1 Wanna ita ce maganar Yahweh da ta zo ga Yowel ɗan Fetuwel. 2 Ku ji wannan ku dattawa, ku kuma kasa kunne dukkan ku mazauna ƙasar. Ko wannan ya taɓa faruwa a kwanakinku ko a kwanakin iyayenku? 3 Ku faɗa wa 'ya'yanku labarinsa, 'ya'yanku kuma su fada wa tsara mai zuwa. 4 Abin da babe ya rage fara ta ci; abin da da fara ta bari burdunnuwa ta ci; abin da burdunnuwa ta rage; ganzari ya cinye. 5 Ku mashaya, ku tashi, ku yi ta kuka! Ku yi ta baƙin ciki, ku dukkan mashayan ruwan inabi, don an datse inabinku mai zaki daga gare ku. 6 Don wata al'umma ta zo kan ƙasata, ƙaƙƙarfa mara ƙidayuwa. Haƙoransu haƙoran zăki ne, kuma su na da haƙoran zãkanya. 7 Sun mayar da kuringar inabina abar wofi. Sun yayyage dangar itacen ɓaurena, sun yayyage dangar sun watsar; rassan sun koɗe sun yi fari. 8 Ku yi makoki kamar amaryar da ke makokin mutuwar angonta. 9 An dena miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Yahweh. Fristoci, bayin Yahweh su na makoki. 10 Filaye sun bushe, kasa tana makoki sabo da an hallakar da hatsi. Sabon ruwan inabi ya ƙare, mai ya kasa. 11 Ku manoma ku ji kunya, ku yi baƙinciki, hakan nan ku wuraren matse ruwan inabi, saboda alkama da sha'ir. Don abin da aka girbe ya lalace. 12 Inabi sun kaɗe, itatuwan ɓaure kuma sun bushe, itacen ruman, da kuma na dabino, da gawasa duk da sauran itatuwa sun bushe. Don farinciki ya ƙare daga cikin mutane 13 Ku firistoci ku sa tufafin makoki, ku firistoci ku yi bakin ciki, ku masu hidima a bagadi ku kwanta cikin tufafin makoki har safiya, ku bayin Allahna. Don an hana miƙa baikon hatsi da na abin sha daga gidan Allahnku. 14 Ku yi kira a yi azumi mai tsarki, ku kuma yi kira a yi tattaruwa mai tsarki. Ku tattara dattatawa da dukkan mazaunan ƙasar zuwa gidan Yahweh Allahnku, ku yi kuka ga Yahweh. 15 Kaito sadoda ranar! Gama ranar Yahweh ta ƙarato. Tare da ita akwai hallakarwa daga Mai iko dukka. 16 Ba a dauke abinci daga gabanmu ba, an kuma ɗauke farinciki da fara 'a daga gidan Allahnmu ba? 17 Iri ya lalace a kofensa, an wulaƙanta hatsi, an banzantar da wuraren ajiya don hatsi ya yanƙwane. 18 Yaya dabbobi ke nishi! Makiyayan dabbobi kuma ke shan wahala saboda ba wurin kiwo. Hakannan kuma garken tumaki na shan wahala. 19 Yahweh, ina kuka gare ka. Don wuta ta cinye makiyayar da ke jeji, harshen wuta kuma ya ƙone bishiyoyin da ke cikin filayen. 20 Har da dabbobin jeji suna yi maka kuka, don ƙoramun ruwa sun bushe, wuta kuma ta cinye makiyayar jeji.