba translationWord domin sanin yadda aka juya kalmar Yahweh.

ba tsire-tsiren a duniya

ba tsire-tsiren da ke girma a jeji domin dabbbobi su ci

Ba shuka a filin duniya

ba shuka masu ganyayyeki kamar kayan lambu da mutane da dabbobi za su iya ci

a nome

a yi duk abin da ake bukatan yi domin shuka ta yi girma da kyau

kãsashi

Mai yiwuwa ana nufi 1) wani abu kamar hazo, ko 2) bubbugowar ruwa daga rafi.

fuskar ƙasa dukka

duniya dukka

Genesis 2:7

kafa

"shafi" ko "kera" ko "halicce"

mutum ... mutum

"ɗan adam mai rai ... ɗan adam" ko " mutum ... mutumin" ba lalle na miji ba

ƙofar hancinsa

"hancinsa"

numfashin rai

"numfashin da ke sa abubuwa su rayu." Anan "rai" na nufin kasance rayyaye a duniya.

gona

Wannan na iya zama gonar itatuwa masu 'ya'ya ko wani wuri da ke da kowani irin itatuwa.

waje gabas

"a gabas"

Genesis 2:9

itacen rai

"itace da ke ba mutane rai"

rai

Wannan na nufi "rai madawwami" ko rai mara iyaka.

itacen sanin nagarta da mugunta

"itacen da ke ba mutane ikon fahimtar nagarta da mugunta" ko "itace da ke sa mutune su san abubuwa masu kyau da mugayen abubuwa idan an ci 'ya'yan ta"

nagarta da mugunta

Wannan karin magana ne da ke nufi sanin farko da iyakar abu da komai da cikin abun. AT: "komai, na nagari da mugunta" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-merism)

a tsakiyar gonar

"a tsakiyar gonar." Mai yiwuwa Itatuwa biyun ba a tsakiyar gonar suke ba.

Wani kogi ya fito Aidan ya shayar da gonar

Gonar na Aidan. Kogin ya ci gaba da malalowa har wa jen Aidan. AT: "Wani kogi ya malalo a cikin Aidan ya shayar da gonar."

Genesis 2:11

Fishon

Anan kadai ne aka ambaci wannan kogin a Littafi Mai Tsarki. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names).

kewaye da dukkan Kasar Hawila

"iyakar ƙasar da a kira Hawila." Yana nan ne a wani wuri a Hamadar Larabawa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names).

inda akwai zinariya

Wannan maganar na ba da bayani ne gama da Hawila. Wasu harsuna na iya sa shi a wani jimla dabam. AT: "Akwai zinariya a Hawila" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

Akwai duwatsu masu daraja

Kalmar "akwai" na farkon jimlar domin jadada maganar. AT: "Anan ne kuma mutane ke iya samun duwatsu masu daraja"

bdellium

Wani abu ne mai da ƙamshi da ke fitowa a wani irin itace. Yana mannewa kuma yana iya konewa. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)

Dutse mai daraja

"duwatsu masu daraja." Wani wani irn dutse ne mai kyau. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-unknown)

Genesis 2:13

Gihon

Anan kadai ne aka ambaci wannan kogin a Littafi Mai Tsarki. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#translate-names)

yake malala kewaye da ƙasar Kush

Kogin bai rufe ƙasar gaba daya ba, amma ya kewaye wurare dayawa a ƙasar.

kewaye da ƙasar Kush

"iyakar ƙasar da ake kira Kush"

wanda yake malala gabashin Assuriya

"wanda yake malala a cikin ƙasar da ke gabashin birnin Assurh" KoginTigiris na malala daga arewa zuwa kudu. Kalmomin "wanda ke malala gabashin Asshur" na bayana inda Kogin Tigiris ya ke. wasu harsuna za su wannan a wani jimla dabam. AT: "kuma yana malala gabashin Asshur" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-distinguish)

Genesis 2:15

gonar Aidan

"gonar da ke a cikin Aidan"

ya yi aiki a cikinta

"ya nome ta." Wannan na nufin cewa ya yi duk abun da ake bukata domin tsire-tsiren su yi girma da kyau.

ya kiyaye ta

ya kiyaye gonar daga kowace muguwar abu da ke so ya faru a cikin ta

daga kowace itace da ya ke cikin gonar

" 'ya'yan kowance itace da ke a gonar"

ka

Wannan wakilin suna ne. (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-you)

kana iya ci ... ba za ka ci ba

A wasu harsu a akan fara irin wannan maganar da ambacin wanda ba a so mutum ya aikata kamin wanda zai iya aikatawa.

na iya ci

"na iya ci ba tare da hani ba"

itacen sanin nagarta da mugunta

itacen da ke ba mutane ikon fahimtar nagarta da mugunta" ko "itace da ke sa mutune su san abubuwa masu kyau da mugayen abubuwa idan an ci 'ya'yan ta."

ba za ka iya ci ba

"ba zan ba ka izinin ci ba" (UDB) ko "ba za ka ci ba"

Genesis 2:18

Zan yi masa mataimakin da ya dace da shi

"Zan yi masa mai taimakon da ke dai-dai masa"

kowace dabba ta filin ƙasa da kowane tsuntsu da ke sararin sama

Maganganu nan "ta filin ƙasa" da kuma "na sararin sama" na faɗin inda ake samun dabbobi da tsuntsu ne. AT: "dukka irin dabbobi da tsuntsaye."

dukka dabbobin gida

"dukka dabbobin da mutane ke kiwon su"

ba a samu mataimakin da ya dace masa ba

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: " babu abokin hira da ya dace da shi" (Duba: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-activepassive)

Genesis 2:21

sa barci mai nauyi ya kwashe mutumin

"sa mutumin yin barci mai zurfi." ba a iya ta da mai zurfi barci a cikin sauki ba.

da haƙarƙarin ... ya yi mace

"daga haƙarƙarin ... ya kera mace." Haƙarƙarin ne abun da Allah ya yi macen da shi.

Yanzu dai wannan ƙashi ne daga ƙasusuwana, nama ne kuwa daga namana

"A karshe dai, ƙasusuwan wannan kamar nawa ne, naman ta kuwa kamar nama na." Bayan neman abokin zama daga dabbobin bai kuma samu ba, yanzu dai a karshe ya ga wani mai kama da shi kuma na iya zama abokinsa. Mai yiwuwa mutumin na nuna gamsuwarsa da murna.

nama

Wannan na nufi jikin mutum kamar fata da tsoka.

za a kirata 'mace' domin daga cikin mutum aka ciro ta

Mai juya wannan na iya sharihinta cewa "kalmar "mace' na kusa da kalmar 'miji' a Ibraniyanci.

Genesis 2:24

Muhimmin Bayani:

Sauran magana daga marubucin littafin ne ba mutumin da aka halitta ba.

Saboda haka

"Don wannan ne"

mutum zai bar mahaifinsa da mahaifiyarsa

"mutum zai rabu da gidan mahaifinsa da mahaifiyarsa." Wannan maganar ga maza ne dukka. Ba wa wani takamamen mutum a wani lokaci ba.

su zama jiki ɗaya

Wannan ƙarin maganar na bayana cewa jikinsu da ke tare a jima'i na zama jiki ɗaya ne. AT: "jikinsu biyun zasu zama ɗaya" (Dubi: /WA-Catalog/ha_tm?section=translate#figs-idiom)

a tsiraice suke

Kalmar "su" na nufin na mijin da ta macen da Allah ya hilitta.

tsirara

"ba tare da sa tufafi ba"

ba su kuwa ji kunya ba

"ba su jin kunyar kasancewa a tsiraice" (UDB)