Allah ya ce wa Yakubu ya tafi Betel ya je ya gina masa bagadi.
Yakubu ya fada masu cewa su fitar da bãƙin alloli da ke a tsakaninsu, su tsarkake kansu, su kuma canza suturarsu.
Mutanen biranen dake kewaye dasu basu runtume su ba domin suna tsoron Allah.
Yakubu ya kira wurin da suka isa "Elbetel" domin wurin ne Allah ya bayyana kansa ga Yakubu a lokacin da yake gudu daga ɗan'uwansa.
Allah ya ba wa Yakubu sabon suna Isra'ila.
Allah ya tabbatar da alkawarin cewa Yakubu zai zama ƙungiyar ƙasashe kuma sarakuna zasu kasance cikin zuriyarsa, kuma ƙasar da ya yi alkawari ga Ibrahim da Ishaku, zai ba shi.
Rahila ta mutu a lokacin naƙudanta da Benyamin.
Isra'ila ya ji cewa Ruben ya kwana da Bilha ƙwarƙwarar sa.
Yakubu na da 'ya'ya maza sha biyu.
Ya'yansa maza daga Rahila sune Yosef da Benyamin.
Ishaku ya rayu shekaru ɗari da tamanin.
Esuwa da Yakubu, 'ya'yansa, suka bizne shi.