Genesis 1

Genesis 1:1

Menene Allah ya hallita a rana ta farko?

Allah ya hallici sammai da duniya.

Menene Ruhun Allah yake yi a farko?

Ruhun Allah yana kewaye saman fuskar ruwaye.

Genesis 1:3

Ya ya ne Allah ya hallici haske?

Allah ya ce, " haske ya kasance".

Genesis 1:6

Menene Allah ya hallita a rana ta biyu?

Allah ya yi tsakani ga ruwayen dake ƙarƙas.

Genesis 1:9

Menene Allah ya kira sandararriyar ƙasa da ruwayen da suka tattaru?

Allah ya kira sandararriyar ƙasa "duniya," ruwayen da suka tattaru kuma ya kira su "Tekuna."

Genesis 1:11

Wane abu mai rai ne Allah yayi a rana ta uku?

Allah yayi ciyayi da itatuwa masu fitar da iri a rana ta uku.

Genesis 1:14

Menene amfanin haske a sararin?

Zasu raba tsakanin haske da duhu, su kuma zama alamu na yanayi, domin ranaku da shekaru.

Genesis 1:16

Menene Allah yayi a rana ta hudu?

Allah yayi manyan haskoki guda biyu da taurari.

Genesis 1:20

Menene Allah yayi a rana ta biyar?

Allah ya hallici manyan hallittu na teku, da kuma tsuntsaye.

Genesis 1:22

Wane umarne ne Allah ya ba wa hallittu na teku, da kuma tsuntsaye?

Ku ruɓanɓaya ku kuma hayayyafa.

Genesis 1:26

Menene Allah yayi a cikin kammaninsa?

Allah yayi mutum a cikin kammaninsa.

Bisa wane abubuwa ne aka ba wa mutum mulki?

Allah ya ba wa mutum mulki akan kifaye na tekuna, da tsuntsayen sararin sama, da dabbobi, da kuma dukkan duniya, da dukkan abu mai rarrafe a bisa duniya.

Menene yayi dabam game da yadda Allah ya yi mutum?

Allah hallici mutum a cikin kammaninsa.

Genesis 1:28

Wane murni ne Allah ya ba wa mutum?

Ku hayayyafa ku kuma ruɓanɓanya, su cika duniya su kuma nome ta.

Menene Allah ya ba wa mutum ya ci?

Allah ya basu kowanne tsiro da ke ba da iri da dukkan bishiyoyi dake da amfani.

Genesis 1:30

Sa'adda Allah ya gan komai da yayi, menene yayi tunani game da ita?

Allah yayi tunani cewa yayi kyau.