Allah ya hallici sammai da duniya.
Ruhun Allah yana kewaye saman fuskar ruwaye.
Allah ya ce, " haske ya kasance".
Allah ya yi tsakani ga ruwayen dake ƙarƙas.
Allah ya kira sandararriyar ƙasa "duniya," ruwayen da suka tattaru kuma ya kira su "Tekuna."
Allah yayi ciyayi da itatuwa masu fitar da iri a rana ta uku.
Zasu raba tsakanin haske da duhu, su kuma zama alamu na yanayi, domin ranaku da shekaru.
Allah yayi manyan haskoki guda biyu da taurari.
Allah ya hallici manyan hallittu na teku, da kuma tsuntsaye.
Ku ruɓanɓaya ku kuma hayayyafa.
Allah yayi mutum a cikin kammaninsa.
Allah ya ba wa mutum mulki akan kifaye na tekuna, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da kuma dukkan duniya, da dukkan abu mai rarrafe a bisa duniya.
Allah hallici mutum a cikin kammaninsa.
Ku hayayyafa ku kuma ruɓanɓanya, su cika duniya su kuma nome ta.
Allah ya basu kowanne tsiro da ke ba da iri da dukkan bishiyoyi dake da amfani.
Allah yayi tunani cewa yayi kyau.