Sura 2

1 Ku hura ƙaho a Sihiyona, ku kuma kaɗa kararrawa a kan duwatsuna ma su tsarki! Bari dukkan mazaunan ƙasar su gigice don tsoro, Don hakika ranar Yahweh tana tafe, hakika ta kusa. 2 Rana ce ta duhu baƙiƙƙirin, rana ce ta giza-gizai da baƙin duhu. Kamar yadda duhu ke rufe duwatsu, babbar rundunar sojoji tana kusantowa. Ba a taɓa samun soja kamarta ba, ba kuma za a sake samun kamar ta ba, Koma a bayan tsararraki da yawa. 3 Wuta na cinye duk abin da ke gabanta, bayanta kuma harshen wutar yana ƙuna. ƙasar ta zama kamar gonar Adnin a gabanta, amma a bayanta akwai jejin da ba komai. Ba kuma abin da zai tsira daga gare ta. 4 Bayyanuwar sojojin kamar ta dawakai ce, kuma su na gudu kamar mahayan dawakai. 5 Suna tsalle da ƙara kamar na ma su karusa a kan duwatsu, kamar kuma ƙarar wutar da ke cin tarin yayi, kamar ta Sojoji ma su iko da ke shirye domin yaƙi. 6 A gabansu jama'a na cikin ƙunci, dukkan fuskokinsu kuma su ka yi suwu. 7 Su na gudu kamar na jarumawa ma su iko; su ka hau katanga kamar sojoji; su na tafiya a jere kowanne dai-dai a kan sawu, ba su kauce matsayinsu ba. 8 Ba wanda ya tunkuɗe wani a gefe, kowa yana tafiya a gefensa, su ka kutsa ta cikin kariyar ba su kuma kauce layi ba. 9 Su ka ruga kan birnin, suna gudu a kan ganuwa, su ka haura cikin gidaje, su ka shiga ta tagogi kamar ɓarayi 10 Duniya ta girgiza a gabansu, sammai kuma su ka firgita, rana da wata sun duhunta, taurari kuma sun dena haskakawa. 11 Sai Yahweh ya ta da muryarsa a gaban sojojinsa, don sojojinsa su na da yawa sosai, su na kuma da karfi, waɗanda ke karɓar umarninsa. Don ranar Yahweh ta na da girma da kuma ban tsoro sosai. Wa zai iya jure mata? 12 ''Amma ko yanzu ma, ''Yahweh ya ce, ''Ku juyo wurina da dukkan zuciyarku. Ku yi azumi da kuka, da makoki.'' 13 Ku keta zuciyarku ba tufafinku kawai ba, ku komo wurin Yahweh Allahnku. Don shi mai alheri ne da jinkai, marar saurin fushi kuma ya na cike da alkawari mai aminci, kuma zai so ya kawar da aiwatar da hukunci. 14 Wa ya sani? Ko zai juyo ya ji tausayi, ya kuma sa ma sa albarka, da baiko na hatsi da na abin sha saboda Ubangiji Allahnku? 15 A hura ƙaho a Sihiyona, a kira ayi azumi mai tsarki, a kuma kira ayi tattaruwa mai tsarki. 16 A tattara jama'a don tattaruwa mai tsarki, a tattara dattawa, a tattara 'yan yara da jarirai masu shan nono. Sai anguna su fito daga ɗakunansu, amare kuma daga kagararsu ta amarcinsu. 17 Sai firistoci bayin Yahweh su yi kuka a tsakanin bagadi da shirayi. Sai su ce Ya Yahweh ''Ka ceci mutanenka, kada kuma ka mai da gãdonka abin ba a, har al'umai su yi mu su ba a. Me ya sa za su faɗa a cikin al'umai cewa, 'Ina Allahnsu?''' 18 Sai ya yi kishin ƙasarsa, ya kuma ji tausayin mutanensa. 19 Yahweh ya amsa wa mutanensa, ''Duba zan aiko ma ku da hatsi, da sabon ruwan inabi, da mai. Za su wadace ku, kuma ba zan ƙara mai da ku abin wulaƙanci ba a cikin al'ummai. 20 Zan kawar da maharan nan na arewa daga gare ku, kuma za ku kore su zuwa yasassun wurare. jagoran sojojinsu zai fuskanci gabashin teku. Bãshinta zai tashi, mumunan warinta kuma zai tashi.' Hakika, ya yi manyan abubuwa. 21 Ƙasa kada ki tsorata, ki yi murna da farin ciki, domin Yahweh zai yi manyan abubuwa. 22 Kada ku ji tsoro, namomin jejin da ke cikin saura, gama tsire-tsiren da ke cikin saura za su tohu, itatuwa za su bada 'ya'ya, kuma itacen baure da na inabi za su bada ''ya'yansu sosai. 23 Mutanen Sihiyona ku yi murna, kuma ku yi farinciki cikin Yahweh Allanhnku. Don zai ba ku ruwan sama da bazara ya kuma buɗe sakatun sama dominku, ruwan bazara da na koramunku kuma kamar dã. 24 Masussuka za ta cika da alkama, wurin matsar inabi kuma zai cika da sabon ruwan inabi da mai. 25 ''Zan komo ma ku da shekarun da ku ka yi asarar hatsinku wanda fara ta cinye wato wannan farar mai hallakarwa da na aiko cikinku. 26 Za ku ci ku ƙoshi sosai, ku yabi sunan Yahweh Allahnku, wanda ya aikata abubuwan al'ajabi a cikinku, kuma ba zan taɓa sake kawo abin kunya akan mutane na ba. 27 Za ku san cewa ina cikin Isra'iila, kuma ni ne Yahweh Allahnku , kuma babu wani sai ni, kuma ba zan ƙara kawo kunya akan mutane na ba. 28 Bayan wannan kuma zan zubo da Ruhuna ga dukkan mutane, 'ya'yanku maza da mata za su yi anabci.Tsofaffinku za su yi mafarkai, samarinku kuma za su ga wahayi. 29 Kuma ga bayi da mata bayi, a waɗancan kwanaki zan zubo mu su da Ruhuna. 30 Zan nuna al'ajabai a sama da kuma a duniya, jini, da wuta, da murtukewar hayaƙi. 31 Rana za ta duhunta, wata kuma zai zama jini, kafin babbar ranan nan ta Ubangiji mai ban tsoro ta zo. 32 Zai zama kuma dukkan wanda ya yi kira ga sunan Yahweh zai tsira. Don a dutsen Sihiyona da kuma a cikin Urshalima za a sami waɗanda su ka tsira, kamar yadda Yahweh ya ce, da kuma cikin waɗanda su ka rayu, wato waɗanda Yahweh ya kira.