Yahweh ya ce wa Ibram kada ya ji tsoro kuma shine garkuwarsa da kuma babban ladansa.
Ibram ya damu domin ba shi da ɗa kuma ma'aikacin shi ne magajinsa.
Yahweh ya faɗa cewa wanda zai zo daga jikin Ibram ne zai zama magajinsa.
Yahweh ya faɗa cewa Ibram zai samu zuriya masu yawa kamar tauraru.
Ibram ya gaskanta Yahweh kuma Yahweh lisafta masa shi a kan adalci.
Ibram ya tambaye Yahweh cewa, "Ta yaya zan sani cewa zan gãje ta?"
Ibram ya datsa su biyu biyu ya kuma ajiye kowanne tsagi a gefen ɗayan.
Sa'adda rana na faɗuwa Ibram ya yi barci mai nauyi sai ga wani babban abin razana da kuma duhu sun lullluɓe shi.
Yahweh ya faɗa wa Ibram cewa za a bautar da zuriyarsa, a kuma tsananta musu har tsawon shekaru ɗari huɗu.
Yahwe ya ce zai hukunta wannan al'umma.
Yahweh ya ce Ibram zai mutu a cikin salama a shekara mai kyau.
laifofin Amoriyawa za ta kai matsayinsa kafin zuriyar Ibram su dawo.
Hayaƙin wuta da kuma harshen wutar tukunya da tartsatsi sun wuce a tsakanin yankin nama.
Yahweh yayi alkawari da Ibram cewa zai ba zuriyar shi wannan ƙasar.