Genesis 26
Genesis 26:1
Don menene Ishaku ya tafi birnin Gerar inda Abimelek ne sarkin Filistiyawa?
Ishaku ya tafi birnin Gerar domin akwai yunwa a ƙasar.
Genesis 26:2
Menene Yahweh ya faɗa wa Ishaku kafin Ishaku ya tafi Gerar?
Yahweh ya faɗa wa Ishaku cewa kada ya je Masar kuma ya zauna a ƙasar da zai faɗa mashi.
Menene Yahweh ya faɗa wa Ishaku game da alkawarin da Yahweh yayi wa mahaifinsa Ibrahim?
Yahweh ya faɗa cewa zai cika alkawarin da yayi wa Ibrahim.
Genesis 26:4
Don menene Yahweh ya faɗa cewa zai yi wannan?
Yahweh ya faɗa cewa zai yi wannan domin Ibrahim ya yi biyayya da muryasa ya kuma kiyaye dokokinsa, da farillainsa, da ka'idodinsa.
Genesis 26:6
Menene Ishaku ya faɗa wa mutanen Gerar game da Rebeka, matarsa?
Ishaku ya faɗa wa mutanen Gerar cewa Rebeka 'yar'uwansa ce.
Genesis 26:9
Bisa ga Abimelek, menene na iya kawo laifi akan mutanen saboda karyan Ishaku?
Saboda karyan Ishaku, da wani ya kwana da Rebeka ya kuma jawo wa mutanen laifi.
Wane umarni ne Abimelek ya bayar game da Rebeka?
Abimelek ya umarta cewa za a kashe duk mutumin da ta taɓa Rebeka.
Genesis 26:15
Wane dalili ne Abimelek ya bayar don rokan Ishaku ya tafi ya bar Filistiyawa?
Abimelek ya roke Ishaku ya tafi daga Filistiyawa domin ya ce, "...gama ka fi mu ƙarfi.
Genesis 26:18
Don menene Ishaku ya haƙa rijiyoyin ruwa wanda an haƙa a lokacin Ibrahim?
Ishaku ya haƙa rijiyoyin ruwa wanda an haƙa a lokacin Ibrahim domin Filistiyawa sun ɓata su bayan mutuwar Ibrahim.
Genesis 26:21
Menene sunar da Ishaku ya sa wa rijiyan da har makiyayan Gerar basu yi faɗa da shi ba?
Ishaku ya sa wa rijiyan da har makiyayan Gerar basu yi faɗa da shi ba, Rehobot.
Genesis 26:23
Menene Yahweh ya jaddada wa Ishaku a lokacin da ya bayyana masa a Beyersheba?
Yahweh ya jaddada cewa zai albarkace Ishaku ya kuma ruɓanɓanya zuriyarsa.
Genesis 26:28
Menene alkawarin da Abimelek ya na so yayi da Ishaku, kuma don menene?
Abimelek ya so ya yi alkawarin cewa ba zasu cutar da juna ba domin ya gan cewa Yahweh ya na tare da Ishaku.
Genesis 26:30
Ya ya ne Ishaku ya amsa roƙon Abimelek don rantsuwar alkawari da juna?
Ishaku yayi biki, sai suka yi rantsuwar alkawari da juna.
Genesis 26:34
Matayen Isuwa suna daga wane kabila ne?
Matayen Isuwa 'yan Bahitte ne.
Yaya ne dangantakan sakanin matayen Isuwa, Ishaku da kuma Rebeka?
Matayen Isuwa sun kawo baƙinciki ga Ishaku da Rebeka.