Ibram ya kai shekaru tasa'in da tara a lokacin da Yahweh ya bayyana masa.
Yahweh ya umarce Ibrm ya yi tafiya a gabansa ya kuma zama da rashin laifi.
Yahweh ya canza sunar Ibram zuwa Ibrahim wanda ke nufin "uban al'ummai masu yawa."
Yahweh ya ba wa zuriyar Ibrahim dukka ƙasar Kan'ana domin ta zama ɗaya daga cikin alkawarin.
Ibrahim ya faɗa cewa zai zama Allah ga zuriyar Yahweh.
Yahweh ya umarta cewa ɗole a yi wa kowane na miji kaciya don ya zama alamar alkawari sakanin Ibrahim da Yahweh.
Ana yi wa yaro kaciya bayan kwana takwas.
An yi wa bãƙin da ke cikin iyalin da aka yi alkawari da Yahweh.
Duk wani namiji wanda ba shi da kaciya za a fitar da shi daga cikin mutanensa domin ya karya alkawarina.
Yahweh ya canza sunar Sarai zuwa Saratu.
Yahweh yayi alkawari cewa ɗan Ibrahim zai fito ta wurin Saratu.
Ibrahim yayi dariya ya kuma tambaya yadda za a haifa ɗa wa mutunen da sun tsufa.
Allah ya faɗa wa Ibrahim cewa ɗole ne sa wa ɗan suna Ishaku.
Allah ya ce zai kafa alkawarinsa da Ishaku.
Allah yayi alkawari cewa zai ruɓanɓaya Isma'ila ya kuma wadatar da shi sosai ya kuma maishe shi babban al'umma.
A wannan ranar, Ibrahim ya yi wa dukka mazajen gidansa kaciya.
Isma'ila yana da shekaru sha uku a lokacin da aka yi masa kaciya.