1 A waɗannan kwanaki da lokatai, sa'ad da na komar da ma su zaman talallar Yahuda da Urshalima, 2 Zan tattara dukkan al'umai in kuma kawo su kwarin Yohoshafat. A can zan yi masu shari'a, saboda jama'ata da abin gãdona Isra'ila, waɗanda su ka warwatsar cikin al'umai, saboda kuma sun raba ƙasata. 3 Sun kuma jefa ƙuri'a kan mutanena, sun sayar da yaro saboda da karuwa, sun kuma sayar da yarinya saboda ruwan inabi don su sha. 4 Yanzu don me ku ke fushi da ni, ku Taya, da Sidom da dukkan yankin Filistiya? ko za ku sãka mani? Ko da ma kun sãka mani nan da nan zan komo mu ku da ramuwarku a kanku. 5 Don kun ɗauke zinariyata da azurfata, kun kuma kawo kayayyakina ma su daraja zuwa cikin masujadanku. 6 Kun sayar da mutanen Yahuda da na Urshalima ga Girkawa, don ku cire su can nesa da ƙasarsu. 7 Duba, ina gab da in tayar da su, daga inda ku ka sayar da su, ku ne kuma za ku biya kuɗin fansa da kanku. 8 Zan sayar da 'ya'yanku maza da mata ta hannun mutanen Yahuda. Za su sayar da su ga Sabiyawa, ga al'uma mai nisa, Don Yahweh ne ya furta. 9 Yi wannan shela a cikin al'umai, 'Ku shirya kanku domin yaƙi, ku horar da manyan mutane, ku bar su su zo kusa, ku bar dukkan jarumawan yaƙi su hauro nan. 10 ku mayar da dumɓayen garemaninku takkuba, ku kuma mayar da wuƙaƙenku mãsu. Sai raunana su ce ''muna da ƙarfi.'' 11 Ku yi sauri ku zo ku makusantan ƙasashe, ku tara kanku wuri ɗaya a can.Yahweh ya kawo ƙarshen mayaƙanku masu iko.' 12 Bari al'ummai su tada kansu tsaye su zo kwarin Yohoshafat. Don a can zan zauna don in yi wa dukkan al'umman da ke kewaye shari'a. 13 Ku ɗauki lauje don girbi ya nũna. Ku zo, ku mãtsi abin sha, don tulunan ruwan inabi sun cika. sun cika su na zuba, saboda muguntarsu tana da yawa sosai.'' 14 Akwai hayaniya, a cikin kwarin shari'a, gama ranar Yahweh ta kusa a cikin kwarin shari'a. 15 Rana da wata sun zama baƙi, taurari kuma sun dena bada haskensu. 16 Yahweh zai tada muryarsa daga Urshalima da Sihiyona, Duniya da sammai za su girgiza, amma Yahweh zai zama mafaka ga mutanensa, da kuma kagara ga Jama'ar Isra'ila. 17 Da haka za ku sani cewa ni ne Yahweh Allahnku wanda ke a Sihiyona, dutsena mai tsarki. Daga nan Urshalima za ta tsarkaka, kuma ba wani sojan da zai ƙara ratsa ta. 18 A wannan rana kuma duwatsu za su cika da ruwan inabi mai zaƙi, tuddai kuma za su kwararo da madara, dukkan ƙoramun Yahuda za su ɓulɓulo da ruwa, magudanu za su zo daga gidan Yahweh su jiƙe kwarin Shittim. 19 Masar za ta zama yasasshiya, Edom kuma ta zama jejin da a ka yi watsi da shi, saboda tayarwar da a ka yi wa mutanen Yahuda, saboda an zubar da jinin marasa laifi a ƙasarsu. 20 Gama za a zauna a Yahuda har abada, Urshalima kuma zata zama wurin zama na dukkan zamanai. 21 Zan yi ramuwar da ban yi ba tukuna a kan jininsu,'' don Yahweh ya na zaune a Sihiyona.