Genesis 3
Genesis 3:1
Menene tambaya na farko da macijin ya tambayi macen?
Macijin ya tambayi macen, "da gaske ne Allah ya ce ba zaku taɓa ci daga kowanne 'ya'yan itacen da ke cikin lambun ba?"
Genesis 3:4
A loƙacin da matan ta ce Allah ya faɗa cewa za su mutu idan sun ci daga itacen tsakiyar lambun, menene macijin ya ce?
Macijin ya ce, "Hakika ba za ku mutu ba".
Menene macijin ya ce zai faru da mutumin da kuma matan idan sun ci daga 'ya'yan?
Macijin ya ce zasu zama kamar Allah, suna sanin nagarta da mugunta.
Menene ya rinjaye matan a 'ya'yan itacen?
Ta duba ta ga yana da kyau domin abinci, yana kuma ƙayatar da idanu, abin marmari ne ga sa hikima.
Wanene ya ci daga cikin 'ya'yan itacen?
Matan ta ci, ta kuma bada waɗansu ga mijinta wanda shi kuma ya ci.
Genesis 3:7
Menene ya faru da su a lokacin da suka ci 'ya'yan itacen?
Sa'adda suka ci, Idanun dukkan su su ka buɗe, sai suka gane tsirara suke.
Menene mutumin da macen suka yi a lokacin da Allah ya zo lambun?
Sun ɓoye kansu daga Allah.
Genesis 3:9
Don menene mutumin ya ɓoye kanshi daga Allah a lokacin da ya zo cikin lambun?
Mutumin ya ɓoye kanshi daga Allah domin tsirara yake kuma ya ji tsora.
Genesis 3:12
Wanene mutumin ya ce ke da alhakin ba shi 'ya'yan itacen?
Mutumin yace macen ne ke da alhakin.
Wanene macen ta ce ke da alhakin ba ta 'ya'yan itacen?
macen ta faɗa cewa macijin ke da alhakin.
Genesis 3:14
Wane irin zumunci ne Allah ya ce zai sa ya kasance tsakanin macijin da macen?
Allah ya ce zai sa su tsane juna.
Genesis 3:16
Wane la'ana ne Allah ya ba wa macen a lokacin haifuwa?
Allah ya ninka shan wuyarta sosai ahaifuwa.
Genesis 3:17
Wane la'ana ne Allah ya ba wa mutumin bisa ga aikinsa?
Allah ya la'anata ƙasan domin ta wurin aiki mai zafi mutumin zai ci daga cikinta.
Genesis 3:20
Wane suna ne mutumin ya ba wa macen, kuma don menene?
Mutumin ya kira macen Hauwa domin ita ce maifiyar dukkan rayayyu.
Menene Allah yayi wa Adamu da Hauwa, kuma don menene?
Allah yayi masu sutura ta fatu domin ya rufe su.
Genesis 3:22
Don menene Allah ya faɗa cewa kada Adamu ya ci daga itacen rai?
Allah ya ce tun da Adamu ya san mugunta da nagarta, kada ya ci daga itacen rai domin zai rayu har abada.
Menene Allah ya yi domin ya hana Adamu daga cin itacen rai?
Allah ya kori mutumin daga lambun, ya kuma sa kerubim domin suyi tsaron hanya ta zuwa itacen rai.