Yosef ya sa aka nannaɗe Isra'ila da maganin hana ruɓewa.
Yosef yayi roƙo domin ya iya zuwa ƙasar Kan'ana don ya bizne mahaifinshi kamar yadda mahaifinsa ya sa shi ratsuwa.
Dukkan 'yan majalisar Fir'auna suka tafi tare da shi - dattawan gidansa, dukkan manyan masu gari da 'yan gidan Yosef da 'yan'uwansa, da gidan mahaifinsa, karusai da mahaya dawaki suka tafi tare da shi.
Kan'anawan sun ce wannan taro ne na baƙinciki sosai ga masarawa.
Bayan da Yosef ya bizne mahaifinsa, sai ya koma cikin ƙasar Masar, shi, tare da 'yan'uwansa.
'Yan'uwan Yosef sun damu cewa Yosef zai riƙe su da fushi gãba da su domin dukka muguntan da sun yi mashi.
'Yan'uwan sun roƙo Yosef ya gafarta masu laifin da suka yi akan Yosef.
Sa'addda suka zo wurin Yosef, 'yan'uwan Yosef sun rusuna a gabansa.
Yosef ya ce Allah ya yi niyyar alheri domin a adana rayuwar mutane da yawa.
Yosef ya yi rayuwa shekaru ɗari da goma.
Yosef ya ce yayi kusan mutuwa.
Yosef ya ce Allah zai zo wa mutanen ya kuma bida su hayewa daga wannan ƙasa zuwa ƙasar da ya rantse zai ba Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu.
Yosef ya sa su rantsuwa cewa zasu ɗauki ƙasusuwan Yosef daga Masar sa'adda sun bar Masar.
An nannaɗe jikin Yosef da maganin hana ruɓa kuma aka ajiye shi cikin akwati a Masar.